new update
=> 1
Cewa yayi wannan wani labari ne da ya shafi rayuwata. da farko dai sunana Usman kuma haifaffen garin Gombe.
Haƙiƙa kowa ne ɗan adam baza'a rasashi da wani muhimmin muradin da yake tattare dashi a zuciyarsa ba.
To amma ni kuma ahalin da nake ciki yanzu bani da wani muhimmin muradin da ya wuce naga ƙanwata ta samu lafiya.
haka kuma kowa ne ɗan adam baza'a rasashi da muhimmin abun da yake sashi a ɓacin rai ba.
Ni kuma a ɓangaran rayuwata mahaifina shine sular kasancewata a baƙin cikin da nake ciki wanda hakan yasa nake jin cewar ba wanda na tsana fiye da mahaifina. lokaci ɗaya mahaifina ya rikita gidanmu ta hanyar ƙara aure.
Duk da cewar ba'a gida ɗaya mahaifin nawa ya haɗa mahaifiyata da wadda ya ƙara aurowa ba hakan bai hana afkuwar matsala a garemu ba.
Kafin mahaifiyata ta tsunci kanta a wani baƙon yanayi banajin cewar akwai wata damuwar da zata iyasa ɗan adam zubar da hawaye sai dai idan shi yaso faruwar hakan a gareshi.
Domin a lokutan da su shuɗe na rayuwar ban ɗauka cewar mahaifiya tana da wani babban matsayi a zuciyar ɗan da ta haifa ba, sai a lokacin da naga hawaye ya zubo daga idanun mahaifiyata sannan na fahimci cewar ba'akan dai-dai nake tafiyar da tsarin rayuwata ba.
A tsarin rayuwata dukkanin wani nau'in abincin da za'asashi a tukunya domin sarrafashi ta hanyar dafawa to ba yadda za'ai nacishi muddun ba mahaifiyatace ta dafashi ba domin kallanshi nake amatsayin ƙazanta.
Duk da cewar nine ɗan fari a wajan mahaifiyata hakan baya taɓa hana mahaifiyata tsokanata ta hanyar cewa "Zainab zata auramin wanda hakan yasa zainab take yawan bayyana zumuɗinta a gareni domin tana matuƙar jin daɗi a duk lokacin da taji mahaifiyata tayi wannan furucin.
Ni kuma bana taɓa iya buɗa baki domin cewa komai a game da mahaifiyar yawa ko ita Zainab ɗin saboda nasan hakan ba abune mai yiwuwa ba.
Kafin na fahimci wani al'amari ina yawan samun saɓani da ƙanwata Maryam wanda hakan yasa idan ta ɓatamin rai tofa bana taɓa haƙura har sai nayi mata shegen duka.
Mahaifiyarmu ce kaɗai take shiga tsakaninmu a duk lokacin da wani akasi ya shiga tsakanina da Maryam nadan komai ba sai dan buƙatar ganin mun haɗa kanmu.
Amma gaba ɗaya sai mu kasa fahimtar amfanin haɗa kan namu da mahaifiyata take ƙoƙarin yi a garemu.
Abun yana matuƙar ɗauremin kai musamman idan muna faɗa haka mahaifina zai zuba mana ido ba tare da yace komai a garemu ba.
Haka ƙanwata Maryam ta kasa haƙurin daina ɓatamin rai nima kuma na kasa haƙurin kauda kai na a game da abun da take yawan aikatamin wanda hakan yasa ako da yaushe nake yawan dukanta.
kwatsam rannan sai wani babban saɓani ya sake shiga tsakanin mahaifina da mahaifiyata haɗe dani karan kai na, duk a dalilin Maryam.
Matsalar ta faru ne a ranar wata alhamis lokacin ni da maryam mun tafi school kafin lokacin dawowarmu gida yayi sai maryam taji zazzaɓi yana neman hanata sakewa wanda hakan yasa ta farajin matsanancin sanyi yana neman takura mata.
Cikin gaggawa ta fito daga school ba tare da ta sanar da malaman makarantar ba saboda ko kaɗan batason allura. da fitowarta sai ta tsaida wani ɗan acaba domin ya kaita gida.
A yayin da ta isa gida bayan tasha magani sai ta kwanta a falo har bacci ya ɗauketa.
Koda mahaifiyarmu ta dawo gida sai ta samu Maryam kwance a falo.
Cikin yanayin mamaki mahaifiyar tamu ta tashi Maryam daga baccin da takeyi haɗe da cewa" lafiya kuwa naganki kwance a gida domin na tabbata lokacin tasowarku daga school baiyi ba?
Budɗar bakin maryam sai tace "umma bani da lafiya ne.
Jin haka ne yasa mahaifiyar tamu tace "Ayya! to sannu amma kinsha magani kuwa?
Sai Maryam tayi murmushi haɗe da cewa "eh nasha umma.
Buɗar bakin mahaifiyarmu sai tace "to ke da baki da lafiya meye kuma na murmushi haka?
Sai maryam tace "umma saboda kinasona.
Zuwa can da daddare bayan maryam ta samu lafiya, domin ko nima kaina bansan da cewar tayi zazzaɓi a wannan ranar ba.
A yayin da muke tsaka da cin abinci sai maryam tace "au abba namanta ban sanar da kaiba, dama ɗazu ne da naje school sai naji zazzaɓi yana neman hanani sakewa shine na fito daga school na tsaida wani ɗan acaba domin ya kawoni gida, sai bayan ya kawoni sai na tuna ashe umma bata gida kuma gashi ba kuɗin da zan sallami ɗan acaɓan da ya kawoni a wajena ganin haka ne yasa nashiga ɗakinka domin dubawa ko zan samu ƴan kuɗin da zan sallameshi, sai kuma Allah yasa ban samu wasu kuɗi ba sai wata dubu ɗayar da na gani a bed site ɗin dake gadonka.
Bayan naba ɗan acaɓan da ya kawoni haƙƙinsa sai na mayarma da sauran canjin a inda na ɗauki kuɗin.
___A wannan lokacin ne al'amarin mahaifina yai matuƙar bani mamaki domin bani kai na ba hatta ita kanta mahaifiyar tamu sai da ta tsorata a yayin da mahaifina ya ɗauke Maryam da mari.
Cikin yanayin mamaki mai tattare da ruɗani na kalli mahaifin namu a fusace haɗe da cewa "Abba marintafa kayi!
Buɗar bakinshi sai yace "to ai da ace kai ne kayi kuskuran taɓamin kuɗi ba tare da ka sanar dani ba to ina mai tabbatarma cewar da abun da zanyima sai yafi haka.
