life story...
new update
Fitowata daga gida kenan sai a kirani a waya da wata baƙiwar nomber.
Bayan mun gaisa a yayin da na amsa kiran sai yace " Nima dai Uzee bari na baka labarin tawa soyayyar domin kaji yadda ta kasance a fagen tawa soyayyar.
___Baƙuntace ta kai ni jahar Adamawa gidan wani abokin mahaifina. Bari dai kuji yadda labarin ya samo asali.
Sati na ɗaya da kammala jarabawar fita daga matakin secondary sai mahaifiyata ta sanar dani cewar gobe zamu tafi Adamawa, saboda tsabar zumuɗi haɗe da yarinta a wannan ranar da maurna na kwana domin nasan a lokacin shekaruna ba wasu masu yawa bane.
Mahaifina ne ya jamu a motarshi domin jagorantar tafiyar, da isarmu Adamawa bayan naci abinci na ƙoshi sai ɗaya daga cikin yaran gidan mai suna Faruq ya jani waje domin yawatawa.
Bayan munyi yawanmu mungaji sai mu dawo gida mu zauna a ƙofar gida domin shan iska.
Jim kaɗan da zamanmu sai faruq ya tashi ya shiga wani gidan da yake kusa da nasu gidan, ganin hakane yasa nima nabi bayamshi, bansani ba ashe tsokanace ta kai shi gidan.
Da shigarshi sai ya fusge sweet daga hannun wata yarinyar da shekarunta basu yawaita ba yai waje da gudu.
Ganin yadda na saki baki ina kallan yarinyar ne yasa mahaifiyar yarinyar tayi dariya haɗe da cewa "lafiya kuwa?
Sai nace "ai naga ya ƙwace mata sweet ne ya gudu kuma ta kasa buɗa baki tayi magana kawai ta bishi da kallo.
Sai mahaifiyar yarinyar tace "to yazatai dashi dama kullun idan bai sata kuka ba bayajin ɗadi gashima har ta saba da abun da yake mata.
Nan take na ciro #100 daga aljihuna na bata haɗe da cewa "kije kisai wata kuma idan ya kwace miki ki fadamin.
A wannan lokacin ji nayi kamar kar na fito daga gidan saboda tun da nake a rayuwata ban taɓa sanin menene kyau ba sai a lokacin da nayi ido biyu da yarinyar da faruq ya kwace ma sweet.
Ga fuskarta cif-cif, hasken fatarta dai-dai musali, idanunta yan madaidaita gasu farare tas, haɓarta abar burgewa, kai da ganin gashin kanta kasan yarinyar ta musammance, gata ƴar ɗas da ita.
Bayan ta siyo sweet ɗin sai tazo ta zauna kusa dani haɗe da yima faruq gwalo.
Satinmu 1 a Adamawa amma duk da kasancewata mai makatsaitun shekaru hakan bai hana fadeela shiga zuciyata ba.
Bansani ba ashe nima nayi nisa a tata zuciyar kuma ban tashi gane hakan ba sai a lokacin da tafiyarmu tayi nisa.
Buƙatar son kasancewa a tare da fadeela ne yasa naƙi amince da batun komawata gida wanda hakan yasa na fake da cewar "ni kawai so nake naci gaba da kasancewa a tare da faruq.
Jin haka ne yasa mahaifin faruq ya shawarci mahaifina cewar, to indai haka ne me zai hana su barni na zauna a tare dasu in yaso sai naci gaba da karatu tare da faruq.
Allah cikin ikonsa sai mahaifina haɗe da mahaifiyata su amince da wannan buƙatar.
Bayan tafiyar iyayena sai naci gaba da ƙoƙartawa wajan sake neman kusanci da zuciyar fadeela.
Amma fa ako da yaushe a cikin kulawa nake tafiyar da dukkanin wani abun da yake faruwa a tsakanina da fadeela, saboda banason kowa yasan cewar akwai wata alaƙa a tsakanin zuciyata da fadeela.
Ita kuma fadeela tana bayyana dukkanin wani abun da ranta ya ƙudurta mata a gareni a fili saboda batasan meye So ba balle ayi batun ƙauna.
Sannu a hankali har fadeela ta riƙa aikata abubuwan da susa ake kallanta a matsayin wadda take matuƙar sona.
