new update
=> 1
wannan wani dan taƙaitaccen labari ne zan baku wanda yasani kukan zuci.
Mafi yawancin mutane suna kirana da Young Uzee amma asalin sunanan shine Uzairu.
An haifeni a 1994 a garin kano, ni kaɗai ne namiji a wajan mahaifina sai kuma yayata zainab da kuma kanwata Ameen.
Ita zainab ta kasance mai ƙoƙarin karatu gata da maida hankali wajan addini.
Ita kuma Ameena 60% na rayuwarta rainin hankali ne haɗe da wulaƙanci gata da rashin kunya.
Ni kuma Allah yasa mutun ne mai matuƙar rashin haƙuri.
Haka ne yasa ko wace rana sai nayi rigima da ƙanwata Ameena musamman idan na fita yawo har fargabar komawa gida nakeyi.
Babban abun haushima duk wata rigimar da zamuyi ita ake ba gaskiya.
wannan ne babban dalilin da yasa Ameena ta samu kwarin guiwar ci gaba da aikata duk wani abun da taga dama a garemu.
Kwatsam wata ranar litinin da sassafe sai mahaifina ya aikeni wajan wani abokin kasuwancinshi, a wannan lokacin bani na dawo ba sai misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Tabbas a wannan lokacin ne naga abun da yai matuƙar ɓatamin rai a game da Ameena shigata gida kenan sai nayi kaciɓus da Ameena sanye da kayan sawata a jikinta tana wanki.
Ganin haka ne yasa nan take naji wani ɓacin rai yazomin wuya ya tsaya.
Kai tsaye na zare belt ɗin da nake sanye da ita a jikina namata shegen duka.
Koda anti zainab taji kukan Ameena sai ta fito waje a tsorace, da zuwanta gareni sai jinayi ta ɗaukeni da mari har nima na ɗaga hannu zan mareta sai naji mahaifiyata ta dakamin tsawa haɗe da cewa karka kuskura.
Ba yadda na iya haka na sauke hannuna raina a ɓace.
Zuwacan da yamma bayan mahaifina ya dawo daga wajan aiki sai ya sami labarin duk abun da ya faru a tsakanina da Ameena haɗe da yayata Zainab.
Ina kwance a daki sai mahaifina yasa Ameena ta kirani.
Fitowata daga ɗaki kenan sai naga mahaifina zaune a falo.
Koda na fuskanci ranshi a ɓace yake nan take nacire duk wata fargabar da take a zuciyata, da zuwana sai na zauna daf dashi a ƙasa haɗe da cewa "gani Abba.
A wallan lokacin ita kuma Ameena tana zaune a kujera.
Sai mahaifina ya kalleni haɗe da cewa "wane abune ya haɗaka da ƙanwarka har ka daketa da belt, har kuma kayi yinƙurin marin yayarka, alhalin kuma duk waɗannan ɗabi'u ne irin na mashaya kodai ka fara shaye-shaye ne bamu sani ba?
Jin haka ne yasa na kalli mahaifin nawa a tsorace haɗe da cewa "haba abba, wallahi tun da nake a rayuwata ban taɓa shan wani abun da nasan zai gusarmin da tunani ba, nan take nayi mai bayanin duk yadda al'amarin ya kasance sannan nace "dan Allah abba kayi haƙuri in Allah ya amince haka bazata sake faruwa a tsakanina dasu ba.
Sai yace "to shikenan tashi kaje.
Ko cikakken sati biyu da faruwar haka ba aiba kwatsam wata ranar juma'a da safe sai na shiga ɗakin mahaifina domin gaishe dashi bayan mungaisa sai ya bijiromin da wata maganar da ta girgizani domin cewa yayi nashirya jibi zan tafi jahar ADAMAWA makaranta.
Nan take naji ƙirjina yayi wata irin bugawa domin ni a son raina nafison na kammala karatuna a jahata ta kano.
Sai nace "amma abba me zai hana kabarni naci gaba da karatuna a nan saboda ko kaɗan banason nayi nesa da gida.
Sai ya girgiza kai haɗe da cewa "bafa neman shawararka nayi ba domin wannan umarnine.
Bayan kwana biyu da misalin karfe 7:30 na safiya bayan na kammala duk wani shirin da zanyi sai mahaifina ya ɗaukeni a mota zuwa adamawa.
Tabbas adamawa akwai nisa domin har gajiya nayi da zaman motar saboda tsabar gajiya bansan lokacin da bacci ya ɗaukeni ba.
Bani na buɗe ido ba saida mushiga cikin garin adamawa.
Da isarmu ƙofar wani gida sai naga mahaifina ya ßakko (remote gate) bayan ya danna remote ɗin gate ya buɗe mun shiga gidan.
Fitowar mu daga motar kenan sai nace "abba wannan gidan ko dai shima nakane?
Sai ya danyi dariya haɗe da cewa nawa ne mana anan zaka rika kwana idan an tasoku daga school.
Waigawar da zanyi sai naga wata tsaleliyar mota a bayana.
Buɗar bakina sai nace "abba waccan motar kumafa? sai yace ai wadda zaka rika hawace ko baka bukatar tane?
Sai nayi dariya haɗe da cewa "a'a abba inaso mana bayan gari ya waye sai ya zagaya dani lungu da saƙo na gidan.
Bayan gari ya ƙarasa wayewa sai ya ɗakko wasu kuɗi masu yawa ya bani haɗe da cewa "ga waɗannan kariƙe a wajanka saboda nasan baza'a rasaka da yan ƙananun buƙatu ba kuma nan gaba idan ka fuskanci sun kusa ƙarewa kasanar dani domin turoma wasu ta account ɗinka, sannan kuma dan Allah ka kasance mai maida hankali wajan karatu.
Kuma karka biyewa abokan banza ka ɓata rayuwarka, muddun nasamu labarin kana biyema mutanan banza to wallahi ranka sai yayi mugun ɓaci tun inajin rashin daɗin zama a school ɗin har na goge duk wani tunanin gida daga zuciyata a haka dai har naje "level 2".
Kwatsam wata rana da daddare lokacin na ɗan fita wata majalisa fira koda naga karfe 9:30 na dare tayi sai na tasarma gida domin kwantawa na buɗe ƙofa kenan zan shiga sai ji nayi an hankaɗoni da ƙarfi har sai da na faɗi ƙasa.
Tabbas a wannan lokacin sai da nayi matuƙar tsorata.
Haka na miƙe a tsorace, juyowar da zanyi sai naga wata kyakkyawar budurwa a gefena tana shash'sheka haɗe da kuka kanta ko ɗan kwali babu balle ayi batun gyale ko shijab kafartama ko takalmi babu.
Cikin yanayin tsoro muryarta tana ɓari tace "dan Allah malan kayi haƙuri kataimakeni wallahi kasheni zasuyi.
Koda naji batun kisa cikin gaggawa na rufe ƙofar.
=> 2
Allah cikin ikonsa ina rufe ƙofar sai mutanan dasu biyota su ƙaraso har ƙofar gidan.
Haka su ƙaraci ƴan haske-haskensu suyi gaba.
Har nashiga falon gidan tare da ita bata dai na zubar da hawaye ba.
Koda na kalleta sai nace "baiwar Allah yakamata ki dai na wannan kukan tun da Allah ya kwaceki daga hannunsu
Buɗar bakinta sai tace "wallahi har ƙarshen rayuwata banajin cewar zan iya dai na zubar da wannan hawayen.
Jin haka ne yasa na jinjina kai haɗe da cewa "to Allah ya kyauta.
Har na miƙe tsaye sai na fuskanci cewar akwai yunwa a tattare da ita.
Kai tsaye na wuce kitchen na nakawo mata wani sauran abinci haɗe da ruwa mai sanyi.
Bayan taci abincin tasha ruwa sai na nuna mata ɗakina haɗe da cewa "kishiga wancan ɗakin ki kwanta ni kuma zan kwanta a wannan falon.
Sai ta kalleni fuskarta cike da tausayi cikin yanayin sanyin murya tace "naga kamar gidan ba kowa sai kai kaɗai?
Sai nace da ita "eh gaskiya ni ɗan jahar Kano ne, kuma iyayena hade da sauran dangina duk suna can, karatu ne kawai ya kawoni wannan jahar taku.
Wannan ne dalilin da yasa mahaifina ya damƙa wannan gidan a hannuna domin nariƙa kwana idan na dawo daga school.
Buɗar bakinta sai tace "wallahi tsoro nakeji domin banason kayi nesa dani, saboda har yanzu hankalina bai gama kwanciya a game da mutanan da suke neman hallaka rayuwata ba.
Sannan ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa "dan Allah idan bazaka damuba me zai hana mukwana tare, saboda ko kaɗan banason kayi nesa dani?
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "toke in ban da abun ki ai hakan bazai taɓa yiwuwa mukwana a ɗaki ɗaya ba, saboda mahaliccinmu ya hanemu da aikata haka, saboda gudun sharrin shaiɗan.
Sannan na kalleta haɗe da cewa "kar kiji komai duk wani tsoran dake ranki ki cireshi kisaki jikinki kije ki kwanta.
Sai tace "to shikenan nagode bayan ta shiga ɗaki ni kuma sai na shimfiɗa sallaya/darduma na kwanta
Zuwa can cikin dare a yayin da nake kwasar bacci bansani ba sai ta buɗe ƙofa ta fito ta kwanta a kusa dani.
Allah cikin ikonsa bani na farka ba sai zuwa lokacin da asuba tayi.
Farkawar da zanyi sai naganta kwance a kusa dani.
koda nayi ido biyu da ita sai nayi gaggawar tashi zaune.
Koda taji motsina a yayin dana tashi sai itama ta tashi a tsorace.
A yayin da tayi ido biyu dani sai ta sunkuyar da kanta ƙasa haɗe da furta cewar "dan Allah kayi haƙuri.
Hmm!! ita ƙoƙarin bani haƙuri takeyi ni kuma a wannan lokacin gaba ɗaya sai hankalina ya karkata izuwa ga kallan kyawun halittar da Allah ya mallaka mata domin sai bayan gari ya waye sannan na tabbatar da cewar ita kyakkyawace.
Gata fara hancinta ɗan ɗagwar dashi idanuwanta farare tass tsayinta dai-dai misali.
Koda taga alamun kallan yayi yawa sai ta tashi a kunyace ta shiga ɗaki.
Bayan nayi alwallah nayi sallah sai na ɗakko wani shirami daga cikin kayana na bata haɗe da cewa "ki lulluɓa wannan a jikinki kema kiyi salla kafin gari ya ƙarasa wayewa na siyo miƙi hijab da takalmi.
Sai tayi murmushi tace "nagode sannan na shiga kitchen domin haɗa mana breakfast.
Bayan munyi breakfast sai na tafi school na barta a gidan ita kaɗai amma kafin na tafi sai da na gargaɗeta akan cewar karta fita zuwa ko ina har sai na dawo saboda a wannan ranar muna da leture ƙarfe 8:30.
A hanyata ta dawowa sai na taho mata da shijab haɗe da takalmi.
Da zuwana bayan na bata hijab ɗin haɗe da takalmin.
Sai tayi godiya sannan tace kaje kayi wanka sannan kazo kaci abinci domin nasan ka dawo da yunwa.
Jin haka ne yasa na kalleta fuskata cike da mamaki haɗe da cewa "kardai kice kafin na dawo harkin haɗamin abincin da zanci?