Cikin yanayin takaici na kalleshi haɗe da cewa "kace kawai kasheni zakayi?
Wani mugun kallo naga yamin haɗe da cewa "bazan kasheka ba, amma sai ka gwammaci mutuwa fiye da abun da zan zartar a gareka.
Wallahi bansan lokacin da zuciya ta ingizani wajan watsar da dukkanin abincin da yake saman Table ɗin dake gabanmu ba.
Ganin haka ne yasa mahaifiyata ta tsunkeni da mari sannan ta shiga ɗaki tana kuka.
Tun daga wannan ranar gaba ɗaya mahaifina ya ɗauke kanshi a garemu, haka ya daina bamu kulawar ɗaya saba bamu.
Idan har kaga munci ko munsha to mahaifiyarmuce tayi fafitikar nema mana abun da zamusa a bakinmu hatta makarantar da muke zuwa mahaifiyar tamuce taci gaba da ɗaukar nauyin biya mana dukkanin wasu kuɗaɗan da makarantar take buƙata.
Duk da cewar tun daga wannan lokacin mahaifina ya daina ɗaukar ko sisin kobo domin yaba mahaifiyata a matsayin kuɗin cefane hakan baisa ta dai na ajemai abinci ba domin kullun ne dan ta dafa abinci sai ta ajemai, to amma sai dai a yadda ta aje abincin haka zata sameshi domin bayaci..
Ganin haka ne yasa na tunkari mahaifina domin bashi haƙuri a game da laifin da nake tunanin mun aikatamai.
Haka nayimai sallama a yayin dana shiga ɗakinshi amma sai yai banza dani, duk da hakan dai ban nuna ƙosawata ba haka na durƙusa har ƙasa idanuna suna zubda hawaye nace "dan Allah abba kayi haƙuri a game da laifin damu aikatama. aƙalla sai ds na ɗauki tsawon 30 minute inawa mahaifina magana ba tare da ya saurareni ba.
Wallahi ban taɓa tunanin mahaifina ya kai maƙura a fagen zalinci ba sai a lokacin da naga mahaifiyata ta dawo gida fuskarta cike da hawaye.
A yayin dana nemi sanin dalilin zubar da hawayenta sai ta sanar dani cewar "mahaifina ne yasa a koreta daga asibitin da take aiki.
Cikin yanayin kuka mai tattare da ɓacin rai nace "amma gaskiya umma abba azzalumi ne. kuma zanso ki yafe mana saboda ni da ƙanwata ne muka sular faruwar wannan akasin.
Girgiza kai naga tayi haɗe da cewa "ko kaɗan baku da laifi kudai kawai kuci gaba da addu'a sannan ta shige ɗaki.
A ƙalla nafi tsawon 1 hour zaune a falo ba tare da sanin inda hankalina yake ba domin a wannan zaman da nayi ba abun da nake tunani illah irin ƙangin rayuwar da zamu shiga a dalilin raba mahaifiyata da aikin da takeyi.
Haka na riƙa tambayar kai na da kai na ta hanyar cewa "yanzu ya zamuyi a game da harkar karatunmu uwa-uba kuma abun da zamu riƙaci ako wace rana domin mahaifina ba mutun ne mai imani ba.
Gashi kuma ban saba da aikin wahalaba balle na riƙa fita domin nemo abun da zai riƙa kawar mana da yunwar da zata riƙa bijiro mana.
A ƙarshe dai haka na cire duk wata kunyar duniya haɗe da kawar da duk wani son jikina na tunkari gidan Malan Isah domin karɓar hayar kurar ruwan dazan riƙa turawa domin siyar da ruwa badan komai ba sai dan buƙatar kare ƙimar ƙanwata haɗe da mahaifiyata.
Ganin haka ne yasa mahaifiyata ta tattala ƴan kuɗaɗanta domin siyamin sabuwar kurar ruwan da zan riƙa nemo mana abun da zamuci.
Duk da haka dai bamu tsira ba, haka mahaifin nawa yasa a kamani ta hanyar tuhumata da laifin satarmai kuɗin da na sayi ƙurar ruwan da nake turawa sannan yasa a kwace kurar da nake Fafitikar nema mana abun da zamuci sai da a tsareni har tsawon wata ɗaya ba tare da'an barni naga koda mahaifiyata ba.
Kafin a sakeni sai wani gurɓataccen al'amari ya faru da ƙanwata Maryam amma sai mahaifiyata ta kasa sanar dani domin ba wanda yasan abun da ya faru da Maryam.
Haka mahaifiyata taita ɓoye wannan sirrin da bai kamata ace ta ɓoyeshi a gareni ba.
Bayan na fito daga tsarewar da mahaifina yasa amin a yayin da na nemi jin yadda rayuwarsu ta kasance a lokacin da mahaifina yasa a tsareni sai mahaifiyar tawa take sanar dani cewar "Ai zainab ce ta riƙa kawo masu abinci haɗe da ƴan kuɗaɗan da zasu riƙa magan ce ƴan ƙananun buƙatunsu.
A yayin da muke cikin wannan labarin sai ga Zainab ta shigo.
Cikin yanayin bayyana jin daɗi nayi mata godiya kamar yadda addinin musulunci ya tanadar mana sannan na kalleta haɗe da cewa "Zainab gashi ni ba wani Jarumi ba ne a gareki amma ako da yaushe kina ƙoƙarin faranta rai na.
Cikin yanayin kunya tayi murmushi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa haɗe da cewa "to ai tun damacan kai jarumi ne a gareni kuma ai dukkanin wata kyautatawar da zanyima Umma bawai dan kai nakeyi ba domin inayi ne sabods Umma haɗe da Maryam..
Cikin yanayin Raha nace "ah to tunda abun haka ne shikenan.
Haka Zainab taci gaba da kyautata mana wanda har hakan yasa nariƙa jin wani irin yanayi a zuciyata, yanayin da nima kaina na kasa gane ma'anar hakan.
Cikin wasu ƴan kwanaki sai ƙanwata Maryam takamu da wata irin matsananciyar rashin lafiya wanda har hakan ya kaita ga yawan afkuwa a dogon suma.
Ganin haka ne yasa muyi gaggawar kaita asibiti.
A yayin da na sanar da mahaifina halin da ƙanwata Maryam take ciki, sai naga yamin wani mugun kallo ba tare da yace komai a gareniba.
Cikin yanayin ɓacin rai nayi wani ɗan murmushi haɗe da cewa "anya kuwa kai mahaifinmu ne kuwa? Saboda naga alamun ba marabarka da baƙin mugu.
