Tuesday, August 6, 2024

MEENAT complete




new update

=> 1
Tabbas ni a nawa tunanin ba abun da yakai so daɗi. Tabbas abun yana matuƙar bani mamaki ganin yadda mutane suke zuzuta soyayya. Ni kuma ko kaɗan bata wani burgeni, ban saniba ashe tananan zuwa gareni. ni dai haifaffen garin "KANO NE" amma a yanzu ina zaunene a hayin rigasa wato cikin garin KADUNA kenan. ɓangaren karatuna kuma yana ZARIA. A makarantar da nake karatune na haɗu da wani aboki mai suna Musa, musa mutun ne mai haƙuri da sanin ya kamata musamman a ɓangaran zamantakewa da mutane, saboda jin daɗin kasancewarmu a tarene yasa musa ya jawoni gareshi sosai wajan kwananmu ɗaya cin abunci tare yawo tare kai hatta wanka a gidansu nakeyi, iyayenshi sun ɗaukeni tamkar dansu na cikinsu. bazan taɓa mantawa da wata ranar litininba bayan mun dawo daga school munyi wanka munci abunci fitowarmu waje kenan sai idona yai arba da wata haɗaɗɗiyar yarinya a wannan lokacinne zuciyata ta shiga wani irin yanayi, yanayinda hankalina bazai iya gane ma'anar hakan ba.
nan take na kalli musa nace abokina kaga wata "fine girl" can tana tafiya. 
murmushi! naga yayi sannan yace kai dalla waccanfa Ameena ce wadda ake kiranta da meenat wai ko ka mantatane? 
sai na kalleshi cikin yanayin mamaki! nace musa wallahi ban santaba domin wannan shine ganin da nayi mata na farko. 
sai yace "to ai wannan a nan unguwar take, yar gidan alhaji ibrahim cefa wanda gidanshi yake nan baya. 
sai nace "toni ina shiga gidan ne dazansan yana da yarinya kamar waccan? ni dai kawai abun da nakeso dakai idan anjima tayi wato da yamma kenan zaka taimaka domin rakani wajanta. 
cikin gaggawa yace khai! a'a, wallahi bazaka kaini wajan da raina zai ɓaciba domin waccan yarinyar da kake gani ni kaina tsoro take bani domin rashin mutuncin da yake zuciyarta yafi ƙarfin a musaltashi saboda ko kaɗan bata ganin kowa da mutunci. kai saboda tsabar rashin mutuncinta ko a makaranta ba wani saurayin da yake tunkararta da batun soyayya, kai har tsinkama wani mari sai da tayi a bainar jama'a kawai saboda yayi mata magana. 
kuma waccan da kake gani bata da wasu ƙawaye sai wata guda ɗaya mai suna aisha, itama kawai dan halinsu yazo ɗaya ne. 
Jin haka ne yasa nace dashi "kardai kace itama a school ɗin da muke karatu take gudanar da nata karatun? 
sai yace "kwarai kuwa itama anan take karatunta.
Buɗar bakina sai nace alhamdulillah kaga ai takwana gidan sauƙi tunda kana tsoran zuwa gidansu ai bazakaji tsoran rakani wajanta a school ba.
sai yace kaga nifa ba gidansu nake tsoran zuwaba, ita kanta nake tsoro amma idan kaga zaka kai kaɗai to bisimillah ga fili ga mai doki.
Koda naji haka sai nace "shikenan tunda kace haka ba komai kuma nayima alƙawarin sai na san hanyar da nabi wajan ganin soyayyata ta samu karɓuwa a gareta ba tare da na nemi taimakon kowaba kawai ka zuba ido kai kallo.
Tabbas a wannan ranar sai da nayi matuƙar mamakin ganin yadda na daɗe banyi bacciba, haka tunanin meenat yaita kai kawo a zuciyata.
Bayan gari ya waye a yayin da mu gama shirinmu sai mu ɗauki hanyar school, da isarmu sai na tambayi abokina musa nace abokina dan Allah karfa ka gaji dani, ko zaka iya sanar dani ɓangaran da meenat take karatu?
Sai ya kalleni yai murmushi haɗe da cewa "haba abokina, ya tun yanzu zaka fara neman taimako.
Kaifa da bakinka kayi fariya akan cewar sai kasan hanyar da kabi wajan ganin meenat ta karbi soyayyarka ba tare da ka nemi taimakon kowaba.
Dan haka tunda Allah ya baka ƙafa da baki haɗe da ido sai ka duƙufa wajan nemanta.
Gashi saura 5 minutes mu shiga lecture, da yake zuciyata tana muradin kasancewar meenat a tare dani haka nayi watsi da lakcar da zamu shiga a wannan lokacin.
Haka na bazama wajan neman meenat. Abu kamar wasa haka na ƙaraci yawona har na gaji ba tare da na samu haɗuwa da meenat ba.
Haka washe garima ban gajiyaba, da yake a wannan ranar zamu kwashe wajan 30 minutes bamu shiga lecture ba. kaitsaye na tunkari department ɗin yan "science" Allah mai iko kenan, ko karasawa banyiba sai nayi arba da meenat ta fito tare da wannan kawar ta ta da Musa ya bani labari.
Kai da ganinsu kasan ba abun da yake damunsu domin fitowa naga sunyi fuskarsu cike da annuri suna dari.
Ko cikakken 2 minutes basuyi ba su dawo, bayan sun shiga class sun zauna a raina sai nace "anya wannan yarinyar zan samu karɓuwa a gareta kuwa?, tun daga wannan ranar na fara nazarin hanyar da zan ɓullo mata. Musamman nake shiga department ɗinsu badan komai ba sai dan buƙatar idona ya ganta aduk lokacin da kunnuwana suji sautin muryarta ba ƙaramin daɗi nakeji ba a raina.
A ƙalla na dauki kimanin wata 1 ina bibiyarta ba tare dana iya gabatar da soyayyata a garetaba, duk tsawon waɗannan kwanakin dana ɗauk ko magana da ita ban taɓa yiba, kuma ba wani abu ne ya jawo hakan ba sai dan tsoran karta wulaƙantani a bainar al'umma.
Abu kamar wasa har karatuna ya fara samun tangarɗa.
Nine a makaranta tunaninta a gidama tunaninta gaba ɗaya na daina maida hankali a game da karatuna.
Kwatsam wata rana da yamma sai abokina musa ya sameni a daki yace "abokina naga a kwanakin nan duk al'amuranka sun canza, saboda da nasanka da yawan surutu haɗe da yawon son yawo amma yanzu naga duk ka nisanta kanka da waɗannan halayen. kuma karatunkama naga alamun nema kake ka watsar dashi, dan haka ina mai shawartarka daka rabuda wannan wawiyar yarinyar domin wahalar da kai kawai zatayi. 
Budar bakina sai nace, "tabbas ni kaina nasan halayena sun canza, kuma ba komai bane ya jawo faruwar hakan sai dan ganin meenat da nayi, amma inason kasan wani abu domin magana ta gaskiya ba yadda za'ai na iya gaggar rabuwa da meenat saboda tariga ta shiga zuciyata. 
Haƙiƙa zan iya sadaukar da duk wani abun dana mallaka wajan ganin meenat ta zama mallakina.
Koda musa yaji haka sai ya jinjina kai haɗe da cewa "tabbas ban taba ganin wawan mutun kamar kaba akan macen da batasan abun da kakeyiba har kake iƙirarin sadaukar da duk wani abun da ka mallaka a kanta?
Tabbas akwai gyara a wannan maganar taka tun wuri gwara ka tsaya kayi nazari akan wannan banzan tunanin naka.
Haka dai nayi watsi da duk wata maganar da Musa yayi a gareni wanda hakan yasa a wannan ranar na fara nazarin hanyar da zanbi wajan ganin na samu numbar wayar meenat domin ta wannan hanyarce kaɗai nake tunanin haƙona zai cimma ruwa.
Hmm!! Sai dai kuma ba anan gizo ke saƙarba, domin ita kanta numbar ba karamin wahalar samuwa zato a gareni ba, saboda na ɗauki alwashin bazan nemi taimakon kowaba kuma gashi ba abun naje gareta nace ta bani phone numbar taba.
Kawai sai na yanke shawarar rubuta wasika.
A wannan ranar sai na samu takarda da biro na rubuta wata yar ƙaramar wasiƙa kamar haka.
•Assalamu'alaiki. Bayan ɗinbin gaisuwa haɗe da jinjinar bangirma a gareki, Ina miki fatan kasancewa cikin rahamar ubangiji tare da alkhairan wannan ranar su tabbata agareki. Nasan zakiyi matuƙar mamakin ganin isowar wannan wasiƙar a gareki ba tare da kinsan ko waye ya rubuto miki itaba domin wannan wasiƙar ba ta buƙatar wani dan aike sai dai kawai ki ganta kwatsam a gareki. 
 Sannan inason na sanar dake cewar "lokutan baccina sun kasance ɗaya daga cikin lokuta mafi muhimmanci a zuciyata saboda ke kaɗaice wadda take ƙawata baccina a duk lokacin da na rintse idanuwana domin kece wadda take tayani fira a mafarkina na kan ganki cikin shiga irin ta amare, ina fatan mafarkina ya zamto gaskiya na zama naki kema ki zamo mallakina.
kada kiyi shakka ko kokwanto akan son danake miki inayi miki sone nagaskiya cikar burin zuciyata na kusanta dake a koda yaushe, nasan rayuwata zatayi daɗi muddun nasameki amatsayin masoyiya wadda zata faranta raina MEENAT ina fatan zan samu amincewarki saboda hakan shine cikar burina gami da farin cikina? idan har ki aminta dani ina yiwa zuciyarki alƙawarin zan faranta ranki zan kula dake kamar kwai a tafin hannuna, zan shayar dake zumar soyayya bazan taɓa shayar dake gubar soyayya ba, farin ciki shine zai zamto abokin firarki akodayaushe. 
A ƙarshe sai nasa numbar wayata. Bayan na kammala rubuta wasiƙar sai na shiga nazarin hanyar da zanbi wajan ganin wasiƙar ta isa gareta ba tare dana aiki wani ko wataba kuma ba tare dana bata wasiƙar hannuna da nataba.
=> 2
Bayan na rubuta wasiƙar saida na ɗauki tsawon kwana biyu ba tare da na gano hanyar da zanbi wajan ganin wasiƙar ta isa gareta.
Ranar juma'a da musalin 10:30am lokacin ina zaune tare da abokina musa a gaban class ɗinmu sai na hangi meenat ta fito daga wata mota kirar fijo (peugeo) a wannan lokacin ne na daki ƙirjin tunkararta domin isar da saƙo na haka na yayibi littattafan karatuna a hannu nabi bayanta koda musa ya kalleni sai yayi dariya sannan ya girgiza kai da shigarmu class ɗin zata zauna kenan kaina tsaye naje gareta tabbas al'amarin meenat yayi matuƙar bani mamaki domin sallama na mata amma sai tayi banza dani ko kallona batai ba.
 Buɗar bakina sai nace baiwar Allah ko zan iya samun aron biro a wajanki?
Juyowa tayi a fusace buɗar bakinta sai tace "a ina kuma ka baro uban naka, da bai saima biron ba da har zakazo kana tambayata aran biro?
Tabbas wannan kalmar tayi matuƙar sosa min rai wanda hakan yasa na kalleta fuskata cike da mamaki nan take nasa hannu nayi fatali da littattafan dake hannunta suyi watsa-watsa sannan na tsunketa da mari, ta ɗaga hannu zata rama sai wani ya riƙe hannun haɗe da cewa "a'a baza'ai haka ba domin kece baki da gaskiya.
Ganin haka ne yasa nan take naga tayi calling.. Ɗin wata numbar da nima kaina bansan ko numbar waye ba. Kafin a amsa wayar sai nayi gaggar sakin wasiƙar da na rubuta a dai-dai wajan da littattafan nata su zube. 
Ban saniba ashe jami'an yan sanda ta kiramin.
Tabbas nayi matuƙar tsorata alokacin da naji batun yan sanda domin har cikina saida ya kaɗa gashi kuma bani da halin guduwa to guduwar mema zanyi tunda inada gaskiya tabbas babu wanda yakai namiji burga sai na matsa kusa da ita na kalleta tun daga sama har ƙasa nace ki kira duk uban da zaki kira inanan ba inda zanje sai naga abun da ya turema buzu naɗi zuwan yan sandan kenan sai Allah ya kawo ƙawarta A'isha koda A'isha taga yan sanda tsaye a gaban meenat sai tace "ƙawata mekuma yake faruwa naga yan sanda a nan sai tayi banza da ita ba tare da tace komai a gareta ba koda taga alamun bazata sanar da ita abun da yake faruwaba sai ta kalleni tace "malan dan Allah menene yake faruwa nantake na bata labarin duk abun da ya faru.
Koda A'isha taji duk abun da ya faru sai ta jinjina kai sannan ta kalli meenat tace "gaskiya meenat baki kyautaba domin wannan ai laifinkine sannan A'isha ta kalleni tace "dan Allah malan kayi haƙuri kuma ina shawartarka daka ba ta haƙuri domin komai ya wuce.
 Buɗar bakina sai nace, Tab! Allah ubangiji ya kiyaye ai ko sama da ƙasa zata haɗe banga dalilin da zaisa na iya buɗi baki nace da ita tayi haƙuri ba.
Jin haka ne yasa meenat ta kalli yan sandan tace "kunga bankiraku nan domin kuji wasu banzayen kalamanshi ba dan haka ku wucemin dashi station sai nazo bayan an wuce dani sai A'isha ta kwashe littattafan dana zubar mata haɗa da wasikar dana rubuta shiru-shiru abokina musa baiga na koma gida ba har lokacin tafiyarmu gida yayi bai ganniba koda ya gaji da jirana sai yai tafiyarshi gida haka a tsareni a station har tsawon awanni 10 ba tare da meenat tazo station ba.
Bayan meenat ta koma gida sai ta taradda mahaifiyarta zaune a falo ranta a ɓace koda meenat taga haka sai tace "umma mekuma ya faru naga kamar ranki a ɓace ba yadda na saba ganinki ba?
Sai mahaifiyarta tace ke dallacan rufemin baki sha-sha-sha kawai yanzu ashe rashin mutuncin da yake tattare dake har ya fara zarce ƙima to wallahi kiyi gaggawar komawa domin kisa a saki wanda kisa a tsare.
Sai meenat tace "umma waye kuma ya sanar dake hakan ta faru sai tace "au kina mamakine to abbankine ya sanar dani kuma yace kiyi maza-maza kisameshi a can station ɗin yana jiranki.
Nan take meenat ta aje littattafanta a falo sannan ta nufi station.
Da zuwanta bayan tayi sallama sai mahaifinta ya dauketa da mari cikin yanayin bacinrai yace yanzu abunda kiyi kin kyauta kenan kuɗi haukane kawai dan kintaso cikin jin daɗi da walwala sai ki wulaƙanta waɗanda kiga dama to bari kiji arziƙi da rashinsa duk na Allah ne, kuma na tabbata da baki tsunci kanki a cikin kuɗi ba da baki isa ki wulaƙanta wani ba.
Dan haka inason ki durƙusa har ƙasa domin ki bashi haƙuri zata durƙusa kenan sai na dakatar da ita nace a'a Alhaji ba sai ta durƙusa a gabanaba na yafe mata har abada, kuma ban ƙullaceta da wani abu a zuciyata ba.