Sai tayi murmushi tace "Eh mana ko nayi laifi ne dan na dafama abinci?
Sai nace "A'a kawai nayi mamaki ne yau zanci abinci mai daɗi saboda gaskiya abincin da nake dafawa ni kaina bana jin daɗinshi saboda ban iya ba.
Sai tayi dariya haɗe da cewa "A'a wallahi ka iya girki domin abincin da naci jiya yayi matuƙar yimin daɗi.
Bayan nayi wanka a yayin da nake cikin abincin sai na kalleta nace "baiwar Allah har yanzu baki sanar dani sunanki ba balle ki bani labarin dalilin da yasa waɗannan mutanan subiyoki domin cutar da rayuwarki?
Nan take naga damuwa ta bayyana a fuskar ta.
Buɗar bakina sai nace "haƙuri zakiyi domin ki sanar dani duk abun da yake faruwa, saboda hakan ne zai bani ƙwarin guiwar tunkarar iyayenki.
Saboda yaune ya dace na kaiki gida haɗe da yi masu bayanin duk abun da yake shirin faruwa dake.
Nan take naga hawaye ya zubo daga idanun ta sannan ta kalleni tace "tabbas zan baka labarin rayuwata haɗe da dalilin da yasa ake neman rabani da wannan duniyar.
=> 3
Haka ta kalleni da fararan idanun ta haɗe da cewa "sunana HAFSAT.
Rayuwata ta taso cikin jin daɗi da walwala domin mahaifina mai kuɗi ne.
Ko kaɗan mahaifina bayason ganin abun da zai ɓatamin rai.
Amma sai dai nayi rashin wasu mihimman abubuwa a rayuwata.
Domin bansan wacece mahaifiyata ba sai a hoto saboda tun ina yar karama Allah ya mata rasuwa.
Tun daga wannan lokacin mahaifina ya ƙuduri niyar bani cikakkiyar kulawa saboda ni kaɗaice a gareshi, bayan ni bashi da kowa.
Bayan na girma ina kimanin yar shekara 18 sannan na kammala karatuna na secondary.
Kwatsam rannan ina tsaka da cin abinci tare da mahaifina sai nace "abba meyasa baka barina ina shiga cikin al'umma, ko da yaushe daga makaranta sai gida, gashi har na kammala karatuna na secondary ko wata muhimmiyar kawa bani da ita?
Tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin ɓacin ran mahaifina a gareni ba sai a wannan lokacin.
Haka yamin wani mugun kallo haɗe da cewa "to kenan so kike na barki ki riƙa yawo a gari kamar wata tunkiya? to bari kiji ni ba sha-sha-sha bane da zan bari wasu su ɓata tarbiyyar dana baki?
Haka naci gaba da haƙurin zama ni kaɗai a gida.
Idan mahaifina ya fita harkokinshi sai dai na ɗakko ɗaya daga cikin littattafaina na makaranta domin nayi karatu.
Wani lokacin kuma sai dai na dawo falo nayi kallo saboda abun yana matuƙar bani sha'awa idan ina kallo naga sauran muta ne suna harkokinsu a cikin mutane saɓanin tawa rayuwar.
Idan dare yayi kuma bayan nayi sallar isha'i sai na ɗakko Qur'ani domin nayi karatu.
Da safe kuma nafi karanta hadisan Manzon Allah (S. A. W).
Haka naci gaba da haƙurin zama a tare da mahaifina.
To amma duk da cewar yana a matsayin mahaifina hakan bai sa naji kunyar bashi shawarar yin aure ba.
Cikin yanayin ladabi haɗe da tausaya murya nace "Abba tunda Allah yayiwa mahaifiyata rasuwa me zai hana kayi wani auran?
Amma sai mahaifina yaƙi karɓar wannan shawarar tawa domin ko kallona bai yiba balle ya furta wata magana a gareni.
Kwatsam wata rana sai na sake tunkararshi da wannan shawarar.
Cikin yanayin ɓacin rai naga ya nunani da yatsansa ranshi a ɓace yace "muddun baki daina tunkarata da wannan maganar ba to tabbas rainki sai yayi mugun ɓaci sannan yasa kai yayi tafiyarshi.
Kuma a duk lokacin da zai fita kulleni yake a gidan domin baya taɓa barin duk wata hanyar da yasan cewar zata bani damar fita.
Babban abun da yake bani takaicima wani lokacin bai cika kwana a gida ba wasu lokutan har kwana ukku yakeyi ba tare da nasan inda ya tafi ba.
Tun abun baya damuna har akai matakin da na fara zubar da hawaye.
Idan naji yunwa zata takuramin sai na shiga kitchen domin dafa duk abun da rai na yake so saboda kitchen ɗin akwai wadataccan abinci kuma ruwa baya yankewa a gidan.
Wata rana da mahaifina ya fita bashi ya dawoba sai da ya kwashi tsawon kwanaki biyar a wannan lokacin ne na ƙuduri niyar tambayarshi dalilin da yasa wasu lokutan bai cika kwana a gida ba.
Da misalin ƙarfe 1:00 na dare ina kwance a ɗakina sai naji dawowar mahaifin nawa sai nayi kamar bacci nakeyi har ya shigo ɗakin nawa ya fita ban tashi ba.
Bayan gari ya waye lokacin mun kammala breakfast.
Sai na durƙusa har ƙasa na gaishe da mahaifin nawa, sannan nace dashi "abba akwai wata alfarmar da nake nema a gareka, dan Allah ka taimaka ka sanar dani dalilin da yasa kake yawan tafiye-tafiye wani lokacinma har kwanaki kakeyi acan wani wajan ba tare daka sanar dani ba?
Jin haka ne yasa ya kalleni fuskarshi cike da mamaki haɗe da cewa "hafsat wai wanene yake baki ƙwarin guiwar tunkarata da irin waɗannan kananun zantukan marasa daɗin ji a gareni? kwanaki kinyimin magana akan nayi aure, yanzu kuma kin ɓullomin da wata maganar wadda zata iya sawa nayi fishi da ke, to bari kiji ni bazan yi aure yanzu ba.
Kuma batun wannan tafiye-tafiyan da kiga inayi harkokin kasuwancina nake tafiya.
Dan haka kar na sake jin irin wannan maganar daga bakinki.
Jin haka ne yasa na miƙe tsaye jikina a sanyaye ina kuka na kalli mahaifina haɗe da cewa "haba abba wannan wane irin kasuwancine da zaka riƙa fita cikin dare kuma ba kai zaka dawo ba sai tsakiyar dare?
Wani lokacinma kwanaki kakeyi ba tare daka sanar dani ba, ai wannan kasuwanci ne irin na marasa gaskiya.
Tun da nake a tare da mahaifina bai taɓa ɗaga hannu da niyar dukana ba.
Amma a wannan lokacin sai da yasa hannu ya mareni.
Bayan wasu ƴan kwanaki da faruwar haka sai mahaifina ya manta ya fita ba tare da ya rufe ɗakinshi ba.
Bayan nayi wanka na kammala duk wani shirina sai na fito falo domin shan iska.
Zamana kenan sai naga ɗakin mahaifina a buɗe alhalin kuma nasan ya fita, kuma bai saba barin ɗakin nashi a buɗe ba.
Ganin haka ne yasa na tashi domin rufe ɗakin.
Har na jawo ƙofar zan rufe sai nayi ido biyu da wata laida wadda hankalina bai kwanta da ita ba.
Da yake ɗakin mahaifina ne kai na tsaye na shiga ba tare da fargabar komai ba.
A wannan lokacin ne nasan menene tsoro a wannan lokacin ne duk ilahirin jikina ya girgiza a wannan lokacin ne tsoran mahaifina ya shiga jikina.
=> 4
Sannan ta ɗago kai ta kalleni jikinta a sanyaye ba tare da ta sake furta komai a gareni ba.
Koda naga tayi shiru sai na kalleta haɗe da cewa "hafsat me kigani a ɗakin mahaifin naki?
Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da hawaye, haɗe da furta cewar "a lokacin dana buɗe ledar sassan jikin mutun nagani wanda hakan yasa nayi matuƙar razana.
Juyowar da zanyi sai nayi ido biyu da mahaifin nawa tsaye a bakin ƙofar ɗakin.
Ganin yadda ya ƙuramin ido ne yasa na kauda kaina saboda a wannan lokacin banga alamun imani a tattare dashi na.
Ban tashi aune ba sai ji nayi ya dakamin tsawa haɗe da cewa "Uban me kike nema a ɗakina?
Cikin yanayin firgici na ɗago kai na a tsorace, muryata tana rawa nace "abba ashe dama wannan itace sana'arka, ashe dukiyarka duk ta hanyar haram ka tarata?
Cikin yanayin ɓacin rai yace "kwarai kuwa wannan itace sana'ata.
Kuma ba'a iya nan na tsaya ba domin har naman mutane ci nakeyi.
Amma ke bazanyi tsafi dake ba haka zan cinye namanki kamar yadda na cinye naman mahaifiyarki, nadan komai ba sai dan gudun karki tonamin asiri.
Koda naji fitar wannan kalamin daga bakin mahaifina a nan take naji duk ilahirin jikina ya ɗauke wuta hawayen dake idanuwana su daina fitowa.
Haka na matso kusa dashi haɗe da nunashi da yatsana muryata tana rawa nace "abba ashe dama mahaifiyata kai ne wanda kayi sular rabata da rayuwarta.
Cikin yanayin ƙwarin guiwa yace "kwarai kuwa ni nayi ajalinta kamar yadda kema zanyi ajalinki a yau.
Koda ya tabbatarmin da haka nan take na yanke jiki na faɗi ƙasa.
Ganin yadda na ɗauki dogon lokaci ba tare da na farfaɗo ba sai ya ɗakko ruwa daga Fridge ya yayyafamin.
Koda yaga shiru ban tashiba sai ya ɗaukeni yakaini toilet abisa tunanin cewar mutuwa nayi.
Zuwa can da na farfaɗo sai na tashi a tsorace fitowata daga toilet ɗin kenan sai na tasarma ƙofar falo domin ceton rayuwata.
Koda naja ƙofar naji a rufe sai na dawo falo na zauna.
Gaba ɗaya sai hankalina yakasa samun natsuwa.
Zuwa can da dare yayi sai naji shigowar motar mahaifin nawa, cikin suri natashi na ɓuya a bayan kofar falon.
A yayin da ya buɗe ƙofar falon yana shigowa sai nikuma nayi waje da gudu, ban sani ba ashe akwai wasu abokan harkar mahaifin nawa da ya shigo tare dasu a motar da mahaifin nawa ya shigo da ita.
A yayin da mahaifin nawa yaga fitata sai ya fito a tsorace yana mai furta cewar ku taremin ita karku bari ta fita.
Ni kuma tuni naje bakin gate haka naita gudu suna bina a baya sai Allah ya taimake ni na haɗu da kai.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "wannan shine abun da ya faru dani kuma nagode abisa wannan taimakon da kayimin, dan haka yau zan tafi saboda banason wani abu ya faru da kai a dalilina.
Koda naji haka sai na kalleta haɗe da cewa "to amma baki da wasu dangin dasu shafi mahaifinki ko ita mahaifiyar taki?
