new update
Cewa tayi Uzee naga kowa sai baka labarinshi yakeyi to nima bari na baka wani ɗan taƙaitaccen labarin da ya shafi rayuwata.
=>Makaranta ce ta kaini kano wanda hakan yai sular haɗuwata da musa domin ni ƴar jahar Katsina ce.
Musa ba saurayina bane kawai yarda da juna ce tasa muke kyautatawa junanmu.
Ganin yadda bani da kowa a makarantar ne yasa gaba ɗaya na kasa sakewa wanda hakan yasa wani lokacin nake zama ni kadai.
Kwana huɗu da zuwana (B U K) sai wasu daga cikin ɗaliban makarantar su nemi tozartani ta hanyar neman cin zarafina.
Musa ne ya dakatar dasu ta hanyar shiga tsakaninmu, wannan shine farkon haduwata da musa.
Tun daga wannan lokacin sai na riƙa ganin ƙimar Musa.
Ganin mutuntashi ɗin da nake ne yasa shima yake kyautatamin fiye da tunanina.
Kwatsam bayan wasu yan kwanaki sai labarin rashin lafiyar mahaifiyata ya sameni wanda hakan yai matuƙar tayarmin da hankali domin bani da kowa sai ita saboda tun ina yar ƙarama Allah yaiwa mahaifina rasuwa.
Duk da cewa mahaifiyar tawa ba wata mai ƙarfi bace hakan bai hanata ɗaukar nauyin duk wasu harkokina ba.
Ganin yadda nake cikin damuwa ne yasa Musa ya nemi sanin abun dake damuna.
Haka na sanar dashi komai Kuma yai matuƙar nuna tausayawarshi a gareni.
A ƙarshe kuma yace "to Amma sadiya me zaihana kije gida domin duba lafiya mahaifiyar taki?
Saboda hakan yana da muhimmanci a gareki domin iyaye sumfi karfin wasa.
Cikin yanayin damuwa nace "Musa a halin yanzu kuɗin dake hannuna bazasu kaini gidaba.
Shiru naga musa yayi na ɗan wani lokaci sannan daga bisani ya kalleni haɗe da cewa "ba damuwa ɗan jirani ina zuwa.
Jim kaɗan da tashinsa sai ya dawo gareni.
Da zuwanshi sai yasa hannu aljihu ya ciro wasu kuɗi masu ɗan kauri ya miƙomin haɗe da cewa "ga waɗannan kuɗin nasan zasu isheki zuwa gida kuma karki dawo har sai kin tabbatar da cewar mahaifiyar taki ta samu sauƙi.
Ganin yadda yamin wannan babbar gudun mawar ne yasa na kasa furta komai a gareshi nan take naji hawaye ya keto daga idanuna.
Koda na kalleshi sai nace "Musa bani da wata kalmar da zan iya furtawa a gareka da sunan godiya gaskiya kai mutun ne na daban kayimin mutuncin da bazan iya mantawa dashi ba a rayuwata.
Da isata gida sai Musa ya Kira wayata bayan mungaisa sai ya tambayeni ya jikin mahaifiyar tawa?
Gaba ɗaya sai na kasa furtamai komai koda yaji alamun ina kuka sai yace "Wai me yake faruwa ne sadiya?
Cikin yanayin kuka nace "a halin yanzu mutuwar mahaifiyata kawai nake jira, Saboda bamu da kuɗin da asibiti su nema a garemu domin yiwa mahaifiyar tawa magani.
Buɗar bakin Musa sai yace "to amma nawa su nema domin yimata maganin?
Cikin yanayin damuwa nace "Musa kuɗin suna da yawa domin dubu ɗari biyu da saba'in 270k su nema a garemu. Kuma na tabbata akwai waɗanda sufi ƙarfin waɗannan kuɗaɗen a danginmu, Amma duk cikinsu ba mai niyar biyan kuɗin domin mahaifiyata ta samu lafiya.
Furucin da naji Musa yayi ne yai matuƙar bani mamaki haɗe da jefani a kokwanto. Domin cewa yai na turamai da account number domin ya turomin da kuɗin.
Cikin yanayin mamaki nace "Amma Musa meye dangantakata da kai da kakemin irin wannan bautar?