Bayan an sallameni na koma gida sai na taradda abokina musa kwance a ɗaki yana hutawa koda na kalleshi sai nace "amma gaskiya musa bakada mutunci ace tun ɗazu ina tsare a hannun yan sanda kai kuma kana zaune a ɗaki ba wata damuwa a tattare dakai?
Cikin sauri ya tashi zaune fuskarshi cike da mamaki yace "kardai kace meenat ce tamiƙaka hannun yan sanda sai nayi murmushi nace "hum kai dai bari kawai ai abun ba'a cewa komai, nan take naji ya tuntsure da dariya saboda tsabar dariya har hawaye sai da ya zubo a fuskarshi nikuma gaba ɗaya sai abun yai matuƙar bani haushi.
Washe gari da safe musalin 9:30am meenat ta kammala shirinta na tafiya makaranta, ɗaukar littattafanta kenan sai taga wasiƙa ta faɗo daga cikin littattafanta koda ta ɗauki wasiƙar cikin gaggawa ta buɗe wasiƙar.
Haka ta zauna a gefen gadanta ta karanta duk abun da yake tattare da wasiƙar wanda hakan yasa tayi matuƙar mamakin ganin yadda wannan wasiƙar tazo gareta batare da saninta ba.
A wannan lokacin sai tayi ƙoƙarin kiran wayata amma ba ta sameni ba domin a wannan lokacin wayar tawa a kashe take.
=> 3
Da zuwan meenat makaranta sai ta miƙama ƙawata Aisha wasiƙar tace "aisha kinga wata wasiƙa dana gani yau a cikin littattafaina bayan A'isha ta karanta duk abun da yake rubuce takaddar sai ta kalli meenat tace to ai wannan wasiƙar yau kwana ukku kenan da rubutata.
Buɗar bakin meenat sai tace "wallahi da ace zansan wanda ya rubuta wannan wasiƙar da Allah ne kaɗai yasan irin rashin mutuncin da zanyi mai.
Sai A'isha tayi dariya haɗe da cewa "to ai hanyar da zakibi wajan gane ko waye tana tattare da wannan numbar da ya rubuta a karshen wasikar sai meenat tace to ai tun ɗazu nake "try ɗin numbar amma taƙi shiga a duk lokacin da na kira sai dai naji "switch off" amma bari na sake gwadawa na gani. 
Zamu shiga lecture kenan sai naji vibration! A aljihuna har saida na tsorata dubawar da zanyi sai naga number amma ba suna nai jim kamar na amsa kamar karna amsa a ƙarshe dai sai na yanke shawarar amsa kiran zan amsa kenan sai kiran ya yanke koda naga haka sai na maida wayata aljihu na shiga class na zauna koda naga an matsanta da kirana gaba dayama sai na kashe wayar ayyah! Ban saniba ashe meenat ce take calling.. Ɗina zuwacan bayan mun fito waje sai na kunna wayar domin kiran misscall ɗin da amin sallamace farkon kalamina a yayin da'a amsa kiran.
Wata zazzaƙar murya naji wadda tasa gaba ɗa ya jikina yai sanyi a yayin da naji ta amsa sallamar, daga bisani kuma sai naji tace "na amsa sallamarkane saboda sanin muhimmancin addinin da nake ciki.
Buɗar bakina sai nace "haba meenat ai nima sanin muhimmancin addinin nawane yasa namiki sallama. 
Sai tace "au ashe kamasan da wadda kake magana? 
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "ai koda a cikin dubban matane muryarki bazata taɓa boyemin ba saboda musamman nake zama a kusa dake badan komaiba sai dan buƙatar jin daddaɗar muryarki haɗe da shakar wannan daddaɗan ƙamshin da yake tashi daga jikinki nan take naji ta yanke wayar.
Sai ƙawarta A'isha tayi dariya haɗe da cewa ammafa gaskiya wannan bawan Allan da wuri zai sace zuciyarki domin na tabbata ko a fili ki haɗu dashi kalamanshi bazasu bari ki iyi zartar da rashin mutuncin da kike da ƙudirin yimai ba.
Sai meenat tace, "aisha wace hanya ce kike ganin ya dace nabi domin cimma nasarar kama wannan gayen? 
Sai A'isha tace, "ai a yanzu bazai taɓa bari ki haɗu dashi ba, amma shawarar da zan baki ɗaya ce, kawai ki shiryamai gadar zare ta hanyar amincewa da soyayyarshi hannu bibbiyu kuma na tabbata idan kibi wannan shawarar tawa ba abunda zai hana burinki cika ammafa karki kuskura kiyi gaggawar nuna amincewarki da wuri dolene saikin ɗan jamai aji ta yadda zuciyarshi zatai saurin kamuwa.
Sai meenat tayi dariya haɗe da cewa shiyasa nakeson zama dake ƙawata saboda kinada dogon tunani. 
Zuwa can da yamma sai nayi calling.. Ɗinta amma sai dai ta ƙaraci ringing! ta yanke ba tare da an amsa kiran ba nayi calling! Ɗinta yakai sau ukku amma "no answer" a karshema inna kira sai dai naji an yanke kiran domin (call rejected) nake gani a ƙarshe sai na yanke shawarar turamata da text wato message kenan, sai na rubuta text kamar haka.
•Meenat na kiraki har sau ukku amma shiru baki amsa ba a ƙarshema idan na kira sai dai naji an yanke kiran. 
Haƙiƙa nima kaina na tabbatar da cewar So! abu ne da yake da matuƙar haɗari da kuma wahala, saboda haka akwai buƙatar ki yi duba na tsanaki a lokacin da kike ƙoƙarin zabar saurayi na gaskiya wanda zai tafiyar da rayuwar ki cikin girmamawa da kulawa, amma a lokacin da kiyi zaben tumun dare tabbas zaki kasance a cike da danasani haɗe da yin nadama na tsawan rayuwarki. Kasantuwa cikin rayuwa mai inganci a soyayya ta gaskiya hakan na nufin ki zabi mutumin da hankalin ki ya kwanta da shi. Wannan shawara ce a matsayina na masoyin ki. Fatana a kullum ki fahimci cewar, Ina Son Ki.
MEENAT=> 4
Jim kaɗan da turama meenat saƙon sai naji kira ya shigo wayata.
Koda naga sunan meenat ya bayyana a screen ɗin wayata cikin gaggawa na amsa kiran.
Na ɗauka zanji kalmar da zata farantamin rai ashe kalamin meenat ƙonamin rai zaiyi. 
Da amsa kiran ko sallama banji tayiba sai tace "dan Allah malan kadaina takuramin wai wannan wane irin naci ne to bari kaji wallahi idan har kaci gaba da takuramin wajan kirana haɗe da turomin message sai nayi sular jefa rayuwarka a tashin hankali in banda tsabar rainin hankali ta wace hanya kake tunanin zan amince da kai alhalin ko ganinka ban taɓayiba wannan ma ai rainin hankaline?
Jin hakane yasa nayi shiru na ɗan wasu sakonni. 
Daga bisani sai nace, "meenat dan Allah kiyi haƙuri nasan nayi kuskure kuma ba wani abune yasa na kasa zuwa gareki domin bayyana soyayyata a gareki ba saidan gudun rashin samun nasarata a yayin dana bayyana soyayyata a gareki ido da ido, amma daga yanzu bazan sake takura miki da kira ko turo saƙon text message ba saboda haliccemu ya hanemu da takurama junanmu.
Kuma nayi miki alƙawarin sai na kawo miki kaina har inda kike domin samawa zuciyata sauƙi abisa halin da tashiga na sonki nidai fatana Allah yasa na samu nasarar amincewarki, sannan na yanke kiran.
Bayan na yanke kiran sai naji duniya tayimin zafi kaina ya kulle sakamakon rashin sanin hayar da zan bullowa meenat saboda a zahirin gaskiya duk wata dabar da nake tattare da ita ta ƙare.
Ganin yadda na kalli abokina musa ne yasa yayi dariya haɗe da cewa to nidai fatana Allah ya raba bawa da wahala.
Zuwa can cikin dare musalin 12:30 har nayi bacci sai ringing.. ɗin wayata ya tasheni, raina a ɓace na ɗauki wayar dubawar da zanyi sai naga ai meenat ce take calling..
Cikin gaggawa na amsa kiran cikin yanayin sanyin murya naji tayi sallama.
Buɗar bakina bayan na amsa sallamar sai nace "meenat har yanzu bakiyi bacci bane?
Murmushi naji tayi haɗe da cewa "na kiraka ne kawai domin na baka haƙuri a game da abun da ya faru a tsakanina da kai. 
Sai nace haba meenat aini a tunanina bakiyimin laifin komaiba a taƙaicema nine na aikata kuskure a gareki. 
Sai tace, "dan Allah kabar wannan maganar ai komai ya wuce, ni dai so nake kawai naji kace ka haƙura. 
Jin hakane yasa na sanar da ita cewar "zan furta wannan kalmar ne domin faranta ranki dan haka meenat na haƙura. 
Nan take ta bayyana farin ciki haɗe da godiya. 
Sannan tace, "ina da wasu tambayoyi guda huɗu da nake buƙatar jin amsarsu daga bakinka. 
Cikin yanayin sakin fuska nace to yar'uwa ina sauraronki kuma ina fatan Allah ya bani ikon amsasu.
Sai tayi murmushi haɗe da cewa "ai tambayoyin basu da wata wahalar amsawa. 
Tambayata ta farko itace, Menene sunanka?
Ta biyu kuma a ina kake da zama?
Ta ukku kuma a ina kasanni.
Ta huɗu kuma ya ayi kasamu nasarar sa wasiƙa a cikin littattafan karatuna.
Tabbas a yayin da naji waɗannan tambayoyin daga bakin meenat sai da na girgiza. 
Cikin yanayin natsuwa nace "da farko dai sunana uzairu amma anfi kirana da Young Uzee kuma a yanzu haka ina zaune a jahar adamawa tambaya ta ukku data huɗu kuma zanso kiyi haƙuri har sai lokacin dana bayyana a gareki zan baki amsarsu. 
Sai tace, "to amma mezai hana ka bani amsarsu a yanzu?
Sai nayi murmushi haɗe da cewa, " saboda idan gani gaki sai kinfi fuskantata sosai kuma nima sai nafi sakewa wajan yimiki cikakken bayani musamman idan ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki. 
Sai tace, "a'a banda zolaya domin bana daga cikin wadda za'a iya lissafowa a jerin masu kyawun fuska. 
Sai nace, "ai babu batun zolaya a tattare dani saboda abun da idonsa ya gani kenan. Sai tace, "to naji yaushe zakazo domin na matsu na ganka ido da ido? 
Sai nayi murmushi! Haɗe da cewa "ki kwantar da hankalinki in Allah ya amince ranar Asabar wato Monday kenan zanzo gareki. 
Cikin yanayin damuwa haɗe da bayyana tsantsan shagwaɓa, tace "haba dan Allah kwana bakwaifa yayi yawa ina laifima kace gobe ko jibi zakazo. 
Cikin yanayin tausasa murya nace meenat kwana biyu yayi kaɗan ina laifima kice.... Sai ta dakatar dani bata bari na ƙarasa furta maganar dake bakina ba.
Sai tace kaga to nabaka kwana huɗu kawai kazo.
Jin hakane yasa nayi dariya haɗe da cewa "to shikenan Allah ya kaimu rai da lafiya.
Sai ta amsa da ameen.
Tun daga wannan ranar sai soyayya ta shiga tsakanina da meenat. 
Washe gari da sassafe ina duba wayata sai naga text message ɗinta. Abun da tace shine;
•Shauki mafi tsuma zuciya da nishaɗi mafi ƙarfin kore damuwar zuciyata basu kasance a tare da ni ba sai a lokacin dana haɗu da kai. 
Kai ne ka zamo tauraron da hasken sa yayi sanadiyar raba zuciyata da baƙin duhun da ta daɗe a cikinsa.
Haduwata da kai ya haifar da canji mai yawa a tattare da rayuwata.
=> 5
Cikin ƙanƙanin lokaci soyayya mai matuƙar karfi ta shiga tsakanina da meenat wanda hakan yasa batun ƙudirinta na cimin mutunci ya fita daga ranta, sai dai kuma har kawo wannan lokacin batasan cewar da wanda ya mareta a school take soyayya ba. 
Ako wace rana mukanyi waya da junanmu kamar sau 10 kai akwai ranar da saida muyi waya da juna har sau 16 a wannan ranarne zuciyata ta kara amenta da soyayyar da meenat take nunamin gaskiyace.
Cikin yanayin tausasa murya meenat tace, "dan Allah yayana kayi haƙuri da wannan halayyar tawa domin nima kaina nasan ina yawan takurama da yawan kira, wallahi ba yin kaina bane kawai zuciyatace take muradin jin muryarka a kunnuwana bani da wani abun da yake ɗebemin kewa a rayuwata fiye da kai. 
Sai nace "to amma meenat meyasa ki bari har zuciyarki ta kamu da irin wannan matsanancin son alhalin kuma baki taɓa ganina ido da ido ba? 
Sai tace, "duk da haka ako da yaushe idanuwana suna mararin son ganinka. 
Burin idanuwana a kullum baya wuce son ganin ka. 
Ƙwaƙwalwata ba ta da wani aikin da ya wuce tunanin ka. 
Da son ka nake kwana nake tashi, tare da shi nake fatan mutuwa zanso soyayyarka ta kasance manne cikin kirjina na tsawon har abada. 
Ako da yaushe suffarka tana yimin gizo a cikin duniyar baccina. 
Bani da wani abun kauna wanda ya wuce kai. 
A wannan ranar saida mu ɗauki dogon lokaci muna fira a waya, bayan mun kammala wayar sai abokina musa yace "gaskiya abokina ka zarce tunanina wallahi ko kaɗan ban ɗauka zaka iya samun nasarar shiga zuciyar meenat ba ammafa ba anan gizo ke saƙarba ina jiyema ranar da meenat zata gano cewar da kai take soyayya domin na tabbata akwai sauran dirama a yayin da kuyi ido biyu da juna a matsayin masoya.
Jin wannan furucin da abokina musa yayi a gareni baƙaramin tsoratar dani yai ba, kuma gash bazan iya haƙura da meenat ba.
Bayan dare yayi sai hankalina ya kasa samun natsuwa.
Musalin ƙarfe 9 na dare meenat ta kirani a waya kamar dai yadda mu saba a ko wace rana.
Koda na amsa kiran bayan mun gaisa sai tace "yayana kasan wani abu kuwa? 
Cikin yanayin sakin fuska nace "a'a kanwata sai kin fada.
Sai tace "harna matsu gobe tayi domin itace rana mafi soyuwa a gareni saboda a cikinta ne sanyi ido biyu da kai a zahiri. 
Nan take naji kaina yai wani dumm, kaina ya kulle. 
Murmushi nayi haɗe da cewa "ai in Allah ya amince gobe tamkar kin ganni ne sai tayi dariya sannan ta yanke wayar. 
Zuwa can bayan misalin 30 minutes sai naji shigowar text message! Abunda tace shine;
•Kasancewarka a matsayin masoyi a gareni ya wadata zuciyata da farin cikin da ganin karshen sa bazai zamto mai sauƙi ba, saboda ita soyayya ta gaskiya bata taɓa gogewa a zuciyoyin masoya kamarmu, Ina fatan zaka cigaba da sona kamar yadda nima nake son ka na tsawon har abada? Ka huta lafiya.