Idan mahaifin fadeela ko mahaifiyarta su kawo mata tsaraba ko irin abun burgewar nan da iyaye suke sai ma yaransu domin faranta ransu to nima akwai kasona a ciki komai ƙanƙantarshi bazata taɓa cinyewa duka ba har sai ta ajemin nawa.
A haka dai har mutanan unguwa su fara gano abun da yake a tsakanina da fadeela wanda hakan yasa wasu su fara kiran mu a matsayin masoya.
Ganin yadda fadeela bata nuna damuwarta a game da maganganun dake kai kawo a bakin wasu daga cikin mutanan unguwar ne yasa nima naƙi bayyana tawa damuwar.
Sannu a hankali har iyayan fadeela da iyayan faruq su gane cewar soyayyace take yawo a tsakanina da fadeela kuma duk a cikinsu ba wanda ya nemi taka mana burki ko haifar da damuwa a game da soyayyar da take shirin faruwa a tsakanina da fadeela.
Kwatsam rannan sai fadeela ta buƙaci na rakata zuwa gidan da wata yayarta take aure domin karɓo saƙo.
Bayan na rakata a yayin da muke kan hanyarmu ta dawowa gida sai nayi kuɓutar baki wajan furta kalamin da ya haifar da saɓani a tsakanina da fadeela.
Kawai kallanta nayi a cikin yanayi irin na rashin tsoro ko far gaba nace "fadeela wato mutane da dama suna furta cewar soyayyace a tsakanina dake, kuma duk wannan maganar da take yawo a game da batun cewar soyayyace a tsakanina dake ba maganace wadda zata gamsar da zukatan mu ba har sai lokacin da ɗaya daga cikinmu ya tunkari ɗaya da wannan kalmar ta soyayya sannan zukatanmu zasu samu gamsuwa dan haka fadeela ina sonki, shin dagaske kema kinasona kamar yadda sauran mutane suke kallanmu a matsayin masoya?
Nan take ta kwance robar FARO ɗin dake hannunta ta watsamin ruwan dake ciki a jikina sannan tayi gaba ta barni cikin mamaki.
Wannan abun da fadeela ta aikata a gareni ne yasa naji a raina cewar babu sauran wata soyayya a tsakanina da fadeela.
Sai da mu ɗauki kimanin sati biyu ba tare da wata magana ta sake shiga tsakanina da fadeela ba.
Kwatsam rannan sai fadeela ta aiko faruq da saƙo domin ya bani haƙuri a game da abun da ya faru a tsakanin mu.
Maganar gaskiya ina matuƙar son fadeela domin duk da irin abun da ya faru a tsakanina da ita to aduk lokacin da zan ganta ko naji muryar ta ba ƙaramin daɗi nakeji a zuciyata ba.
Sai dai kuma banajin cewar akwai sauran wani dalilin da zai sa na sake tunkarar fadeela da wata maganar da ta shafi soyayya balle har ayi batun aure.
Rannan ina kwance a falo sai fadeela ta shigo domin a lokacin babu kowa a falon cikin yanayin damuwa ta kalleni haɗe da cewa wajanka nazo.
Bayan mun fita waje domin jin abun da yake tafe da ita, cikin yanayin nadama tace "nazone domin na baka haƙuri a game da laifin da na aikatama.
Koda naji wannan furucin daga bakinta sai nace "nine ya kamata na baki haƙuri a game da furucin da na miki wanda hakan ya haifar da ɓacin rai a tattare da zuciyarki, domin nima sai daga baya nayi tunanin cewar bai kamata ace na tunkareki da wata kalmar da ta shafi soyayya ba.
Sai tace "saboda me kace haka?
Sai nace "kamata yai ace mun fara gina rayuwarmu a tafarkin da zamu iya hangen kanmu a matsayin cikakkun mutane domin bai kamata ace munyi gaggawar alaƙanta karatunmu da al'amarin da ya shafi soyayya ba saboda hakan zai iya shagaltar da zukatanmu wajan kasa maida hankali a ɓangaren da ya shafi karatun mu.
Sai tace "to yanzu meye mafita?
Sai nace "bamu da wata mafitar da ta wuce muyi haƙuri da juna na tsawon wani lokaci.
Sai tace "shikenan naji kuma na amince zan cire kai na a game da al'amuran da suka shafi rayuwarka, gaisuwa haɗe da sallamace kaɗai zasu rika shiga tsakanina da kai.