Ganin yadda yaƙi kulani ne yasa nace "dan Allah idan bazaka damu ba ko zaka iya sanar dani dalilin da yasa kake Muzguna mana?
Nunani naga yayi da yatsanshi haɗe da ƙyasta yatsanshi sannan yimin nuni da ƙofar da na shigo, wai nufinshi na fita na bashi waje.
Inaji ina gani haka mahaifiyata ta siyar da gidanta domin nemawa ƙanwata lafiya.
Haka mahaifiyata ta kashe kuɗaɗe masu yawa ba tare da an shawo kan wannan rashin lafiyar da ƙanwata take fama da ita ba wanda a ƙarshe muga ne cewar ba wata rashin lafiya bace take damun Maryam illah ciwon daji.
Duk da haka dai mahaifiyarmu bata nuna gajiyawarta ba har sai da ta kai Maryam ƙasar gana domin nema mata lafiya.
Sai kuma ayi rashin sa'a domin larurar da take damun Maryam tana buƙatar kuɗaɗe masu yawa kuma gashi mahaifiyata bata da hanyar da zata samu waɗan nan kuɗaɗan ba yadda ta iya haka ta dawo da ƙanwata ba tare da'an samu nasarar shawokan rashin lafiyar dake damunta ba, kuma gashi dangin mahaifiyar tawa basu da ƙarfin da zasu iya tallafa mana.
Haka cikin dare na kasa kwance na kasa zaune wanda hakan yasa na fito daga ɗakina na shiga ɗakin mahaifiyata domin neman shawararta. da shigata ɗakin mahaifiyar tawa sai na tarad da ita cikin halin tsaka mai wuya.
Cikin gaggawa naje gareta ina mai cewa "umma! umma!...
Hannuna naji ta riƙe cikin ƙarfin hali muryarta tana rawa tace "dan Allah ka kula da rayuwarka haɗe da ta ƙanwarka domin akwai wani sirrin da nakeson sanar da kai badan komai ba sai dan buƙatar ka ɗaukarwa ƙanwarka Maryam fansar cin zarafin da ayi mata.
Tun kafin naji wannan sirrin tuni hawaye ya gama jiƙemin riga. sannan tace "amma kafin na sanar da kai wannan sirrin zanso ka ɗaukarmin alƙawarin bazaka taɓa barin Zainab a halin damuwa ba domin so nake ka aureta saboda na lura da cewar tana matsanancin sonka domin banajin cewar zan iya cigaba da rayuwa.
Cikin yanayin kuka nace "dan Allah ki dai na furta irin wannan maganar domin bazaki mutuba har sai kinga aurena dana Maryam.
Aiko tana gama faɗamin sirrin da take ɓoyemin wanda ya samo asali tun daga lokacin da mahaifina yasa a tsareni na tawon wata ɗaya sai mahaifiyar tawa tayi bankwana da duniya.
Tun a ranar da ayi jana'idar mahaifiyata na fara nazarin hanyar da zanbi domin nemawa Maryam lafiya haɗe da ƙudirin ɗaukar mata fansar abun da'a aikata mata.
=>2
A wasu lokutan idan kaga maryam sai kayi tunanin ba wani abun da yake damunta balle har kayi tunanin akwai wata larura a tattare da ita, saboda rashin lafiyar bawai tayi irin matsanta mata ɗin nan bane domin sai lokaci-lokaci ciwan yake taso mata.
To amma sai dai kuma a duk lokacin da ciwan zai taso mata kawai sai kaji gwarama ta mutu ta huta saboda wahalar ta kai wahala. kafin mahaifiyata ta rasu a duk lokacin da wannan rashin lafiyar zata tasowa maryam tofa ba yadda za'ai na iya zama a gida balle har na iya kai idona zuwaga maryam, batun zubar da hawaye kuma ba'a magana domin al'amarin yana matuƙar damuna.
bayan mahaifiyar tamu ta rasu sai nafara tunanin yadda zata kasance a tsakanina da ƙanwata maryam musamman idan ace larurar da ke damunta ta taso mata saboda ko kaɗan banason ganin irin wahalar da takesha.
lokaci lokaci nakanyi fira da zainab a ƙofar gidansu ko kuma na kirata a waya domin mugaisa badan komai ba sai dan buƙatar cikawa mahaifiyata burinta na son ganin na auri zainab saboda tun daga lokacin da mahaifiyata ta rasu sai zainab ta ɗaga ƙafa daga zuwa gidanmu, kuma ko kaɗan banga laifinta ba saboda al'umma zasu iya zarginmu kuma hakan zai iya zamewa rayuwarmu matsala.
To amma duk da haka zainab bata fasa kyautata mana ba domin ako wace rana takan bamu ƴan kuɗaɗan da zamu riƙa amfani dasu wajan kawar da yunwar da zata rika addabarmu.
Sai dai kuma abun da yake ɗauremin kai shine "rashin sanin inda zainab take samun kuɗaɗan da take bamu saboda nasan ba yadda za'ai iyayanta suriƙa bata irin waɗan nan kuɗaɗan.
Duk da cewar nasan mahaifin zainab mutun ne mai tsats-tsauran ra'ayi hakan bai taɓa sawa naji cewar akwai wani mutumin da ya isa ya rabani da zainab ba saboda nasan tana ciwon sona.
Kwatsam rannan da misalin ƙarfe 10:00 na dare a yayin da nake zaune a falo ina fira da zainab a waya, sai naga maryam ta fito daga ɗaki sannan ta yanke jiki ta faɗi kasa.
Cikin yanayin kiɗimewa nace "subhanallahi!! bansan lokacin da na saki wayar da nake rike da ita ba.
Haka na miƙe tsaye a tsorace nanfa kaina ya ɗau zafi ga maryam kwance a ƙasa cikin mawuyacin hali gashi kuma bansan hanyar da zanbi domin ceton rayuwarta ba. koda naga yanayin nunfashinta yana ƙara raguwa cikin ƙanƙanin lokaci na sake dimaucewa.
Dubawar da zanyi sai naga wayata tana ringin....
Koda naga sunan zainab cikin gaggawa na amsa kiran. cikin yanayin rikicewa nace "zainab, maryam zata mutu.
Buɗar bakin zainab sai tace "kaga ka kwantar da hankalin ka yi sauri kazo ka buɗemin ƙofa.
Nan take na fita a guje domin buɗe mata ƙofa.
Da shigowarta cikin hanzari ta cire shijab ɗin da ke jikinta sannan ta tsumbulashi a wani ruwa mai sanyi sannan ta lullube jikin maryam da shijab ɗin.