Karka manta gaba ɗaya danginama sun nuna ƙin amincewarsu wajan tallafawa mahaifiyata, Dan haka dolene na shiga kokwanto a game da irin wannan bautar da kake shirin yimin.
Buɗar bakin Musa sai yace "kyawun fuskarki ko kyawawan halayanki basa daga cikin dalilin da yasa nake ƙoƙarin tallafa miki saboda ba soyayya ce a tsakanina dakeba, Kawai ni dai abun da nasani shi ne kina matukar burgeni. Domin ban taɓa tsayawa nayi tunanin soyayya dakeba balle har nayi tunanin aure a tsakaninmu. Dan haka zanci gaba da kyautata mikine iya bakin ƙoƙarina.
Wannan furucin nashi ba kaɗan ya kiɗimani ba wanda hakan yasa na kasa fahimtar inda ya dosa shin sona Musa yake ko kuma wata ɓoyayyar manufar yakeson cimmawa a gareni?
Haka dai naci gaba da kasancewa a tare da Musa a matsayin abokina kuma bai fasa kyautatamin ba wanda har hakan yasa dangina su fara zargin karuwanci nakeyi idan na koma school, alhalin kuma ba wanda nasan ya taɓa taɓa jikina da sunan iskanci balle har ayi batun kwantawa a shinfiɗa ɗaya da wani.
Lokaci ɗaya mahaifiyata ta tarkeni domin sanin inda nake samun kuɗin da nake kulawa da kai na haɗe da kulawa da ita kanta mahaifiyar tawa.
Ba kuma komai ne yasa ta nemi jin hakan daga gareni ba sai dan ganin yadda danginmu suke raɗe-raɗin cewar karuwanci nakeyi.
Nan take na durƙusa har ƙasa ina kuka haɗe da cewa "Dan Allah umma kiyi haƙuri ki yafemin nasan nice sular kasantuwar wannan ɓacin ran a gareki. Amma zanso kisan cewar tarbiyyar daki bani tafi ƙarfin ruɗin duniya ya rinjayeta ta hanyar aikata fasikanci.
Umma wallahi batun yanzu nasan cewar sai kin nemi sanin inda nake samun irin waɗan nan kuɗaɗan ba.
Nan take nayi wa mahaifiyar tawa bayanin komai dangane da batun haɗuwata da musa.
Sannan a ƙarshe kuma nace "umma idan har kuɗin da nake amfani dasu a gareni haɗe dake kanki ta hanyar sadaukar da kai na ga wasu ne nake samunsu to bana fatan Allah ya ɗagani daga nan wajan.
Sannan nace "umma indai har makarantar da nake zuwa ce ta haifar da wannan zargin to daga yau bazan sake taka ƙafata waje da sunan zuwa makarnata ba.
Zanci gaba da zama a tare dake domin baki kulawa.
Buɗar bakin mahaifiyata sai tace "sadiya ni nasan ba yadda za'ai ki iya aikata fasiƙanci. Zargin mutane ne kawai yake neman rinjar wannan kyakkyawan zaton da nake miki izuwa ga kallanki a matsayin fasiƙa.
Dan haka daga yau na yarje miki kici gaba da zuwa makaranta amma ina mai tabbatar miki cewar bazan taɓa yafe miki ba muddun ki bari wani ya ɓata rayuwarki.
Haka dai naci gaba da kasancewa a tare da Musa lokaci-lokaci Musa yana bani ajiyar kuɗi masu yawa.
Yaddar da take a tsakaninmu ce tasa na kasa tambayar Musa a inda yake samun irin waɗannan kuɗaɗen.
Kuma baya min shamaki da dukkanin kuɗin da yake bani ajiya domin cemin yake idan wata buƙatar kuɗi ta tasomin to zaki iya amfani dasu.
Amma hakan baisa na taɓa amfani da ko sisin kobo daga ire-iran kuɗaɗen da yake bani ajiya ba.
Kafin na kammala karatu kuma sai Allah yaiwa mahaifiyata rasuwa wanda hakan yasa na fara tunanin irin ƙalu balan dazan fuskanta a wajan dangina.
Musa ne ya kasance tamkar garkuwa a gareni domin tare dashi na halarci garina na Katsina domin jana'idar mahaifiyata.