Ganin haka ne yasa nima na aika mata da text message kamar haka;
•Nima ako da yaushe nakan shafe tsawon lokaci kafin kwanciya bacci domin yin addu'ar dacewa da samun wani kaso daga cikin kulawar ki masoyiyata, So ya kasance a cikin zuciya ne ita kuma kulawa a bayyane take a saman fuskokin mu, zan kasance a cikin farin ciki na tsawon rayuwa a duk lokacin da ace na mallake ki a matsayin matata. ina ƙaunarki ako da yaushe.
Tun a wannan danar na fara saƙe-saƙen hanyar da zan ɓullowa meenat.
Da musalin ƙarfe 9 na safiya sai ga kiran Meenat ya shigo wayata, cikin yanayin ɓacinrai na kalli wayar nayi tsaki.
Ganin hakane yasa abokina musa yace "haba abokina ka amsa kiran mana. 
Ba yadda na iya haka na amsa kiran.
Sallamace a farkon kalaminta, cikin yanayi irin na marar lafiya muryata a sanyaye na amsa sallamar. 
Cikin yanayin shauƙi haɗe da murna meenat tace yayana inanan ina zaman jira dan Allah ka taho da wuri. 
Sai nayi shiru na ɗan wani lokaci.
Koda meenat taji nayi shiru tace "yayana ya naji kayi shiru kardai kace bazaka samu damar zuwa a yauba? 
Buɗar bakina sai nace "dan Allah meenat kiyi haƙuri zuwana gareki a yau bazai samu yiwuwa ba domin a yanzu haka ina kwance a gadon asibiti ana ƙara min ruwa saboda jiya kwana nayi da matsanancin zazzabi. 
Jin haka ne yasa meenat ta bayyana tausayawarta a gareni sannan ta buƙaci na bata full address ɗina, nan take naji ƙirjina ya buga saboda ganin yadda meenat ta ɗakko hanyar ƙure ramin karyata. 
Cikin yanayin mamaki nace "to amma meenat me zakiyi da address ɗina? 
Sai tace " yayana ai mun riga mun zama ɗaya dan haka banga abun da zai hanani zuwa gareka ba. 
Sai nace "to amma meenat adamawafa tana da nisa domin ba'a kusa take ba, 
Sai tayi murmushi! Haɗe da cewa karka manta garin masoyi baya nisa dan haka ina jiran isowar address. 
Ko ba tare da jin wani tsoro ba na tura mata full address ɗin wani abokina da yake zaune a cikin garin adamawa saboda ko kaɗan ban ɗauka da gaske meenat take ba ko cikakken 2 minutes da tura mata addres ɗin ba aiba sai naji kiranta ya shigo wayata.
Koda na amsa sai tace "naga address nagode ka saurari zuwana sai nace "to ai kin manta baki sanar dani ranar da zakizo ba sai tace "ka kwantar da hankalinka domin zuwan bazata zanyima. 
Bayan na yanke wayar sai musa yace azahirin gaskiya abokina abun da kake shirin aikatawa sam bai dace ba kuma idan kayi haka kayi zalunci a fagen soyayya. 
Sai nayi murmushi nace " haba abokina ni nasan da wasa takeyi saboda banga dalilin da zaisa meenat taje adamawa ba. 
Sai musa yace "amma gaskiya baka da hankali dan Allah tunda kayi nasarar samun soyayyarta ka taimaka ka faɗa mata gaskiya domin wannan hanyar bazata taɓa ɓullewa da kai ba amma idan kaƙiji bakaƙi gani ba.
A wannan ranar ba yadda abokina musa baiyi ba wajan bani shawara domin sanar da meenat gaskiya amma naƙi haka nayi watsi da duk wata maganarshi. 
Washe gari da musalin 6:00pm sai naga musa ya shigo ɗaki jiki shi a sanyaye, koda na duba fuskarshi sai naga hawaye yana zuba daga idanunshi.
Cikin gaggawa na mike tsaye cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba nace abokina meyafaru naga kana zubar da hawaye?
Buɗar bakinshi sai naji yace ("Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un") sai da ya maimaita haka har sau ukku, sannan ya kalleni yace to shikenan burinka ya cika meenat tayi hadari a hanyarta ta zuwa adamawa kuma ba wanda ya rayu a cikinsu domin motar konewa tayi kurmus cikin yanayin kiɗimewa nace "abokina wannanfa ba wasa bane domin Allan daya haliccemu ya hanemu da yima junanmu irin wannan wasan nan take musa yai min nuni da ƙofa haɗe da cewa "ga hanya nan sai ka bita daga nan har zuwa ƙofar gidansu domin tabbatar ma kunnuwanka gaskiyar abun da ya faru.
Cikin gaggawa nayi waje ba'a hayyacina ba da zuwana ƙofargidan su meenat nan take na yanke jiki na faɗi ƙasa domin abunda musa ya sanar dani gaskiya ne.
=> 6
Haƙiƙa nayi kukan ido haɗe da na zuci a sakamakon rashin meenat. 
Tun daga wannan lokacin sai damuwa mai matsanancin zafi ta ziyarci zuciyata.
Haka dai na kammala karatuna a daddafe. 
Bayan na koma gida sai na fara ƙoƙarin ɓatar da damuwar da take ɓoye a zuciyata.
A ƙarshema sai zaman gida ya gagareni saboda na riga na saba da zaman cikin garin zaria wato gidansu abokina musa kenan domin gidansu musa tamkar gidane a gareni.
Ba'ayin sati 1 ko 2 ba tare dana ziyarci garin zaria ba.
Kwatsam wata rana bayan munci abinci sai mu fita yawo, dawowarmu kenan sai Allah ya jarabceni da wani irin matsanancin ciwon ciki musa haɗe da iyayenshi gaba ɗaya sun ɗauka bazan rayuba. 
Ƙanwar musa wato hafsat kenan ta zubar da hawaye sosai a dalilin wannan rashin lafiyar tawa. Bayan andawo dani gida daga asibiti muna zaune a falo ranar mahaifin musa yana hutawa bai fita aikiba sai ga hafsat ta dawo daga school, tabbas a wannan lokacin sai da kai na yau matuƙar daurewa a sakamakon wani baƙon al'amarin da nayi a tattare da hafsat "wani kalar murmushi naga tayimin a lokacin dana haɗa ido da ita wanda ni kaina bansan ma'anarshi ba, bayan ta shiga ɗaki ta aje (school bag ɗinta sai tazo ta zauna kusa da mahaifiyarta.
Cikin yanayi irin na shagwaɓa tace "umma yunwa nakeji. 
Buɗar bakin musa sai "yace ke saboda baki da kunya kina nufin ummance zata kawo miki abincin kenan ko? 
Sai mahaifinta yace "kaji yarinyarnan kamar ba itace ta damemu da kuka ba jiya. 
Buɗar bakina sai nace "amma abba meya faru da ita jiyan har ta dameku da kuka. 
Sai yace "saboda rashin lafiyarka mana. 
Koda na kalleta sai naga tayi kas da kanta cikin yanayin kunya sannan ta tashi ta shige ɗaki.
Ganin hakane yasa mahaifiyar musa tace "haba alhaji kaima in banda abunka meye kuma na dawo da abun da ya wuce baya alhalin kuma bakasan abun da yake a tsakaninsu ba.
Tabbas a wannan ranar sai da naji kamar na nutse a ƙasa saboda tsabar kunya domin a zahirin gaskiya ba wani abun da yake a tsakanina da hafsat, saboda hafsat tamkar ƙanwata ta jini na ɗauketa.
Bayan lokacin sallar azahar yayi munyi alwallah zamu tafi masallaci tun a hanya sai naga musa yana ɗauremin fuska bayan an idar da sallah mun dawo ɗaki sai nace da musa "dan Allah musa meka fuskanta a maganar umma da abba? 
Koda ya kalleni sai yace "amma wannan tambayar taka kamar akwai rainin hankali a tattare da ita, saboda wannan abun mamakine ace cikakken masoyi kamarka kokuma ince cikakken mayaudari kamarkane zai tunkari wanda bai taɓa yin soyayya ba da irin wannan tambayar.
Amma bari na baka amsa dai-dai da tambayarka.
Koda ya kalleni sai yace "ni dai tun da nake ban taba yin soyayya da wata ya mace ba amma hakan bazai hanani fuskantar wani abu daga cikin soyayya ba. 
Dan haka amsar tambayarka anan itace kana soyayya da ƙanwata hafsat, kuma ko kaɗan banji daɗin faruwar hakanba. 
Jin haka ne yasa na kalleshi fuskata cike da mamaki haɗe da cewa "haba abokina bai kamata kakirani da mayaudari ba domin ba wata soyayya a tsakanina da ƙanwarka kuma idan kana tunanin ƙaryane kaje ka tambayeta kaji.
Kuma ko kaɗan banyi mamaki ba dan ka kirani da mayaudari saboda abun da ya faru a tsakanina da meenat yayi dai-dai a kirani da mayaudari.
A wannan ranar da yamma lokacin Musa baya gida ina zaune a ƙofar gida sai ga hafsat ta fito daga gida.
Kai tsaye ta tunkaro inda nake da zuwanta bayan tayi sallama sai ta zauna daf dani.
Koda na kalleta sai naga ta danyi murmushi.
Buɗar bakina sai nace hafsat meke faruwa ne? 
Cikin yanayin kunya tace "akwai maganar da nakeson nayi da kai ne kuma maganar tana da muhimmanci a gareni. 
Jin haka ne yasa na gyara zama domin sauraranta.
Nan take hafsat ta bayyana soyayyarta a gareni koda naji wannan kudurin daga bakinta sai nayi murmushi haɗe da cewa "to amma hafsat bakya tunanin hakan zai iya haifar da matsala a tsakanina da yayanki musa? 
Sai ta kalleni fuskarta cike da mamaki tace ai ni a ganina wannan abun alfaharine a gareshi a sakakon samunka da nayi a matsayin wanda zai aureni, domin suma kansu iyayena sun yaba da kyawawan halayenka dan haka banga wani saɓanin da zai iya shiga tsakaninka da yayana ba.
Saboda nasan akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninka da shi, kuma idanma ya nemi rabani da kai shi zai aureni? 
Sai nace " a'a amma naga alamun sabani zai iya shiga tsakanina dashi domin na fara ganin alamun hakan a tattare dashi. 
Sai hafsat tayi shiru na ɗan wani lokaci sannan ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa "shin kana sona sai nayi murmushi nace " toke in banda abunki wazaiki wannan kyakkyawar halittar.... 
Muna cikin wannan maganar sai ga musa ya dawo da zuwanshi sai ya kalli hafsat yace "ke tashi ki shiga gida. 
Ba yadda ta iya haka ta tashi ta shiga gida ganin hakane yasa na miƙe tsaye raina a ɓace nace "musa meyasa bakason kasancewar ƙanwarka a tare dani? 
Sai yace "saboda kai azzalumin mayaudarine. 
Tabbas wannan furucin da musa yamin ba kaɗan ya sosamin rai ba. 
Sai nace "ko kaɗan ban taɓa tunanin zanyi soyayya da ƙanwarka ba, amma a yanzu na fuskanci sona takeyi dan haka banga yadda za'ayi na iya watsi da wannan ƙudirin nata ba. 
Dan haka inason ka buɗe kunnanka kaji abun da zan sanar dakai "azahirin gaskiya kanwarka kyakkyawace kuma ta burgeni tunda har ta iya bayyana soyayyarta a gareni. 
Tun daga wannan ranar sai na samu saɓani da musa amma batun soyayya a tsakanina da ƙanwarshi bata gushe a zuciyata ba.
Tun daga wannan ranar sai na rage zuwa gidansu kuma koda naje gidan to a ranar nake komawa gida.
Koda musa yaga alamun abotarmu tana neman rushewa sai yazo ya sameni har gida ya bani haƙuri a game da abun da ya faru a tsakanina dashi. 
A haka dai muci gaba da abotarmu kuma soyayya a tsakanina da ƙanwarshi sai ƙara ƙarfi take.
Kwatsam wata ranar Wednesday ina zucizucin shiryawa domin zuwa wajan masoyiyata hafsat fitowata daga ɗaki kenan sai mahaifina ya katsemin hanzari ta hanyar cewa karnaje ko ina domin zai aikeni garin JOS wajan kaninshi wato "Alhaji ibrashim kenan" ba yadda na iya haka na aje wannan uzurin nawa bayan nayi wanka na shirya sai na ɗauki hanyar garin jos.
Kimanin shekara 2 kenan rabona da garin jos. Aikon tun kafin nabar cikin garin kano na ɗau alwashin duk wasu gidajen danginmu da suke zaune a garin jos sai na ziyarcesu.
Kwanana biyu a cikin garin jos washe gari da musalin ƙarfe 9:00 na safiya na ɗauki hanyata ta dawowa gida ina cikin tafiya ko nisa banyi ba sai na tuna da wani abokina mai suna Abdul wanda yake zaune a MANGU local gov't nan take nayi kwana shigata garin mangu kenan sai naji alamun ƙishin ruwa yana neman takuramin wanda hakan yasa nayi packing a kusa da wani shago domin sayan pure water fitowar da zanyi sai idanuwana suyi tozali da MEENAT ayayin da ta fito daga wani gida tare da wasu mata ukku.
=> 7
abun da idona ya ganemin tabbas ba ƙarya bane domin meenat nagani da idona duk da cewar kimanin shekara ɗaya kenan rabona da ganin meenat banga inda zata shiga a faɗin duniyar nan ba tare dana ganeta ba.
Nan take fargaba haɗe da kokwanto ya shiga zuciyata, shirin da naga sunyine yasa na fashimci tafiyar da zasuyi bata kusa bace. 
Ganin yadda su tsaya a ƙofar gidane yasa nayi tunanin akwai abun da suke jira.
Duk da cewar nasan meenat ta mutu kai tsaye na tunkaresu kafin na ƙarasa garesu sai naga wata mota tayi packing a daf dasu koda naga sauran sun shiga motar ita kuma meenat tana daga musu hannu sai na fahimci bada ita za'ai wannan tafiyar ba.
Bayan sun tafi har meenat ta juya zata shiga gida saina tari gabanta cikin yanayin mamaki nace "meenat ashe dama kina raye, ba mutuwa kiyi ba? 
Sai tamin wani kallo haɗe da cewa " meenat kuma gaskiya bani bace wadda kake tunani domin ni sunana aisha. 
Buɗar bakina sai nace "haba meenat wai me kike nufine, yanzu kina nufin ba meenat ɗin dana sani bace wadda take zaune a cikin garin Zaria? 
Sai ta girgiza kai sannan ta kalleni tace "nifa ba sunana meenat ba aisha ne sunana kuma bansan wata zaria ba domin nan shine garin da a haifeni kuma wannan gidan da kake gani shene gidan iyayena, kuma dan Allah ka wuce kar wanda zai aure ni ya ganni tare da kai.
Jin haka ne yasa nan take naji ƙirjina ya buga! 
Cikin yanayin mamaki nace "aure kuma? 
Sai ta jinjina kai haɗe da cewa "kwarai kuwa domin zuwa jibi kamar yanzu ananan ana shirye-shiryen aurena da UMAR sannan ta shige gida.
Tun da na baro garin JOS ba inda na tsaya sai a gida.
Da shigata gida ko cikakken 6 minutes ba aiba nayo waje hanyar zaria na ɗauka a kalla hafsat ta kira numbata a dan wannan takin ya fi a ƙirga amma sai dai ta ƙaraci ringing ta yanke domin a gida na mance wayar tawa da isata cikin garin zaria ko wajan abokina musa banje ba kai na tsaye na tasarma gidansu meenat da isata sai nayi kacibus da mahaifinta a mota zai shiga gida.