Cikin wasu ƴan mintina naga numfashin maryam ya fara dawowa sannan idanuntama su fara dawowa hayyacinsu domin kafin zuwan zainab idanun nata duk sun juye sun koma farare Tas ba alamar wani baki a tattare dasu.
Cikin yanayin mamaki na kalli zainab haɗe da cewa "zainab INA SON KI shin zaki amince ki aureni?
Murmushi naga tayi hade da cewa "A'a har sai ka kwatowa maryam yancinta a wajan muta ne ukkun da kasan sunyi wasa da rayuwarta.
Buɗar bakina sai nace "A'a mutane huɗu dai domin hada mahaifina a ciki.
Koda ta kalleni sai tace "tsakaninka da mahaifinka wannan rigimace ta cikin gida su kuma waɗancan ukkun tsakaninka dasu rigimace ta waje.
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai nace "zainab na ɗaukar miki alƙawarin ba yadda za'ai nabar duk wani mai hannu wajan tozarta rayuwar ƙanwata a raye.
Wani kalar kallo naga tamin haɗe da cewa "amma sanin kanka ne kashe rayuwar ɗan adam da sunan ɗaukar fansa abune da addinin musulunci yai hani dashi saboda ko wane laifi akwai hukuncin da yai dai-dai dashi, dan haka shawarar da zan baka itace "kayi ƙararsu zuwa kotu.
Sannan ta ƙara da cewa amma kabari zuwa safiya zamu tattauna a game da wannan maganar.
Bayan maryam taɗan samu sauƙi ayayin damu mai data ɗaki sai zainab tasa ɗaya daga cikin hijab ɗin da maryam take amfani dashi sakamakon nata ajiƙe yake.
Fitowarmu daga ɗakin kenan a yayin da zainab take gyara shijab ɗin da tasa domin wucewa gida sai muyi arba da jami'an ƴan sandan farin kaya a falon gidan namu. nanfa mu fara yima junanmu kallan kallo na kalli zainab itama ta kalleni sannan mu karkata idanunmu zuwaga jami'an tsaron.
Buɗar bakin ɗaya daga cikin jami'an tsaron sai yace "meye amfanin soyayyar da ake aikata zina a cikinta.
Na buɗa baki zanyi magana sai zainab ta dakatar dani sannan ta kallesu haɗe da cewa "haƙiƙa na fahimci duk abun da kuke nufi, to amma sai dai zarginku a garemu ba haka yakeba domin mu ba mazinata bane a taƙaicema ko hannun junanmu bamu taɓa riƙewa da sunan iskanci ba.
Buɗar bakin ɗayan ɗan sandan sai yace "ke dalla gafaracan karki raina mana hankali, a gabanmufa ki fito daga ɗaki tare da wannan ƙatan banzan kina gyara hijab, shine har zaki iya kallan tsabar idanmu kice wai ko riƙe hannun junanku baku taɓa yiba.
To idanma haka ne me yakaiku cikin ɗaki alhalin gidan ba kowa dagake sai shi kuma a irin wannan lokacin.
Ban tashi auneba sai ji nayi ta tsunkeshi da mari sannan ta nunashi da yatsa haɗe da cewa karka sake alaƙanta wanda nakeso da kalmar da ta danganci ɓatanci.
A kan wannan maganar har kotu mu halarta wanda a ƙarshe mu samu nasarar rabasu da aikinsu.
Sai daga baya na gani cewar ashe mahaifina ne ya kira jami'an ƴan sandan dasu nemi ɗora mana sharri domin ban sani ba ashe a lokacin da wannan ciwon ya tasoma ƙanwar tawa mahaifin namu yana ɗakinshi.
A yayin da zainab ta shigo gidan namu domin taimaka min wajan ceto rayuwar ƙanwar tawa ne sai mahaifina yai amfani da wannan damar wajan kiran jami'an ƴan sanda.
Tun daga wannan ranar gaba ɗaya sai mahaifin Zainab ya shiga tsakanina da Zainab ta hanyar sanar da ita cewar kar ya sake ganinta a tare dani haɗe da ƙanwata, a ƙarshe kuma ya sanar da ita cewar muddun ya samu labarin ta sake shiga gidanmu to sai ranta yayi mugun ɓaci sannan ya gargaɗeni akan cewar muddun ya sake ganinta a tare dani to ba abun da zai hanashi ɗaureni.
Kuma tabbas mahaifinta zai iya sawa a ɗaureni idan kuma haka ta faru to waye zai kula da ƙanwata Maryam.
Tun da nake a rayuwata ban taɓa tunanin cewar zan iya buɗar baki domin tsinewa mahaifina ba amma sai gashi a wannan ranar nayi mai tsinuwar da tafi ƙarfin mai hankali ya iya lissafata saboda duk shine makasudin faruwar wannan matsalar.
To amma sai dai kuma kamar yadda nakejin cewar ba yadda za'ai Zainab ta iya haƙurin rabuwa dani to nima haka nakejin cewar banga wanda ya isa ya iya shiga tsakanina da Zainab ba koda kuwa mahaifin nata ne.
=>3
Washe gari da misalin ƙarfe 9 na safiya Zainab ta sameni har gida a tsakanin ni da ita ba wani alamun farin ciki a tattare damu.
Bayan mun gaisa fuskar Zainab cike da damuwa tace "duk da cewar nasan rabamu ba abu ne mai yiwuwaba hakan bazai hana muyi amfani da wannan damar ba domin cinma burinmu.
Kallanta nayi haɗe da cewa Zainab ban fahimci me kike nufi ba saboda ko kaɗan bazan iya jurar rabuwa dake ba.
Buɗar bakinta sai tace "muddun munason burinmu ya cika to yazama tilas mu nisanta da juna ta hanyar suturta soyayyarmu, kuma nayima alƙawarin ba yadda za'ai na ha'inceka a game da batun soyayyar dake tsakaninmu ni dai burina kawai ya kasance ka cikawa mahaifiyarka burinta a game da batun Maryam.
Zainab tayimin halaccin da ba kowace mace zata iya yimin kwatan-kwacinsa ba domin kuɗin karatunta ta bani domin nayi ƙarar waɗanda su illata ƙanwata.
A yayin da nayi kararsu a game da batun yima ƙanwata feyɗe haɗe da yi mata allaurar data haifar mata da ciwan daji.