Kuma nayima alƙawarin bazan taɓa kula wani da sunan soyayya ba domin kai kaɗai ne zaɓina, kai ma zanso ka ɗaukar min alƙawarin kare kanka daga kula wata mace da sunan soyayya.
Nan take nima na ɗaukar mata alƙawarin kare kaina daga kula wata mace da sunan soyayya.
A ƙarshe sai tace "na baka dama idan ka kamani da tabbacin kula wani da sunan soyayya to ka zartar da duk wani hukuncin da kaga dama a gareni.
Jin haka ne yasa nima na bata damar zartar da duk wani hukuncin da taga dama idan har ta kamani da tabbacin kula wata mace da sunan soyayya.
Tun daga wannan lokacin sai alaƙata da fadeela taja baya ba abun da yake haɗamu idan ba gaisuwa ko sallama ba.
Lokaci ɗaya na daina ganin fadeela, sai daga baya na samu labarin cewa ai makaranta fadeela ta tafi.
Bayan mun samu hutun da bai wuce na sati biyu ba sai na tafi gida domin yin hutuna acan.
Kwana huɗu da komawata gida sai faruq ya kirani a waya da sassafe domin sanar dani cewar fadeela fa ta ɓace domin an nemeta an rasa.
Cikin ya nayin ruɗani nace "kamarya ta ɓace, to a makarantar ta ɓace ko a ina?
Sai yace "ai kwana biyu da tafiyarka gida itama ta dawa daga school, kuma a lokacin da na sanar da ita cewar kayi tafiya zuwa gida sai da naga kamar akwai damuwa a tattare da ita washe gari kuma sai a nemeta a rasa.
Rashin sanin halin da fadeela ke cikine yasa nayiwa mahaifina ƙaryar ana son ganin yan department ɗin mu a school wanda hakan yasa na samu damar komawa Adamawa ba tare da wani tsaiko ya shiga tsakanina da mahaifina ba.
Washe garin ranar dana koma Adamawa sai mahaifin fadeela yasa a kirani.
Da shigata gidan sai nayi arba da fadeela zaune, a gefe ɗaya kuma mahaifinta ne tare da mahaifiyarta.
Cikin yanayin girmamawa na gaishe dasu sannan na kalli fadeela ba tare da nace komai a gareta ba.
Buɗar bakin mahaifinta sai yace "na kiraka ne domin nayi wata muhimmiyar magana a tsakanina dakai saboda ni ba mutun ne mai neman tashin hankali ko neman rigima da wasu ba.
Sannan ya kalleni yace "nasan akwai soyayya a tsakaninka da fadeela kuma zanko ka dubi tsakaninka da Allah ka tuna zaka mutu ka koma ga mahaliccinka ka faɗamin gaskiya kuma gaskiyar da nakeson ji daga bakinka bazatasa na zageka ko nayi ƙararka zuwaga hukuma ba ni dai kawai abun da nasani shine duk wanda ya cuceni to na barshi da Allah domin shine mai sakayya a rana gobe ƙiyama, dan haka ka dubi girman Allah ka faɗamin gaskiya, shin a soyayyar ka da fadeela baka taɓa kasancewa tare da ita domin aikata Zina ba?
Saboda ta sanar damu cewar kai ne kayi mata cikin da take ɗauke dashi sannan kai ne ka gudu da ita zuwa garinku.
Cikin yanayin furgici nayi gaggawar ɗago kai na kalli mahaifinta sannan na kalli fadeela.
Fuskata cike da mamaki mai tattare da ruɗani nace "ko hannun fadeela ban taɓa riƙewa ba balle ayi batun afkuwar irin wannan ɗanyan aikin a tsakanin mu, amma tabbas inason fadeela fiye da yadda nakeson kai na.
Sannan na kalli fadeela haɗe da cewa shin da gaske nine wanda ya miki cikin da kike ɗauke dashi?
Tabbas nayi mamakin jin yadda ta iya buɗar baki tace "kwarai kaine kayi min cikin da nake ɗauke dashi.
Jin haka ne yasa na kalli mahaifinta haɗe da cewa "a matsayinka na mahaifin ƴar da take ɗauke da cikin da ake iƙirarin cewar ni nayi matashi wane taimako kake buƙata a gareni.