A gaban idan Musa dangina su riƙa yimin kallan banza haɗe da furta baƙaƙen maganganun da basu da daɗin ji.
Ganin yadda nake kuka ne yasa shima kanshi Musa ya zubar da hawaye sannan yace dani na daina kuka tunda yana tare dani.
Bayan mun koma school sai Musa ya riƙeni tamkar ƙanwarshi.
Buƙatar na samu kusanci da gidansu ne yasa Musa ya haɗani da wata ƙanwarshi mai suna Nusaiba domin mu zama ƙawaye, Badan komai ba sai dan na samu damar shiga gidansu aduk lokacin da naso.
Bayan mun kammala karatu sai na fara tunanin wannan kammala karatun namu shine zai zamto ƙarshen rabuwata da Musa saboda tun dama can ba soyayya ce a tsakanin mu ba.
Haka Musa ya sameni a keɓaɓɓan waje domin sanar dani maganar da ta ɗan ɓatamin rai.
Cewa yai "Sadiya dabadan mahaifina mutun ne mai tsanani ba da ba abun da zai hana na aureki.
Sannan ya ƙara da cewa "bazan ɓoye miki gaskiya ba domin tun kafin haɗuwata dake nake soyayya da wata mai suna Ummey..
Ummey yar uwata ce wadda mahaifina yake matuƙar ji da ita badan komai ba sai dan ganin yadda ta rasa mahaifiyarta.
Duk da cewar mahaifin ummey yana raye hakan bai hana mahaifina ɗakko Ummey domin taci gaba da zama a gidanmu ba.
Saboda Ummey ƴar ƙanin mahaifina ce. Abun yana matuƙar bani mamaki ganin yadda mahaifina yake matuƙar nuna kulawarshi akan Ummey.
Domin duk a cikin ƴaƴan da mahaifina ya haifa ba wanda yake samun kwatan-kwacin kulawar da Ummey take samu a gidanmu.
Kuma Allah cikin ikonsa a cikinmu ba wanda ya taɓa nuna kyashinsa ko hassadarshi a game da irin wannan kulawar da Ummey take samu, Saboda itama yace a gidanmu wadda ta isa tayi duk abun da taga dama..
Sai abun da Ummey ta zaɓa a dafa a matsayin abun da zamuci to Amma sai dai itama tana matuƙar son ganin farin cikinmu.
Lokaci ɗaya Ummey ta fara bayyana alamun soyayyarta a gareni.
Ganin haka ne yasa mahaifina ya takamin burkin daina kula ko wace yarinya haɗe da sanar dani cewar Ummey zai auramin.
Duk da cewar Ummey bata da makosa hakan bai hanani bayyana ɓacin rai na ba.
Amma ba yadda na iya haka na amince da wannan buƙatar da mahaifina ya tunkareni da ita.
Tun daga wannan lokacin sai soyayya mai ƙarfi ta shiga takanina da Ummey.
Tabbas Ummey yarinya ce mai matuƙar kishin tsiya haka ne yasa nima kai na nake tsoran kishinta domin har ƙorafin kula wasu ƴan matan sai da Ummey ta taɓa kaiwa mahaifina wanda hakan yasa mahaifina ya tabbatarwa Ummey cewar ita kaɗai zan aura, Kuma ba wadda na isa na ƙara aura da sunan yi mata kishiya.
Wannan ne babban dalilin da yasa kiga na haɗaki da ƙanwata Nusaiba domin ku zama ƙawayen juna badan komai ba sai Dan gudun ɓacin ran mahaifina musamman idan yasan cewar kina zuwa gidanmu ne a dalilina.
A halin yanzu dai Ummey tana England domin yin karatu ni kuma gani a gida nageria.
Dan haka itama Ummey zata dawo gida ne a ƙarshen wannan watan kuma ina mai tabbatar miki cewar tana dawowa mahaifina zai ɗaura aurena da Ummey.
Bayan ya gama yimin wannan bayanin sai yaga alamun damuwa a tattare dani wanda hakan yasa ya ɗan yi murmushi haɗe da cewa "karki damu in Allah ya amince tafiyarmu bazatazo ƙarshe ba.