Shigarshi gida kenan sai nima nabi bayanshi fitowarshi daga mota kenan bayan mun gaisa sai nace "alhaji wajanka nazo da wata magana mai muhimmanci koda yaji wannan furucin nawa sai yace "ah to mushiga ciki mana.
Wannan itace rana ta farko dana taɓa shiga gidansu meenat, da shigarmu sai na taradda mahaifiyarta zaune a falo tabbas meenat tana matuƙar kama da mahaifiyarta.
Bayan mun gaisa sai na kalli mahaifin meenat nace "alhaji ina fatan baka manta wannan fuskar tawa ba.
Sai yace "ai ba yadda za'ai na mantaka ko ba kai ne wanda yata meenat tasa yan sanda su tsare ka ba? 
Sai na jinjina kai haɗe da cewa kwarai kuwa nine. 
Sai yayi murmushi haɗe da cewa "ikon Allah kenan kaga har wanda ya halicceta ya ɗauke kayarshi, domin yau kimanin shekara ɗaya kenan da rasuwarta.
Koda naji haka sai nayi murmushi haɗe da cewa "haƙiƙa maganar da nazo gareku da ita zatayi matuƙar girgizaku.
Sai mahaifin meenat yace "to wannan wace irin maganace da har kake iƙirarin zata girgizamu? 
Koda na kallesu sai nace "Maganar gaskiya meenat ba mutuwa tayi ba domin tana nan a raye amma saidai kuma ina kyautata zaton kwakwalwarta ta ɗan samu matsala ta hanyar mantawa da wasu muhimman abubuwan dasu faru a rayuwarta. 
Jin haka ne yasa nan take su miƙe tsaye fuskokin su cike da mamaki buɗar bakin mahaifiyar meenat sai tace "wannan wace irin maganar banzace kodai kazo ne domin tayar mana da hankali ta hanyar tuna mana da rasuwar yarmu?
Sai nace " hajiya nima kai na sai da na shiga mawuyacin hali a yayin da labarin rasuwar meenat ya iso gareni, amma dan kunƙi amincewa da wannan maganar tawa bazan taɓa ganin laifinkuba saboda baku ganta ido da ido ba.
Dan haka zanso kuyimin uzurin wayewar daren yau nayi maku alƙawarin sai na kaiku har inda take da zama a garin JOS.
Cikin yanayin ruɗewa mahaifin meenat yace "a'a ai basai gari ya waye ba., domin zamu iya ɗaukar hanya a yanzu, kaga idanma mun isa cikin dare ko a hotel sai mu kwana. 
Ba yadda na iya haka mahaifin meenat ya kira direban shi ya kwashemu zuwa garin Jos.
Da misalin ƙarfe 12:00 mun isa garin Jos wanda hakan yasa mu kwana a hotel.
Bayan gari ya waye da misalin ƙarfe 7 na kai su har ƙofar gidan da naga meenat wani karamin yaro na aika domin ya mana sallama da mai gidan.
Bayan yaron ya fito sai ya sanar damu ai mai gidan bayanan bai jima da fita ba.
Allah cikin ikonsa sai ga meenat ta fito daga gidan.
Koda tayi ido biyu da iyayenta cikin yanayin tsoro mai tattare da furgici tace "umma!!! abba!!! Sannan ta yanke jiki ta daɗi ƙasa.
=> 8
tun da nake ban taɓa ganin farin ciki mai sa zubar da hawaye ba, sai a wannan lokacin. 
Ganin hawayen da yake zuba daga idon mahaifan meenat ne yasa nima na zubar da kwalla. 
Bayan an yayyafa mata ruwa ta farfaɗo daga suman da tayi sai ta kalli mahaifiyarta tace umma mekuma ya kawoni nan? 
Sai mahaifiyar meenat ta fashe da kuka haɗe da cewa "meenat bani da amsar wannan tambayar taki. 
Muna cikin wannan halin ne sai ga mai gidan ya dawo. 
Cikin yanayin ɓacin rai ya ƙare mana kallo tun daga sama har ƙasa yace "meye dalilinku na shigomin gida ba tare da izinina ba?
Buɗar bakina sai nace "dan Allah malan kayi haƙuri munsan munyi kuskure amma zamuso kaji dalilinmu na zuwanan kafin ka yanke duk wani hukuncin da kake tunanin zartarwa a garemu.
Sai nace "mun shigo gidanka ne a dalilin meenat. 
Buɗar bakinshi sai yace "wacece kuma meenat? 
Nan take na mai nuni da meenat hade da cewa "wannan da kake gani itace meenat waɗannan kuma da kake gani iyayanta ne. 
Jin hakane yasa yai shiru na ɗan wani lokaci sannan daga bisani sai ya jinjina kai haɗe da cewa "ikon Allah kenan, hakika wannan babbar maganace.
Bayan mun shiga ciki anyi mana shimfiɗa mun zauna, gani ga meenat ga kuma iyayenta sai maigidan yace "zan so naji bayanin yadda ai hakan ta faru daga bakinku.
Buɗar bakin meenat sai tace "A'a nice wadda ya kamata tayi bayanin yadda wannan al'amarin ya faru domin a yanzu zan iya tuna komai.
 Sai tace "Ni kadaice yarinyar da mahaifina ya haifa. 
Hakane yasa yake matuƙar nuna kulawarshi a gareni domin bayason ganin ɓacin rai na.
Duk wata buƙatar da zata tasomin cikin gaggawa mahaifina yake magance min ita.
Ba yadda mahaifiyata bata yiba wajan ganin ya rage abubuwan da yake min saboda gudun kar hakan ya haifar da matsala a gareni.
Shi kuma a duk lokacin da naji haka daga bakin mahaifiyata sai yace "to menene amfanin dukiyar tashi idan wadda ya haifa bataji daɗi a lokacin da nake rayeba.
Haka dai al'amura suci gaba da kasancewa a tsakanina da mahaifina.
Ko kaɗan bayason nayi nesa dashi.
Kwatsam wata ranar asabar ranar zai halarci wani meeting a garin abuja.
Musalin ƙarfe 8:00 na safiya, ya shiga mota kenan sai na tsayar dashi.
Bayan na ƙarasa gareshi sai nace " dama abba bikin wata ƙawata nakeson zuwa a jahar adamawa? 
Tunda nake da mahaifina ban taɓa tun kararshi da wata buƙatar da ta ɓata mai rai ba, sai a wannan lokacin.
Cikin yanayin mamaki yace "what! meenat kinsan me kika kaɗa kuwa, adamawafa kice?
Sai na jinjina kai haɗe da cewa "eh Abba.
Rainshi a ɓace yace to bazai yiwu ba.
Jin haka ne yasa nan take na juya na nufi falo ina kuka.
Koda yaga haka gaba ɗaya sai hankalinshi ya tashi saboda bayason ganin ɓacin rai na wanda hakan yasa ya fito daga mota yazo gareni.
Da shigowarshi falon sai ya sameni kwance ina kuka. 
Buɗar bakinshi sai yace "meenat kinsanfa ko kaɗan banason ganin ɓacin ranki. 
Cikin yanayin kuka nace "to Abba indai bakason ganin ɓacin rai na to ka barni nayi wannan tafiyar.
Jin haka ne yasa yace "to shikenan amma yaushene zakiyi tafiyar? 
Buɗar bakina sai nace "yau nakeso nayi tafiyar saboda bikin na gobene.
Sai yace "khai amma meenan wannan wane irin shirmene ai tun ana irin saura 1 week ya dace ki sanar dani, amma tun da kinnuna kina buƙatar zuwa ai bazan iya hanaki ba.
Sai ya buɗe ɗakin shi ya ɗakko 100k ya bani.
Buɗar bakina sai nace "a'a Abba ai akwai kuɗi a account ɗina kawai ka barsu.
Sai yace to shikenan Allah ya kaiki lafiya ya kuma dawo dake lafiya. 
A wannan ranar sai da mahaifiyata ta nuna tsantsar ɓacin ranta a dalilin tafiyar da zanyi, kawai dan ba yadda zatayi ne wajan ganin ta kawo sular fasa tafiyar tawa.
Bayan na kammala duk wani shirina tsaf sai nayi bankwana da mahaifiyata.
Da fitowata sai nasa jakata a mota sannan na shiga tayiwa motar key amma sai motar taƙi tashi.
Koda naga alamun rana zatayi sai naje wajan mahaifiyata domin ta bani aran motarta amma sai ta hanani haɗe da cewa "aiko sai dai ki fasa tafiyar saboda banga daliln da zaisa na ɗauki motata na baki ba, tunda ke bakya jin magana. 
Koda naga haka sai na yanke shawarar zuwa tashar mota domin na hau motar haya saboda ni dai a rai na bazan iya fasa wannan tafiyar ba.
Fitowata kenan sai na haɗu da wata ƙawata mai suna Ummi. 
Sai Ummi tace "meenat ina kuma zaki, domin na tabbata wannan tafiyar dai bata kusa bace? 
Rai na a ɓace nace "Kinga Ummi rabudani kawai yau rai na a ɓace yake wannan fitowar da kiga nayi YOLA zani, kuma gashi motar tawa taƙi tashi gashi kuma abba ya tafi abuja da tashi motar naje wajan umma kuma domin tabani tata motar amma ta hanani.
Dan haka wannan fitowar da kiga nayi tasha zani domin hawa motar haya.
Sai ummi tayi dariya haɗe da cewa "meenat yau kuma kece zaki hau motar haya? amma gaskiya kin kwafsa wallahi.
Kuma kinga fitowata daga gida kenan gashi zainab ta ɗauki tawa motar kinga da sai ki tafi da ita, amma bari na kirata naji ko ba nisa tayi ba.
Haka ummi ta kira zainab akallah yakai sau 10 amma sai zainab taƙi amsa kiran.
Koda naga haka sai nace kinga muje ki raka ni kawai na hau mota saboda banason rana tamin.
Muna cikin tafiya sai ummi tace "amma meenat duk da cewar bansan mezai kaiki adamawa ba, mezai hana ki ɗaga wannan tafiyar taki sai gobe.
Jin haka ne yasa nayi dariya haɗe da cewa "haba ummi tarefa muyi karatu basai kinbi ta hanyar low ba, kawai ki fito ƙiri da muzu kice kinason kiji inda zani sai ummi tayi dariya haɗe da cewa "khai amma kawata kinada wayaufa to inason a sanar dani dalilin da zaisa ayi wannan tafiyar.
Sai nace "to ai bazakiji ba domin ba wanda nakeson yasan taka maiman inda zani.
Da isarmu tasha ko cikakkun mintina 10 ba aiba sai motar da na shiga ta tashi.
Bayan munyi nisa sai muyi accident wanda hakan yasa na manta da komai.
Sai mahaifin meenat yace "a daran da haɗarin ya faru yayan ummi da ta rakaki ki hau mota yazo ya sanar damu abun da ya faru dake.
Sannan mahaifin meenat ya kalli mai gidan haɗe da cewa to kaji yadda abun ya faru. 
Sai mai gidan yace haƙiƙa wata mota ta ƙone a ranar da ɗana umar yazo mana da wannan yarinyar to amma mu bamu da masaniyar itama tana ɗaya daga cikin fasinjojin motar saboda a bayan gari al'amarin ya faru kuma a wannan lokacin dare yayi kuma shi ɗana umar direban motane.
A yadda ya sanar damu yace "cikin dare yana kan hanyarshi ta dawowa gida sai yayi kaciɓus da wannan yarinyar a hanya tana tafiya batama san inda take dosaba da yake umar mutunne bamai tsoroba sai yayi packing ɗin motarshi a gefen hanya kai tsaye ya tunkareta koda ya karasa gareta sai ya fuskanci ba'a hayyacinta take ba.
Sai ya riko hannunta zuwa inda motarshi take, cikin dare umar ya tasheni daga bacci bayan na fito sai naga mace zaune a ƙasa duk jikinta ya ɓaci da jini. 
Buɗar bakina sai nace umar wannan kuma wacece sai yamin bayanin komai dangane da yadda haduwarshi da ita ta kasance bayan gari ya waye sai muga alamun hankalinta ya fara dawowa gareta amma saidai jikinta akwai wasu raunuka amma ba masu yawa ba.
A yayin da mu buƙaci sanin sunanta sai tace "aisha ne sunanta. 
Damu tambayeta batun iyayenta kuma cewa tayi sun mutu.
Batun garin da take kuma bamu samu wannan amsarba, domin yawo da hankali ta riƙa yi mana "tace taraba tace kaduna tace kano kai har bauchi ma saida ta ambata a matsayin sunan garinsu wanda hakan yasa gaba ɗaya mu kasa sanin takamaiman sunan garin da iyayenta suke.
A wannan lokacin sai mu fahimci hankalintane bai gama dawowa dai-dai ba abu kamar wasa har tsawon sati ɗaya ba wani chanji a tattare da ita a wannan lokacin gani ga umar ga kuma mahaifiyarshi sai na basu shawarar meƙawa jami'an yan sanda ita.
To amma duk inda mu kaita sai suƙi karɓarta domin cewa suke mu kaita gidan mahaukata.
Haka dai mu ɗauki ƙudirin ci gaba da kasancewa a tare da ita har lokacin da Allah zai bata lafiya gashi yau kimanin shekara ɗaya kenan.
A kwana a tashi har Allah ya dasa soyayya a tsakaninta da ɗana Umar.
Domin yau saura kwana ɗaya auranta da Umar ashe dai rabon hankalin ta zai dawo gareta ne kafin aurenta. 
=> 9
Sai meenat tace "nayi danasanin ƙaryar da nayima iyayena. 
Sai ta kallesu tace "dan Allah abba kuyi haƙuri abisa ƙaryar da nayi muku akan batun zuwana adamawa, a zahirin gaskiya bani da wata ƙawa a damawa a taƙaicema bansan kowa ba a adamawa kawai ruɗin soyayya ne ya rinjayi zuciyata har na ƙudiri niyar zuwa gareshi ba tare dana taba ganinshi a zahiri ba. 
Sai mahaifiyar meenat tace " amma gaskiya meenat a matsayinmu na iyayenki baki kyautata mana ba, kuma bari kiji idanma wayewa kike taƙama da ita to batai miki amfani ba domin iliminki bashi da wani amfani.
To amma bazanga laifinki ba domin wannan kuskuran na mahaifinki ne.
Koda naji haka sai nace "dan Allah kukyale wannan maganar saboda a wannan ranarce ya dace kununa farin cikinku abisa ganin yarku da kuyi a raye.
Sai mahaifin meenat yace "haƙiƙa ka cancanci godiya a garemu.
Saboda bakayi duba da irin wulaƙancin da meenat tayima a baya ba wanda hakan yasa ka bimu har gida domin sanar damu maganar da tasamu a farin ciki.
Sannan mahaifin meenat ya kalleta yace "meenat wannan shine dalilin dayasa nake nisantaki da yima mutane wulaƙanci, yau gashi wanda kisa jami'an yan sanda su kama shine ya bimu har gida domin sanar damu cewar kina raye. 
Sai ta kalleni tace " dan Allah kayafemin laifin da nayi ma domin nasan ban kyautaba.
Buɗar bakina sai nace "a'a meenat baki aikata laifin komai a gareni ba saboda gaba ɗaya wannan al'amarin ya farune a dalilina.
Sannan na kalli meenat nace meenat nacutar dake na kuma zalinceki.
Nanfa meenat haɗe da iyayenta su kalleni fuskarsu cike da mamaki. 