1 bazan iya bayar da goyan bayan kashe ɗan da ke cikin mahaifiyarsa ba domin aikata hakan wani babban laifi ne a wajan mahaliccinmu.
2 zan iya bayar da kuɗi domin a kaita waje mai nisa kuma a bata duk wata kulawar da take buƙata har zuwa lokacin da zata haihu, kuma bayan ta haihu nayi alkawarin karɓar ɗan da ta haifa a matsayin ɗana sannan kuma bazan taɓa bayyana ma kowa cewar fadeela ce wadda ta haifamin ɗan zina ba.
3 idan kun amince kuma kun bani dama a tsakanin yau ko gobe fadeela zata iya kasan cewa a matsayin matata.
Sannan na kalli mahaifinta nace "zan iya ɗaukar zabi na 2 da na 3 domin kar mutuncinku haɗe da na fadeela ya zube a idan mutan da suke ganin girman ku saboda har kawo yanzu akwai son fadeela a tattare da zuciyata, amma gaskiyar magana bani da wata alaƙa a game da cikin da take ɗauke dashi.
Jin haka ne yasa mahaifinta ya ɗauke ta da mari haɗe da cewa "muddun baki sanar dani haƙiƙanin wanda ya miki cikin da kike ɗauke dashi ba to wallahi bazaki sake kwana a raye ba domin kasheki zanyi.
Buɗar bakina sai nace "kayi haƙuri Abba saboda duka ko wata barazana bazasu iya kawo ƙarshen wannan matsalar ba sai dai su ƙara dagula al'amurin kuma hakan zai iya sawa kowa ya fahimci halin da ake ciki domin zaɓukan da na bakune kaɗai zasu iya rufa asirin bayyanuwar wannan sirrin a iya nan duniya.
Jin haka ne yasa mahaifin fadeela ya bani damar auran fadeela.
Tun daga wannan lokacin sai na shiga taraddadin ƙalubalan da zan fuskanta a wajan mahaifina saboda shekaruna basuyi irin nisan da ya kamata ace nayi gaggawar yin aure ba.
Wannan tunanin da nayi ne yasa na samu mahaifin fadeela domin shirya hanyar da zata bamu damar cimma nasarar ganin aurena da fadeela ya samu yiwuwa ba tare da wata babbar matsala ta gifta a tsakanina da mahaifina ba.
Bayan na gama tsara duk wasu hanyoyin dasu dace abi sai mahaifin fadeela ya tunkari mahaifin faruq domin yi mai magana a game da soyayyar da take a tsakanina da fadeela.
Bayan sun gaisa sai yace da mahaifin faruq "wato nazo garekane domin yin wata muhimmiyar magana a game da soyayyar da take a tsakanin yaron da yake zaune a gidanka da fadeela, saboda nima ban ɗauka cewar soyayyar da take a tsakaninsu tayi nisa sosai ba a taƙaice dai yau kwana biyar kenan da dawowar fadeela daga school, bayan ta dawo sai take sanar da mahaifiyarta cewar itafa bazata koma makaranta ba aure kawai take so.
Jin haka ne yasa nayi ƙoƙarin yi mata nasiha, nace "kinga ba kiyi irin girman da ya kamata ace munyi gaggawar yi miki aure ba dan haka kiyi haƙuri idan kin kammala karatun da kikeyi sai ayi miki auran.
To akan wannan maganar ne fadeela ta bar gida ta tafi can wajan yayana ta barmu anan muna nemanta.
A halin da ake ciki yanzu yayana ya matsanta akan lallai sai nayi mata Aure kamar yadda ta buƙaci hakan.
Bayan na nemi jin ta bakinta a game da wanda takeso sai ta sanar dani cewar yaron da yake zaune a gidanka shi takeso wato abokin faruq kenan wannan ne dalilin da yasa kaga na tunkareka da wannan maganar domin wallahi tun da abun yazo da haka bazan bari ta haura sati biyu a gidana ba tare da na aurar da ita ga koma waye ba.
Koda mahaifin faruq yaji haka sai ya tuntunɓi mahaifina a waya domin jin ta bakinshi a yayin da mahaifina yaji haka sai ya nemi ƙin amincewa.
