life story
=> 1
Ko wane ɗan adam yana tattare da wasu mabuɗan cimma nasara guda uku to amma idan kayi rashin sa'a ɗaya daga cikin mabuɗan cimma nasarar ka ya gurɓata to an samu babbar matsala.
Ga mabuɗa. Kamar haka.
¹) Tsayawa akan addini na gaskiya.
²) Ingantacciyar tarbiyya daga wajan iyaye.
³) Ingantattun Abokai masu tafiyar da rayuwarsu akan tsari mafi dacewa.
Bari na baku wani ɗan taƙaitaccen labari a game da wani bawan Allah domin jin yadda tashi rayuwar ta kasance.
___Cewa yayi "tabbas ba wani abun da zan iya cewa na rasa a wajan mahaifina.
Duk da cewar bani kaɗai ya haifa ba hakan bai hanashi bani cikakkiyar kulawa ba.
Tun da nake a rayuwata ban taɓa jin mahaifina ya ambaci sunana ba domin da babana yake kirana saboda sunan mahaifinshi ne dani.
Amma sai dai kash ni kaɗai ne namiji a wajan iyayena A'isha itace babbar yayarmu sai kuma mai bi mata Ameena wadda akema laƙabi da meena, sai kuma ni da ƙanwata fareeda.
Dukkanin wata buƙatar da zan tunkari mahaifina da ita musamman wadda ta shafi kuɗi cikin gaggawa mahaifina yake biyamin ita.
Ganin haka ne yasa nake yawan samun saɓani da mahaifiyata saboda ko kaɗan batajin daɗin yadda mahaifina yake shagwaɓani.
Kuruciyar da nake tattare da ita ne yasa nake aikata duk wani abun da naga dama domin ni kaina nasan ko ba'a tambayeni ba nasan ba yadda za'ai na wuce 19 years zuwa 20.
Tun a matakin Secondary abokaina su fara cusamin munanan ɗabi'u badan komai ba sai dan irin kuɗaɗan da suga ina wadaƙa dasu.
Dukkanin wasu abokan da nake tare dasu da zaran sun bijiromin da ƴan ƙananun buƙatu masu amfani haɗe da marassa amfani cikin gaggawa nake taimaka masu.
Ganin haka ne yasa su bugi ƙirjin bani shawarar kafa group.
Haka kuwa ayi domin wannan shawarar banyi watsi da ita ba.
Haka mu kafa ƙungiyar da bamu wuce mu takwas ba biyar maza ukku mata.
A cikin ƙungiyar tamu akwai "faruq abubakar wanda akewa laƙabi da Young Faruq. Sai kuma "Abdul Musa shima anamai laƙabi da Young Abdul Sai kuma Idris abdullahi, Wato Young Idris kenan. Sai kuma Ishaq Abubakar, laƙabinshi Young Ishaq. Sai kuma Uzairu Sha'aibu, wato Young Uzee.....
Ɓangaran mata kuma akwai Aisha Ahmad wadda akema laƙabi da Sister. Sai kuma Ameera Adam. Laƙabinta Meera. Ta ukkunsu kuma ba musulma bace sunanta Jeniffer John amma anfi kiranta da Merry.
Ganin yadda nake faɗa aji ne ta hanyar sawa ayi ko abari yasa suke kirana da (Babban Yaya).
A yayin damu bar junior mu shiga Senior sai al'amarin namu ya sake ƙarfi domin tun muna ss 1 mu fara fito da rashin mutuncinmu ƙarara ba tare da fargabar komai ba.
A haka har akai matakin da ss 2 da 3 tsoran mu sukeji ganin haka ne yasa malamanmu sukai ƙararmu zuwa ga iyayanmu.
Tabbas ba kaɗan muci duka ba saboda ba abun da zan iya ɓoye maku.
Tun daga wannan lokacin sai mu janye batun cin mutuncin na ƙasa damu haɗe dana sama damu.
Musamman nake cire kuɗi daga Aljihuna domin siya mana kayan da zamuyi ado dasu.
Kamar ranar asabar ko lahadi idan mun bushi iska mukan ɗauki shatar mota zuwa wani state ɗin da sunan yawon buɗe ido kokuma ince yawon shaƙatawa amma duk inda zamuje bama taɓa wuce kwana ɗaya haka ne yasa muke yima wannan fitar laƙabi da "1 day".
Da zaran mun dawo gida idan an tuhumemu domin jin a inda mu kwana sai muyi ƙarya da junanmu.
Musamman idan an tuhumeni a gida cewa nake "gidan su abdul naje muyi karatu danaga dare yayi shine na yanke shawarar kwana a can.
Wani lokacin kuma nakanyi ƙarya da batun zuwa wani garin da sunan bukin ɗaya daga cikin abokaina, amma nafiyin ƙarya da zuwa ziyarar wasu daga cikin dangina.
Duk tafiyar da zamuyi hotel ne yake kasancewa masaukinmu.
Mafarin lalacewarmu ya samo asali ne bayan mun gama shan wani rake a garin na Jos domin a wannan lokacin ne na yadda Eh lallai mace zata iya juya koma waye.