Haka ya kaini ɗaya daga cikin gidajan da mahaifinshi ya mallaka domin na riƙa kwana batare da kowa ya sani ba.
Bayan kwana biyu da faruwar haka kwatsam da daddare bayan sallar Isha A yayin da nazo rufe ƙofa sai ji nayi an fincikoni haka wasu mutanan da bansan ko su waye ba susani a mota suyi gaba dani.
Can wani gida su kaini ba tare da sanin dalilin kaini can ba.
Zuwa can sai ga Musa yazo wanda hakan ya haifarmin da zazzafan ruɗani.
Koda Musa yazo cikin yanayin mamaki yace "haba Abbas wannan matsalar a tsakanin ni daku ne ba ta shafi wannan yarinyar ba.
Buɗar bakin babban cikinsu sai yace "Ina kuɗinmu?
Sai Musa yace "yadda dani ɗin da kuyi ne yasa ku ɗauki ajiyar kuɗinku ku bani.
Dan haka ni ba mutun ne wanda zai cuceku ba domin bayanin da nayi maku akan cewar sace kuɗin ayi gaskiya ne saboda wannan ba magana ce ta wasa ba.
Amma tunda abun yazo da haka zanso kuɗan bani nan da sati in Allah ya amince zan kawo maku 10 millions ɗinku.
Jin haka ne yasa na riƙe baki domin kuɗin ba ƴan kaɗan ba ne.
Sai babban nasu yace "to shikenan tun da kace haka munji mun amince kudinmu sun ɓace a hannunka. Dan haka zamu kyaleka haɗe da ita wannan budurwar taka abisa wani sharaɗi.
Nan take Musa yace "wane sharadi ne?
Buɗar bakin babban nasu sai yace "zakayi amfani da wannan budurwar taka ne a gaban idan mu. Saboda tun damacan muna jin raɗe-raɗin cewar karuwarkace kaga hakan zai taimaka wajan cire kokwantan dake zuciyarmu sannan kuma mu kyaleka.
Idan Kuma ba haka ba to ko wane daga cikinmu zai yi amfani da ita a gaban idanka, sannan kuma mu kasheka ta hanyar tarwatsa kanka da bindigar dake hannunmu.
Ganin yadda na fara kuka ne yasa Musa ya kalleni sannan yai ƙas da kanshi saboda kunya.
Koda Musa ya kallesu sai yace "yau kwana biyu kenan da bani ajiyar waɗan nan kuɗaɗan banciba kuma bansha daga cikinsu ba a sacesu.
Amma duk da haka na ɗaukar maku alƙawarin zan biyaku amma hakan baisa kunji tausayina ba har sai kun tozarta wadda ba ta ji ba Kuma ba ta gani ba, saboda haka naji kuma na amince ku kawar dani ta hanyar harbeni da bindigar dake hannunsu.
Amma ina mai roƙonku da kar wanda ya kusanci yarinyarnan da sunan aikata saɓon ubangiji saboda ba ta da hannu wajan ɓatan kuɗinku ni ne wanda ya kamata kuyima duk wani hukuncin da ya dace a matsayin fansar kuɗinku.
Musa bai tashi aune ba saiji yai an daki kanshi da ƙotar bindiga wanda hakan yasa ya zube kasa yana numfashi sama-sama.
Idanunshi kuma basu gushe daga kallona ba.
Haka su fara cire kayan dake jikina domin tabbatarwa Musa mummunan ƙudirinsu a gareni.
=>2
Bayan sun cire rigar dake jikina a yayin da suke ƙoƙarin cire breziyar da nake sanye da ita.
Cikin gaggawa babban cikinsu wato Abbas kenan yace "ku dakata maza ku bata rigarta.
Haka na mayar da rigar tawa ina kuka.
Cikin yanayin sanyin jiki babban cikin nasu ya matso kusa dani haɗe da cewa "yarinya meye sunanki?
Cikin yanayin kuka nace "sadiya.
Sannan yace wane gari?
Sai nace "Katsina.
Sai yace "sunan mahaifiyarki?
Sai nace "Maryam.
A ƙarshe sai yace "sunan yayanki?
Buɗar bakina sai nace "ni kaɗa ice a wajan iyayena domin bani da yaya.