Buɗar bakin meenat sai tace "dan Allah ko zan iya sanin laifin daka aikatamin? 
Sai nace " meenat zan sanar dake komai a gaban iyayenki kuma dan Allah zanso a yankemin hukunci dai-dai da laifin dana aikata.
Buɗar bakina sai nace "nasan zakiyi matuƙar mamakin jin wannan maganar da zan sanar dake a yanzu. 
Nan take na shiga yi masu bayani kamar haka.
•Ni mazaunin garin kaduna ne Hayin Rigasa itace unguwar da nake zaune karatu ne ya kaini Zaria domin a canne na hadu da wani aboki mai suna Musa.
Musa mutunne mai mutunci ga sanin ya kamata hakane yasa abotarmu tayi ƙarfi har nake gudanar da dukkanin wasu harkokina a gidansu kwatsam wata ranar Monday sai Allah ya kai idona gareki kuma naji kinyi matuƙar burgeni wanda hakan yasa na buƙaci abokin nawa ya min rakiya zuwa gareki domin bayyana soyayyata a gareki, amma sai yaƙi rakani saboda yana tunanin cewar bazaki amince da batun soyayyata ba. 
Tun daga wannan lokacin sai na ƙudiri niyar gabatar da kai na a gareki a matsayin masoyi.
Bayan musa ya tabbatar min cewar a school ɗin da muke karatu kema kike gudanar da naki karatun sai na fara bibiyarki, duk da cewar ba department ɗinmu ɗaya ba.
Hakan bai hanani zuwa inda kike ba musamman nake shigo class ɗinku na zauna badan komai ba sai dan na riƙa kallon kyakkyawar fuskarki da kuma sauraron daɗaɗan kalamanki hakane yasa nakaranci wasu kaɗan daga halayenki.
A cikin halayenki na fuskanci kamar akwai wulaƙanci haɗe da rashin mutunci hakane yasa na gane bakya shakkar zartar da ko wane irin rashin mutunci a kan komawaye.
Tabbas a lokacin dana fuskanci hakan ni kai na sai da nayi fargabar tunkararki saboda ba ɗan adam ɗin da zaiso a wulaƙantashi hakane yasa na yanke shawarar rubuta miki wasika. 
Bayan na kammala rubuta wasiƙar sai na fara nazarin hanyar da zanbi dan ganin wasiƙar ta isa gareki ba tare da kinyi ido biyu dani ba.
Kuma gashi banason naba wani wasiƙar domin ya isar da ita a gareki.
Ina sane nazo gareki da sunan arn biro na tambayeki aran biro ne saboda nasan zaki iya neman wulaƙantani wanda hakan zai bani damar watsar da littattafan da suke hannunki.
Sai kuwa nayi sa'a a wannan lokacin ki furtamin kalmar da tayi matuƙar ƙonamin rai hakane ya bani damar kaɓar da littattafan dake hannun naki bayan sunyi watsa-watsa a kasa sai na saki wasiƙar tawa a wajan ba tare da kowa ya gani ba.
Lokacin da ƙawarki Aisha zata kwashe littattafan naki sai nayi sa'a ta haɗa da wasiƙar dana rubuta da yake nasa numbata a ƙarshen wasiƙar sai nayi sa'a kiyi calling ɗina tun daga wannan lokacin sai na fara bin hanyoyin dasu dace wajan ganin soyayyata ta samu karɓuwa a gareki.
A wannan lokacin sai da nayi kokwanto akan cewar anya soyayyar da kike nunamin ta gaskiyace kuwa.
Gaba ɗaya sai kokwanto ya baibaye zuciyata fargabar haɗuwa dakene yasa nayi miki ƙaryar ni a jahar adamawa nake nuna.
Zumuɗin son ganina dakiyi ne yasa na ɗaukar miki alƙawarin zuwa gareki. 
A ranar da ta kasance itace rana ta ƙarshe a cikin kwanakin dana ɗaukar miki alƙawarin zanzo inda kike sai na miki ƙaryar cewar bani da lafiya badan komai ba sai dan gudun kar ƙaryata ta kare.
Alokacin da kiji batun rashin lafiya a tattare dani sai naji kin tambayeni address ɗin inda nake da zama.
Nan take na turo miki address ɗin wani abokina wanda yake zaune a can. 
Saboda ko kaɗan banyi tunanin zaki iya ɗaukar hanya tun daga zaria zuwa Adamawa ba.
A wannan lokacin sai da abokina musa ya nuna ɓacin ranshi a bisa tura miki address ɗin da nayi domin ba yadda baiyi dani ba domin na sanar dake gaskiyar abun da yake faruwa amma naki.
Saboda ni a nawa tunanin ba zuwa zakiyi ba kwatsam washe gari da yamma sai musa yazomin da labarin cewar kinyi haɗari a hanyarki ta zuwa adamawa kuma jama'ar ciki basu rayuba.
Tabbas alokacin da wannan labarin ya iso gareni sai da na shiga mawuyacin hali domin har saida a kwantar dani a sibiti.
Bayan na kammala karatuna na koma gida sai na fara ƙoƙarin rage tunane-tunanenki.
Kwatsam ranar talatar da ta wuce sai abbana ya aikoni wannan garin na jos wajan wani ƙaninshi kwanana biyu a wannan garin. Ban tashi tunawa da wani abokina ba sai a ranar da zan koma gida ban nuna gajiyawa ba haka na sake ɗaukar hanyar gidansu inda yake saboda mun daɗe bamu haɗu ba bayan na shigo wannan unguwar sai nayi packing a gefen wani shagon da yake kusa da wannan gidan domin siyan pure water.
Fitowar da zanyi daga mota sai naga meenat ta fito daga nan gidan ita da wasu mata su ukku ruwan da banshaba kenan. 
Bayan matan sun shiga mota sun tafi sai nazo gareki.
Amma sai ki mukamin alamun sam baki Sanni ba.
Ganin hakane yasa nayi gaggawar sanar da iyayenki kuma gashi Allah cikin ikonshi sun tbbatar da maganata gaskiyace.
Saboda a lokacin da naje musu da wannan batun ƙaryatani su nemi yi.
Sannan na kalli iyayen meenat nace nasan na aikata laifi mafi muni a gareku dan haka zanso ku zartar da duk wani hukuncin daya dace a gareni.
=> 10
Ko kaɗan banyi mamakin jin saukar mari a fuskata ba.
Dago kan da zanyi sai mahaifin meenat ya sake ɗaga hannu zai mareni sai meenat ta tare ba ta bari ya sake marina ba. 
Hada idon da zanyi da ita sai naga ta fashe da kuka. 
Buɗar bakin meenat sai tace "abba tun kafin na ganshi ido da ido zuciyata ta kamu da soyayyarshi dan haka bazan iya jurar ganin ana wulaƙantashi a gaban idona ba saboda bashi da laifi a game da abun da ya aikata.
Sannan ta ƙara da cewa "tabbas nasan akwai wulaƙanci da rashin mutunci a tattare da rayuwata kuma ba komai ne ya haifar da haka a game da ni ba sai dan ganin iyayena masu kuɗi ne, kuma suna biyamin dukkan wasu buƙatuna.
Hakane yasa bana shakkar wulaƙanta duk wanda yazo gareni da batun soyayya.
Dan haka bashi da laifi dan yabi duk wata hanyar da yasan zatasa yacimma burinshi a kaina ba tare da wulaƙancina ya shafi rayuwarshi ba.
Sannan meenat ta ƙara da cewa "dan Allah abba kuɗauki wannan al'amarin a matsayin ƙaddara, kuma ku barni na aureshi.
Buɗar bakin mahaifiyar meenat sai tace "ai idan har kiga kin aureshi to sai dai idan bana raye, dan haka tun wuri gwara kiyi gaggawar cire shi daga zuciyarki saboda usman ne ya cancanta ya zama mijinki.
Meenat ta buɗa baki zatayi magana sai na dakatar da ita nace "A'a meenat karki sake kiyi jayayya da mahaifanki, kawai kibi umarninsu nidai fatana Allah ya haɗaki da miji nagari wanda zai baki cikakkiyar kulawa na tsawon rayuwarki.
Hawayen da naga yana zuba daga idanun meenat ne yasa na ƙara tausaya mata.
A wannan ranar nayi bankwana dasu.
Har na dawo gida ban dai na tunanin meenat ba tabbas a wannan lokacin nashiga damuwa mafi tsanani dana duba wayata Miss calls din hafsat 34 na gani da kuma message guda daya. Cewa tayi; rashin amsa wayarka a gareni ba ƙaramin tashin hankali zai iya jawo ma rayuwata ba, sanin kankane ako da yaushe kunnuwana suna buƙatar jin muryarka dan Allah idan laifi nayi zanso kasanar dani domin nayi gaggawar neman yafiya a gareka.
Bayan na karanta message ɗin nan take nayi calling.. ɗinta amma bata amsa ba koda na kirata har sau biyu ba tare da naji ta amsa ba sai nayi tunanin ko ba ta kusa da wayar ne.
Jim kaɗan da aje wayar sai naji ƙarar shigowar massage a karo na biyu kenan.
Cewa tayi " banƙi amsa kiranka domin na wulaƙantaka ba, kawai ina tsoran jin laifin dana aikatama ne.
Zanso ka fara cewa ka yafemin ta hanyar aikomin da saƙon messege kafin kasanar dani laifin dana aikatama a yayin da na amsa kiranka.
Kuma inason kasan da cewar ni mai ƙaunarkace ako da yaushe.
Murmushi nayi a yayin dana karanta wannan text ɗin. 
Sai nima na tura mata da message kamar haka;
•Ameencin Allah ya ƙara tabbata ga ma'abociyar iya sarrafa kalamai masu yaye duk wata damuwar data halarci zuciyata. 
Azahirin gaskiya hafsat baki aikata wani laifi a gareni ba. Kuma batun soyayyar da take a tsakaninmu tananan a zuciyata domin bana tunanin cewar zata samu wata ƙofar fita daga zuciyata. Ina tare da ke zan kuma cigaba da kasancewa a tare da ke cikin dare da rana.
Ko cikakken 2 minutes da tura saƙon ba aiba sai calling.. Ɗinta ya shigo wayata.
Cikin gaggawa na amsa kiran, murmushinta ne ya fara sauka a kunnena sannan tace "yayana ko kasan irin mawuyacin halin da na shiga a sanadin rashin jin muryarka da nayi a daranji kuwa? 
Aduk lokacin da na kiraka sai dai wayarka ta ƙaraci ringing.. ta yanke ba tare da an naji an amsa kiran ba, alhalin kasan ina kwana na tashi cikin tinanin ka saboda kaine farin cikina wanda nakejin muryarsa na samu natsuwa ako wane lokaci, wallahi ji nake kamar a ɗaura aure na dakai a yau.
Jin haka ne yasa nima nayi murmushi haɗe da cewa "hafsat kin kawo haske a cikin rayuwata, kin wadata zuciyata da farin-ciki, kin kore dukkan wata damuwa daga zuciyata da makami mafi kaifi zan so na kasance cikin kallon fuskar ki a dukkan lokacin da kike murmushi, tabbas ke kyakkyawa ce, ina godiya a bisa kulawar da kike bani, ina son ki saboda kyawawan halayanki domin ba batun yaudara ko ha'inci a tsakanina dake. Dan haka nayi miki alƙawarin daga ke ba ƙari kema zanso ki riƙemin wannan alƙawarin. 
Cikin yanayin sanyaya murya hafsat tace "amma yayana duk da cewar akwai banbancin shekaru a tsakanina da kai sai naga kamar wannan alƙawarin daka ɗaukar min yayi nauyi sosai. 
Sai nace "bana tunanin wannan alƙawarin zai iya canzawa daga zuciyata. 
Sai tace "to dan Allah ko zan iya sanin dalilin da yasa ka ɗaukarmin wannan alkawarin? 
Sai nayi shiru na ɗan wani lokaci zuwa can sai nace "hafsat kinsan meenat yar gidan Alhaji ibrahim wadda suke zaune a unguwarku??
Sai tace "kana nufin meenat wadda ta daɗe da rasuwa kenan? 
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "a'a meenat ba mutuwa tayi ba tananan da ranta. 
Nan take hafsat tayi matuƙar mamakin jin wannan furucin da nayi. 
Daga busani kuma sai ta nemi na bata labarin yadda ai har nasan meenat ba mutuwa tayi ba.
=> 11
Koda na sanar da hafsat duk yanda al'amarin ya kasance sai tayi matuƙar mamakin jin abun da ya faru a tsakanina da meenat. 
Tun daga wannan lokacin sai hafsat ta ƙuduri niyar maye gurbin meenat a zuciyata, badan komai ba sai dan buƙatar na daina tunawa da meenat.
Hafsat tana iya bakin ƙoƙarin ta wajan kawar da duk wani ɓacin ran da ya halarci zuciyata
Bazan iya iyakance adadin wayar da mukeyi a ko wace rana ba.
Ina matuƙar jin daɗin karanta text ɗinta saboda daɗaɗan kalamata sun zarce na iya musaltasu.
Aduk ranar dana halarci gidansu hafsat batacin abinci sai tare dani.
Tun ina nuna jin kunya har nagaji na daina. 
Tun kafin soyayya ta shiga tsakaninmu hafsat ta gane lokacin kwantawa ta bacci.
Duk da cewar bama kusa da juna karfe 10:30 tanayi hafsat zatayi calling.. Dina a waya.
Da zaran na amsa kiran cewa take "yayana lokacin bacci yayi muje mukwanta domin rushinmu ya huta.
Idan kuma takirani a lokacin da ina wani aikin ko kuma bana gida to ba yadda za'ai ta kwanta harsai lokacin kwanciyata yayi, sai dai ko baccin ya saceta ba tare da sanin taba.
Kwatsam wata ranar alhamis ina gida sai a kira wayata da wata baƙuwar number, koda na amsa kiran sai naji muryar wata mace wadda ni kaina bansantaba, 
Furucin da naji tayine ya jefa zuciyata a cikin tsoro haɗe da fargaba.
Domin bayan na amsa sallamar da naji tayi sai tace "dan Allah na taimaka naje (ALMADINA HOSPITAL) dake garin zaria yanzu yanzu sannan ta yanke wayar.
Jin wannan furucin ba kaɗan ya jefa zuciyata a ruɗani ba.
Kai tsaye na shiga dakin yayata MARYAM da shigata sai na sameta kwance a gado tana bacci koda nayi ido biyu da key ɗin motarta nan take nayi awan gaba dashi ba tare dana nemi izinin ta ba, saboda nasan idan nace ta aramin motar ba yadda za ai tabani.
Bayan na samu nasarar daukar motar cikin gaggawa na ɗauki hanyar zaria.
To ashe zuwana zaria a wannan lokacin ba karamin tashin hankali zai zamemin ba.
Shigata asibitin kenan sai naji ƙirjina yai wata irin bugawa a sakamakon ganin iyayen meenat da nayi.
Cikin sauri aisha ƙawar meenat tazo gareni.
Fuskata cike da yanayi irin na fargaba nace "Aisha dan Allah ki sanar dani abun da yake faruwa? 
Buɗar bakin ta sai tace "dan Allah ka taimaki rayuwar meenat. 
Domin a yanzu haka meenat tana kwance a gadan asibiti, duk da cewar munsan Allan da ya haliccemune yake da ikon cire wannan matsanancin ciwon da yake addabar rayuwar meenat hakan bazaisa mu kasa neman taimakon kaba, saboda zata iya yiwuwa ta sularka ne zata iya samun lafiya domin komai yana da dalili. 