Bayan mun gama shan raken sai Merry ta miƙomin pure water haɗe da cewa. "Please wash me my hand.
Tun da nake a rayuwata bazan iya cewa yau ga ranar da na taɓa sa hannu a jikin wata ƴa mace da sani na ba sai a wannan lokacin.
Haka na karɓi ruwan daga hannunta domin aiwatar da abun da ta buƙata.
Ganin haka ne yasa sauran abokan tafiyarmu su riƙa dariya.
Bayan munyi yawanmu mun gaji da misali ƙarfe 9:30 na dare sai mu nufi masaukinmu wato hotel kenan.
=> 2
Tabbas a record ɗinmu dole ne musa garin jos a sahun farko saboda shine garin damu fara halarta da sunan shaƙatawa.
Amma kuma ta wani ɓangaran zan iya cewa a garin jos ne tarbiyyarmu ta ƙara samun nakasu.
Hotel ɗin da ya kasance masaukinmu shine (crest hotel jos) ɗaki biyu nayi niyar karɓa wanda zai kasance ɗaya namu ɗaya kuma nasu Aisha saboda bazai yiwu mu kwana a ɗaki ɗaya ba.
Buɗar bakin Abdul sai yace "gaskiya baza'ai haka ba kamar yadda muzo tare to ba makawa tare zamu kwana.
Koda naga dukansu sun goyi bayan maganar Abdul kawai nima sai na amince da hakan.
Tab! Ai abun ba'a cewa komai koda naga Ameera ta dafa kafaɗar idis a raina sai nace "tabbas a wajannan baza'a aikata abun arzuƙi ba, can kuma naga Abdul ya rungume A'isha wai duk a cikin ɗaukar selfie nikuma ina zaune a gefe ɗaya ina danna wayata.
Dama masu iya magana sunce zama da maɗaukin kanwa shi yake kawo farin kai.
Haka Merry tazo ta zauna kusa dani, koda naji jikina yana taba nata jikin sai na nemi matsawa daga kusa da ita kawai sai ji nayi ta riƙe hannuna ba yadda na iya haka na zauna kusa da ita.
A yayin da naga abun yana neman wuce gona da iri cikin gaggawa na dakatar dasu ta hanyar bayyana ɓacin rai na.
Ganin haka ne yasa ameera ta kalleni haɗe da cewa "haba babban yaya kayi haƙuri kasan ko kaɗan bamason ganin ɓacin ranka sannan ta miƙomin drink mai sanyi haɗe da cewa "ga wannan kasha domin zuciyarka tayi sanyi bansan lokacin da murmushi ya bayyana a fuskata ba.
Hana na karɓa haɗe da bayyana godiya a gareta.
Jim kaɗan da shan wannan drink ɗin sai naji bacci yana neman ɗaukeni wanda hakan yasa na nemi wuri na kwanta.
Bayan kwanciyata bazan iya cewa ga abun dasu aikata ba.
A yayin da nake tsaka da bacci kawai sai ji nayi merry tana jijjigani haɗe da cewa "ka tashi gari ya waye.
A wannan lokacin ko sallar asuba bazan iya cewa akwai wanda ya samu damar yin ba.
Maganar gaskiya tun farkon tashina salla bata wani dameni ba amma a wannan lokacin sai naji wani sabon imani ya shiga zuciyata wanda hakan yasa na nemi ruwa nayi alwallah domin yin sallah, tun daga wannan lokacin na daina yin sake da sallah.
A irin wannan yawon namu mun halarci jahohi da dama kuma hakan bai haifar mana da komai ba face gaggarumar matsala.
Kwatsam wata ranar asabar sai na shimfiɗawa iyayena ƙarya kamar dai yadda na saba,
Da sassafe na samu mahaifina bayan mun gaisa sai na bijiro mai da batun tafiya jahar katsina domin kaima kakannina ziyara.
Cikin yanayin farin ciki yace "khay babana daɗina da kai akwai son zumunci.
Jin daɗin haka ne yasa ya bani motarshi haɗe da wasu ƴan kudaɗe domin naji armashin tafiyar.
Tab ai tun kafin na fito daga gida na aikama Abdul da saƙon text message ɗin inda zamu haɗu.
Ina taƙaice maku dai a wannan ranar a garin kaduna mu yada zango.
Misalin ƙarfe 3 na rana a yayin da muke ƙoƙarin fita daga gamji gate muna cikin tafiya domin zuwa inda mu aje motarmu sai naji wayata tana ringing..
Koda na duba sai naga ai anti ameena ce take calling ɗina.
Bayan na amsa kiran cikin yanayin girmamawa nace anti meena anwuni lafiya?
Buɗar bakinta sai tace "kaga dakata, yanzu kana ina?
Cikin yanayin murmushi nace ai a yanzu haka ina katsina.
Tabbas nayi matuƙar tsorata a yayin da naji tace to dan waigo bayanka kaɗan ka gani.
A wannan lokacin ne naji duk ilahirin jikina ya ɗauke wuta domin ita na gani a yayin da na juya.
Cikin yanayin fargaba na tunkari inda take.
Koda na ƙarasa gareta kawai sai ji nayi ta tsunkeni da mari.