Sai mahaifina ya ƙaryatani haɗe da ƙanwar tawa akan cewar tun damacan tana biye biyan maza sannan ya ƙara da cewa yayi iya faɗanshi domin ta daina amma taƙi dan haka baya tuhumar kowa a game da batun larurar dake damun Maryam sannan ya buƙaci kotu da tayi watsi da wannan ƙarar. agabana mutane su riƙa yima ƙanwata kallan banza wanda hakan yasa nayi danasanin kai wannan maganar kotu.
Bayan mun dawo gida sai maryam ta zauna kusa dani.
Koda taga hawaye a fuskata nan take ta fashe da kuka, haka ta kwanta a jikina tana kuka haɗe da cewa "dan Allah yayana kayi haƙuri nasan duk nice sular faruwar wannan matsalar domin nice sular samun saɓanin umma da abba haɗe da kai kanka gashi a dalilina umma tabar duniya a halin yanzu bani da kowa sai kai idan babu kai bansan yadda rayuwata zata kasance ba.
Haka na ɗago kanta na kalleta sannan na girgiza kai haɗe da cewa "bawai ina zubar da hawaye a dalilin abun da abba yai manaba ne, kawai ina kuka ne saboda gazawata wajan nema miki lafiya.
Kuma ai ko kaɗan baki da laifi a game da abun da ya faru a tsakaninmu da abba.
Muna cikin wannan maganar sai mahaifinmu ya shigo hannunshi riƙe da wata wayar wuta.
Ganin yadda yake ƙoƙarin dukan maryam ne yasa nayi gaggawar kareta.
Buɗar bakinshi sai yace "yanzu ni zakuciwa mutunci, ashe har kanajin isarka takai ta kaɗauki maryam zuwa kotu da sunan wadda ayiwa feyde?
To bari kaji wallahi zamanka a wannan gidan ya ƙare domin a yau zakabarmin gidana.
Buɗar bakina sai nace "naji zanbarma gidanka amma tare da ƙanwata.
Jin haka ne yasa yamin wani bahagon kallo haɗe da cewa "idan wannan tunanin ne a kwakwalwarka to tun wurima ka shareshi saboda ba inda zaka da ita domin na cireka daga sahun ƴaƴana.
Na buɗa baki zanyi magana sai maryam ta dakatar dani haka ta tsaya a gaban mahaifinmu tace "Abba kai ne mahaifinmu wanda Allah ya damƙa amanarmu a hannunka domin ka bamu kulawa ta hanyar bamu ci dasha haɗe da bamu ingantacciyar tarbiyya.
Amma sai gashi ba tare da mun aikatama laifin komai ba ka ɗauki babbar tsana ka ɗora mana.
Nima kaina ban dauka maryam tana da dakakkiyar ziciya ba sai a wannan lokacin haka ta ɗagakai ta kalli mahaifinmu haɗe da cewa "wallahi ba sauran biyayya a tsakanina da wanda yai sular mutuwar mahaifiyata.
Haka ya nunata da yatsanshi haɗe da cewa "to tun daga yau ya kamata ki fara tsanar kanki saboda kece sular faruwar duk wannan al'amarin.
sannan ya ƙara da cewa me yakaiki taɓamin kuɗi ba tare dakin tambayeni ba?
Sai maryam tace "saboda duk wani tanadinka namu ne, kuma bada niyar sata na ɗaukarma kuɗi ba na ɗauka ne domin biyan wanda ya kawoni gida hakkinshi, kuma naira 100 na ɗauka a cikin dubu ɗayar dana ɗauka sannan na mayarma da sauran canjin a inda na ɗauki kuɗin kuma da ace da niyar sata na shiga ɗakinka to da ba yadda za'ai na mayar da sauran canjin balle har nasanar dakai cewar nashiga ɗakinka na ɗauki kuɗi domin biyan bukatata.
Amma sai gashi a dalilin haka ka tsani mahaifiyarmu haɗe damu kanmu, kaharamta mana dukkanin wata kulawar da ta dace uba yaba ƴaƴanshi.
Sai ya zamto mahaifiyarmu ce jigonmu.
Haka ka hanamu abinci, ka hanamu kuɗaɗan da zamuyi amfani dasu wajan magance ƴan ƙananun buƙatun mu, ka lalata duk wani muradin mu nason yin karatu, kasa mahaifiyarmu kuka haɗe damu kan mu kasa an kori mahaifiyarmu daga wajan aikin da take samun ƴan kuɗaɗan da zata riƙa ɗaukar ɗawainiyarmu ba tare da ta damu da abun hannunkaba. Kayima yayana ƙazafin satarma kuɗi.
Abba nicefa ƴar da ka haifa, amma haka kayimin kazafin bin maza a bainar jama'a.
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai mahaifin namu ya daka mata tsawa, hatta nima kaina saida na tsorata.
A dalilin wannan tsawar ne yasa nan take naga maryam ta yanke jiki ta faɗi ƙasa.
Cikin yanayin ɗimaucewa mai tattare da mamaki na durƙusa domin ɗaukarta zuwa asibiti, amma sai mahaifin namu ya dakatar dani ta hanyar sake dakamin tsawa haɗe da "cewa muddun ka kuskura hannunka ya taɓata to ba makawa sai na tsinema.
Haka ya nunamin ƙofa haɗe da cewa "maza ka ficemin daga gida.
=>4
Cikin yanayin izza na mai wani mugun kallo haɗe da cewa" ka aikata kuskuran daba makawa sai naga bayanka. sannan na durƙusa har ƙasa na ɗauki Maryam zuwa asibiti.
Haka ya saki baki yana kallona ba tare da Allah ya bashi ikon furta kalmar tsinuwa a gareni ba, sai dai kuma ya gargaɗeni akan cewar karna kuskura na sake dawomai gida.
A wannan ranar zainab wuni tayi a kusa da ƙanwata maryam har saida taga alamun sauƙi ya fara samuwa a gareta sannan ta fita da ƙudirin zuwa gida domin kawo mana abinci.
Bansaniba ashe zainab ta fita ne da ƙudirin siyar da wayar da take amfani da ita.
Can shagon wani mai suna abdul taje da zuwanta bayan sun gaisa cikin yanayin damuwa tace "abdul wayata zan siyar.
Da yake abdul abokin wasanta ne cikin yanayin rainin wayo yace "nasiya 30 thousands.
Fuskar zainab ba alamar wasa tace, "bani kuɗin.
Cikin yanayin mamaki abdul, "yace zainab me yake damunki, saboda naga duk al'amuranki sun canza ba kamar yadda nasanki ba?
Buɗar bakin zainab sai tace, "abdul yau ba ranar wasa bace, kawai bani 30 thousands na wuce.