Nan take naga wani sabon hawaye ya faso daga idanunta cikin yanayin kuka tace "bani da kowa kuma bansan inda zani ba kawai zan tafi ne saboda banason nayi sular jefa rayuwarka a haɗari saboda nasan yanzu haka mahaifina yasa a nemoni duk inda nake, kaga idan har yayi arba dani a tare da kai to na tabbata kaima bazai barka a raye ba.
Jin haka ne yasa nan take na share hawayen dake fuskarta haɗe da cewa "hafsat ba inda zaki, daga yau kin zama ƙanwata dan haka zan ci gaba da zama a tare dake a nan gidan.
Cikin yanayin sanyin jiki hawaye yana zuba daga idanunta tace "na gode kuma in Allah ya amince zan kasance mai yima biyayya, kuma in Allah ya amince bazan taɓa aikata abun da zaisa ranka ya ɓaci a dalilina ba.
Tun daga wannan lokacin sai na ƙudiri niyar kyautatama rayuwar Hafsat.
Washe gari da yamma sai na ɗauketa a mota na kaita wata plaza domin tayi saye-saye kayan da zara riƙa sawa.
Bayan mun dawo gida sai tayi wanka ta canza kaya ni kuma sai na shiga kitchen domin haɗa mana abun da zamuci.
A yayin da nake cikin ƴan haɗe-haɗen kayan girkin sai hafsat ta shigo kitchen ɗin.
Koda na kalleta sai tayi murmushi haɗe da cewa "haba yayana ai girki na mata ne dan haka ka koma falo kayi kallo domin ni zanyi wannan girkin.
Haka dai muci gaba da zama a tare cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba.
Mukanyi karatu tare muci abinci tare idan dare kuma yayi ɗakinta daban nima nawa ɗakin daban yake.
Badan kowa nasawa motata baƙin tinted ba sai dan buƙatar lokaci-lokaci na riƙa fita da hafsat domin yawatawa da ita wuraren da batasani ba.
Akwana a tashi dai har son hafsat ya shiga zuciyata.
Kwatsam wata rana sai hafsat ta matsantamin akan lallai sai na kaita Kano domin taga iyayena.
Haka ne yasa nayi dariya alokacin da hafsat ta tunkareni da wannan buƙatar.
Ganin yadda tayi matuƙar nuna son zuwa Kano domin taga ahalina ne yasa nace "to shikenan ki shirya gobe idan Allah ya kaimu zan kaiki garin kano.
Tun a wannan ranar hafsat ta fara zumuɗi saboda tun da take a rayuwarta bata taɓa zuwa kano ba.
Ita a nata tunanin daga Adamawa zuwa Kano ba wata tafiyace mai nisa ba.
Washe gari da misalin ƙarfe 12:00 na rana mu ɗauki hanya.
Koda hafsat taga sai faman zuba tafiya muke sai ta kalleni haɗe da cewa "yayana wai sai yaushe zamu isane?
Buɗar bakina sai nace "akwai sauran tafiya sosai idan bacci kikeji ki kwanta kiyi baccinki.
A haka dai har hafsat ta gaji da zama wanda hakan yasa bacci yayi awan gaba da ita.
A taƙaice dai bamu mu samu shiga Kano ba sai cikin dare.
Da isarmu gida bayan an buɗe mana get mun shiga sai nayi shiru domin nazarin amsar da zanba mahaifina ko mahaifiyata musamman idan su nemi jin dalilin zuwana gida da mace alhalin kuma makaranta a turani.
Koda hafsat taga nayi shiru sai tace "lafiya kuwa naga kayi shiru.
Sai na lalle ta haɗe da cewa "nasan dole ne sai iyayena sun nemi jin dalilin taho dake wannan gidan namu.
Koda na kalleta sai nace "hafsat bazai yiwu ba ace na sanar da iyayena gaskiyar dalilin haɗuwata da ke ba.
Dan haka dole ne sai munyi masu ƙarya badan komai ba sai dan gudun samun matsala.
Sai tace "to yanzu wace amsa zaka basu kenan, saboda ko kaɗan ban ɗauka cewar za'a samu wannan al'adun ba.
Sai nayi murmushi haɗe da cewa karki damu, kawai abun da nakeso a gareki shine karki kuskura kinuna kamar munyi matuƙar shaƙuwa da juna, ni nasan hanyar dazan ɓullo masu.
Sai tace "to shikenan.
Da shigarmu bayan nayi sallama sai nayi ido biyu da mahaifina zaune a falo.
Gefe ɗaya kuma Ameena ce zaune tare da mahaifiyata.
Ɗayan ɓangaren kuma yayata ce zainab kwance a saman kujera tana bacci.
Koda Ameena taji muryata a yayin da nayi sallama sai ta taso da gudu ta rungumeni tana murna.
A gidanmu kowa sai murna yake saboda mundaɗe bamu haɗu ba.
Koda na hada ido da mahaifina banga alamar wani farin cikiba face ɓacin rai.
Kawai sai na fuske ba tare da na nuna wata fargaba ba haka na durƙusa har ƙara na gaishe da mahaifiyata.
Haka shima mahaifina nawa na gaishe shi kamar yadda na gaishe da mahaifiyar tawa, amma sai ya amsa ranshi a ɓace.
Haka itama hafsat ta gaishesu cikin girmamawa.
Bayan mun zauna sai nace "abba itama wannan a school ɗin da nake karatu take gudanar da nata karatun.
Lokacin da zan taho gida ne sai Allah yasa itama a wannan ranar zata dawo gida, wannan ne dalilin da yasa mutaho tare.
Ganin dare yayi ne alokacin da mu shigo Kano yasa na yanke shawarar kawota nan domin ta kwana idan Allah yasa gari ya waye sai ta wuce gida saboda itama yar nan jahar Jigawace.
Koda mahaifina yaji wannan bayanin daga bakina sai naga ya saki fuskarshi haɗe da cewa "to sannunku da zuwa.
Sannan ya kalleta haɗe da cewa "to ke kuma me kike karanta a school ɗin naku?
Koda naji haka sai na ɗanyi dariya haɗe da cewa "abba ai department ɗinmu ɗaya duk abun ɗaya muke karanta.
Sai yace "to yayi yau Allah ya taimaka sai mu amsa da Ameen.
Bayan gari ya waye lokacin munyi breakfast har mahaifina ya fita sai ya dawo, da shigowarshi falo sai ya kirani.
Wasu kuɗi naga ya miƙomin haɗe da cewa "ga wannan kaba abokiyar karatun taka idan zata tafi saboda zata iya yiwuwa kafin nadawo ta tafi.
Koda na kalli hafsat sai nace "abba ai ɗazu takira numbar mahaifinta bayan sun gaisa shine take sanar dasu yau zataje gida sai.
Abban nata yace ai basa gida sunje bikin wani ɗan uwansa a jahar bauchi tare da mahaifiyarta kuma zasu kai kamar kwana biyu acan.
Sai mahaifin nawa yace "au itama kai tsaye ta taho batare da ta sanar dasu ba kamar yadda kaima ka taho kanka tsaye batare da ka sanar dani a waya ba ko?
Sai nace "A'a abba tun jiya take ƙoƙarin kiran mahaifin nata amma shiru wayar bata shiga sai yanzu da safe ne tasamu sa'a wayar ta shiga.
Sai yace "to shikenan amma dan Allah ku riƙa kiyayewa domin sanarwa kafin ayi tafiya tana da matuƙar amfani.
Sannan yace "to amma me zai hana ta zauna anan har zuwa lokacin da zasu dawo.
Sai nace "to shikenan abba.
Bayan ya tafi sai hafsat ta kalleni tayi murmushi.
A wannan ranar haka na fita yawo tare da hafsat ba tare da kowa yasan abun da yake a tsakanina da ita ba.
A yayin da muke cikin tafiya sai hafsat ta kalleni haɗe da cewa "amma gaskiya ka iya wayo.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "na iya ƙarya dai, kuma ita ƙarya bata ɗaya daga cikin wayo domin ba abace mai kyau ba.
Kawai na aikata haka ne domin kar a samu sabanin da zaisa mu nisanta da junanmu.
Saboda nayi miki alƙawarin bazan bari wani abu ya faru dake ba.
Cikin yanayin tausasa murya tace "gaskiya bani da abun da zan iya sakama dashi wanda ya wuce godiya saboda kai mutun ne mai tausayi haɗe da kyautatawa.
> 5
bayan kwana biyu da misalin ƙarfe 7:00 na safiya sai na samu mahaifina a ɗaki bayan mun gaisa sai nace "abba yau zan koma school yanzu zanje nakai hafsat tashavne domin tahau mota zuwa jahar jigawa, sannan ni kuma na dawo na shirya domin tafiya.
Bayan hafsat ta kammala shirinta sai ummata da abbana su kawo wasu ƴan kuɗi su bata haɗe da cewa "ga wannan kisha ruwa a hanya.
Bayan mun fito waje a yayin da muke shirin shiga mot sai ƙanwata ameena ta biyo bayanmu fuskarta cike da damuwa.
Sai hafsat tayi murmushi haɗe da cewa "Ameena me yake faruwa ne domin naga kamar akwai damuwa a tattare dake?
Sai tace wallahi anty hafsat ko kaɗan banason wannan tafiyar taki, wallahi da abba zai amince da sai na biki saboda nalura halinki ba ɗaya ba ne dana yayana.
Nan take naji raina yai matuƙar ɓaci koda hafsat taga rai na ya baci sai ta kalli Ameena haɗe da cewa "habaameena wannan kuma wace irin magana ce haka, yanzu ko kunya bakiji ba kike faɗama yayanki irin wannan maganar?
Sai ameena takalli hafsat tace "haba hafsat me kuma yai zafi haka ai kamata yai ki tambayeni dalilin furta wannan kalamin kafin ki bayyana ɓacinranki a game da maganata.
Sai hafsat tace "A'a kiriƙe dalilinki kibarni da rashin sanina.
A wannan lokacin ni kuma ina tsaye rai na a ɓace ina kallan ikon Allah.
Saboda maganar gaskiya bani da yadda zanyi da ameena.
Muddun nakuskura na taɓata to lallai rai na sai yai matuƙar ɓaci a wajan mahaifina, nikuma ko kaƙan banason abun da zai haifar da ɓacin ran iyayena.
Ba yadda na iya haka nahau mota mu tafi ba tare da na furta wata magana a gareta ba.
Bayan mun tafi, a yayin da mu kusa fita daga cikin garin Kano sai nayi packing a kusa da wani restaurant na aje hafsat a shagon wani mutumina nace tajirani bazanjima ba zan dawo gareta.
Ji nayi ta riƙe hannuna haɗe da cewa "dan Allah yayana kayi sauri ka dawo saboda hankalina bai gama kwanta da wannan wajan ba.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "haba ƙanwata karkiji komai domin ina tare dake dan haka ba abun da zai rabani dake.
Kawai kisa a ranki cewar a duk inda na tafi to zuciyata tana tare dake.
Sai tayi murmushi haɗe da furta cewar "to shikenan yayana Allah ya dawomin da kai lafiya domin kalamanka suna tattare da wani sinadarin da yake kawarmin da dukkanin damuwar dake shirin samawa kanta wajan zama a zuciyata.
Sannan kuma dan Allah karka biyema ƙanwarmu Ameena.
Duk abun da zatayima zanso ka kauda kanka a gareta.
Bayan na koma gida sai mahaifiyata tace "har ka kaita tashar?