Koda nayi ido biyu da meenat ba kaɗan na tausaya mata ba.
A wannan lokacin sai duk ilahirin jikina ya mutu a dalilin ganin mawuyacin halin da meenat ke ciki.
Durkusawata kenan a gaban meenat sai naji ta rike hannuna cikin yanayi irin na wahala hawaye yana zuba daga idanunta tace "yayana idan babu kai a tare dani bazan iya ci gaba da rayuwa ba, saboda jin daɗina haɗe da walwalata duk sun ta'alaƙa ne a gareka. kai ne kayi sanadin canza munanan halayena.
Sannan ta ƙara da cewa "dan Allah ka manta da duk wani cin mutuncin da iyayena suyima domin ka dawo gareni.
Saboda suma kansu iyayan nawa sungane sun aikata kuskure kuma sunyi nadama a game da abun da su aikata a gareka.
Wannan taimakon da meenat ta nema a gareni ba kaɗan yasa ƙwaƙwalwata ta ɗau zafi ba, saboda akwai alƙawarin dana ɗaukarma hafsat kuma wannan alƙawarin bazai taɓa karyuwa a gareni ba.
Ɗago kan da zanyi sai meenat taga hawaye yana zuba daga idanuwana.
Duk da irin rashin lafiyar da take damun meenat hakan bai hanata share hawayen dake fuskata ba.
=> 12
Buɗar bakin meenat sai tace "yayana meyasa kake zubar da hawaye a lokacin da na nemi wannan taimakon a gareka? 
Sai na kalleta cikin yanayin tausayawa haɗe da cewa "meenat ko kaɗan ban taɓa tunanin zanyi danasanin samun nasarar dasa soyayyata a zuciyarki ba, tabbas na tafka babban kuskure a rayuwata kuma na cancanci a kirani da gawur taccen mayaudari, wanda ya kasance mugu, kuma azzalumi. 
Jin haka ne yasa meenat ta kalleni fuskarta cike da mamakin jin yadda na kira kaina da irin waɗannan munanan halayan. 
Cikin yanayin kuka muryar meenat tana rawa tace "subhanallahi, yayana meye dalilinka na danganta kanka da irun wadannan munanan halayen? 
Duk da cewar iyayen meenat sunajin duk maganar da mukeyi hakan bai hanani furta abun da yake raina ba. 
Buɗar bakina sai nace "na furta hakane saboda bazan iya cika miki wannan burin naki ba. 
Koda meenat taji wannan furucin daga bakina nan take naji ta kwalla kara sannan tayi wata irin ajiyar zuciya meenat su rufi zuwa gareta! "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" ga meenat dai a kwance amma babu alamun rai a tattare da ita. 
Nanfa mahaifiyar meenat haɗe da sauran danginta su fashe da kuka suna sallallami.
Ga mahaifin meenat kuma a gefe baice komai ba.
Nan take mahaifin nata ya ciro waya daga aljihu ya kira jami'an yan sanda.
Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga yan sanda sun bayyana a asibitin.
 An sani a mota kenan za'a wuce dani station sai meenat ta farfaɗo daga dogon suman da tayi cikin gaggawa likitan da ke kula da lafiyarta ya fito a gaggauce ya dakatar da batun tafiya dani.
Tun da nake ban taba ganin likitan daya zubar da hawayenshi akan rashin lafiyar wani ba sai a wannan lokacin, cikin yanayin tausayawa yace dani "dan Allah kataimaki rayuwar waccan yarinyar domin a yanzu haka ba wani agajin da take buƙata wanda ya wuce amincewarka a game da batun soyayyar da take tsakanin ka da ita. 
Cikin yanayin mamaki haɗe da ruɗani nace "doctor meenat ba mutuwa tayi ba kenan?
Nan take ya dafa kafaɗata haɗe da cewa "dogon suma tayi. 
Cikin gaggawa muje gareta koda naga eh lallai ba mutuwar tayi ba, nan take na furta cewar "meenat ina sonki kuma ina ƙaunarki dan haka na yadda na karya alƙawarin dana ɗauka domin ceton rayuwarki.
Saboda mawuyacin halin da take ciki gaba daya sai ta kasa buɗa bakinta domin yin magana hannu naga tana mikomin alamun tanason naje gareta da zuwana sai na zauna daf da ita a gefen gadon da take kwance haka ta kama hannuna ta damke har sai da ledar ruwan da'a samata ta ƙare.
A wannan lokacin sai da na kwashi tsawon awa 2 da rabi zaune a kusa da meenat ba tare da ta saki hannuna ba. 
Zuwacan sai ta buɗe idanta a gigice! 
Cikin yanayin sanyin murya tace "yayana sanin kankane wannan rashin lafiyar tawa ta samo asaline daga gareka, kuma sanin kankane maganin wannan cutar tawa a hannunka Allah ya damƙashi, a yanzu haka bakaji irin zafin da nakeji a cikin ƙirjina ba. 
Dan Allah..... Sai na dakatar da ita ban bari ta ƙarasa furta abun da take son furtawa ba.
Sai nace "meenat daga yau babu batun roƙo a tsakaninmu domin mun riga mun zama daya. Cikin yanayin farin ciki meenat ta kalleni tace "kaine cikon burin rayuwata daɗaɗan kalamankane suyi silar ƙulla alaƙar soyayyata da kai dan Allah karka bari wata kalmar rabuwa ta sake shiga tsakaninmu,.
Saboda kalmar rabuwa itace kalma mafi munin ji a wajan masoya irin mu. 
A yayin da muke cikin magana sai naji kira ya shigo wayata jin haka ne yasa zuciyata a cikin ruɗani tun kafin na duba wanda ke calling!! Ɗina a zuciyata nace Allah yasa dai ba hafsat bace.
Jinayi ƙirjina ya buga a yayin da idona yaga sunan hafsat a screen ɗin wayata. 
Koda meenat taga naƙi amsa kiran sai tace "ka amsa kiran mana. 
Jin haka ne yasa na kalleta haɗe da cewa "meenat a tsakanina dake ba wani abun da zan iya boye miki kamar yadda itama hafsat ba wani abun da zan iya boye mata, dan haka a yaune zan bayyana miki dalilin da yasa kiji ɗazu na nuna ƙin amincewata a game da batun ci gaba da kasancewarmu a tare. 
Sai na kalleta nace "meenat tun daga lokacin da iyayanki su nuna ƙin amincewarsu da ni a tare da ke sai da na shiga damuwa sosai gaba ɗaya ma sai da naji na tsani soyayya.
Kwatsam sai Allah ya haɗani da wata yarinya mai suna hafsat domin zata iya yiwuwa kema kinsanta saboda itace ƙanwar musan da na baki labarin yaƙi rakani wajanki domin neman soyayyarki tun a wancan lokacin gidansu yana a unguwar da kuke da zama sunan mahaifinta alhaji hamisu.
Abun da ya faru a tsakanina dake ne yasa musa ya nuna matsanancin ɓacin ranshi a lokacin da ya gano cewar soyayyace take niyar shiga tsakanina da kanwarshi. 
Saboda shi a nashi tunanin yaudarar ƙanwarshi kawai zanyi kamar yadda mafi yawancin mutane suke tunanin yaudarar ki nayi wanda hakan ya jawo sular rasa ranki kafin a gane cewar kina raye baki mutuba. 
Tun kafin soyayyata da ita tayi ƙarfi hafsat ta lashi takobin ba mahaluƙin da ya isa ya kawo tsaikon da zaisa ta rabu dani, tun yayanta musa yana nuna matsanancin ɓacin ranshi a dalilin soyayyar da muke nuna ma junanmu har ya gaji ya daina hafsat ta nunamin matsananciyar soyayya fiye da tunanina jin daɗin haka ne yasa na ɗaukar mata alƙawarin ba abun da zai rabani da ita kuma daga ita ba batun ƙari ma'ana bazan yi mata kishiya ba dan haka wannan kiran da kiga ya shigo wayata ba wata bace illah hafsat.
=> 13
Koda meenat taji duk bayanin abun da ya faru a tsakanina da hafsat. Cikin yanayin sanyin jiki ta ɗago kai ta kalleni, buɗar bakinta sai tace "yayana meyasa ka karya mata wannan alƙawarin daka ɗaukar mata? 
Sai nima na kalleta nace "meenat meyasa kike neman rasa rayuwarki akaina? 
Sai tace "ai nasan kafi kowa sanin dalilin faruwar haka domin ba abun da bazan iya aikatawa a game da soyayyar ka ba. 
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "na karya alƙawarin dana ɗaukarma hafsat ne saboda soyayyar da naga kin nuna akaina badan komaiba sai dan buƙatar ceton rayuwarki, kinga ai banyi laifi ba ko? 
Sai tayi murmushi sannan haɗe da cewa "tabbas bakayi laifiba, amma mezai hana ka auremu duka biyun domin na tabbata itama hafsat tana matuƙar sonka?
Muna cikin wannan maganar sai kiran yayata maryam ya shigo wayata.
Koda na amsa kiran sai naji tace "kayi gaggawar dawomin da motata idan ba hakaba ranka sai yayi mugun ɓaci.
Tun a hanyata ta komawa gida naketa nazarin hanyar da zan ɓulloma hafsat wajan ganin cewar ta fuskanci halin da nake ciki yawan tunanin da yai ma zuciyata yawane yasa na buge wani mai mashin i, amma Allah cikin ikonsa Abun a iya motar da nake tuƙawa ya tsaya, sai kuma danjojin mashin ɗin guda biyu dasu fashe.
A wannan ranar daƙyar 7 thousands ta rabani da mai mashin ɗin bayan na ƙarasa gida fitowata daga motar kenan sai jinayi maryam ta ɗaukeni da mari.
Azahirin gaskiya ba kaɗan naji zafin marin da maryam tamin ba wanda hakan yasa na ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa raina a ɓace.
Ganin haka ne yasa tacimin kwala, cikin yanayin ɗaga murya tace "ko zaka rama marin da nama ne? 
Cikin yanayin ɓacin rai nace "maryam kiyi gaggawar sakarmin riga tun kafin raina ya ɓaci nan take ta sake daga hannu ta ɗaukeni da mari.
A wannan lokacin ne nima zuciyata ta tunzuro harna ɗaga hannu zan rama, sai naji abbana ya dakamin tsawa.
Ba yadda na iya haka na sauke hannuna ba tare da na rama ba.
Tun daga wannan lokacin sai saɓani ya shiga tsakanina da yayata maryam.
Bayan kwana biyu da faruwar haka fitowata daga gida kenan sai nayi kacibus da hafsat a ƙofar gidanmu, yanayin bugawar da naji ƙirjina yayi ne yasa na tabbatar da cewar sai an samu matsala a tsakanina da hafsat.
Da yake tsakanin gidanmu dana yayana ba wani nisane sosai ba sai na sauketa acan bayan taci abinci tasha ruwa muna cikin fira sai naga hafsat ta kalleni sannan tayi murmushi.
Buɗar bakina sai nace "hafsat wannan murmushin naki yana nuna alamun kamar akwai wani abun da yakeson fitowa daga bakinki. 
Sai tayi dariya haɗe da cewa "kawai ji nake sonka yana ƙara nisa a cikin zuciyarsa wallahi ina matuƙar sonka domin kai ne wanda nake burin nayi rayuwa ta tsawon har abada a tare dashi, kanada kyawawan halaye, waɗanda suke karamin sha'awar son kasancewa a tare da kai. 
Amma sai dai har yanzu yayana musa bai daina sa shakku a zuciyata ba, saboda ako da yaushe burinshi bai wuce yaga na rabu dakai ba. 
Saboda shi a nashi tunanin kawai yaudarata zakayi. 
Sai nace "hafsat inasonki kuma ina ƙaunarki zuciyatama ta gaskata haka.
Amma sai dai jiya na aikata wani kuskure wanda zanso kiyimin uzuri abisa aikata hakan da nayi. Cikin yanayin fargaba tace " yayana wane irin kuskure kuma ka aika wanda har kake son nayima uzuri a game da abun da kakeson sanar dani? 
Sai na kalleta nace "jiya ina gida sai akira wayata da wata baƙuwar number bayan na amsa kiran sai a sanar dani cewar nayi gaggawar zuwa. ALMADINA HOSPITAL wanda yake cikin garin zaria sannan a yanke wayar.
A wannan lokacin gaba ɗaya sai hankalina ya tashi saboda nayi tunanin ko kece baki da lafiya.
Cikin gaggawa na ɗauki hanyar zaria da zuwana asibitin sai na taradda meenat kwance a gadon asibiti cikin wani irin mawuyacin hali kuma ba wani abu ne ya jawo mata hakanba illa soyayyar da take a tsakanina da ita. 
Da kyar ta iya buɗa baki wajan roƙona domin ceton rayuwarta ta hanyar dawo da soyayyar da take a tsakanina da ita.
A lokacin dana neme ƙin amincewa da wannan buƙatar tata har dogon suma tayi.
Bayan ta farfaɗo daga suman da tayi bayadda na iya haka na amince da wannan buƙatar da ta tunkareni da ita.
Sannan kuma daga bisani sai na sanar da ita alƙawarin dana ɗaukar miki hakane yasa ta bani shawarar na aureku duka biyun. 
Koda hafsat taji haka sai tayi murmushi sannan tace "ai dama nasan wannan alƙawarin daka ɗaukarmin bazai taɓa ɗorewa ba, saboda nasan duk daren daɗewa meenat sai ta dawo gareka. 
Cikin yanayin mamaki nace "hafsat kema kina nufin kin amince da wannan shawarar da meenat ta bayar kenan?
Dariya naga tayi haɗe da cewa "karka manta itamafa yar uwatace musulma kuma ai Allan daya haliccemu cewa yayi ku auri mace 2 ko 3 har zuwa 4 hudu idan kuma bazaku iya adalci a tsakaninsu ba to ku auri 1. 
Jin hakane yasa nan take nayi murmushi haɗe da cewa "to idan kuma bazan iya adalci a tsakanin kuba fa wacece ya kamata tayi haƙuri a cikinku? 
Sai tamin wani kallo irin na masoya haɗe da cewa "to saika aureni ita ta haƙura. 
Tun daga wannan lokacin sai kyakkyawar alaƙa ta shiga tsakanin hafsat da meenat gaba ɗaya sai na tattara soyayyata na ɗora a kansu bayan wasu yan watanni sai na tunkari abbana da batun aure, cikin yanayin ɓacinrai abbana yamin wani kallo haɗe da cewa aure kuma? 
Yanayin kallon da naga yamin ne yasa naji a jikina sai ankai ruwa rana kafin wannan burin nawa ya cika. 
Buɗar bakinshi sai yace to a ina yarinyar take? 
Cikin yanayin fargaba nace "abba a zaria suke. 
Sai yace "kai ban gane abun da kake nufiba kana nufin wadda zaka aura ba guda daya bace kenan?
=> 14
Koda yaji haka sai yace "ban gane abun da kake nufiba kana nufin wadda zaka aura ba guda ɗaya bace kenan?
Cikin yanayin kunya na sunkuyar da kaina ƙasa haɗe da cewa "abba kamar yadda meenat da hafsat suke sona nima haka nakesonsu. 
Jin haka ne yasa ya jinjina kai sannan yace "kana nufin dukansu zaka aura kenan? 
Koda na ɗago kai na kalleshi sai nace "eh abba. 
Shiru naga yayi na ɗan wani lokaci, zuwacan da ya buɗi baki sai yace "to bari kaji duk a cikinsu ba wadda zaka aura.