Cikin yanayin takaici yai ƙas da kanshi a yayin da zai ɗago kanshi domin kallona sai naga hawaye a idanunshi.
Buɗar bakinshi sai yace "haƙiƙa sadiya ni yayanki ne uwa ɗaya uba ɗaya.
Na ganeki ne a dalilin tabon raunin da na gani a cikinki.
Tabbas na aikata kuskure mafi muni a rayuwata domin wannan al'amarin ya samo asali ne tun......
Nan take na dakatar dashi ta hanyar cewa bana buƙatar jin wani labari daga bakinka domin tun kafin mahaifiyata tabar duniya ba abun da ta ɓoyemin a game da labarinka wanda har hakan yasa ta sanar dani cewar basu da wani ɗan da ya wuceni.
Sannan ta sanar dani cewar na ƙaddara bani da wani yaya sannan mahaifiyar tawa ta kalleni hade da cewa "to amma sai dai nasan duk runtsi muddun kina raye to akwai lokacin da zaki haɗu da Abas.
Haka mahaifiyata tasa hannunta a kai na tana kuka haɗe da shimin albarka a yayin da nima nake tsugune a gabanta ina kuka.
Furucin da tamin a ƙarshe ne yai matuƙar tsoratar dani domin cewa tayi muddun na haɗu da kai har nayi kuskuran kiranka ko ɗaukarka a matsayin yayana to bazan taɓa kasancewa mai albarka ba domin bazata taɓa yafemin ba, dan haka koda ace zan rasa rayuwata ne a yayin da wasu suke ƙoƙarin cutar dani to karna taɓa neman tallafinka, sannan ko a hanya na haɗu da kai muddun na nuna wata alamar sanayya a tsakanina da kai to bata yafemin ba.
Sai gashi tun dana taso a rayuwata ba wanda yai yinƙurin aikata irin abun da kayi shirin aikatawa a gareni, Bugu da ƙari kuma wanda ya taimaki mahaifiyata kafin tabar duniya kuma yamin taimakon da ba wanda nakejin cewar zai iya yimin kwatankwacinsa shi kayima irin wannan cutarwar.
Kafin na farga sai naji jiniyar motar jami'an tsaro wanda hakan yasa su abas suyi gaggawar tarwatsewa ta hanyar guduwa.
Haka wasu daga cikin jami'an tsaron subisu wasu kuma su tsaya garemu domin ceton rayuwar Musa sakamakon dukan kanshi ɗin da suyi da ƙotar bindiga.
Muna asibitin ne labarin kashesu ya zo garemu domin jami'an tsaron ko ɗaya daga cikinsu basu bari ba.
Bayan Musa ya samu sauƙi haka a sallamemu ba tare da neman wani jawabi daga bakinmu ba.
Ganin haka ne yasa na tambayi Musa dalilin da yasa a sallamemu ba tare da neman jin wani bayani daga bakin mu ba.
Murmushi naga Musa yayi haɗe da cewa kiyi haƙiri domin ni ɗaya daga cikin jami'an C I D ne a ƙarƙashin hukumar SS.
Zanso ki gafarceni a game da kashe yayanki ɗin da hukumarmu tayi domin sun daɗe suna aikata ta'asa a wannan ƙasar tamu.
Cikin yanayin kuka nace "Musa kayimin komai a rayuwata domin abun da hukumarku ta aikata shi yafi dacewa ga duk masu aikata ɗabi'a irintasu Abas.
Abas shiya kashe mahaifina da hannunshi ta hanyar daɓa mai wuƙa a ciki, sannan yamai yankan rago.
Wannan al'amarin ya samo asali ne a dalilin shaye-shayan da abas yake yawaita yi wanda hakan yake matuƙar ƙonawa mahaifina rai.
Alokacin da hakan take faruwa ni yarinyace yar ƙarama wadda batama san kantaba balle ayi batun sanin dai-dai ko akasin haka.
Kwatsam wata rana da sanyin safiya bayan mahaifiyata tayimin wanka tasamin kaya masu kyau sai na fito daga ɗaki ina wasa kamar dai yadda yara ƙanana suke gudanar da harkokinsu wanda har hakan ya kaini izuwa ga shiga ɗakin Abas.