Cikin yanayin ɗaga murya tace "ban key ɗin motar.
Ba yadda na iya haka na miƙa mata key ɗin motar.
Cikin yanayin nadama nace "dan Allah anti kiyi haƙuri kar abba ya sani.
Nan take naga tayimin wani mugun kallo haɗe da cewar "to idanma kana fargabar karyasan abun da kake aikatawa ne tun wuri gwara ka daina domin shine yasani na biyo sawunka saboda ba tun yau yake jin labarin iskancin da kake aikatawa a tare da waɗancan wulaƙantattun abokan naka ba.
Duk da wannan bayanin da anti ameena tamin haɗe da karɓe motar da tayi baisa na bayyana ɓacin rai na ga abokain nawaba.
Bayan ta tafi sai suke tambayata dalilin da yasa ta karɓi motar.
Kaka na ɓoye masu gaskiyar al'amarin ta hanyar sanar dasu cewar "tazo bikin wata kawarta ne kuma sai a samu akasi motar ta ta samu matsala wanda hakan yasa tazo gareni domin na bata motar da take wajena.
Haka dai muci gaba da harkokinmu kamar yadda mu saba ta wani ɓangaran kuma ni kaɗai nasan abun da nakeji a zuciyata A'isha ce kaɗai ta fahimci alamun akwai wani abun da yake damuna.
Ganin haka ne yasa tazo gareni, da zuwanta sai ta ɗora hannunta a kafaɗa sannan ta kwanto a jikina cikin yanayin damuwa ta kalleni haɗe da cewa "Babban yaya me yake damunka?
Koda na kalleta sai nace "ƙanwata ai kasancewata a tare daku bazai taɓa barin damuwa ta tunkareni ba.
Sai ta girgiza kai haɗe da cewa "me yasa kakeson ɓoyemin gaskiyar abun da yake damunka karka manta mun ɗauki tsawon lokaci a tare, dan haka idan kai baka da fahimtar gane ɓacin rai na toni zan iya gane taka damuwar koda kuwa kayi ƙoƙarin boyeta ne saboda kasancewarmu a tare yafi ƙarfin wasa.
Koda na kalleta sai nayi murmushi sannan nace "tabbas kece wadda ta dace na riƙeta da muhimmanci a game da rayuwata.
Haka nima na dafa kafaɗarta haɗe da ceea "aisha zanso kiyimin alƙawarin komai daɗi ko wahala wannan kawancan namu bazai taɓa samun nakasu ba.
Haka tasa hannunta ta shafa fuskata haɗe da riƙe haɓata sannan tayi murmushi tace "nayima alƙawarin bazan taɓa juyama baya ba zan kasance a tare da kai komai daɗi ko wahala.
Bayan nayi mata bayani a game da abun da ya faru sai itama ta nuna ɓacin ranta sannan tace "yanzu kana nufin shikenan wannan ƙungiyar tamu ta watse kenan.
Sai na girgiza kai haɗe da cewa. "ai yanzu a fara.
A ranar damu koma gida bayan mun rabu kowa ya kama hanyar gida tun kafin na ƙarasa gida sai ƴan sanda suyi ram dani.
Wai ashe mahaifina ne yasa duk inda su ganni suyi arresting ɗina abun bai yimin daɗi ba domin kwanana biyu a hannunsu.
Batun duka kuma bazan iya musalta irin dukan da naci ba.
Tabbas nasha matuƙar wahala, bayan an sallameni na koma gida.
Haka na shiga ɗakina nayi kwanciyata saboda a wannan lokacin nayi matuƙar gajiya.
Har bacci ya fara ɗaukata sai ƙanwata fareeda ta shigo ɗakin.
Buɗe idon da zanyi sai na ganta rile da plate na abinci.
Allah sarki ƙanwata cikin girmamawa tace "yayana ga abinci.
Tashin da zanyi zaune ji kake tass!! Na dauketa da mari sannan nayi fatali da abincin waje.
Ban sani ba ashe mahaifina yana gidan domin ranar bai fita office ba.
Kawai sai ji nayi mahaifiyata tace "wane tabbataccen ne ya watso abinci waje.
Haka fareeda ta dafe fuskarta ta fita tana kuka.
Ban tashi aune ba sai ganin mahaifina nayi a tsakiyar ɗakin nawa.
Cikin yanayin takaici yace "babana yaushe kakai wannan matsayin, wace irin kwaya kakesha, da har zatasa ka rika aikata mana abun da kaga dama?
Buɗar bakin mahaifiyata sai tace "a'a karka ɗauki alhakin kwaya domin kai ne sular faruwar wannan mummunar halayyar a gareshi.
Saboda tun farko sai da na haneka a game da shagwabashi ɗin da kakeyi, yanzu ga irintanan.
Haka mahaifina ya jinjina kai sannan yai waje ranshi a ɓace.
Tun daga wannan ranar na fara fuskatar matsala a tsakanina da mahaifina.
Ni kuma ko kaɗan bazan taɓa iya rabuwa da abokaina ba.
Koda naga mahaifina ya juya min baya kuma gashi rashin kuɗi ya addabeni Sai kawai na cire duk wata fargabar da ke zuciyata.