Cikin yanayin sanyin jiki nace "amma abba... 
Bai bari na ƙarasa furta maganar da take bakina ba ya dakatar dani ta hayanyar daga hannunshi haɗe da cewa "kaga dakata ba neman shawararka nake ba domin wannan umarni ne zan baka a matsayina na mahaifinka.
Gyara zama naga yayi sannan yace "nasan kasan waye malan usman wanda yake zaune a jahar Taraba. 
Cikin yanayin fargaba nace "eh abba.
Sai mahaifin nawa yace "eh kasanshi amma sanin da kuyimai kai da yayarka maryam na banzane, tun da bakusan matsayinshi a gareni ba.
Dan haka a yaune zan fayyace maku duk wani abun da yake tsakanina da malan usman. 
Sannan mahaifin nawa ya kalleni haɗe da cewa "sanin kankane ni haifaffen cikin garin hadejia ne wadda take jahar jigawa.
Tun kafin nayi aure bayan na kammala karatuna na secondary lokacin ina ɗan kimanin shekara 21 nake barin gida domin neman halak ɗina kuma kasuwancina baya wuce leburanci. 
Nayi yawo sosai a game da wannan sana'ar tawa tawa ta leburanci, rabon haɗuwata da alhaji usman ne ya kaini jahar taraba saukata daga mota kenan sai Allah ya jarabceni da wata irin kasala cikin ƙanƙanin lokaci dukkanin gaɓoɗin jikina su mutu.
Bayan ansaukemin kayana a gefen titi daƙar na iya ɗaukar kayan nawa na ƙarasa dasu ƙofar wani gida.
Bayan wani ɗan lokaci sai zazzabi mai matsanancin zafi ya saukarmin gashi bansan kowa ba a garin.
Kuma gashi bani da wasu wadatattun kuɗi a tattare dani gashi kuma a lokacin yamma ta farayi.
Ina kwance sai naji an tasheni, daƙar na iya yunƙurawa na tashi zaune. sai wanda ya tasheni yace malan lafiya kuwa, kazo ka kwanta anan gashi dare ya fara yi?
Kafin na buɗa baki na mai magana sai ya fahimci halin da nake ciki, buɗar bakinshi sai yace "malan amma ga dukkan alamu baka da lafiya ko? 
Daƙyar na iya buɗa baki na bashi amsa. 
Cikin gaggawa ya ɗakko mota ya kaini wani asibiti.
Bayan ya kaini asibitin anyimin wasu allurai sannan a bani wasu ƙwayoyin magani ace idan naci abinci nasha.
Haka wannan bawan Allan ya kaini gidanshi yasa akawomin abinci mai rai da lafiya haɗe da lemo ga kuma ruwa mai sanyi.
Bayan naci abinci nasha maganin sannan ya bani makwanci tun a wannan daren naji duk wani zazzaɓin dake damuna ya bar jikina.
A yayin da gari ya waye nayi sallah sai a sake kawomin abinci naci har ya isheni.
A wannan safiyar ne ya gabatarmin da sunanshi, bayan na bashi labarin dalilin zuwana wannan garin nasu, sai yace "naci gaba da zama a gidan har zuwa lokacin da zan koma gida.
A ƙarshema sai ya jani a jika idan zai fita harkokin kasuwancinshi tare yake tafiya dani alhaji usman yayimin komai a rayuwa saboda jin daɗin zaman da yai dani ne yasa yabiyamin kujerar makka ina saudiyya kafin na dawo yasai ma iyayena gida a kano.
Bayan kimanin shekara 2 da faruwar haka sai kuma yabani jari mai kauri wanda nima zan iya rike kaina. 
Tun daga wannan lokacin na ɗaukar ma kaina alƙawarin ba abun da alhaji usman zai nema a gareni muddun ina dashi ba tare da ya samuba.
Sannan mahaifina ya kalleni haɗe da cewa "sanin kankane alhaji usman yarshi ɗaya ce tak, daga ita bashi da wani yaro ko wata yarinya. 
Kuma a halin da ake ciki yanzu tace "ba wani wanda takeso sai kai. 
Cikin yanayin ruɗani mai tattare da tsoro na kalli mahaifina. 
Buɗar bakin abbana sai yace "dan haka daga yau karka kuskura naji labarin ka sake zuwa Zaria balle naji kayi magana da ɗaya daga cikin Yan matan da naji kace kanason aure, idan kuma ba hakaba to magana ta haskiya zaka haɗu da fushina wanda hakan zai iya sawa nayi hannun riga dakai.
Nan take ya umarceni dana bashi wayata. 
Kafin na fara soyayya idan naga masoya suna zubar da hawaye a kan soyayya ba ƙaramin haushi suke bani ba.
Sai gashi a wannan ranar nine nake zubar da hawayen baƙin ciki.
Bayan na bashi wayar nan take ya ciro layikan dake wayar ya karyasu sannan ya nunani da yatsansa haɗe da cewa "ka shirya gobe zakaje gareta kuma soyayyar gaskiya nakeson kayi da ita, dan haka idan har ka kuskura wani saɓani ya shiga tsakaninka da ita to ba abun da zaisa na daukeka a matsayin ɗana.
=> 15
tabbas ba yadda za'ai na bijirewa maganar mahaifina domin ba yadda na iya haka na amsamai ta hanyar cewa to Abba. 
A wannan ranar ne damuwa mafi tsanani haɗe da ɓacinrai su addabi zuciyata.
Bayan na shiga ɗaki sai na kasa zaune na kasa tsaye kwanciya ta gagareni, gaba ɗaya na rasa abun dake min daɗi. 
Batun zubar da hawaye kuma ba'a magana tun da nake ban taɓa yin sallar nafila a game da soyayaya ba.
Amma sai gashi a wannan ranar rana nayi alwallah sannan na dawo ɗaki na shimfida sallaya ina sallah ina kuka.
Bayan na idar da sallar sai na ɗaga hannayena sama nace "Ya Allah kai ka haliccemu badon komai ba sai dan mubautama kuma kayimana umurni da muroƙeka zaka biya mana buƙatunmu, yau ina mai ƙasƙantar da kaina agareka bani da karfi ko wani iko ko wata dabara ko wayo a game da wannan halin da nake ci.
Ya Allah ina roƙonka kataimakeni ka bani mafita mafi sauƙin a game da wannan halin da nake ciki badan halayena ba sai don tausayawarka.
Dariyar yayata maryam naji a bayana kai tsaye tazo ta zauna daf dani tace "to kai in ban da abunka ai godiya ya kamata kayima ZAINAB saboda zabinka da tayi a matsayin wanda takeson ya zama mallakinta ba domin hakan ba ƙaramar nasara bace ga rayuwarka.
Sanin kanka ne zainab kyakkyawace ga ilimi da maida hankali wajan bautar Ubangiji.
Nan take na kalleta cikin yanayin ɓacin rai nace "haba anti ai duk da cewar nasan zainab kyakkyawace da ilimi haɗe da sanin ya kamata hakan bazai taɓa sawa na mance da irin halaccin da hafsat da meenat suyimin ba. 
Nan take na bata labarin duk abun da ya faru a tsakanina dasu, sannan daga ƙarshe nace "naji zanbi umarnin abba kamar yadda ya buƙata.
Kuma zan nuna mata soyayya ta gaskiya kamar yadda ya nema daga gareni. 
Ammafa batun rabuwa da hafsat da meenat bazata taba yiwuwa ba koda kuwa haka ne zai jawu sular barina gidannan.
Washe gari da sassafe bayan na kammala shirina nayi breakfast sai Abbana ya bani ɗaya daga cikin motarshi haɗe da yan kuɗaɗan da zanyi guzuri dasu a hanya. 
Fitowata daga gida kenan sai tunanin meenat da hafsat ya faɗomin a rai.
Hakane yasa naji a raina bai kamata na tafi ba tare dana sanar dasu abun da yake faru dani ba domin gudun karsu ɗaukeni a matsayin mayau dari.
Hakane yasa na karkata akalar tafiyata zuwa zaria da zuwana na kira hafsat da meenat domin sanar dasu halin da nake ciki.
Bayan mun gaisa sai hafsat ta kalleni tayi murmushi haɗe da cewa "yayana yau naga kamar fuskarka akwai damuwa saɓanin yadda mu saba ganinka.
Jin haka ne yasa na cire duk wata fargabar dake raina haɗe da cewa "hafsat wannan damuwar da kike gani ba'a iya fuskata ta tsayaba domin har cikin zuciyata take. 
Nan take naga fuskokinsu sun canza cikin yanayin damuwa meenat tace "dan Allah ko zaka iya sanar damu dalilin faruwar wannan damuwar taka? 
Sai na kallesu nace "ai sanar daku dalilin faruwar haka ne ya kawoni gareku a yanzu. 
Sai na kalli hafsat nace "hafsat wane irin laifine kike tunanin zan iya aikatawa a gareki wanda zaisa kiji gaba ɗaya kin tsaneni. 
Cikin yanayin fargaba tace "haba yayana wannan wace irin tambayace, aini a tunanina ba wani abun da zaisa naji ka fita daga ra nai koda iyayena da kaf dangina zasuji basasonka to hakan bazai taɓa sawa naji banasonkaba.
Sannan na kalli meenat nace "meenat... Sai ta dakatar dani haɗe da cewa "kaga idanma irin tambayar da kayima yar uwata hafsat zaka maimaita a gareni to ka hutar da bakinka domin ni da kai mun riga mun zamto ɗaya koda ace idan ka aureni naman jikina zaka rika yanka kana bani ina gasawa a matsayin abincina to bazan iya rabuwa da kai ba. 
Sai nayi shiru na ɗan wani lokaci zuwacan sai nace "tabbas nasan kun fuskanci matsaloli da dama a game da ni wadanda hakan baisa kun nisanta kanku dani ba. 
Kwatsam bayan an warware waɗannan matsalolin na ɗauka komai yazo ƙarshe to ashe abun ba haka yake ba. 
Nan take nayi musu bayanin duk abun da ya faru dani a tsakanina da mahaifina. 
Jin haka ne yasa meenat tayi ƙas da kanta tana zubar da hawaye cikin yanayin ruɗewa hafsat tace "yanzu kana nufin rabuwa zakayi damu kenan sai nayi murmushi nace "a'a ba batun rabuwa a tsakanina daku zan jajirce wajan bin duk wasu hanyoyin dasu dace wajan ganin burina da naku ya cika ni dai kawai abun da nake buƙata a gareku itace addu'a.
=> 16
Har nayiwa mota key zan tafi sai meenat ta leƙo ta glass ta kalleni haɗe da yin wani tattausan murmushi sannan tace "dan Allah duk runtsi karka rabudamu. 
Sai na kallesu nayi murmushi haɗe da cewa "tsakanina daku tamkar hanta da jini ne. 
Sannan su ßago min hannu sunamin bye! bye! Har nayi nisa fuskata cike da annuri. 
Tabbas a wannan ranar sai da nayi matuƙar gajiya domin tafiya daga kaduna zuwa jahar taraba na tabbata ba karamar tafiya bace.
Na isa jahar taraba cikin dare, saukata daga mota kenan sai nayi calling.. 
Ɗin Hafsat da Meenat a waya na sanar dasu cewar na sauka lafiya kuma in Allah ya amince bazan taɓa basu kunya ba. 
Cikin yanayin sakin fuska haɗe da jin daɗi mahaifin zainab ya kamo hannuna yace "taho nan ɗana ai nan gidanku ne, duk wata kulawar da kake samu a wajan mahaifinka ananma in Allah ya amince bazaka rasata ba. 
Haka yaja hannuna zuwa babban falon gidan, koda zainab tayi ido biyu dani sai ta taso da gudu zuwa gareni saboda murna kamar zata rungumeni gaba ɗaya sai al'amarin yayi matuƙar bani kunya. 
Koda zainab ta fahimci akwai gajiya a tattare dani, sai ta kalleni tayi murmushi haɗe da cewa "yayana naga kamar akwai gajiya a tattare da kai dan haka zomuje na kaika Bathroom domin kasama jikinka ruwan sanyi.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "kuma kinga zai taimaka wajan rage wannan gajiyar da nake tattare da ita.
Haka zainab ta riƙe hannuna ta kaini har inda zanyi wanka.
Bayan nayi wanka na canza kaya ga iska mai daɗi tana ratsani sai zainab ta kaini denny table ina cin abinci ina kallon kyakkyawar fuskarta zuwa can sai na ɗan sha ruwa sannan na kalleta nace "zainab kinsan wani abu kuwa? 
Sai ta girgiza kai haɗe da cewa "a'a sai ka faɗa.
Buɗar bakina sai nace "zainab inasonki, wannan itace kalmar da nayi miki guzurunta tun kafin nazo gareki.
Cikin yanayin kunya ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi.
Koda naga ta sunkuyar dakanta ƙasa tana murmushi sai nace "zainab wannan murmushin naki yana nuna alamun zuciyarki ta karɓi wannan kudurin nawa kenan? 
Sai ta ɗan ɗago kanta kadan ta kalleni da fararen idanunta sannan tace "nima batun yauba nake fama da matsanancin ciwon sonka nauyin bakine ya hanani isar da wannan saƙon nawa zuwa ga taka zuciyar.
A wannan ranar saida mukai wajan 1:30 na dare muna fira a falon dake gidan.
A wannan ranar ne na fuskaci zainab tana da matukar son labari musamman labarin daya shafi soyayya. 
Koda taga na kalleta nayi dariya, cikin yanayin murmushi tace "masoyina me kakema dariya? 
Sai nace "zainab kinada yawan son labari hakane yasa kike burgeni, dan haka ki bari zuwa gobe da safe zan baki wani labari mai ɗauke da abun tausayi haɗe da ruɗani. 
Jin haka ne yasa tayi farin ciki har ta nuna matsuwa wajan son ganin gari ya waye.
Aiko gari yana wayewa bayan nayi wanka munyi breakfast sai zainab ta ɗaukeni a motarta zuwa wani wajan shaƙatawa. 
Tabbas wajan da zainab ta kaini yana da bansha'awa ga daɗin zama ga iska mai sanyi tako ina, kowa harkokin gabanshi yakeyi ba ruwan wani da wani, ga kukan tsuntsaye mai daɗin gaske.
Bayan mun samu wani keɓaɓɓen waje mun zauna ga drinks mai sanyi a gabanmu zainab ta kalleni tace "Honey" wane kalar drink kake buƙatarsha?
Buɗar bakina sai nace "ai zaɓinki shine zabina.
Jin hakane yasa tayi murmushi sannan ta zuba wanda ranta yafiso ta ajemin a gabana.
Muna cikin shan drink sai na kalleta nace "yauwa zainab labarin da nace zan baki labarine wanda ya shafi wani abokina. 
Kuma zanso idan kinji wannan labarin ki taimakamin da irin taki shawarar domin na tabbata a yanzu haka zuciyarshi tana cike da damuwa.
Murmushi naga tayi sannan tace "ba damuwa in Allah ya amince zan taimaka mai da irin tawa gudunmawar wajan bashi shawarar da ta dace. 
Sai nabata labarin duk abun daya faru a tsakanina da meenat da kuma hafsat a matsayin labarin da ya shafi abokin nawa. 
Koda zainab taji yadda labarin ya kasance sai tayi shiru na ɗan wani lokaci.
Ganin yadda tayi shiru ne yasa na ɗan kurɓi ruwa, sannan na kalleta. 