Koda naji mahaifiyata tayimin wannan tambayar nan take naji ƙirjina ya buga saboda nayi tunanina ko sun gane abun da nake boyewa a garesu ne.
Cikin yanayin saurin baki nace "eh umma ai ban baro wajan ba har sai da naga tafiyarta.
Koda naji tace "to Allah ya saukesu lafiya sai naji hankalina ya samu natsuwa.
Bayan na shiga ɗaki na ɗakko handbag ɗina, sai nayi ban kwana da iyayena.
Sannan naje gaban yayata zainab haɗe da cewa "to aunty ni zan tafi.
Sai tace to Allah ya saukeka lafiya.
Koda na kalli Ameena sai na dafa kafaɗarta nace ƙanwata bakimin addu'a ba?
Sai tayi murmushi haɗe da cewa "to Allah ya kaika lafiya ya kuma baka ilimi mai amfani.
Cikin yanayin sakin fuska nace ameen ƙanwata nagode.
A yayin da na shiga mota ban tsaya ako ina ba sai a wajan da na aje hafsat.
Da zuwana bayan nayi packing hafsat ta taso zata shiga mota kenan sai tayi ido biyu da mahaifinta adai-dai lokacin da ya fito daga wani gida.
Koda hafsat taga alamun eh lallai ya ganeta sai ta shiga motar da sauri a gigice.
Ganin haka ne yasa nace da ita "hafsat lafiya kuwa, me yake faruwa naga duk kinbi kin ruɗe?
Muryarta tana rawa tace "dan Allah kayi sauri mu tafi wallahi abbana ya ganni.
Juyawar da zanyi sai naga har yazo kusa da motar.
Ganin haka ne yasa na kalli hafsat haɗe da cewa "karkiji tsoro kuma karki kuskura kiyi wata magana.
Sai ta jinjina kai tace to.
A yayin da mahaifinta ya ƙaraso gareni sai ya kwankwasa glass.
Dayake motar tanada baƙin tinted wanda hakan yasa ba yadda za'ai ya iya ganin abun dake ciki.
Sai na zuge glass ya kalleni na kalleshi, bayan mun gaisa sai yace "dan Allah malan ko zan iya ganin wadda ta shiga motarnan yanzu?
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "haba malan wannan kuma wace irin maganace.
Sai yace "dan Allah karka damu nasan dole ne kaji tambayar tayima wani iri domin a zahirin gaskiya yarinya tace ta ɓace yau kimanin watanni bakwai kenan rabona da ganinta.
Kuma wadda naga ta shiga wannan motar taso tayi kama da ita.
Sai na kalleshi da fuskar tausayawa haɗe da cewa "to gaskiya wannan ba ita bace domin wannan matatace kuma munkai kimanin shekara ukku da aure.
Amma bari ta fito domin idanka yaga zahiri.
Sai yace "a'a ai baza ayi haka ba saboda na aminta da duk maganarka sannan ya juya ya tafi.
Bayan ya tafi a yayin da muke cikin tafiya sai hafsat ta dawo gaban motar.
Haka ta kwanta a jikina tana kuka haɗe da cewa "kayimin komai a rayuwata gashi har ƙarya kayi a kaina duk dan buƙatar ka ceci rayuwata.
Sai nace "haba hafsat ai wannan ba lokacin kuka ba ne domin wannan lokaci ne da ya kamata kiyiwa mahaliccinmu godiya abisa taimakon bayinsa da yakeyi a lokacin da suke namen taimako.
A yayin da muyi nisa da tafiya sai naga tayi murmushi.
Ganin haka ne yasa na tambayeta domin jin abun da yasa take murmushi ba tare da wani dalili ba.
Buɗar bakinta sai tace "A lokacin da naji ka furtawa mahaifina cewar ni matarkace ba ƙaramin daɗi naji ba shiyasa idan natuna dole ne sai murmushin farin ciki ya bayyana a fuskata.
Sai nace "kuma kinga murmushinki ba ƙaramin kyau yake miki ba, inama dai ace zaki mallakamin wannan murmushin naki na tsawon har abada na tabbata da ba wanda zai fini farin ciki a faɗin duniyar nan.
Sai tayi dariya sannan tace "haba yayana ai tuntini na zama taka.
Haka dai muci gaba da fira har ta gaji tayi bacci.
Hafsat tana matuƙar jin daɗin zama a tare dani kamar yadda nima nakejin daɗin zama a tare da ita.
Kuma allah cikin ikonsa shaiɗan bai taɓa shiga tsakanina da hafsat ba.
Duk ranar asabar da lahadi ina fita tare da ita domin yawatawa cikin gari amma munfi fita da yamma.
To ashe dai rashin sani yafi dare duhu domin shaiɗan yana nan zuwa garemu domin ba mantawa yai da shafinmu ba.
Kwatsam wata ranar litinin da misalin ƙarfe 9:00 na dare sai nace da hafsat ta ɗan dafamin Tea nasha saboda a wannan ranar banajin marmarin abinci.
Koda hafsat ta shiga kitchen domin haɗa tea ɗin sai ta duba taga ai lipton tuni ya ƙare.
Ganin haka ne yasa ta fito domin sanar dani cewar ba Lipton.
Haka ta sameni zaune a falo cikin yanayin tausasa murya tace "yayana sai dai kayi haƙuri domin na manta tun jiya ban sanar da kai cewar Lipton ya kare ba.
Jin haka ne yasa na fita domin zuwa wani shagon dake kusa damu domin siyo Lipton ɗin.
Da zuwana sai na sami mai shagon har ya kwashe kaya yana shirin rufe shagon.
Bayan na dawo gida a yayin da na siyo Lipton ɗin.
Koda nayi sallama naji shiru sai na leƙa ɗakin hafsat ban ganta ba.
Na shiga kitchen babu ita sai nayi tunanin ko ta shiga wanka ne.
Wannan tunanin ne yasa na sake komawa ɗakin nata domin yin sallama.
Da zuwana bayan nayi sallama a ƙofar ɗakin nata sai naji tayi gyaran murya wanda hakan yasa na fahimci wanka takeyi.
Nan take naji jikina yai sanyi domin na ɗauka ko wani abun ne yake shirin faru da ita.
Haka na koma falo na zauna.
Bayan ta fito sai tace "dan Allah yayana kayi haƙuri na ɗan shiga wanka ne.
Sai nace "to ai tunda Allah yasa kinyi wanka kinga babu batun dafa lipton kenan ko?
Sai tace "haba yayana yanzu wankan da nayi ne zai hanani dafama lipton?
Sai nace "a'a kawai nacanza shawara ne nima abincin da zakici shi zanci saboda munriga mun zama ɗaya kinga yazama dole abun da zamuci shima ya zama ɗaya.
Sai tace "khayyayana kaifa kace bakajin marmarin abinci kafison na dafama Tea?
Sai nace to ai yanzu inajin marmarin abinci tunda na tabbata kema kinason abincin.
Nan take na tashi na buɗe fridge na ɗakko lemo na'aje a gabana sannan na kalleta haɗe da cewa "maza kije ki dakko mana abinci domin yunwa nakeji.
Bayan munci abinci munsha lemon dana dakko a fridge cikin ƙanƙanin lokaci sai bacci ya ɗauke hafsat.
Koda hafsat ta farka daga bacci sai ta tsinci kanta a kwance a saman gado cikin wani mummunan yanayi.
Nanfa hafsat ta fito daga ɗaki tana kuka.
Koda sautin kukanta ya sauka a kunnena firgigit na tashi a tsorace.
Haka hafsat ta kalleni haɗe da nunani da yatsanta sannan tace "Allah ya isa tsakanina dakai, wallahi da nasan haka halinka yake da tuni na nisanta kaina a gareka.
Kuma wallahi bazan taɓa yafema ba sannan tasa ƙafa tayi waje tana kuka.
=> 6
Ganin yadda ta fita tana kuka ne yasa al'amarin yai matuƙar ɗauremin kai wanda hakan yasa a zuciyata nace "me yasa cikin ƙanƙanin lokaci hafsat zatamin haka?
Fuskata cike da ruɗani nabi bayanta.
Bayan na fito daga gidan haka na ƙaraci yan duɓe-duɓena amma ban samu ganin Hafsat ba.
Haka na koma gida fukata cike da mamakin ganin yadda Hafsat ta juyamin baya.
Haka na damu kaina a game da tunanin halin da zata tsinci kanta a ciki ba domin zaiyi wahala hafsat ta samu wanda zai kyautata mata fiye dani.
Na ɗauka hafsat zata dawo gareni abu kamar wasa har a ɗauki tsawon kwanaki ukku ba hafsat ba labarinta.
Sannu a hankali dai kwanaki sai tafiya sukeyi har a cimma sati ɗaya da tafiyar hafsat.
Ganin haka ne yasa na cire tsammanin sake haɗuwa da hafsat, domin zata iya yiwuwa wajan mahaifinta ta koma.
Kuma gashi Allah baisa nasan takamaiman gidan da mahaifin nata yake da zama ba.
Tun daga wannan lokacin walwalata haɗe da farin cikina su samu tangarɗa, saboda zuciyata ta kamu da matsanancin son hafsat.
A haka dai har Allah yasa na kammala karatuna na koma gida Kano ba tare da na sake sa tsammani haɗuwa da hafsat ba.
Kimanin watanni 6 da komawata gida.
Kwatsam wata rana ina zaune a falo tare da ƙanwata Ameena da kuma yayarmu zainab munata wasa da dariya gefe ɗaya kuma mahaifiyarmuce zaune tana sauraran mu.
Bansani ba a she tashin hankali ne yake tunkaroni a dai-dai wannan lokacin.
Fitowar mahaifina daga ɗaki kenan a yayin da yake haramar tafiya office sai Allah yai shigowar hafsat.
Muryarta kaɗai naji a lokacin da tayi sallama wanda hakan yasa nayi gaggawar waigawa a tsorace.
Abun mamaki ganin hafsat nayi rungume da ƙaramin jariri a hannunta.
Cikin yanayin mamaki mai tattare da murnar sake haɗuwarmu nace "hafsat dama kina raye, ina kishiga tsawon wannan lokacin, wannan jaririn kumafa, kodai kinyi aurene ban sani ba?
Cikin yanayin ɗaga murya tace "dalla rufemin baki, ko kunya babu ka wani zo gabana ka tsaya sai wasu wawayen tambayoyi kakemin, to nazo ne domin na baka ɗan da kamin ciki na haifa.
Nan take naji wani dumm!! cikin ƙanƙanin lokaci duk na rikice.
Jin fitar wannan kalamin daga bakin hafsat ne yasa yayata zainab haɗe da ƙanwata ameena da mahaifiyata duk su mike tsaye a tsorace.
Koda na haɗa ido da mahaifina sai naga ya cire farin glass ɗin dake fuskarshi.
Buɗar bakin mahaifina a yayin da ya kalli hafsat sai yace "ke ki dubi tsakaninki da Allah ki faɗamin gaskiya shin wannan jaririn nawaye?
Nan take wani sabon hawaye ya faso daga idanun hafsat.
Haka ta kalli mahaifina fuskarta ba alamar wasa tace "wallahi dama nasan dole ne sai kunyi mamakin wannan al'amarin da ya faru a tsakanina da ɗanku.
Amma bari na baku labarin yadda wannan al'amarin ya faru tun daga farko har ƙarshe domin bazan iya ɓoye maku komai ba.
Nan take hafsat ta basu labarin komai.