Kai na tsaye na tunkari mahaifina da buƙatar kuɗin da zansa a aljihuna.
Wani kalar kallo naga ya min sannan yasa hannu aljihu.
Haka ya fito da kuɗi masu yawa amma sai abun yai matuƙar bani mamaki domin dubu ɗaya naga ya miƙomin haɗe da yimin bayanin cewar "ka ɗauki ɗari biyar ka dawo min da sauran canjin.
Buɗar bakina sai nace "amma abba ai ɗari biyar ko kuɗin kati bazusu isheni ba.
Koda ya kalleni sai yace "ka godema Allah da har na iya ɗaukar ɗari biyar na baka, dan haka maza ka ɓacemin da gani.
Haka na tashi rai na a ɓace ba tare da na samu biyan buƙata ta ba.
Haka na zauna a falo nayi shiru domin tunanin hanyar da zan bi wajan ganin na samu kuɗin da zasu kawar da damuwata.
A haka dai na ɗauki tsawon wasu kwanaki ba tare dana riƙe wasu kuɗi masu kauri ba.
Duk da cewar mun kusan yin candy a school ɗin mu hakan bai hanani jin kunyar halartar makaranta ba.
Saboda duk makarantar sunsanni wajan facaka da kuɗi sai kuma a samu akasi lokaci ɗaya kamar anyi ruwa an ɗauke.
Ganin haka ne yasa na shiga damuwa mai tsanani wanda hakan yasa na kasa jurewa.
Kasa jurewar da nayi ne yasa cikin dare na ɗauke wayar babbar yayarmu wato A'isha kenan.
Alhalin kuma ban san ko nawa ta sayi wayar ba layikan kawai nasan na bar mata.
Cikin dare nayi wiping ɗin wayar washe gari kuma da misalin ƙarfe 9 na kaita kasuwa.
Koda naga an sayi wayar 35 thouthans cikin gaggawa na karɓe kuɗi.
A wannan ranar dai bani na koma gida ba sai cikin dare.
Dawowata daga yawo kenan sai anti Aisha ta shigo ɗakina.
Haka ta zauna kusa dani sannan ta kalleni haɗe da cewa "talaucifa ba hauka bane, me yasa ka ɗaukemin waya?
Cikin yanayin rashin gaskiya muryata tana rawa nace "anti wace waya kuma?
Budar bakinta sai tace "kaga ni banzo gareka domin muyi cacar baki ba kawai abun da nakeso da kai shine "karka sake taɓamin kaya muddun ba tambayata kayi ba, sannan ta fice daga ɗakin.
Tun daga wannan ranar sai na nemi kare zuciyata a game da taɓa abun da ba mallakina ba.
Ban sani ba ashe kare zuciyar tawa daga aikata hakan ba abu ne mai sauƙi ba domin ko cikakken sati da faruwar haka ba aiba na nemi kuɗin da na siyar da wayar na rasa domin tuni naga bayan su.
Nanfa wani sabon talaucin ya sake bijiromin ganin haka ne yasa na yanke shawarar yiwa mahaifina dogon hannu wato sata kenan.
Amma kafin na samu sa'ar aikata hakan sai da na kwashi tsawin wasu kwanaki domin yin nazarin hanyar da zanbi wajan ganin na ragewa lalitar mahaifina nauyi.
A yayin da na samu nasarar shiga ɗakin mahaifin nawa sai da na tafka mai babbar satar da ni kai na bansan adadin kuɗin dana ɗiba ba.
Ban sani ba ashe bayan na shiga ɗakin ƙofar ta koma wanda hakan ya bata damar kulle kanta.
Bayan na saci abun da zan sata haka naja ƙofar iya jana amma taƙi buɗewa.
Cikin gaggawa mai tattare da fargaba na fara neman key ɗin ɗakin ta hanyar caje kaina.
Bayan na samu nasarar ganin key ɗin a aljihuna haka nasa key ɗin a ƙofar domin buɗewa nanfa naji gumi ya fara ketomin sakamakon ƙin buɗewar da ƙofar tayi.
Abu kamar wasa nine har wajan 3 hours ina kici-kicin buɗe ƙofar amma abun yaci tura duk da irin yunwar da nakeji a wannan lokacin gaba ɗaya sai na manta da ita.
In taƙaice muku dai nine har yamma a ɗakin ni ba'a zaune ba ni ba'a tsaye ba Ni kaɗai sai sun batu nake kamar wani tsohon mahaukaci.
Haka duk nabi na jike da gumi duk bayan wasu yan saconni ko mintuna sai na tuna da abbana kuma hakan ba kaɗan yake cutar da zuciyata ba domin wata irin bugawa zuciyar tawa takeyi yadda kasan motocin da suyi karo da juna koda naji ƙarar horn ɗin mota sai zuciyata ta shiga kokwanto domin a wannan lokacin ba yadda za'a i na iya gane abbana ne ya dawo ko kuma ƙarar wata motar naji a can waje.