Buɗar bakin abdul sai yace, "to ina kwali haɗe da risit? wani kallo tamai mai tattare da bayyana ɓacin rai haɗe da cewa, "kazo gida ka karɓa.
Murmushi kawai Abdul yayi haɗe da cewa, "wai yanzu fisabilillahi dagaske kike, wayar 170 thousands zaki siyar 30 Thousans?
Koda zainab taga yana neman raina mata hankali ranta a ɓace tace, "wallahi Abdul idan har ka bari raina ya ɓaci to ba makawa sai kayi mamakina a wajan nan, sannan ta miƙamai hannu haɗe da cewa bani kuɗi na wuce.
Fuskarshi cike da mamaki ya ciro kuɗi daga aljihu haka ya damka mata 30 thousands sannan ta juya tayi tafiyarta ta barshi cikin mamaki.
Zuwacan saiga zainab ta dawo garemu hannunta riƙe da kular abinci.
Kuɗi naga ta miƙomin a yayin da ta aje abincin da ta kawomana haɗe da cewa "ga wadannan kuɗin kayi amfani dasu domin biyan kuɗin jinyar maryam.
Cikin yanayin mamaki nace "amma zainab waɗan nan kuɗin daga ina su fito? saboda.....
Sai ta dakatar dani ta hanyar yin murmishi haɗe da cewa "A'a dakata wayata nasiyar domin matsalarka matsalatace.
Haka na girgiza kai haɗe da cewa "amma zainab banji daɗin hakan da kiyiba, saboda nasan baki siyar da ita da daraja kamar yadda asiyeta ba.
Ta buɗa baki zatai magana kenan sai ga mahaifinta ya shigo.
Ganin haka ne yasa duk wata walwalar da zainab take tattare da ita ta dusashe domin tasan ba arziki ne ya kawo mahaifinta garemu ba.
Da zuwanshi ko sallama banji yayi ba, budar bakinshi sai yace, "amma zainab kin bani kunya da har ki fifita matsayin wannan fiye da nawa matsayin.
Me ki nema ki rasa a gareni; karatu, kuɗi, kyakkyawan makwanci, kula da lafiyarki tun kina ƴar ƙarama har izuwa wannan lokacin duk nine mai yi miki waɗan nan buƙatun.
Babu abun daki nema ki rasa a gareni, amma duk da haka ban taɓa tunkararki da wata babbar buƙatar da ta wuce naga kin rabu da wannan sha-shashan ba.
Sannan ya ƙara da cewa "dan Allah dan...... sai na dakatar dashi ta hanyar cewa dakata abba.
Haka na kalli zainab idanuna suna zub da hawaye sannan na kalli mahaifinta haɗe da cewa "abba nayima alƙawarin daga yau bazaka sake ganin zainab a tare dani ba zan nisanta daku na tsawon har abada.
Amma har kawo yanzu na rasa dalilin da yasa al'umar gari haɗe da mahaifina suke nuna tsanarsu a gareni.
Cikin yanayin kuka nace "dan Allah ko zaka iya sanar dani dalilin faruwar haka?
Kalamin da naji yamin ne ya ɗimautani wanda hakan ya jefani a zazzafan kokwanto.
Domin kallona yayi fuskarshi ba alamar wasa yace "saboda kai da ƙanwarka baku da asali domin ku yayan zina ne. bani kaina ba hatta ƙanwatama sai da tayi matuƙar mamakin jin wannan kalamin.
Buɗar bakin zainab sai tace "dan Allah abba kar kayi ƙoƙarin kasancewa a ɗaya daga cikin mutanan dasu tsani waɗan nan bayin Allan.
Kallanta nayi haɗe da cewa "zainab tashi ki tafi gida, saboda bazai yiwu na shiga tsakaninki da mahaifinki ba.
Washe gari bayan ƙanwata maryam ta samu lafiya sai nabar garin tare da ita ta hanyar tafiya can wani ƙauye tare da ita.
=> 5
Kafin na ƙarasa ƙauyan zainab ta kirani yafi a kirga amma sai naƙi amsa kiran.
A yayin da ta sake kirana cikin yanayin damuwa ƙanwata tace "haba yaya ka amsa kiran mana.
Banyi mata musuba haka na amsa kiran.
Koda na kara wayar a kunnena banji sautin komaiba face sautin kukan zainab cikin yanayin rarrashi mai tattare da damuwa nace zainab bawai na rabu dake bane amma inason kisan da cewar ke lafiyarki ƙalau ita kuma ƙanwata ba wata cikakkiyar lafiya ce da itaba kuma bata da wani gatan da ya wuce ni dan haka a matsayinki na mai hankali da tunani kuma wadda takeson taga farinciki a tare dani zanso kiɗan ƙauracema yawan kiran wayata na ɗan wani lokaci saboda hakan zai bani kwanciyar hankalin dagewa wajan nema mata lafiya.
Cikin yanayin sakin jiki tace "ina son ka, domon wannan kalamin naka yakawar da duk wata damuwar dake zuciyata.
Haka dai naci gaba da tafiya tare da maryam harmu isa wani ƙauye amma sai mutan ƙauyan suƙi karɓarmu a matsayin baƙin da zasu kwana a garesu domin a lokacin damu isa ƙauyan yamma tayi da ƙyar mu samu su bamu ɗan ruwan da zamusha.
Duk da cewar maryam ba wata cikakkiyar lafiya take tattare da ita ba haka mu ƙara gaba. ayayin da muke gaf da isa wani ƙauyan dake gabanmu sai muyi arba da fataken dare wato ɓarayi kenan.
Haƙiƙa nayi matuƙar tsorata a yayin da muyi arba dasu to amma ba wani tsoro najiba illah gudun karsu illata ƙanwata.
Cikin yanayin rainin wayo su dakatar damu kai da ganinsu kaga gidadawa domin ba karamin aikinsu bane su iya bude mana wuta.
Basu tunkaromu da wata magana ba illah maganar kuɗi.
Cikin yanayin sanyin jiki nace "dan Allah kuyi haƙuri domin mu matafiya ne babu kuɗi a tattare damu.
Koda su tabbatar da cewa Eh lallai ba kuɗi a garemu sai ɗaya daga cikinsu ya kalli maryam sannan ya kalleni haɗe da cewa "wannan ƙanwarka ce ko matarka?
Cikin hanzari nace "A'a ƙanwata ce.
Can wani kuma ya sake kwaɓo wata maganar da tayi matuƙar ƙonamin rai domin cewa yai wai na kwanta da ƙanwar tawa a gaban idonsu idan kuma ba hakaba to su zasu kwanta da ita a gaban idona sannan su nisantani da ita ta hanyar tafiya da ita.