Cikin rashin sani na zubar mai da irin madararnan da mashaya suke sha domin kawar da hankalisu.
Buɗe idan da zaiyi a yayin da ya tashi daga bacci sai yaga wannan madarar gaba ɗaya ta gama zubewa nanfa ya tashi ranshi a ɓace ya hauni da duka sannan ya jefoni waje wanda hakan yaisular jimin ciwo a cikina.
Bayan an kaini asibiti sai mahaifina yasa jami'an tsaro su kama Abas.
A yadda mahaifiyata take bani labari sai da abas ya ɗauki tsawon watanni 5 a gidan yari.
Bayan an sallameshi daga wannan tsarewar da mahaifina yasa ayi mai.
A yayin da ya dawo gida sai ya natsu kamar wani mutumin arziki domin har kuka saida yayi a lokacin da yaga tabon raunin da ya jimin.
Ashe da mummunan ƙudiri ya dawo domin kwana biyu da dawowarshi cikin dare ya shiga har ɗakin mahaifina ya caka mai wuƙa a ciki yanayin karar da mahaifiyata taji abban nawa yayi ne yasa tayi gaggawar fitowa daga ɗakinta kafin taje gareshi tuni Abas yayiwa mahaifin nawa yankan rago.
Da zuwan mahaifiyar tawa bakin ƙofar ɗakin mahaifina nawa sai taga Abas ya fito daga ɗakin hannunshi riƙe da wuƙa duk jini.
Ganin yadda mahaifiyar tawa take sallallami ne yasa Abas yai gaggawar jefar da wuƙar sannan ya fice daga gidan a guje bai kuma sake dawowaba.
Sai bayan na girma mahaifiyata take bani wannan labarin wanda hakan yasa nayi matuƙar tsanar kai na saboda nice sular kashe mahaifina.
Ganin yadda na ɗauki kai na a matsayin sular kashe mahaifina ne yasa mahaifiyata tayi matuƙar nuna ɓacin ranta a gareni haɗe da cewa muddun na sake danganta kai na game da kashe mahaifina to sai tayi matuƙar saɓamin domin bani da laifi a game da mutuwar mahaifina.
Tun daga wannan lokacin na ƙyamaci sake haɗuwa da Abas saboda tun damacan bansanshi ba kuma bana fatan saninshi.
Da yake Allah mai ikone sai da yai sular nunaminshi domin na tabbata dabadun Abas yaga tabon raunin dake cikina ba da ba yadda za'ai mu iya gane junan mu.
Sannan na kalli Musa idanuna suna zubar da hawaye nace "musa a halin yanzu bani da kowa dangina kallon mazinaciya sukemin mahaifina haɗe da mahaifiyata duk sunbar duniya dan Allah dan annabi koda ace bazaka aureni ba karka nisanta dani.
=>3
Cikin yanayin alhini Musa ya kalleni haɗe da cewa "ba yadda za'ai na iya nisantarki domin rabuwa dake tamkar rabuwa da ahalina ne.
Haka ya matso kusa dani yace "komai runtsi kina tare dani amma sai dai kuma banajin cewar aure a tsakaninmu zai yiwu saboda banason bun da zai haifar da saɓani a tsakanina da mahaifina.
Haka dai Musa yaita faman saƙe-saƙen hanyar da zaibi wajan ganin ya gabatar dani ga ahalinshi badan komai ba sai dan buƙatar naci gaba da zama a tare dasu.
Amma sai ya kasa gano hanyar da zaibi har Allah yai dawowar Ummey daga England.
Ganin bashi da hanyar da zaibi ne yasa ya kira Ummey a compound ɗin gidansu haka su keɓe gashi ga Ummey domin sanar da ita halin da yake ciki.
Haka ya kwashe labarin komai dangane da alaƙar da take a tsakaninshi da ni ya sanar da Ummey ba tare da ya nuna mata wata alaƙar da ta shafi soyayya a tsakaninmu ba.
Al'amarin yayi matuƙar bashi mamaki sakamakon ganin yadda ran Ummey ya ɓaci.
Haka Ummey ta kalli Musa sannan ta jinjina kai haɗe da cewa "amma kasan irin son da nakema kuwa, yanzu ashe har zaka iya barin wata ƴa mace ta raɓeka?