Zuwa can koda naji anyi sallama sai nace to wannan kuma waye ya shigo Allah yasa dai ba abbana bane koda naji fareeda tana cewa "oyoyo abba, you are welcome" saboda tsabar tsoro bansan lokacin da na saki fitsari a wando ba saboda nasan ba batun jin daɗi a yayin da abbana yai ido biyu dani a ɗakinshi.
=> 3
Cikin yanayin tsoro na zura key ɗin a gigice Allah cikin ikonsa koda na murza key ɗin a hankali sai ƙofar ta buɗe saɗaf-saɗaf na afka ɗakina ba tare da kowa yayi ido biyu dani ba bayan nayi wanka ko abinci banciba sai na kira Sister Aisha a waya.
Bayan ta amsa kiran sai na sanar da ita cewar "mu haɗu a bayan makaranta kusa da gidansu.
Jim kaɗan da isata wajan sai itama ta halarci wajan bayan tayi gaisuwa irin ta girmamawa a gareni sannan na miƙa mata hannu muyi musabeha kamar yadda mu saba aduk lokacin damu haɗu murmushi naga A'isha tayi sannan tace "lafiya kuwa kazo gareni cikin dare haka?
Buɗar bakina sai nace amma A'isha tsakanina dake bai kamata irin wannan tambayar ta riƙa shiga tsakaninmu ba saboda a tunanina kamar mun riga mun zama ɗaya ne.
Sai tayi murmushi haɗe da cewa "haba babban yaya ai jin daɗin zuwanka gareni a dai-dai wannan lokacin ne yasa kaji nayi wannan tambayar a gareka.
Sai nace "dama wasu ƴan kuɗaɗe ne nazo miki dasu domin ki ajeminsu saboda gudun samun matsala.
Koda aisha taga kuɗin sun zarce tunaninta sai ta kalleni a sufane haɗe da cewa amma babban yaya waɗannan kuɗin.....
Koda naji tayi shiru ba tare da ta ƙarasa maganarta ba sai na ɗanyi murmushi haɗe da cewa "A'isha karkiji komai zaki iya yin duk wata tambayarki a gareni domin bazan iya ɓoye miki komai ba.
Sai tace "dama tambayar da zanyima bazata wuce neman sanin inda ka samo waɗannan kuɗin ba.
Buɗar bakina sai nace "A'isha ke tawace wadda bana tunanin cewar zaki gujeni aduk halin dana tsunci kai na a ciki.
Amma sai dai kuma bazan taɓa jurar ganin ƙasƙanci a tattare dani ba, dan haka a matsayinki na wadda na aminta da ita zanyi miki bayanin komai a yanzu.
Haka na kalli A'isha sannan na dafa kafaɗarta haɗe da cewa "A'isha abbana ya kwaɗaita zuciyata da masifar son kuɗi lokaci ɗaya naji ɗuf! Kamar anyi ruwa an ɗauke gaba ɗaya abbana ya juya min baya.
Abbana yana bani kuɗi sama da 40 thouthan abun takaici wai yanzu nine zan tunkareshi da buƙatar kuɗi wai ya rasa abun da zai bani sai dubu ɗaya,a dubu ɗayarma wai na ɗauki ɗari biyar na dawomai da sauran canjin.
Bayan na shiga ɗaki da abun yai matuƙar ƙonamin rai bansan lokacin da na yaga dubu ɗayar daya bani ba.
Sannan na kalleta nace "A'isha kinsan me nayi a yayin da talauci ya fara yimin nisa a cikin zuciyata kuwa?
Sai ta girgiza kai haɗe da cewa "a'a.
Sai nace to wayar yayata na sace iya Sun card ɗin kaɗai na barmata na kuma sai da wayar 35 thouthan kinsan kuɗin sata bawani albarka ne dasuba cikin ɗan taƙaitaccen lokaci na rasa abun da nayi da kuɗin domin tuni naga bayansu a wannan lokacinne wani sabon talaucin ya sake bijiromin mai matuƙar karfin tsiya.
Ganin haka ne yasa na shiga ɗakin abbana na sato waɗannan kuɗaɗan.
Nan take naga A'isha ta girgiza kai haɗe da furta kalmar "subhanallahi" amma baban yaya kana ganin hakan daka aikata itace mafita a gareka?
Buɗar bakina sai nace to A'isha idan banyi haka ba ya kikeson nayi da rayuwata?
Matsowa tayi daf dani haɗe da cewa "na aminta da kai kamar yadda ka aminta dani ka samar mana da nishaɗi mai matuƙar diɗi ta hanyar sakar mana kuɗaɗan da muke da yaƙinin cewar abbanka ne yake bakasu.
Halaccin da kayi mana bazai bari na zuba ma ido wajan aikata ba dai-dai ba, dan haka idan har zaka karɓi shawarar da zan baka a yanzu ina mai tabbatarma cewar abbanka zaiji daɗi kuma zai dawoma da duk wani abun da ka rasa na jin daɗi a game da rayuwar ka.
Cikin yanayin zumuɗi na riƙe hannunta haɗe da cewa "A'isha kiyiwa Allah da Manzonsa ki sanar dani wannan shawarar domin a shirye nake wajan binta.
Sai tace "wannan shawarar dazan baka dolene sai ka cire tsoro haɗe da kawar da duk wata fargabar da ke zuciyarka.