Jin bayanin da hafsat tayi ne yasa mahaifiyata taja hannun zainab haɗe da ƙanwata ameena su shiga ɗaki suna kuka.
Na buɗa baki zanyi magana sai mahaifina ya dakatar dani hade da cewa "kaga dakata bana buƙatar jin komai daga bakinka saboda kai maƙaryqci ne shi kuma maƙaryaci munafiki ne.
Sannan ya kalleni haɗe da cewa "shi kuma munafiki yana da babbar illa domin illarsa tana haifar da babban tashin hankalin da zai iya shafar waɗan da basuji ba kuma basu gani ba.
Dan haka a matsayinka na munafiki illarka ta cutar dani kuma ta cutar da mahaifiyarka haɗe da yayarka da ƙanwarka da dukkanin zuri'armu baki ɗaya.
Dan haka bani ba kai daga yau nayima iyaka da shigowa gidan nan kuma karka sake tun karata da wata buƙata domin ka gurɓata daga cikin ƴay'ƴa managarta.
Sannan yasa hannu ya karɓi jaririn dake hannun hafsat.
Bayan hafsat ta tafi sai na tasarma ɗakina domin ɗaukar wasu daga cikin kayana.
Kawai sai ji nayi mahaifina ya dakamin tsawa haɗe da cewa "ina kuma zaka shiga?
To bari kaji wallahi ba inda kake da damar shiga a gidannan dan haka maza ka fice min daga gida.
Tabbas abun ya bani mamaki sakamakon ganin yadda mahaifina ya dakamin tsawa.
Ba yadda na iya haka nayi waje hannu rabbana.
Hatta wayatama bai bari na ɗauka ba haka natafi ba tare da nayi bankwana da mahaifiyata ba.
Bayan ya koma ɗaki ko nisa banyi ba sai ƙanwata ameena ta biyo bayana ba tare da mahaifina ya sani ba.
A yayin da nake cikin tafiya sai ji nayi ameena tace "yayana ina kuma zaka?
Cikin yanayin kuka nace "zan tafi inda zaku daɗe ba tare da kun sake ganina ba.
Sai ta rungumeni tana kuka haɗe da cewa "dan Allah yayana karka tafi kabarni, wallahi nasan bazaka taɓa iya aikata haka ba.
Sai nace "A'a Ameena ni nasan zuciyarki ta gama amincewa da wannan maganar da hafsat tazo da ita domin akaf gidanmu kece wadda ta fara challenging a game da halayyata.
Sai tace "haba yayana kasan hankalina da naka ba ɗaya bane.
Wallahi duk wata rigimar da zakaga tana faruwa a tsakanina da kai a matsayin wasa nake ɗaukarta, yanzu ashe bakasan idan zaman lafiya yai yawa a gida wasa yakan shiga tsakanin yaya da ƙanwarsa ba.
Sannan ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa wallahi abun yana matuƙar bani sha'awa ne idan naga ƙawayena suna wasa da dariya a tsakaninsu da yayyunsu.
Haka ne yasa nima nake wasa da kai amma dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba.
Sai nace ba komai ƙanwata ai ke tawace na haƙura.
Sai tace "to yayana idan kuma ka tafi sai yaushe zaka dawo?
Ban kaiga bata amsaba sai mahaifina ya fito daga gida wanda hakan yasa nace da ameena maza ki koma gida kar laifina ya shafeki.
Haka ta tafi tanamin kallon tausayawa fuskarta cike da hawaye.
Da yake ATM ɗina yana aljihuna kai tsaye na wuce First Bank ɗin da yake a bayan layinmu da zuwana na ciri 50 thousand daga account ɗina.
A wannan ranar ne nayi bankwana da kano.
Ba inda na tsaya sai a KWARA state.
Bayan kuɗin dake ATM ɗina sun ƙare nasha matsanan ciyar wahalar rayuwa a garin kwara.
Domin sai da takai matsayin abincin da zancima yana nema ya gagareni.
Wajan kwana kuma ba'a magana domin wasu lokutan a rumfar kasuwa nake kwana tare da wasu daga cikin yan ci rani.
Tabbas na shiga halin damuwa da tashin hankali wanda hakan yasa na fahimci cewar wasu matan basusan halacci ba.
Haka ne yasa na gwammaci mutuwa ba tare dana sake kula wata mace da sunan taimako ko soyayya ba.
A yayin da al'amurana su gama rincaɓewa sai na koma ɗaukar dako a kai na.
Kai har faskaran itace sai da nayi domin na samu kuɗin da zanci abinci.
Kuma ba ranar da bana tunanin gida a kwana a tashi dai har na ɗauki tsawon shekara 1 a garin kwara.
Kawai wata ranar laraba ina zaune a kusa da wani shagon da nake siyen garin kwaki gashi ranar na wayi gari ba ko sisi a aljihuna wanda hakan yasa nayi tagumi.
Abun duniya ya isheni tun daga wannan ranar na ƙuduri niyar jajir cewa wajan tara kuɗin da zasu maidani gida kano.
Domin na tabbata idan yunwa tayi ajalina a garin kwara to banga yadda za ai gawata ta koma gida ba.
A tsakanin sati 3 Allah ya bani sa'a na samu wasu ƴan kuɗi masu dan kauri.
Domin 7 thousand a wannan halin da nake ciki kuɗi ne masu matuƙar daraja a wajena.
Kai tsaye na tasarma tashar moto domin komawa gida.
Tun kafin na shiga tashar motocin zuciyata take bani shawara.
Haka na riƙa saƙe-saƙen cewa "anya idan na koma gida bazan sake fuskantar wata matsalar ba kuwa?
Koda na shiga tashar motocin sai zuciyata ta canza min ra'ayi.
Ba kuma wani ra'ayi ta canzamin ba illa ra'ayin komawa jahar Adamawa wato garin da nayi karatu kenan.
Ta wani ɓangaran kuma sai zuciyar take bani shawara akan cewar "me zaisa na koma adamawa alhalin acan ne matsalata ta samo asali.
Ba yadda na iya haka na watsar da duk wasu saƙesaƙen dake zuciyata.
Haka na hau mota zuwa Adamawa saboda ina kyautata zaton sai nafi samun natsuwa acan.
Haka na dage da neman taimakon manyan motocin dake wucewa saboda kuɗin dake wajena ba yadda za'ai su iya kaini jahar adamawa.
A yayin da na samu nasarar sauke ƙafata a garin Adamawa sai na sauka a wajan wani classmate ɗina wanda muyi karatu tare.
Amma ko kaɗan ban bari yasan abun da ya faru dani ba.
Kwana ɗaya da saukata garin adamawa sai Allah ya jarabceni da wata matsanan ciyar rashin lafiya.
Koda abokin nawa yaga haka sai ya ɗaukeni zuwa wani babban asibitin dake garin domin duba lafiyata.
Da zuwanmu bayan anyimin wasu yan aune-aune sai likitan ya sanar damu cewar jinina ne ya hau sakamakon yawan tunane-tunanan da nake damun kai na dasu wanda hakan yasa yimin wasu yan allurai sannan ya samin ledar ruwa.
Kwananmu biyu a asibitin a sallameni.
Munzo fita kenan sai akawo wani marar lafiya ana turashi a irin kekennan na guragu.
A wannan lokacin nayi matuƙar mamakin ganin yadda yakemin kallan sani domin har mufita daga asibitin bai daina waigena ba.
Fitarmu daga asibitin kenan sai wanda yake turashi a keken guragun ya biyo bayanmu.
Da zuwanshi garemu bayan mun gaisa sai yace "dan Allah kuyi haƙuri wani bawan Allah ne da na kawoshi nan asibitin yanzu yakeson magana daku.
=> 7
bayan mun ƙarara gareshi sai ya miƙomin hannu mugaisa.
Sannan ya kalleni yace "dan Allah malan ina wannan ƙanwar taka?
A wannan lokacin ne ya jefani a ruɗani domin bansan wace ƙanwar tawa yake nufi ba.
Buɗar bakina sai nace "kana nufin Ameena?
Sai yace "Eh amma gaskiya ban san sunanta ba, wannan wadda nake yawan ganinka tare da ita amma nafi ganinku kamar ranar asabar ko lahadi domin yanzu an samu kimanin shekara ɗaya kenan rabo a da sake ganinta.
Jin haka ne yasa na fahimci hafsat yake nufi.
Nan take ɓacin rai ya bayyana a fuskata domin ko kaɗan bana ƙaunar abun da zaisa na tuna da Hafsat.
Buɗar bakina sai nace "malan me ya faru kake tambayata inda hafsat take?
Sai yace "dan Allah idan bazaka damu ba ina buƙatar mukoma gefe domin wannan maganar tana buƙatar sirri.
Nan take naji ƙirji na ya buga saboda bansan wace maga zanji daga bakinshi ba.
Buɗar bakinshi a yayin da mu koma gida sai yace "gaskiya malan bazan iya ɓoyema komai ba.
Domin a zahirin gaskiya na cuci hafsat, kuma na cuci iyayenta.
Saboda gaskiya na aikatama hafsat babban laifi.
Kuma nayi nadamar abun da na aikata a gareta.
Sannan ya lalle i haɗe da cewa "na fara ganin hafsat ne a wata ranar asabar lokacin na shiga wata supermarket.
A wannan lokacin ne naji hafsat takwanta min a rai na wanda hakan yasa naje gareta.
A yayin da na ƙarasa gareta bayan nayi mata sallama ta amsa shikenan sai taja bakinta tayi shiru.
Haka na ƙaraci maganata tayi banza dani ba tare da ta sake furta wata magana a gareni ba.
Bayan ta kammala siyan abun da zata siya har ta juya zata tafi sai tsautsayi yasa na riƙe mata shijab haɗe da cewa "haba baiwar Allah ya zaki tafi kamar ba dake nake magana ba.
Ban tashi aune ba sai naji saukar mari a fuskata hatta mutanan dake wajan sai da suyi mamakin ganin yadda hafsat ta tsunkeni da mari.
Tun daga wannan lokacin na ƙuduri niyar wulaƙanta rayuwar hafsat.
Bayan anyimata calculating ɗin abun da ta siya ta biya sai tayi waje.
A wannan lokaci ne nima na biyo bayanta, fitowata kenan sai naga ta hau wata mota ƙirar corolla tare da kai.
Haka nayita bin bayanku har Allah yasa na gane gidan da kuke da zama.
Bayan na dawo gida saina fara shirya tagged ɗin da zaisa na rama cin mutumcin da hafsat tamin.
A ƙalla nakai kimanin sati ukku ina bibiyarku wanda hakan yasa na gane cewar iya ku biyu ne kawai kuke rayuwa a gidan da kuke zaune.
Yanayin yadda naga kuna gudanar da rayuwarku ne yasa na fahimci cewar hafsat ƙanwarkace ba matarka ba.
Kuna gudanar da duk wasu harkokinku tare domin har cin abincima tare naga kunayi amma bakwa kwana ɗakk ɗaya kuma bakwa taɓa jikin junanku haka ne yasa na gane cewar hafsat ƙanwace a gareka.
Kwatsam wata ranar litinin da misalin ƙarfe 9:00 na dare lokacin ina zaune a kusa da gidan naku sai naga ka fito daga gidan.
Ganin yadda ka fito ba tare da mota ba yasa na fahimci ba nisa zakayi ba.
Da fitowarka ko nisa bakayi ba sai na shiga gidan kaina tsaye.