Nace zainab kinsan meya faru a lokacin da abokin nawa ya tunkari mahaifinshi da batun auren Hafsat da Meenat kuwa? 
Sai tace, "A'a. 
Sai na gyara zama haɗe da cewa "a lokacin da abokin nawa ya tunkari mahaifinshi da batun auran Hafsat da Meenat sai mahaifin shi ya nuna ɓacin ranshi a ƙarshema cewa yayi "muddun ya sake kulasu to sai ya hadu da mummunan ɓacin rai a tattare da mahaifin nashi. 
Nan take zainab ta kalleni tace "to amma wane daliline yasa mahaifin nashi yaƙi amincewa da buƙatar auransu? 
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "saboda mahafin nashi akwai wadda yakeson ya auramai. 
Buɗar bakin zainab sai tace "azahirin gaskiya yana da kyau yabi umarnin mahaifinshi kuma idan bai auri Hafsat da Meenat ba ya zalincesu. 
Sannan tayi shiru na ɗan wani lokaci wanda hakan yasa na fashimci cewar ta shiga nazarin shawarar da ta kamata ta bayar ne.
Zuwa can sai ta kalleni haɗe da cewa "hanyar da nake ganin ta dace yabi itace ya fara auren wadda mahaifinshi ya umarceshi da ya aura, daga baya kuma sai ya auri biyun da ya ɗaukarwa alƙawari. 
Buɗar bakina sai nace "to idan kuma wadda abban nashi ya umarceshi da ya aura tanuna ƙin amincewarta a game da batun auren sauran biyun ya kike gani? 
Sai tace "na tabbata idan har ita mai hankali da tunanice haɗe da ilimi zata bada goyon bayan hakan. 
Jin haka ne yasa na kalleta fuskata cike da mamaki nace "zainab kina nufin idan kece amincewa zakiyi kenan? 
Sai tayi dariya haɗe da cewa "to me zai hanani amincewa. 
Nan take na miƙe tsaye na kalli zainab nace "zainab wannan labarin dakiji na dangantashi da abokina bai faru da kowaba sai a kaina.
Sai na kalleta nace zainab inasonki har a zuciyata, sai dai kuma bansan hanyar da zan bi ba wajan ganin na cikawa meenat da hafsat alƙawarin da na ɗaukar masu, domin har ga Allah suma suna matuƙar sona.
Sai zainab ta kalleni tace "yayana na tabbata kalmankane suyi silar cusa soyayyarka a zukatansu kamar yadda nima hakan ya faru dani tun a lokacin dana ziyarceku.
A lokacin da na ziyarceku ba kaɗan naji daɗin kasancewata a tare da kai ba.
Bayan na koma gida gaba ɗaya sai na kasa sakewa wanda hakan yasa na kwashi dogon lokaci ina fama da tuninka.
Idan zanci abunci ko zan kwanta bacci fuskarkace takemin gizo ko cikakken wata ɗaya da dawowata gida ba aiba sai na cire duk wata kunyar da nake tattare da ita wajan sanar da mahaifiyata cewar kai nake so 
Bayan mahifina ya dawo daga office da yamma sai mahaifiyar tawa ta sanar dashi duk abun da na sanar da ita.
A wannan lokacin ne naga tsantsan farin ciki a tattare dasu saboda sunsan banyi zaben tumun dareba, saboda jin daɗin hakane yasa abbana ya sanar da mahaifinka duk abun da yake faruwa.
Dan haka ka kwantar da hankalinka ninasan hanyar da zanbi wajan ganin wannan burin nawa da nasu yacika.
Bayan munbar wajan shaƙatawar mun koma gida ban saniba sai zainab ta kwashe labarin duk abun da yake faruwa ta sanar da mahaifinta. 
Koda mahaifinta yaji wannan batun sai yakirani gani ga zainab ya kalleni yace meyasa ka kasa sanar dani halin da kake ciki? 
Cikin yanayin kunya na sunkuyar da kai na ƙasa, nace "abba ai nasan abbana bazai kaini inda zan cutuba domin na tabbata ku iyayene na gari kuma zainab tana da tarbiyyar da bakowane namijine zai samu kamarta ba. 
Dan haka na aminta da zainab ɗari bisa ɗari, kuma zan riƙeta amana haɗe da nuna mata cikakkiyar soyayya. 
Sai mahaifin zainab yace "to sukuma waɗancanfa sai nace "zan rabudasu kamar yadda abbana ya umarceni. 
Sai zainab tace "a'a hakan bazai yiwuba dole mu ukku mu kasance a karkashinka sai mahaifiyar zainab tayi dariya haɗe da cewa "to kaji umarnin da abokiyar zaman taka ta bayar. 
Sai nayi murmushi nace "a'a zainab abbana bazai taɓa bari hakan ta faruba domin dake kaɗai yakeson yaga na zauna. 
Sai mahaifinta yace "a'a ai idanma haƙurin ne zainab ce ya kamata ace ta haƙura dan haka nima ina bayan zainan sai dai ka auresu duka. 
Bayan mun ɗan fita waje sai na kalli zainab nace "nifa tsoro nakeji kar wannan batun ya isa kunnan abba saboda hakan ba ƙaramin tashin hankali zai haifar min ba.
Koda zainab taji wannan maganar tawa sai ta tuntsure da dariya sannan tace "haba (may dear) meyasa kake da tsoro ne haka,? to kabari idan ka tashi komawa gida saimu tafi tare kaga idanma dukane kake tsoro sai a dakemu tare.
=> 17
Sai nayi dariya haɗe da cewa "haba dai duka sai kace wasu ƙananan yara.
Kwana na 4 a jahar taraba ranar da zan dawo gida, sai zainab ta fahimci akwai damuwa a tattare dani sai tazo gabane ta kalleni tayi murmushi tace "my dear Ya naga kamar fuskarka ta canza, ba yadda na saba ganinta ba?
Sai na ɗan saki fuskata cikin yanayin murmushi nace "zainab ba kowane zaiyi nasarar samun masoya na gaskiya a wannan lokacin ba dolene na godema Allah daya bani zainab da meenat haɗe da hafsat. 
Sai dai kuma zuciyata tana fargabar haɗuwa da irin ɓacinran da zan fuskanta a wajan mahaifina saboda dake kaɗai yakeson yaga na zauna ba tare da nayi miki wata kishiya ba. 
Cikin yanayin damuwa zainab tace "yayana idan har baka auri meenat da hafsat ba kacuci rayuwarsu dan haka idan ka koma gida kasanar da abba cewar "na amince ka auremu duka. 
Sai nace "zainab karfa ki manta abba umartata yayi akan cewar karna kuskura na bari kusan da batun meenat da hafsat a karshema cewa yayi idan har na bari hakan ta faru to ba yadda za'ai ya ɗaukeni a matsayin ɗanshi. 
Wannan shine dalilin da yasa kiga damuwa a tattare dani. 
Sai tace "to amma me zai hana mu tafi tare? 
Domin na tabbata hakan zai kawo sauƙin ɓacinran abban. 
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "a'a zainab kiyi zamanki kawai ni zanji da komai kinga idanma naga ɓacin ran nashi yayi tsanani gaba daya sai na dawo nan da zama sai tayi dariya haɗe da cewa "to shikenan Allah ya saukeka lafiya.  
Na isa gida cikin dare bayan nayi packing ɗin motar jikina a gajiye na shiga falo koda mahaifina yaji shigowata sai naga ya fito daga ɗaki ranshi a ɓace hannu naga yamiƙomin haɗe da cewa "bani key ɗin motar sannan ka ficemin daga gida. 
Cikin yanayin tsoro nace "abba...... 
Sai ya dakatar dani ta hanyar cewa "banason jin komai daga bakinka mutumin banza kawai, maza ka ficemin daga gida.
Gashi dare yayi ba yadda na iya haka nayi waje. 
A wannan daran sai a ɗakin wani abokina da yake kusa da gidanmu na kwana.
Tun daga wannan ranar naji gaba ɗaya soyayya ta fitarmin daga rai, kuma gashi bani da ikon yakice yan mata ukkun dasu shiga rayuwata.
Bayan gari ya waye sai na rasa hanyar da zanbi domin kawo ƙarshen wannan matsalolin da suke tunkarata, a ƙarshema sai na yanke shawarar haƙura dasu gaba ɗaya ta hanyar barin garin.
Bayan na gama yanke wannan shawarar, fito wata daga gidan su abokin nawa kenan sai na hangi abokina musa wato yayan hafsat da zuwanshi gareni ko gaisawa bamuyi ba. 
Buɗar bakinshi sai yace "yanzu kana tunanin abun da kayi ka kyauta kenan, to na samu labarin duk abun da yake faruwa kuma nayi Allah wadai da kasancewarka a matsayin abokina saboda kasancewarka a matsayin abokina ne yasa kayi nasarar yaudarar meenat da kuma ƙanwata hafsat. 
Sai dai kuma har yanzu banga ribar da kaci a dalilin wannan yaudarar da kayi musu ba.
Cikin yanayin ɓacin rai na kalli musa haɗe da cewa "ko kaɗan bani da wata mummunar manufar da zatasa na yaudari hafsat da meenat, kawai kaddaratace tazo da haka. 
Jin haka ne yasa ya kalleni haɗe da cewa "to meyakaika jahar taraba?
Sai nace "a'a musa karka riƙi tafiyar da nayi taraba a matsayin hujja, saboda dolece ta kaini.
Sai yace "kaga dan Allah ka taimaki rayuwar kanwata wajan cire soyayyar daka dasa a zuciyarta saboda ina da tabbacin nan bada jimawaba zata iya rikidewa ta koma gubar da zatayi sular hallaka rayuwarta. 
Buɗar bakina sai nace "koda ace dangina da danginka zasu nuna ƙin amincewarsu a game da batun aurena da hafsat to banga dalilin da zaisa na rabuda ita ba. 
Muna cikin wannan maganar sai naji wayata tana ringing.. Koda naga sunan hafsat cikin gaggawa na amsa kiran. 
Cikin yanayin kuka naji tace "yayana sannan ta fashe da kuka ban san lokacin da nima hawaye ya zubo daga idanuna ba. 
Cikin sanyin murya nace "hafsat kukanki tashin hankali ne a gareni, dan Allah ki sanar dani abun da yake faruwa. 
Abun da ta sanar dani ne ya jefa zuciyata a ruɗani domin cewa tayi "iyayenta sunce idan har bata fita harkataba to Allah ya isa basu yafe mata ba. 
Nan take na yanke wayar ba tare dana furta komai a gare ta ba. 
A wannan ranar ne na gane cewar soyayya ba ƙaramar matsala bace wanda hakan yasa na ɗauki soyayya a matsayin shirme. 
Kai tsaye na shiga gida na ɗakko karamar jakata da niyar barin gari fitowata daga ɗaki kenan sai na tuna da cewar babu ko sisi a aljihuna sai wata ragowar 2 hundred
Kai tsaye na shiga ɗakin yayata maryam, da shigata sai na sameta kwance a gado tana damna waya.
Wani kallon rainin hankali naga tayimin haɗe da cewa "meye kuma na shigo min ɗaki?
Cikin yanayin girmamawa nace "dan Allah aunty kuɗi nake buƙata a wajanki? 
Haka ta ƙaremin kallo tun daga sama har ƙasa sannan tace "ai ka manta nan ɗakin maryam ne ba ɗakin ubanka ba. 
Sai ka bari anjima idan ya dawo sai ka tunkareshi da wannan buƙatar saboda nima idan buƙatata ta taso wajanshi nake zuwa. 
Jin haka ne yasa nace "ke wai wannan wane irin zancan banzane? 
Nifa ko kaɗan banason aci mutuncina idan baki dasu sai ki sanar dani ta hanyar furta kalma mai daɗi a gareni amma kinzo sai wasu zantukan iska kikemin kamar ba iyayenmu ɗaya ba. 
Nan take ta ciro wasu kuɗaɗe daga bed site ɗin gadanta ta nunamin haɗe da cewa "ni ba matsiyaciya bace kamarka kawai bayarwane bazanyi ba. 
Cikin yanayin gadara nace "to wallahi tunda har Allah yasa naga kuɗinnan a gareki, to ba yadda za ayi na tafi ba tare da sunzo hannuna ba. 
humm! Abun dai ba'a cewa komai domin na daku a wajanta dakyar na iya murde hannunta na kwace gaba ɗaya kuɗaɗan dake wajanta.
Cikin gaggawa na tunkari tashar motoci banma san garin da zan tunkaraba da isata har na shiga mota na zauna fuskata cike da damuwa sai naji kira ya shigo wayata dubawar da zanyi sai naga ai zainab ce take calling ɗina.
Ganin haka ne yasa nai jim kamar na amsa kamar karna amsa ba yadda na iya haka na koma gefe na amsa kiran.
Murmushi naji tayi haɗe da furta kalmar gaisuwar ban girma a gareni. 
Cikin sanyin murya nace "zainab tafa ɓaci, nan take nayi mata bayanin duk abun da yake faruwa dani wanda hakan yasa tayi matuƙar tausayamin abisa jin halin da nake ciki, a karshe sai tace "dan Allah ka bani 2minutes kafin ka tafi. 
Sai nace "to shikenan zainab. 
Ban saniba ashe mahaifinta takeson ta sanarma halin da nake ciki. 
Jim kaɗan da yanke kiran sai kiranta ya sake shigo koda na amsa kiran sai naji muryar mahaifinta. 
Bayan mungaisa sai yace "karka kuskura kaje ko ina, sannan ya sanar dani cewar idan Allah ya kaimu gobe zaizo domin kawo ƙarshen matsalar da take faruwa.
A wannan ranar dai banyi tafiyarba ban kuma koma gida ba. 
A ranar da mahaifin zainab yazo gidanmu washe gari da sassafe sai zainab ta kira wayata bayan mun gaisa, cikin yanayin shagwaba tace "haba yayana ina ka shiga, tun jiya da daddare nake ta ƙoƙarin kiranka amma bata shiga. 
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "zainab kardai kice tare dake abba ya taho sai tace "kaga kazo gida yanzu-yanzu abba yana son ganinka koda naji wannan batun daga bakin zainab sai na fito daga dakin abokina na na tasarma gida.
Tun kafin na shiga gidan naji tsoro ya daki zuciyata haka dai na shiga gidan a tsorace. 
Ina shiga gidan sai zainab ta taso da sauri cikin murna kamar zata rungumeni.
Koda na haɗa ido da aunty maryam sai naga ta gallamin wata harara ranta a bace, Allah ne kadai yasan irin rashin mutuncin da ta ƙudiri niyar zartarwa a garemu.
Bayan an warware matsalar sai abbana ya amince a game da batun auransu duka, amma da farko aurena da zainab za'a farayi sannan daga baya sai ayi na sauran.
Sai zainab tace "a'a ita idan son samuntane ayi duka a rana ɗaya.
A wannan ranar sai mahaifin zainab tare da wani makwafcinmu mai suna malan Abubakar su ɗauki hanyar zaria domin maganar aurena da meenat haɗe da hafsat sai kuwa ayi sa'a komai ya dai-daita.
Dawowarsu kenan sai musa ya kirani a waya ya domin bani haƙuri a game da abun da ya faru a tsakanina dashi. 
Sai nayi dariya haɗe da cewa "haba babban yaya karkaji komai ai rayuwa tagaji haka. 
Sai shima yayi dariya yace "gaskiya abokina kai maƙura ne mata ukku a lokaci ɗaya, gaskiya ka aje record. 
Sai nayi dariya sannan nace to ka gaishemin da abar ƙaunata.

Alhamdullah
The End.