Buɗar bakina sai nace A'isha zan iya yin komai domin kawar da talaucin da nake tare dashi a halin yanzu.
Sai tace "samun mahaifinka zakayi kamar da safe kafin ya fita wajan aiki, bayan kun gaisa cikin yanayin ladama zaka miƙamai waɗannan kuɗin da ka sato mai haɗe da roƙonshi domin neman yafiyar duk wani laifin da kayimai.
Sannan ka ɗaukarmai alƙawarin canza duk wasu munanan halayanka daga ƙarshe kuma saika sanar dashi gaskiyar yadda ai kuɗin suje hannunka ta hanyar sanar dashi cewar satarmai su kayi a ɗakinshi.
Sannan kayi mai bayanin cewa "Abba nayi nazari ne haɗe da dogon tunani akan cewar duk wani neman da kakeyi yanayi ne domin mu badan komai ba sai dan gudun karmu tsinci kanmu cikin wahalar duniya.
Sannan sadiya ta kalleni haɗe da cewa "na tabbata idan har kayimai wannan jawabin kamar yadda nayima to zaiyi matuƙar jin daɗinka fiye da baya cikin yanayin jin ɗaɗi na mika mata hannu muyi musabeha haɗe da yimata godiya.
Washe gari da sassafe mahaifina yana zaune a falo gefe ɗaya kuma babbar yayarmuce tare da ƙanwata fareeda suna wasa da dariya ɗayan ɓangaran kuma mahaifiyatace zaune tare da ameena kaina tsaye na fito da kuɗin bayan na gaishe da ummata sannan na durƙusa har ƙasa na gaishe da abban nawa haka na miƙa mai kuɗin kamar yadda sister aisha ta bani shawara cikin yanayin ladama nace "dan Allah abba kayi haƙuri a game da laifukan dana aikatama kuma nayima alƙawarin canza duk wasu munanan halayena daga ƙarshe kuma nace "abba son zuciyata ne ya ingizani ta hanyar satarma waɗannan kuɗaɗan.
Nan take naga abbana haɗe da mahaifiyata da sauran ƴan uwana duk sun kalleni fuskarsu cike da mamaki.
Cikin yanayin kunya na sunkuyar da kai na ƙasa sannan naci gaba da yimai bayani.
Nace abba bayan na saci kuɗin sai nayi tunanin ai duk wani neman da kakeyi bazai taɓa wuce akanmu ba badan komai ba sai dan gudun karka barmu cikin wahala. wannan tunanin da nayi ne yasa nayi takaicin satar waɗannan kuɗaɗan domin nasan kasancewata a tare dasu bazai taɓa amfanata da komai ba face tsantsar wahala.
Haka na riƙe hannun abbana haɗe da zubar da hawaye ina mai cewa dan Allah abba kayi haƙuri na bazan sakeba.
Sai ya shafa kai na haɗe da cewar ba komai babana na yafema tunda kayi ladama haka ya cire 50 thouthan daga cikin kuɗin ya damƙamin haɗe da yimin bayanin cewar duk cikin ƴayana ba wanda nake sakarma kuɗi kamarka tunda nake a rayuwata ban taɓa ɗaukar 10 thouthan na damƙawa yayarka A'isha ko Ameena ba kuma hakan bawai yana nufin duk bana son ku ba.
Tabbas ina matuƙar son ku kawai abun da nakeso a gareku shine tsare mutuncinku domin idan mutuncin ɗaya daga cikinku ya zube to nimafa nawa ya zube haka ya ɗauki 50 thouthan yaba A'isha itama Ameena ya bita da 50 thouthan autarmu kuma wato fareeda 30 thouthan badan komai ba sai dan buƙatar mu kawar da buƙatun dake gabanmu ba tare da munsa idanmu gana wasu ba.
Aiko a wannan ranar na kira sister aisha a waya domin yi mata godiya a game da hanyar da ta ɗorani wanda hakan yasa itama na bata 20 thousands daga cikin kuɗin da mahaifin nawa ya bani.
Tun daga wannan ranar gaba ɗaya sai harkokin da mu saba zartar dasu ba'a kan ka'idaba suja baya ganin haka ne yasa sauran abokaina suja baya a gareni amma ita aisha ko kaɗan bata wani canzamin fuska daga yadda na santa ba.
Bayan kwana ukku da faruwar haka sai mahaifina yazomin da albishirin samamin Admission a (Federal university of birnin kebbi) koda na sanar da sister aisha wannan batun sai tayi matuƙar tayani farin ciki ban saniba ashe akwai abun da yake damunta a zuciya ana gobe zan tafi cikin dare da misalin 9:30 sai jeniffer wato merry tayi calling.. ɗina a waya.
Ban wani ɓata lokaci na haka na amsa kiran.
Duk da cewar ita ba musulma bace hakan bai hana hausa ta samu masauki a bakintaba koda nace "hello a yayin dana amsa wayar sai tace "please may bro i need your help.
Buɗar bakina sai nace "merry me kuma ya faru kike neman taimakona cikin dare haka?
Cikin yanayin damuwa tace yanzu haka ina bayan gidanku.