Sai nayi sa'a a wannan lokacin ita wadda ta mareni ta shiga wanka wato hafsat kenan.
Haka ne ya bani damar buɗe fridge ɗin da kuke amfani dashi wajan aje drinks.
Haka na zuba kwayar da zata saku bacci a wani babban drink ɗin da maga kunfi shansa musamman idan dare yayi.
Bayan ka dawo sai da na dai-daici kunsha wannan drink ɗin bacci ya daukeku sannan na fito daga wani ɗakin dake kusa da kitchen ɗin gidan.
Haka na ɗauki hafsat na kaita daki na biya buƙatata a gare ta.
Allah cikin ikonsa bayan na fito daga gidan a yayin da nake cikin tafiya sai wata mota ta bugeni.
=> 8
koda naji bayanin komai daga bakinshi nan take nayi ƙas da kai na haɗe da furta kalmar "innalillahi-wa'inna-ilaihi- raji'un.
Sannan na kalleshi haɗe da cewa "yanzu meye amfanin aikata irin wannan?
Tabbas kacuci hafsat kuma nima ka cuceni domin yau kimanin shekara ɗaya kenan da mahaifina ya koreni daga gida, domin su a nasu tunanin ni nayima hafsat ciki.
Koda yaji batun ciki a game da wannan al'amarin cikin yanayin firgici ya yace "subuhanallahi, yanzu kana nufin hafsat ta samu ciki a dalilin amfanin da nayi da ita?
Sai na jinjina kai haɗe da cewa "kwarai kuwa hafsat ta samu ciki kuma har ta haihu.
Kuma dan Allah ina roƙonka da ka taimaka muje wajan iyayena saboda kai kaɗai ne a fadin duniyarnan zaka iya wankeni daga wannan mummunan laifin da iyayena suke kallona dashi.
Nan take ya fashe da kuka yana mai furta cewar "dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin nasan na aikata laifi mafi muni a gareku, amma yanzu nayi nadama kuma a shirye nake wajan tunkarar iyayanka domin wankeka daga wannan baƙin laifin da suke tunanin kai ka aikata.
Bayan na sanar da abokin nawa duk halin da ake ciki washe gari da sassafe sai mu ɗauki hanyar KANO.
Koda naga mun isa garin kano sai farin ciki ya fara ratsa zuciyata.
Saboda na daɗe rabon da ace nasa ahalina a idanuna.
Da shigarmu gidan namu bayan munyi sallama sai naji ƙirjina ya buga a sakamakon kallon da naga mahaifina ya min.
Cikin gaggawa naga ya miƙe tsaye ranshi a ɓace ya nunani da yatsansa haɗe da cewa "me kuma ya sake dawo da kai garemu?
Buɗar bakina sai nace "abba dan Allah ka tsaya ka saurari maganar da muzo da ita, domin ko babu daɗi ni ɗanka ne.
Kuma wallahi bani da hannu a game da laifin da kuke tunanin na aikata.
Jin haka ne yasa mahaifiyata ta kalleni haɗe da cewa "to idan ba kai ka aikata ba to waya aikata?
Buɗar bakina sai nace "yau ne zan sanar daku bayanin komai a game da dalilin da yai sukar haɗuwata da hafsat saboda a wancan lokacin iya bayanin cikin da take ɗauke da shi kawai ta sanar daku, amma sauran bayanin yadda ai ciki ya samu shiga jikinta wannan bawan Allan da nake tare da shi ne zai yi sanar daku cikakken bayanin komai.
Nan take na fara yi masu bayanin yadda haɗuwata da hafsat ta samo asali, tun daga lokacin da ta nemi taimakona a yayin da'a biyo cikin dare har izuwa lokacin da ta nisanta kanta dani ta tafi tana kuka a game da laifin da take tunanin cewar ni na aikatashi a gareta.
Haka mahaifina da mahaifiyata haɗe da yayata zainab da kuma ƙanwata ameena duk suyi shiru suna sauraron bayanina.
Sannan na ɗora da bayanin cewar "ko kaɗan bai kamata ace an yankemin hukunci ba tare da anji wani bayani daga bakina ba to amma a wannan lokacin ba yadda na iya haka nabar gida domin bin umarnin mahaifina akan cewar na fice mai daga gida.
Haka na ɗago kaina idanuna suna zubar da hawaye nace "tabbas nasha wahala adalilin wannan fitar da nayi domin a dalilin fitar ne har nakai matakin da a kwantar dani a asibiti wanda hakan yai sular haɗuwata da wannan bawan mutumin domin shine wanda ya sanar dani bayanin komai a game da cikin da hafsat ta haifi jaririn da ta kawo gidannan.
Bayan na gama sanar dasu nawa jawabin sai shima wanda yai nake tare dashi ya ɗora da nash jawabin kamar yadda ya sanar dani a lokacin da mu haɗu a asibiti.
Koda iyayena suji bayanin duk abun da ya faru sai suyi matuƙar mamaki haɗe da nuna tausayawarsu a gareni wanda hakan yasa mahaifina ya furta kalmar ban haƙuri a gareni.
A ƙarshe sai shima mutumin da ya haifar da wannan matsalar ya nemi yafiya a gareni wanda hakan yasa nayi murmushi haɗe da cewa "ba komai na yafema.
Sannan na roƙi mahaifina domin a taimaka mai da wajan kwana kafin gari ya waye.
Sai mahaifina yace "to ai ba damuwa.
Haka ameena ta rungumeni tana zubar da hawayen farin ciki.
Bayan an bashi abinci yaci yasha ruwa sai mahaifina yace "to malan ko zamu iya sanin sunanka?
Buɗar bakinshi sai yace "ai sunana Ibrahim.
Sai mahaifina yace "to malan ibrahim abun da zan sanar da kai yanzu shine "Allah yaiwa ɗanka rasuwa yau kimanin watanni shida kenan.
tun daga wannan ranar sai na ƙudiri niyar nemo hafsat a duk inda take badan komai ba sai dan buƙatar wanke kaina a game da laifin da take tinanin na aikata mata.
Tabbas neman hafsat ba ƙaramin aiki ya zamemin ba domin ko hotanta babu a gareni.
Ba ranar da zan kwanta ba tare da nayi tunanin hafsat ba.
Kwatsam wata ranar juma'a bayan na dawo daga masallaci ina zaune a falo ga abinci a gabana amma a wannan lokacin ba abincin ne a raina ba.
A yayin da nake cikin tunani sai zuciyata take sanar dani cewar "to kai in banda abun ka taya kake tunnin zaman hafsat a kano, ai sai dai ka nemeta a wasu jahohin amma ko kaɗan hafsat bazata zauna a kano ko adamawa ba.
Bayan zuciyata ta gama karantar dani wannan darasin, kawai sai na biyema zuciyar tawa wanda hakan yasa a wannan ranar da yamma bayan mahaifina ya dawo daga wajan aiki sai na sameshi a yayin da yake zaune a falo.
Bayan nayi mai sannu da zuwa sai nace "dama abba gobe in Allah ya kaimu inason zanje garin bauchi ɗaurin auran wani abokina.
Sai yace to shikenan Allah ya kaimu goben lafiya.
Washe gari da sassafe bayan nayi breakfast sai nahau mota na tasarma hanyar bauchi.
Koda na shiga bauchi sai nayi shiru ina tunanin ko ta wace hanya zan fara neman hafsat gashi bansan kowa a garin ba haka dai na ƙaraci yawona kamar wani sabon mahaukaci amma Allah baisa nayi arba da hafsat ba.
Bayan sati ɗaya da dawowata gida sai na tunkari jahar jigawa canma dai ban samu wata nasara ba haka na dawo gida hannu rabbana.
Yawona bai tsaya iyanan ba domin har yobe da jahar taraba sai da naje duk dan buƙatar na sake haɗuwa da hafsat amma duk ba labari.
Koda naga alamun yawan da nakeyi domin neman haduwata da hafsat bashi da wani amfani gaba ɗaya sai na miƙa ragamar komai ga mahalicinmu.
Ko wace rana idan nayi sallah nakan roƙi Allah domin ya haɗani da hafsat.
Musamman nake tashi cikin domin yin nafula badan komai ba sai dan buƙatar haɗuwa da hafsat.
Allah mai iko kuma mai yadda yaso da bawansa.
Kwatsan wata ranar talata lokacin in gida sai saƙon taron Old Boys ya iso gareni wanda zamuyi a garin KADUNA 5/jan/2018.
Bayan na halarci taron a yayin da'a gama komai a watse, a hanyata ta dawowata gida sai na tsaya a wata plaza domin yin wata ƴar siyayya.
Bayan na sayi abun da zan siya fitowata kenan sai nayi arba da hafsat a wajan wata mai dafa abincin dake kusa da plazar.
Koda nayi ido biyu da hafsat cikin gaggawa ta miƙe tsaye wanda hakan yasa mu tsaya yima juna kallan-kallo.
=> 9
Tabbas nayi mamakin ganin hafsat a wannan wajan fuskata cike da mamaki na ƙarasa gareta.
Da zuwana gareta sai nayi sallama amma sai ta amsa ranta a ɓace.
Buɗar bakina sai nace "hafsat ashe dama kinanan wajan naketa faman nemanki shiru bake ba labarinki?
Buɗar bakinta sai tace "kwarai kuwa anan nake da zama kuma a yau zan nisanta da wannan wajan saboda na tsani ganinka bana ƙaunar cigaba da jin muryarka saboda nasan ko ka tafi dolene ka sake dawowa nan wajan saboda mazinata ba kumya su sani ba, amma inason na sanar da kai wata magana daga yau ko a ina ka ganni karka sake ƙoƙarin kawo ƙafarka inda nake balle ka nuna wata sanayya a tsakanina dakai idan kuma ba hakaba to ina mai tabbatarma cewar sai nayi ajalinka, kuma har ƙarshen rayuwata bakina bazai taɓa daina furta kalmar tsiniwa a gareka ba.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "haba hafsat me yasa ƙwaƙwalwarki take da gajeren tunani ta yadda bazata iya gane abun da zan iya aikatawa da kuma wanda bazan iya aikatawa ba.
A wancan lokacin haka ki nisanceni ba tare dakin tsaya domin jin wata magana daga bakina ba, gashi yanzu ma kina ƙoƙarin sake aikata wannan banzan shirmen.
Koda ta kalleni sai tace "karkaga laifina saboda a halin da nake ciki yanzu gaba ɗaya maza ababen tsoro ne a gareni tun daga kan mahaifina har izuwa koma waye.
Saboda tun da nake a rayuwata ban taɓa haɗuwa da macuta mugaye azzalumai wawaye marassa tunani haɗe da rashin sanin haƙƙin addinin musulunci fiye da kai da mahaifina ba.
Wallahi har kwanan gobe kai da mahaifina bazan fasa yi maku mummunar addu'a ba.
Haka ta nunani da yatsanta haɗe da furta cewar "in Allah ya yadda wutace makomarku, kuma bana fatan ka gama da duniya lafiya.
Sannan ta shige ɗaki tana kuka.
A wannan ranar har na koma gida zuciyata ba ta daina tunanin irin cin mutuncin da hafsat tayi a gareni ba.
Da zuwana gida bayan nayi wanka na ɗan ci abinci sai na shiga ɗaki na kwanta domin a wannan ranar nayi matuƙar gajiya.