Ganin haka ne yasa mahaifin faruq yai ƙoƙarin shawo kan mahaifina haɗe da sanar dashi cewar "shi aure da kuma mutuwa abune waɗan da suke zuwa lokaci ɗaya dan haka idanma tunani kake a game da karatunshi ka dai na saboda yin aure bazai hanashi cigaba da karatu ba kawai tun da suna son junansu kuma yarinyar tana da asali mai kyau kuma gata ƙyaƙyawa kawai ka bayar da goyan baya wajan haɗa sunnar ma'aiki.
Bansani ba ashe duk wannan matsalar da fadeela ta nemi haifarwa a game da rayuwata ya samo asali ne a dalilin ƙanwata ZAINAB.
Bayan anyi aurena da fadeela sai nayi bankwana da Adamawa haka na tare da amaryata a gida ɗaya da iyayena.
A ranar da fadeela tayi ido biyu da ƙanwata Zainab to a ranar ne gaskiya ta bayyana a game da batun cikin da fadeela take ɗauke dashi.
Ji nayi fadeela ta fashe da kuka sannan ta riƙe hannuna haɗe da cewa dan Allah kayi haƙuri wallahi ƙarya nayi a game da batun cikin da nace kai ne wanda kayi min shi.
Cikin yanayin furgici na kalli mahaifina haɗe da mahaifiyata sannan na kalli fadeela nace "wai wane irin shirme kike aikatawa haka?
Na buɗa baki zanyi magana sai mahaifina ya dakatar dani sannan ya kalli fadeela yace "ke me yake faruwa a game da batun cikin da naji kinyi magana a tattare da ke?
Bayan ta share hawayen dake fuskarta sai tace da mahaifina "Alƙawari mu ɗaukar ma junanmu akan cewar zamu dai na soyayya har zuwa lokacin da zamu kammala karatu.
Bayan mun samu hutu na dawo gida da muradin son ganin Habeeb sai faruq ya sanar dani cewar Habeeb ya koma gida, ni kuma a lokacin bani da wani burin da ya wuce son ganin Habeeb wanda hakan yasa tun daga Adamawa nazo har nan garin ba tare da sanin kowa ba domin ko iyayena a lokacin basu da masaniyar bari na gida.
Bankaiga ƙarasowa nan ba sai na hangi Habeeb tare da wannan ƙanwar tashi suna gudanar da harkokinsu kamar wasu masoyan da suyi matuƙar shaƙuwa da juna.
Jin haushin haka ne yasa na yanke shawarar komawa gida domin sanar da iyayena cewar "cikin Habeeb nake ɗauke dashi, badan komai ba sai dan buƙatar ɓata sunan Habeeb wanda hakan zai sa iyayen wadda na ganshi a tare da ita su kawo ƙarshen soyayyar da take a tsakaninsu.
Duk da cewar ya nemi kare kanshi a game da batun cikin dana furta cewar ina ɗauke dashi hakan bai hana shi ƙoƙarin kare mutuncin iyayena ba domin duk shine wanda ya tsara hanyar da za'abi wajan ganin ya aureni ba tare da kowa ya fahimci halin da ake ciki ba hatta mahaifin faruq bashi da masaniyar komai a game da abun da ya faru.
Bansani ba ashe tsananin kishine yajani zuwaga kallan ƙanwar Habeeb a matsayin wadda yake soyayya da ita.
Bayan ta gama wannan jawabin sai nace "to amma ya ai har ki iya gane cewar anan nake da zama saboda ban taɓa sanar dake address ɗina ba.
Sai tace "a ɗaya daga cikin ID Card ɗin da kake tattare dasu na san cikakken inda kake da zama, amma dan Allah kayi haƙuri a game da laifukan da nake aikatawa a gareka, kuma zanso kaci gaba da haƙuri dani saboda ni yarinyace zata iya yiwuwa ƙuruciyar da nake tattare da ita tasa na riƙa aikata kurakurai a game da zamana da kai.
Wannan jawabin da tayine yasa naga mahaifina ya saki ranashi daga ɗaure fuskarshi ɗin da naga yayi.
Haka dai naci gaba da kasancewa a tare da fadeela cikin jin daɗi da walwala har Allah ya albarkacemu da samun haihuwar ƴa mace, daga ƙarshe suma iyayen fadeela susan gaskiyar cewar fadeela bata ɗauke da ciki kafin muyi aure kawai ta shirya haka ne saboda tsananin kishi.
THE END