Cikin yanayin mamaki musa ya cire farin glas ɗin dake fuskarshi ya kalli Ummey haɗe da cewa "Ummey wannan wane irin zancan banza ne, cemiki nayi soyayya nake ce a tsakanina da ita da har zaki nuna damuwarki a gareni?
Ganin yadda Ummey ta tashi ranta a ɓace ne yasa Musa yai gaggawar riƙe hannunta domin rarrashinta. Amma sai taƙi sauraronshi wanda hakan yasa ta fusge hannunta tayi gaba.
Koda ta shiga falo sai ta fashe da kuka nan take mahaifiyar Musa ta taso zuwa gareta domin jin abun da ke faruwa.
Haka Ummey ta sanar da iyayen Musa cewar "ai Musa soyayya yakeyi da wata mai suna sadiya.
Ko kadan mahaifiyar musa bata nuna wani ɓacin ranta ba saboda ko kaɗan batason ganin ɓacin ran musa.
Koda babban yayansu wato Abdul kenan yaji dalilin da yasa Ummey take kuka sai yayi dariya hade da cewa "toke in banda abunki ai namiji ba'a halicceshi dan mace ɗaya ba.
Nan take mahaifin Musa ya dakawa Abdul tsawa haɗe da cewa "be quiet, karna sakejin bakinka a wannan maganar. Sannan ya kalli ummey yace "maza kije ki kiraminshi shigar Musa falon gidan kenan sai nima na shigo gidan ba tare da sanin halin da Musa ke ciki ba.
Buɗar bakin mahaifin Musa a yayin da yai ido biyu da Musa sai yace "wane dalili ne yasa kayi sular zubar da hawayen ummey?
Cikin yanayin girmamawa musa yace "Amma abba sai inga kamar bai cancanta kariƙa shiga tsakaninmu ba saboda ita soyayya ta gaji irin wannan, kawai kabarmu zamu dai-daita kanmu.
Buɗar bakin mahaifin Musa sai yace wacece sadiya?
Koda naji mahaifin musa ya tunkari musa da wannan tambayar cikin yanayin fargaba na kalli Musa.
Nan take kuwa musa yayiwa mahaifinshi bayanin komai a dangane da alaƙar da take a tsakaninshi da ni ba tare da ya nuna masu alamun nice sadiyan da wannan al'amarin ya faru da itaba.
Koda mahaifin Musa ya gamajin duk bayanin da Musa ya masu sai yace "to yazama dole a gareka ka rabu da ita domin ta koma wajan danginta koda kuwa basa ƙaunar ganin ta a tare dasu saboda ummey itace zaɓin da nayima.
Buɗar bakin Musa sai yace "Abba nifa ba soyayyace a tsakanina da sadiya ba kawai gani nayi tana buƙatar taimako a matsayinta Na musulma wanda har Allah yasa mukawo wannan lokacin da ta rasa iyayanta danginta kuma su gujeta mu, mukuma ai bamurasa ci da sha haɗe da makwanci mai kyau ba.
Sannan musa ya kalli mahaifinshi nashi yace "abba itafa sadiya mace ce banamiji ba domin ta cancanci a tallafa mata saboda kar rayuwarta ta lalace.
Kuma sanin kanka ne bayan gidajan da kake dasu a wannan gidan muna da Empty ɗin dakuna a ƙalla sunkai biyar me zai hana..... Nan take naji ya dakawa Musa tsawa haɗe da cewa "me zai hana ayi me?..
Sai Musa yace "Abba itama a bata ɗaki ɗaya domin takasance a tare damu.
Jin haka ne yasa mahaifin Musa ya jinjina kai haɗe da cewa "to dacan a ina take kwana a yayin da ta kammala karatun nata?
Buɗar bakin Musa sai yace "Abba a ɗaya daga cikin gidajanka nakaita domin tariƙa kwana.
Wallahi saida nayi matuƙar tsorata a yayin da naji mahaifin Musa ya furta kalmar "innalillahi-wainna-ilaihi-raji'un" Sannan ya kara da wani furucin da ni kai na naji na tsani kai na a wannan lokacin.