Gani dai a kwance amma bacci yaƙi zuwa saboda tunani yai ma zuciyata ƙawanya.
Koda nagaji da kwanciya sai na tashi zaune nayi shiru ina tunanin hanyar da zanbi wajan ganin na warware wannan matsalar.
Haka dai na kwana ko baccin kirki ban samu nayi ba.
Bayan gari ya ƙarasa wayewa sai nayi waje ko breakfast ban samu nayi ba.
Da fitowata sai na hau mota na tasarma garin kaduna.
Ƙarfe 9:30 na shiga kaduna kuma ba inda na tsaya sai a wajan dana haɗu da hafsat.
Bayan na fito daga mota sai na ƙarasa wajan mama mai abinci.
Bayan mun gaisa sai nace "dan Allah mama ina hafsat?
Koda mama ta kalleni sai ta ɗanyi dariya haɗe da cewa "ai hafsat tace zamanta anan bazai yiwu ba domin tasan komai daran daɗewa sai ka dawo nemanta, haka ne yasa ta yanke shawarar komawa adamawa wajan mahaifinta domin ko cikakkun muntina 30 da tafiyarta ba ai ba.
Jin haka ne yasa cikin sauri na miƙe tsaye fuskata cike da mamaki.
Sannan na kalli mama haɗe da cewa "to dan Allah mama ko zan iya samun address ɗinta a gareki saboda akwai wata magana mai matuƙar mahimmancin da nakeson nayi da ita, saboda banason hafsat ta koma ga mahaliccinmu da zargin ai kata wani mummunan abu a tsakanina da ita.
Koda mama mai abinci taga alamun akwai damuwa a tattare dani, nan take ta bani full address ɗin da zai kaini zuwaga hafsat.
Bayan na ɗauki hanya sai na tuna mutar ba wadataccen mai kuma gashi ba kuɗi a aljihuna domin iya Naira 350 ne kaɗai a tattare dani.
Ba yadda na iya haka na jinginar da wayata a wani shago akan Naira dubu 20,000 bayan nasha mai sai na ɗauki hanya.
Da misalin ƙarfe 8:00pm na shiga Adamawa.
Kuma Allah cikin ikonsa bansha wata wahala wajan neman gidan su hafsat ba.
Da zuwana ƙofar gidan sai nayi packing.
Bayan na fito daga motar sai na fara nazarin hanyar da zanbi wajan ganin na haɗu da hafsat.
Ga dai gidan a buɗe amma bani da tabbacin hafsat tana cikin gidan.
Haka dai na tsaya na ɗan wani lokaci, a ƙarshe sai na yanke shawarar shiga gidan saboda ko kaɗan bani da fargaba a game da duk abun da zai faru.
Har naje bakin gate ɗin gidan na ɗora hannuna a ƙofar da ƙudirin buɗewa sai na hangi hafsat ta taho.
Sai a wannan lokacin ne na fahimci cewar hafsat tana da tsatstsauran ra'ayi.
Domin da zuwanta ko kallona batayi ba koda naga alamun zata shige ba tare da ta tsaya ba sai nayi ƙoƙarin dakatar da ita amma sai han ya gagareni domin iskar da take wucewama tafini muhimmanci a gareta.
Buɗar bakina sai nace "hafsat laifin wani baya shafar wani.
Dan haka yana da kyau ki tsaya domin ki saurari maganar da nazo da ita gareki.
Tsaki kawai tayi sannan ta wuce wanda hakan yasa nima kaina na kasa tantance irin zuciyata domin a wannan lokacin jina nayi kamar wani wawa kuma marar zuciya.
To amma duk da haka dai kasa jurewa nayi wanda hakan yasa nima nabi bayanta.
Da shigarmu falon gidan sai nayi sallama.
Haƙiƙa mahaifin hafsat ba mutun ne mai kama da masu imani ba.
KANWATA=>10
Haƙiƙa mahaifin hafsat ba mutun ne mai kama da masu imani ba domin yanaji nayi sallama amma yaƙi amsawa
A yayin da na haɗa ido da hafsat sai naga alamun a tsorace take.
Nan take mahaifin hafsat ya miƙe tsaye ranshi a ɓace ya matso daf dani haɗe da cewa "ai dama nasan duk daran daɗewa sai ka dawomin da ƴata har gida, yanzu in banda rainin wayo ya za'ai naga ƴata ido da ido a tare dakai har ka nemi yimin musu akan cewar ba ita nace.
Sai yai wata yar dariya haɗe da cewa "wato hafsat matarkace ko, to yaushe kuyi auran, kuma a ina ka aureta, sannan waye uban nata da ya baka aurenta?
Buɗe bakina sai nace "kayi haƙuri a game da ƙaryar da nayima saboda nayi haka ne domin cika alƙawarin da na ɗaukar ma hafsat akan cewar bazan taɓa barin wani abu ya cutar da ita ba.
Amma bari na baka labarin asalin yanda yaɗuwa ta da hafsat ta samo asali.
Nan take na fara yimai bayani tun daga lokacin da Allah ya haɗani da ita har zuwa lokacin da mahaifina ya koreni daga gida.
Sannan na kalli hafsat haɗe da cewa "hafsat kin zargeni akan laifin da ban taɗa aikatashi akan wata ya mace ba.
Tun daga lokacin dana haɗu dake har kawo yanzu ban taɓa sha'awar aikata alfasha dake ba.
Amma ko kaɗan banga laifinki ba dan kin zargeni a game da wannan al'amarin.
Amma idan baki manta ba akwai wani bawan Allan daki taɓa haɗu dashi a wata super market har ki ɗaga hannu ki mareshi a dalilin riƙe miki hijab ɗin da yayi.
To shi wannan daki mara ne ya kwanta dake.
Koda naga tayi gaggawar ɗago kai ta kalleni ba tare da ta iya furta wata magana ba sai na fahimci cewar a cikin ruɗani take.
Sannan na ƙara da cewa "nasan zakiyi mamakin yadda ai haka ta faru a gareki.
Sai nace "idan baki mantaba a daran da wannan al'amarin ya faru dake na buƙaci ki dafamin Tea, bayan kin shiga kitchen sai ki duba kiga lipton ya ƙare wanda hakan yasa na fita domin siyo lipton ɗin
Futowata kenan daga gida sai wanda ki mara ya samu nasarar shiga gidan sai kuma yai sa'a a dai-dai wannan lokacin kin shiga wanka wanda hakan ya bashi damar buɗe fridge ya zuba kwayoyin bacci drink ɗin da yasan cewar munfishansa musamman idan dare yayi saboda ya jima da karantar halayyar mu.
Bayan na dawo gida kuma sai na canza ra'ayin shan Tea wanda hakan yasa muci abinci tare kuma musha drink ɗin da wanda ki mara ya zuba maganin da zai haifar da bacci a garemu ba tare da sanin mu ba.
A yayin da muke tsaka da kwasar bacci sai wanda ya zuba maganin ya ɗaukeki zuwa ɗakin da kike kwana domin cika mummunan ƙudurinshi a gareki.
Bayan gari ya waye a yayin da nake kwance a falo lokacin bacci bai gama sakina ba sai naji sautin kukanki ya sauka a kunnena wanda hakan yasa na tashi a tsorace.
Cikin kuka ki furta kalmar Allah ya isa a gareni sannan kiyi waje ki barni cikin tunanin dalilin dayasa ki nisanceni.
Jin wannan bayanin da nayi ne yasa hafsat ta furta kalmar "innalillahi-wa'inna ilaihin-raji'un, sannan ta kalleni fuskarta cike da yanayin tausayawa a gareni.
Idanunta suna zubar da hawaye tace "to amma taya ai kasan yadda haka ta faru?
Sai nace bayan mahaifina ya koreni daga gida a dalilin sanar dasu ɗin da kiyi cewar ni na miki cikin da ki haifi ɗan da ki kai gidanmu nasha matuƙar wahalar rayuwa wanda hakan wanda har hakan yai sanadin kwantawata a asibiti.
A ranar da'a sallamemu ne na haɗu da wani bawan Allah a lokacin da shima yaje asibitin.
A wannan lokacin ne yasa a kirani ya kuma sanar dani komai a tattare da abun da ya aikata a gareki, ya kuma nuna nadamarshi a bisa abun da ya aikata a garemu.
Nan take hafsat ta fashe da kuka ta rasa abun da zata cemin.
Koda mahaifinta yaga kukan yana neman wuce iyaka sai ya daka mata tsawa wanda hakan yai sular haifar da firgice a gareta.
Buɗar bakinshi a yayin da mahaifin nata ya kalleni sai yace "tabbas kai mutun ne mai imani haɗe da nuna tausayawa, to amma inason ku gane cewar fitarku daga wannan gidan abune wanda zai yi matuƙar wahala a gareku.
Domin a kaf duniyarnan banga wanda zai iya kuɓutar daku daga gidannan ba.
koda hafsat ta kalleni taga nayi shiru ba tare da na sake wata magana ba.
Sai ta kalli mahaifinta cikin yanayin fargaba tace "dan Allah abba kayi haƙuri ka barshi ya tafi saboda yayimin halaccin da bana tunanin cewar har ƙarshen rayuwata zan iya yi mai kwatan-kwacinsa.
Sannan ta ƙara da cewa "wallahi idan har kayi sanadin mutuwarshi har in koma ga ubangijina raina bazai taɓa yafema wannan butulcin ba.
Haka hafsat ta kalli mahaifinta fuskarta cike da hawaye cikin yanayin kuka tace "nasan ka hallaka rayuwar mutane da dama kuma ciki hada mahaifiyata duk dan buƙatar ka tara dukiya.
Sai gashi Allah cikin ikonsa kamallaki dukiya mai ɗinbin yawa wadda ni kaina bansan adadinta ba, to amma idan ka koma ga ubangijinka da wace fuska zaka kalleshi?
Sannan ita dukiyar da kake tunanin ka tara waye magajinta?
A ƙarshe sai tace "tabbas yawancin iyaye suna jajircewane wajan tara tsarkakakkiyar dukiyar da zasu ji daɗi su huta tare da ƴaƴansu, amma sai gashi yau kaine da bakinka zaka kashe yarka ta cikinka.
Nan take taje har gaban mahaifinta ta durkusa har ƙasa haɗe da cewa "abba a matsayina na yarka na yarjema ka cika wannan mummunan ƙudurin naka a kaina, amma dan Allah wannan bawan Allan ka rabudashi ya koma ga iyayenshi domin nasan suna matuƙar sonshi fiye da soyayyar daka nunamin.
Jin haka ne yasa mahaifin nata yai shiru na ɗan wani lokaci.
Zuwacan sai yai wata yar dariya sannan ya kalleni ya kuma kalli hafsat haɗe da cewa "naji duk wannan batun naki amma inason ki san cewar wannan sana'ar tawa bazan taɓa dainata ba.
Dan haka tunda har Allah yasa wannan mutumin ya faɗo a komata to ba makawa sai ya baƙunci lahira.
Sannan ke kuma zan barki a matsayinki na ƴata kuma zan baki kulawa haɗe da soyayyar daki rasa a gareni idan Allah ya kari kwanana sai ki gaji wannan dukiyar tawa.
Nan take hafsat tayima mahaifinta wani kallo haɗe da furta cewar "Allah ubangiji ya kiyaye naci wannan kazamar dukiyar a matsayin gado.