Nan take naji wani ɓacin rai yazomin wuya ya tsaya, buɗar bakina sai nace muddun kuga haka ta faru to ina mai tabbatar maku cewar sai bayan ba rai na.
Nan take wani ya ɗaga ƙotar bindiga zai bugamin sai wani tsoho ya dakatar dasu ta hanyar cewa "kai dakata. cikin gaggawa duk su sauke bindigunsu a yayin da tsohon ya ƙaraso garemu sai yace "ba'a farauta a gida.
Haka su wuce sannan muma mu kama gabanmu.
Tabbas mu muga sauyin rayuwa domin a gidan damu sauka daƙyar mu iya cin abincin da'a bamu.
Bayan gari ya waye a yayin damu fito waje sai naga wata baiwar Allah zaune a waje.
Koda nayi ido biyu da matar cikin yanayin mamaki na kalli maryam sannan na sake kallan matar ganin haka ne yasa maryam tace "yayana lafiya kuwa?
Buɗar bakina sai nace "maryam kina matuƙar kama da wannan matar. koda matar taji na ambaci maryam cikin gaggawa ta miƙe tsaye ta nuna maryam haɗe da cewa "maryam. sannan ta nunani haɗe da cewa "Usman.
haka taita nunamu haɗe da kiran sunanmu "Maryam, Usman.. Maryam, Usman..
Jin haka ne yasa mutanan gidan mamaki domin tun da suke a tare da ita basu baɓa jin t furta wata maganar da ta wuce gida ba..
Abun da mai gidan yace a game da batun matar shine "wata rana ne da yamma na fita daji domin yin farauta ko nisa banyi ba sai naji motsi a gefen wani ruwa, jin wannan motsin ne yaja hankalina zuwa gefen ruwan domin ganin abun da ke wannan wajan.
Haskawar da zanyi sai nayi ido biyu da wannan matar kwance a gefen ruwan ga kuma jini na zuba a kanta.
Cikin gaggawa naje gareta domin ceton rayuwarta.
Bayan na kawota nan gidan a yayin da muga cewar taɗan samu sauƙi sai muyi ƙoƙarin jin sunanta haɗe da inda take amma sai hakan ya gagareta domin ba abun da take iya furtawa sai gida aduk lokacin da ayi mata magana ba abun da take faɗa sai gida alhalin kuma bamuda wata hanyar da zamu iya dangantata da gida saboda bamusan daga inda ta fito ba.
Cikin yanayin mamaki nace "to amma gashi yanzu tana iya kiran sunana haɗe da na ƙanwata, kuma babban abun da yake ɗauremin kai shine yadda ai har tasan sunana. buɗar bakin mai wannan gidan sai yace "to amma duk yadda ayi akwai wata muhimmiyar alaƙa a tsakaninku da wannan matar tunda har ta iya furta sunanku.
Jin haka ne yasa naja hannun ƙanwata zuwa gaban matar.
Cikin yanayin girmamawa nace mama ni sunana "Usman wannan kuma ƙanwata ce Maryam.
Sai ta jinjina kai alamun banyi mata ƙarya ba kenan.
Sannan na ƙara da cewa "sunan mahaifiyarmu kuma Aisha amma a halin yanzu bata raye domin ta rasu. sai ta girgiza kai alamun maganata ba haka takeba kenan. ganin haka ne yasa na kalli maryam domin ko kaɗan ban fahimci inda wannan matar ta dosaba wanda hakan yasa gaba ɗaya nayi forget ɗin wannan al'amarin ban saniba ashe wannan wani babban al'amari ne da zai taimaka wajan dawo da rayuwarmu fiye da tacan baya.
Bayan na fita domin yawatawa a wannan ƙauyan sai maryam ta ɗauki wayata domin binciko hotan mahaifinmu koda tayi iya bincikenta ba tare da taga hotan mahaifinmu ba sai ta yanke shawarar shiga Google domin binciko hotanshi.
Bayan ta shiga browser sai kuma network yaƙi bata haɗin kai saɓanin yadda ta saba amfani da waya a inda mu baro wato cikin gari kenan kawai sai ta fita domin neman network.
A yayin da ta samu network cikin gaggawa ta shiga Googe ta ɗakko hotan mahaifinmu sannan ta rugo gida zuwaga wannan matar.
Shigar Maryam gidan kenan sai nima Allah yai dawowata.
=> 6
Da shigar Maryam sai ta nunama wannan matar hotan mahaifinmu.
Cikin gaggawa matar ta fusge wayar daga hannun Maryam haka ta kura ma wayar ido na tsawon wasu mintina.
Zuwacan sai ta saki wayar ta faɗi ƙasa sannan ta dafe kanta tai shiru na tawon wani lokaci.
Ɗago kan da zatayi sai ta kalli maryam haɗe da cewa "ke kuma baiwar Allah daga ina, kuma ya ai na kasance a wannan gidan?
Buɗar bakin maryam sai tace "bani da masaniyar abun da ya faru dake ammani sunana Maryam sauyin rayuwa ne ya kawomu nan ƙauyan tare da yayana mai suna Usman.
Cikin yanayin mamaki ta miƙe tsaye haɗe da nuna maryam muryarta a sanyaye tace "maryam yanzu kece ki girma haka, sannan ta kalleni haɗe da cewa "ba shakka wancan Umar ɗina ne.
Koda naji wannan kalamin daga bakinta cikin gaggawa na matso zuwa gareta.
Buɗar bakina sai nace "amma idan bazaki damuba ko zaki iya sanar damu yadda ai muzama ƴaƴa a gareki?
Haka mutanan gidan su zuba mana ido domin kallan ikon Allah.
Buɗar bakin matar sai tace "nice mahaifiyarku. cikin yanayin ruɗani mai tattare da mamaki maryam tace "ta wace hanya ki zama mahaifiyarmu gaskiya ba yadda za'ai na iya aminta da wannan zancan naki.
Nan take na dakatar da maryam ta hanyar daga mata hannu.
Sannan na kalli matar nace "idan har ke mahaifiyarmu ce to zanso naji dalilin zuwanki wannan ƙauyan?
Haka ta kalleni haɗe da cewa "zata iya yiwuwa dalilin da ya kawoni wannan ƙauyan kuma shine ya kawoku domin mahaifinku azzalumi ne.
Ni a tunanina auran soyayya ne a tsakanina da mahaifinku to ashe abun da yake hange da ban ne.