Sai nace to ki jirani ganinan fitowa turƙashi ai maganar da merry tazo da ita ba ƙaramar magana bace.
Buɗar bakina a yayin da nayi ido biyu da ita sai nace "merry what happing to you?
Tabbas furucin da ya fito daga bakin Merry ba kaɗan ya jefani a ruɗani ba domin cewa tayi "ciki nake ɗauke dashi.
=> 4
Cikin yanayin ruɗani mai tattare da mamaki na kalli Merry haɗe da cewa "to amma merry waya miki wannan cikin?
Buɗar bakinta sai tace " abdul ne cikin gaggawa na zafga salati haɗe da kiran "innalillahi-wa'inna-ilaihi-raji'un" domin nasan muddun wannan maganar ta fito fili to ba makawa mutuncin gidansu Abdul sai ya samu nakasu saboda mahaifin Abdul babban malamin addini ne wanda yai fice a idan al'umma kasancewata na abokin abdul ne yasa na ɗauki mahaifinshi tamkar mahaifina wannan ne yasa ko kaɗan bazan juri ganin mutuncin gidansu ya samu rauni ba koda na kalleta sai nace "to amma merry kin sanar da abdul halin da kike ciki kuwa?
Sai tace "na sanar dashi amma yace shi ba ruwanshi har marinama yayi cikin gaggawa nayi calling.. ɗin abdul a waya
Koda ya amsa sai na sanar dashi cewar ina buƙatar ganinshi cikin ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba sai gashi ya bayyana a garemu.
Koda yaga merry a tare dani cikin yanayin ɓacin rai yace "me kuma wannan munafukar takeyi a nan?
Buɗar bakina sai nace "amma abdul baka da hankali yarinyar nan fa cutarta kayi dan haka kai ne da alhakin nema mata mafita a halin yanzu tun kafin abun yai nisa.
Ya buɗa baki zaiyi magana sai nace " kaga dakata sai na jashi gefe.
Bayan mun samu wuri mun tsaya sai na riƙe hannun Abdul fuskata ba alamar wasa nace Abdul kai abokina ne wanda bazanso ganin tashin hankali a tattare da shi ba dan haka kamar yadda bazan iya ɓoyema duk wani sirrina ba zanso kasanar dani gaskiyar abun da yake a tsakaninka da merry.
Buɗar bakinshi sai yace tabbas ni nayi mata cikin amma gaskiya bansan hanyar da zan bi wajan ganin asirinmu ya rufu ba.
Dan Allah babban yaya kabi hanyar da zaka karemu daga wannan abun kunyar.
Sai nace "Abdul duk irin ingizani ɗin da kuyi wajan aikata al'amuran da basu dace ba hakan bazai iya sawa na tunkari wata mace da sunan aikata fasiƙanci ba.
Ba kuma wata bace tayi sular dawo dani kan hanya da ta dace ba illah A'isha duk da haka bazan taɓa gudunka a matsayinka na abokaina ba dan haka na ɗaukarma alƙawarin bada gudun mawata wajan kawar da wannan damuwar.
Koda mu dawo wajan merry sai na sanar da ita duk maganar da muyi sannan nace "yanzu merry ya kikeson ayi da cikin nan.
Koda naji tayi batun zubarwa sai nace "ai wannan duk mai sauƙi ne kawai kije gida gobe zan nemeki.
Abun da tace shine idan ta koma gida mahaifina bazai barni da rai ba domin sun riga sun gane abun da yake tattare dani gudun kar kowa yasan abun da yake faruwa ne yasa naƙi sanar dasu wanda ya min cikin kuma gashi bani da wasu abokan dasu wuce ku balle na nemi makwanci a garesu.
A wannan ranar dai a ɗaya daga cikin motocin gidanmu ta kwanta ba tare da kowa ya saniba.
Gudun kar mutanan gidanmu susan na kawo wata gidan namu ne yasa na sama wayata Alarm ɗin da zai tasheni misalin ƙarfe 5:30 daga bacci domin fitar da merry ba tare da kowa ya sani ba.
Da yake ƙaramar waya nake amfani da ita ban sani ba garin jiye-juye a yayin da nake bacci ashe tuni wayar ta faɗo daga saman gado wanda hakan yai sukar fitar batirin daga wayar.
Kawai sai ji nayi an tsunkamin mari a fuskata wanda hakan yasa na tashi daga baccin da nakeyi a gigice.
Koda nayi ido biyu da Anti Ameena tsaye a gaba sai tace "wawa kawai tun wajan awa nawa kake kwance kamar wani mashayi gashi har ƙarfe 9 tayi ko sallah baka tashi kayi ba balle ayi batun breakfast.
Cikin yanayin fargaba nace "kar dai kice har abba ya tafi office?
Sai tace "au da zai tsaya jirankane.
A tsorace nasa rigata nayi waje saboda bansan wace motar ya hauba.
Koda naga ba motar da merry take ciki ya ɗauka ba sai naji wani sanyi a zuciyata.
Da zuwana gare ta sai na buɗe motar.
Koda na haɗa ido da Mery sai naga tayi murmushi.