Dan haka kafin ka cika wannan mummunan ƙudurin naka a kan wannan bawan Allan nice wadda zan fara mutuwa in taso shi sai ya biyo bayana.
Nan take hafsat ta afka kitchen ta banke ƙofa.
=>11
Koda mahaifinta yaga haka nan take ya gigice domin yasan ba makawa hafsat kashe kanta zatayi.
Cikin gaggawa yaje bakin ƙofar a ɗimauce yana bubbuga ƙofar haɗe da cewa "hafsat karki aikata haka, ki tsaya ki saurareni idan ki tafi wa nake dashi da ya wuce ke.
Amma haka hafsat tayi banza dashi.
Ni kuma a wannan lokacin gashi ina kallon ƙofar da zanbi domin ceton rayuwats amma gaba ɗaya sai hankalina ya karkata izuwa ga rayuwar hafsat domin zuciyata bazata iya jurar ganin hafsat a cikin wani mawuyacin hali.
Haka nima naje bakin ƙofar da sauri ina dukan ƙofar haɗe da cewa hafsat karkiyi gaggawar aikata haka.
Karki manta idan har ki kashe kanki Allah bazai miki uzuri ba domin haka zai jefaki cikin wuta.
Cikin yanayin ƙarfin hali ta buɗa baki muryarta tana rawa tace "dan Allah yayana kayi haƙuri karkayi ƙoƙarin danganta ruhina da shiga aljanna domin tun tuni taurin kaina ya min iyaka da shigarta, domin da ace nayima uzuri a baya da duk haka bata faru ba.
Sannan ta ƙara da cewa "dan Allah ka yafemin duk laifukan dana aikata a gareka domin samun mutun mai halacci kamarka da akwai wahala ka ceci rayuwata a lokacin da ake ƙoƙarin kasheni, ka bani wajan kwana domin gudun kar wani mummunan abu ya sameni, ka ciyar dani domin gudun kar yunwa tayimin illa, ka shayar dani domin gudun kar ƙishin ruwa yamin illa, kayima iyayenka ƙarya domin buƙatar dawwamar da farin ciki a gareni, tun da nake da kai ban taɓa ganin ka bayyana ɓacin rai a kan halayena ba.
Duk irin wannan halaccin da kayimin ban tashi sakama da komai ba sai sharri haɗe da ƙazafi mafi muni wanda idan na tuna dashi gaba ɗaya sai naji na tsani kaina.
Tabbas ban kyautama ba ban kuma kyautata ma iyayenka ba domin har korarka suyi daga gida na tsawon wani lokaci duk a sakamakon ƙazafin da nayima.
Amma duk da irin wannan rashin halaccin dana aikata a gareka baisa ka nisanceni ba.
Sai gashi nice nayi silar jawo rayuwarka ga mahalaka.
To ta wace hanyar kake tunanin zan samu jin dadin zaman duniya ba tare da kai ba?
Nan take naji tayi wata ƙara wadda nima kaina bansan dalilin faruwar wannan ƙarar ba.
Jin haka ne yasa gaba ɗaya naji duk ilahirin jikina yai wani iri cikin gaggawa naja da baya na tokari ƙofar da kafata nan take ƙofar ta buɗe "a wannan lokacin ne naga hafsat kwance cikin jini ba ta ko motsi, ga kuma wuƙa a hannunta.
Ganin hakane yasa na fahimci cewar da wuƙar dake hannunta tayi amfani wajan wajan yin ƙurin kashe kanta.
Koda mahaifina hafsat ya ɗaga hannunta ya saki sai naga yamin wani kallo a gigice haɗe da furta cewar tamutufa.
Nanfa mutsaya tuna juna kallan kallo.
Har na miƙe tsaye sai naga hannunta yai motsi alamun tana da sauran rai kenan.
Ganin haka ne yasa nayi gaggawar ɗaukarta nayi waje.
Tabbas nayi mamakin ganin yadda mahaifin hafsat ya manta da batun aikani lahira.
Saboda ban ɗauka cewar zai barni na fita waje ɗauke da hafsat ba.
Da isarmu asibitin cikin gaggawa a kawo gado a ɗora hafsat.
Za'a shigar da ita ciki kenan sai wani doctor ya hana a shigar da ita.
Ganin hakane yasa na kalli likitan haɗe da cewa "dan Allah doctor kutaimaki rayuwar wannan baiwar Allar domin tana matuƙar jin jiki.
Sai likitan ya dafa kafaɗata haɗe da cewa "kaga malan ba yadda za'ayi mu karɓeta muddun baganin wani jami'in tsaro muyi a tare da ku ba.
Dan haka kayi gaggawar fita domin kiran ɗaya daga cikin yan sandan dake nan kusa da wannan asibitin.
Jin haka ne yasa nayiwa doctor ɗin wani kallo haɗe da cewa "wallahi muddun wannan kanwar tawa ta rasa ranta kafin dawowata to ba shakka sai rayuwarka ta shiga wani hali sannan nayi waje.
Sai likitan yai wata ƴar dariya haɗe da cewa "kaji zancan banza.
Ba'a fara duba hafsat ba har sai da nazo da ɗaya daga cikin jami'an ƴan sanda.
Bayan an fara yi mata aiki sai police ɗin yake tambayata yadda ai har a soki hafsat da wuƙa a ciki.
Koda na kalli mahaifin hafsat sai naga alamun tsoro a tattare dashi.
Ganin haka ne yasa na sunkuyar da kaina ƙasa na ƴan wasu sakonni domin tunanin amsar da zan bashi.
Ɗago kan da zanyi sai nace "ina zaune a falo ni da mahaifina kawai sai wasu mutane su shigo su huɗu amma a cikinsu ba wanda zan iya shaidawa saboda fuskokinsu suna lulluɓe da irin hularnan ta ɓarayi haɗe da safa a hannayensu ga kuma biyu daga cikinsu kuma suna riƙe da bindiga.
Bayan sun buƙaci a basu kuɗi sai mahaifina ya tashi ya shiga ɗaki domin dakko musu kuɗin da suke buƙata.
Shigarshi ɗaki kenan sai wannan kanwar tawa ta fito daga kitchen.
Koda ta shigo falo taga mutane riƙe da bindiga sai ta kwalla ƙara ta koma kitchen a guje ta rufe ƙofa.
Ganin haka ne yasa ɗaya daga cikinsu ya tunkari kitchen ɗin.
Da zuwanshi sai ya tokari ƙofar da ƙafarshi nan take ƙofar ta buɗe.
Da shigarsa kitchen ɗin sai muji hafsat tayi wata ƙara ashe wuka ya caka mata a ciki.
Bayan sunfita sai naje gareta da sauri ina shiga kitchen ɗin sai naga jini yana malala daga jikinta ga kuma wuka a gefenta.
Cikin gaggawa na ɗakkota zuwa nan asibitin domin a ceto rayuwarta.
Buɗar bakin police ɗin sai yace "to ita kuma mahaifiyar ta tana ina a lokacin da hakan ta kasance?
Buɗar bakina sai nace mahaifiyarmu tabar duniya tun muna yan ƙanana.
Sai police ɗin yace "to Allah ya kiyaye.
Sannan yace "bayan an gama yi mata treatment zaku kaimu gidan domin gudanar da bincike a game da wannan al'amarin.
Bayan sun gudanar da yan bincikensu sai su tafi da wuƙar zuwa station.
Bayan hafsat ta samu sauƙi nine na fara zuwa gareta.
Haka na karanta mata duk bayanin da nayiwa police ɗin domin gudun kar a samu matsala a yayin da su buƙaci jin ta bakinta.
Koda mahaifin hafsat yazo gareni sai ya riƙe hannuna haɗe da cewa "gaskiya kai mutun ne mai kawaici domin wallahi ban taɓa tunanin cewar bazaka tonamin asiri ba.
Dan haka nayi nadamar abun da na aikata a gareku.
Sannan kuma daga yau na daina wannan sana'ar tawa.
Sai ya riƙe hannunta haɗe da furta cewar "dan Allah hafsat ku yafemin wannan laifin dana aikata a gareku wallahi bazan sake ba.
Da ƙyar hafsat ta iya buɗe baki tace "to shikenan abba na yafema.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "yayana dan Allah kayi haƙuri a game da wannan kuskuran da na aikata a gareka.
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "haba hafsat aini baki aikata komai a gareni ba kawai rashin fahimta ne ya shiga tsakaninmu domin duk abun da ya faru ya faru ne a bisa kuskure.
Dan haka karki sake buɗar baki domin neman yafiya a gareni.
Jin haka ne yasa tayi wani ɗan murmushi haɗe da cewa "to shikenan yayana.
Bayan an sallamemu daga asibitin hafsat ta koma gida.
Kimanin sati ɗaya da komawata gida sai na ɗauki ƙanwata ameena zuwa garin adamawa domin taga hafsat.
Da isarmu garin adamawa ba inda mu tsaya sai a gidan su hafsat.
Da shigarmu bayan munyi sallama sai hafsat ta taso da gudu ta rungume ameena haɗe da bayyana tsantsan murna.
Haka shima mahaifin hafsat yai murna da zuwanmu ya kuma yi mana babbar tarba.
Bayan munci abinci sai mu fita cikin gari domin yawatawa.
Muna ta tafiya har nakai hafsat gidan su ibrahim ba tare da saninta ba wato wanda ya mata cikin da ya haddasa matsala a garemu.
Tun kafin mu ƙarasa kusa da gidan sai na ciro wayata daga aljihu na kirashi.
Ko cikakkun mintina hudu ba ayi ba sai Allah yai fitowarshi daga gida yana dogara sanda.
Koda hafsat tayi ido biyu da ibrahim nan take ta kalleni ranta a ɓace haɗe da cewa "yayana tun da nake da kai baka taɓa ɓatamin rai ba sai a wannan lokacin, me yasa zaka kawoni wajan wannan macucin kuma azzalimi?
Sai nace "A'a hafsat bai kamata ki furta irin wannan kalmar ba domin wannan bawan Allan yayi nadama a game da laifin da ya aikata a gareki.
Da ace baiyi nadama ba to da ba yadda za'ai ya sanar dani duk abun da ya faru a tsakaninshi dake.
Dan haka zanso kiyi haƙuri ki yafemai wannan mummunan laifin da ya aikata a gareki, saboda Allan da ya haliccemu yana matuƙar son mutun mai yawan haƙuri da yafiya aduk lokacin da'a cuceshi.
Nan take naga hawaye ya zubo daga fuskar hafsat buɗar bakinta sai tace "shikenan yayana na haƙura na yafemai.
Bayan mun dawo daga yawonmu sai hafsat tace dani "gaskiya bazan iya ɓoyema duk wani surrin dake zuciyata ba dan haka a yau ne zan bayyanama duk wani abun da yake zuciyata.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "to hafsat wannan kuma wane irin surri ne zaki bayyana a gareni yanzu, Allah yasa dai mai daɗi ne.
Sai tayi murmushi haɗe da cewa "nifa wallahi na kamu da dinka ne, gaba ɗaya ji nake kamar a ɗaura aurena da kai a yau.
Buɗar bakina sai nace "to hafsat idan kuma naƙi amincewa da wannan ƙudurin naki fa?
Cikin yanayin shagwaba tace "sai na sake shiga kitchen domin.......
Fuskata cike da annuri na dakatar da ita ba tare da na bari ta ƙasa furucin bakinta ba.
Alhamdulillah
The End