Kimanin shekara ɗaya da wasu ƴan watanni da haihuwarka sai Allah yaiwa mahaifina da mahaifiyata rasuwa a dalilin wani accident ɗin da ya rutsa dasu a hanyarsu ta dawowa gida daga garin bauchi. kuma gashi ni kaɗaice yar dasu haifa wanda hakan yasa na kasance mamallakiyar dukiyar da iyayena su mallaka.
Bayan rasuwarsu sai aitabin dangina na wajan uwa da uba aita kashesu ba tare da sanin wanda yake aikata wannan ta'asarba.
Kwatsam sai mahaifinku ya buƙaci na shirya domin mubar garin Gombe ta hanyar komawa garin Kano da zama saboda yawancin dukiyar da mahaifina ya mallaka tafi yawa a Kano badan komaiba sai dan gudun kar muma aga bayanmu.
Ganin yadda nake gaf da haihuwa ne yasa na buƙaci yayi haƙuri sai bayan ma haihu sannan sai mu koma duk inda yakeson mu koma, saboda a wannan lokacin ina ɗauke da cikin maryam ne. bayan na samu kimanin wata ɗaya da haihuwar maryam sai mu koma garin Kano da zama.
Kwananmu biyu da tarewa a garin Kano sai mahaifinku ya ɗaukeni tare daku a mota zuwa can wani ƙauye domin neman taimakon yadda za'ai a gano wanda yake aikata wannan kisankan ga dangina a wajan wani malami.
Haka ya ɗaukeni a mota tare daku muyita tafiya har mushiga wani daji.
Bayan munyi nisa a wannan dajin kawai sai naga ya tsaya, ban saniba ashe ya tsaya ne domin bayyanamin suffarshi ta ainashi wadda ya daɗe yana ɓoyeta a gareni.
A wannan lokacin ne yamin kallan da yai matuƙar tsoratani.
Buɗar bakinshi a yayin da yamin wannan kallan sai yace "kinsan me yasa na dage wajan ganin cewar na aureki kuwa?
Haka na girgiza kai haɗe da cewa "a'a.
Sai ya jinjina kai haɗe da cewa "to ba komai bane illah buƙatar mallakar dukiyar mahaifinki.
Sanin cewar ke kaɗaice ƴar da iyayanki su haifa ne yasa na dage wajan ganin cewar na aureki.
Sai bayan na aureki sannan nasa a kawar da mahaifinki haɗe da mahaifiyarki a hanyarsu ta dawowa gida daga jahar Bauchi, saboda nasan duk wata dukiyar dasu mallaka hannunki zata dawo.
Bayan na samu nasarar dawo da wannan dukiyar hannunki sannan nasa abi danginki ɗaya bayan ɗaya a kawar dasu badan komaivba sai dan gudun karsu samu wani kaso daga wannan dukiyar dake hannunki wato bayan kema na kasheki kenan.
Haka naita riritaki ta hanyar bayyana miki tsantsar soyayya har zuwa wannan lokacin daki haifamin yara biyu wato Usman da Maryam kenan.
Kinga yanzu idan kibar duniya dukiyar dake hannunki ta dawo hannun ƴaƴan daki haifamin kenan.
Kuma masu iya magana sunce da kai da kaya duk mallakar wuya ne ma'ana dukiyar ƴaƴana tawace.
Haka na kalleshi a tsorace nace "haba Abban Usman yanzu ashe kai ne ka kashe iyayena haɗe da sauran dangina duk saboda abun duniya, yanzu me kanema ka rasa a gareni? karfa ka manta duk ilahirin dukiyar da nagada a dalilin rabani da iyayena ɗin da kayi a hannunka take domin kai ne mai tafiyar da ita aduk yadda kaga dama.
Sai ya girgiza kai haɗe da cewa "Ai hakan bazai taɓa gamsar dani ba muddun ban rabaki da duniyar nanba domin so nake dukiyar ta zama mallakina ni kaɗai ba tare da fargabar komaicba.
Jin haka ne yasa na fashe da kuka haɗe da cewa "dan Allah kayi haƙuri ka riɗe dukkanin dukiyar amma ka kyaleni tare da ƴaƴana, ko dan darajar wannan jaririyar ya kamata ka kyaleni domin nice wadda ta cancanci ta shayar da ita haɗe da basu tarbiyar da ta dace.
Buɗar bakinshi sai yace "wato sokike idan sun girma ki basu labarin cewar babansu mugu ne ta yadda zasu ƙudiri niyar ganin bayana kenan ko?
To bari kiji wallahi ba abun da zai hanani aikaki lahira a wannan dajin. na buda baki zanyi magana sai ji nayi ya zafgamin mari har sai da kaina ya gwaru da jikin motar da muke ciki.
Ganin yadda yake ƙoƙarin hallakani ne yasa nayi ƙoƙarin ceton rayuwata ta hanyar guduwa.
Haka yaita bina ina gudu har nagaji na yanke jiki na faɗi ƙasa wanda hakan ya bashi damar bugamin wani itace a kaina sannan ya ɗaukeni ya jefani a wani ruwa mai cike da yayi domin shi a tunaninshi na mutu tun daga wannan lokacin gaba ɗaya na manta da komai a dalilin bugamin itacan da yayi a kaina gashi har Allah yasa kun girma ba tare dani a kusa dakucba.....
Buɗar bakin maryam sai tace "lallai kuwa Abba ya cika azzalumi kuma butulu.
Yanzu kenan bashine ya kamata ya koremu ba, mune ya kamata mu koreshi.
Bayan munba mahaifiyarmu cikakken labarin yadda rayuwarmu ta kasan ce sai mu shigar da ƙarar mahaifinmu.
A yayin da kotu ta gano cewar mune keda gaskiya cikin gaggawa kotu ta bayar da izinin sakina haɗe da maida mana gaba ɗaya dukiyar da mahaifina yake riƙe da ita a hannunsu.
Sannan kotu ta yankewa mahaifina hukuncin ɗaurin rai da rai ta hanyar tsareshi a gidan yari.
Bayan mahaifiyata ta nemawa ƙanwata maryam lafiya haɗe da kama masu hannu a game da batun cutar da ita wanda hakan yasa a yanke masu hukuncin ɗaurin shekara 7 a gidan yari.
Ganin yadda haka ta kasance ne yasa mahaifin Zainab ya bani damar auran ƴarshi wato Zainab kenan.
Bayan anyi bikin aurena da Zainab sannan mahaifiyata ta mallakama waɗanda su ɗauki haƙurin zama da ita a yayin dasu tsinceta a daji wani babban gida haɗe da kuɗi har kimanin miliyan 5 domin suma su dawo gari da zama.
Alhamdullah.
The End