Haka ya kalli Musa haɗe da cewa "Ashe kagama lalacewa ban sani ba, kace kawai ka kaita gidana ne a matsayin karuwarka domin na tabbata ba yadda za'ai ka kaita keɓaɓɓan waje ba tare daka nemi wani abu a garetaba.
Musa ya buɗa baki zaiyi magana sai mahaifin nashi ya tsunkeshi da mari haɗe da cewa maza ka ficemin daga gida mazinacin banza kawai.
Ganin haka ne yasa na fashe da kuka sannan na yanke jiki na faɗi ƙasa sumammiya.
Nan take mahaifin Musa ya nunani da yatsanshi a yayin dana yanke jiki na faɗi sannan ya kalli Musa haɗe da cewa kenan wannan ce sadiyan da kake nufi?
Ganin yadda Musa yake ƙoƙarin ɗaukata domin kaini asibi ne yasa mahaifin nashi ya dakatar dashi haɗe da cewa indai itace wannan to sai dai ta mutu anan domin ba wanda zai taimaketa.
Koda Musa ya kalli mahaifinshi sai yace "Abba ina mai tabbatarma cewar muddun yarinyarnan ta mutu anan to a matsayina na jami'in SS ba abun da zai hanani kamaka a matsayin wanda ya aikata kisankai.
=>4
Bayan musa ya samu nasarar kaini asibiti ayayin da na samu sauƙi sai ya wuce dani jahar katsina domin damƙani a hannun dangina, Amma sai suƙi karɓata ta hanyar sanar dashi cewar sai da ya gama lalata rayuwar tawa sannan zai kawoni garesu.
Ganin haka ne yasa naba Musa haƙurin rabuwa dani Amma yaƙi.
Haka ya sake dawo dani zuwaga iyayanshi domin roƙonsu akan su barshi ya aureni.
To ashe ɓacin ran iyayanshi yafi na sauran dangina domin a lokacin da musa ya sake maidani zuwa gidansu sai mahaifinshi ya koreshi daga gidan gaba ɗaya.
A yayin da Musa zai fita daga gidan sai na riƙe hannunshi ina kuka haɗe da cewa "A'a Musa karka lalata gobenka saboda ni.
Cikin yanayin kuka nace "Musa bansan laifin dana aikatawa diniyar nan ba da take shirin jefani a kangin da.... Sai Musa ya dakatar dani ba tare da ya bari na ƙarasa maganar dake bakina ba sannan ya kalleni haɗe da cewa "zanso ki gafarceni sakamakon kasa taimakonki ɗin da nayi.
Haƙiƙa kowa ce mace tana buƙatar jigon da zai riƙa kareta daga afkawa ruɗin duniya to amma sai gashi ahalinki haɗe da nawa ahalin sun kasa fahimtar taimakon da nake buƙatar suyi miki.
Haka Musa ya matso kusa dani haɗe da cewa "zan rabu da ke ne badan komai ba sai dan bin umarnin iyayena.
Nan take ya durƙusa har ƙasa yana mai nemen gafarar mahaifinshi domin ya yafe mai laifin da yake kallonshi dashi.
Har na juya domin fita daga gidan sai Ummey ta dakatar dani ta hanyar kiran sunana haɗe da cewa "ina kuma zaki, haƙiƙa kin cancanci a tallafa miki.
Haka ummey ta kalli mahaifin nasu tace "Abba dan Allah kayi haƙuri kabarta ta zauna a tare damu domin rashin fahinta ta ne ya kawo wannan matsalar domin muma bamu gagara irin wannan ƙaddarar ta afka manaba.
Jin haka ne yasa mahaifin nasu ya amince da zamana a tare dasu.
Allah cikin ikonsa kuma sai yayan Ummey wanda akecema Ahmad yazo gareni da batun aure.
Haka ayi bikin aurena haɗe dana Ummey a rana daya.
Duk da cewar nasamu kwanciyar hankali haɗe da jin daɗi hakan baisa na manta da dangina ba domin ina yawan ziyartarsu.
Gaba ɗaya sai batun tsangwamata haɗe da yimin kallan banza yaja baya a tsakanina dasu duk a dalilin kyautata masu ɗin da nakeyi.
alhamdulillah.
The End