Haka na kawo mata ruwa ta wanke fuskarta a sace na kawo mata abinci haɗe da ruwan da zatasha sannan nace da ita "ammafa merry nayi mantuwa yaune ranar da zan tafi school yanzu ya kike ganin za'ayi.
Koda ta kalleni sai tace "nifa ba yadda za'ai na koma gida ba tare da an zubar da cikin da nake ɗauke dashi ba.
Ƙuruciyar da nake tattare da itane yasa nayi mata tayin tafiya tare da ita makarantar da zani wato birnin kebbi kenan da ƙudurin bayan an warware matsalar acan sai ta dawo gida ba tare da kowa yasan abun da ya faru ba.
Bayan mun fito daga gidan sai na sanar da ita inda zamu haɗu da zaran na kammala shirina.
Bayan mun rabu a yayin da na shiga gida sai nayi calling ɗin abbana a waya.
Bayan ya amsa kiran sai nace "abba yaunefa zan wuce school kuma gashi naga har ka fita.
Sai yace "au meka maidani to da kana tunanin zaman jiranka zaanyi, ka tambayi A'isha na bata duk wani abun da ya dace domin ta baka.
Koda na samu anyi A'isha kwance a ɗaki cikin yanayin girmamawa nace anti abba yace ki bani saƙon da ya baki.
Key ɗin mota naga ta miƙomin haɗe da wasu kuɗaɗe masu sai kuma key ɗin gidan da zai kasance masauki a gareni.
Bayan nayi wanka na kammala duk wani shirina a yayin da na haɗu da merry a inda nace mu haɗu haka na ɗauketa mu tafi ba tare da tunanin abun da zai biyo baya ba.
=> 5
Da misalin ƙarfe 9 na dare mu isa burnin kebbi tun kafin mu doshi masaukinmu na fuskanci akwai yunwa a tattare da merry.
Ganin haka ne yasa na siya mana abun da zamuci kafin mu ƙarasa.
Da isarmu bayan munyi wanka sai mu zauna a falo kamar dai yadda mu saba haka mu zauna muci abincin tare sakamakon akwai matsananciyar gajiya a tattare dani ne yasa naji bacci yana neman ɗaukeni wanda hakan yasa na umarci merry da ta shiga ɗaki ta kwanta sannan na nemi guri a falo na kwanta.
Ɗabi'ata ce rashin tashi da wuri.
A yayin da nake cikin baccina mai daɗi kawai sai ji nayi merry ta tasheni haɗe da cewa "katashi gari ya waye.
Misalin ƙarfe 7:30 nayi alwallah da ƙudirin yin sallar asubah bayan nayi kara'in sallar da ni kaina bani da tabbacin karɓuwarta a wurin ubangijina sannan na shiga toilet domin yin wanka.
Bayan na kammala shirina tsaf sannan na wuce school na bar merry ita kaɗai da ƙudirin bayan na dawo zan kaita inda za'ai mata abortion wato a zubar da cikin da take ɗauke dashi.
A yayin da nake kan hanyata ta dawowa gida sai zuciyata take bani shawara akan abun da nake shirin aikatawa a game da batun zubar da cikin da merry take ɗauke dashi.
Haka zuciyata ta riƙa razanani ta hanyar saƙe-saƙen cewar "muddun ka kuskura ka aikata haka to ba makawa sai ka samu kaso mai tsoka na alhakin zubar da cikin da zakasa ayi, kuma zata iya yiwuwa alhakin ka yafi nasu yawa.
Wannan tunanin da zuciyar tawa tayi ne yasa nayi packing ɗin motar da nake tuƙawa a gefen hanya.
Haka nayi shiru domin tunanin hanyar da ta dace wajan kaucema wannan baƙin aikin.
Kuma gashi na ɗaukarwa merry alƙawarin cika mata burinta na zubar da cikin da take ɗauke dashi.
Haka dai na tunkari gida ba tare da zuciyata ta daina tunanin neman mafita ba.
Da isata gida bayan nayi packing cikin yanayin damuwa na shiga falo.
Da shigata falo sai naga merry zaune tana jiran dawowata.
Cikin yanayin sakin fuska ta kalleni haɗe da cewa "you're welcome"
Haka na zauna kusa da ita cikin yanayin tausayawa na riƙe hannunta nace "merry kiyi haƙuri a game da maganar da zan sanar dake a halin yanzu.
Koda na kalleta sai nace "merry addinina na musulunci ya hanemu da aikata zubar da ciki, dan haka kiyi haƙuri ki kasance a tare dani har zuwa lokacin da zaki haifi abun da yake cikin ki.
Kuma nayi miki alƙawarin zan kasance garkuwa ga rayuwarki har zuwa lokacin da zamu rabu kuma na ɗaukar miki alƙawarin zan mayar dake ga iyayanki da zaran kin haihu ba tare da kin fuskanci wata matsala a garesu ba.
Nan take naga wani sabon hawaye ya keto daga idanunta wanda hakan ya ƙara sani jin tausayinta.
Duk da cewar cikin da take ɗauke dashi bai wani ɗauki dogon lokaciba haka na rungumi ƙaddarar kasancewa a tare da ita ba dan komai ba sai dan kare mutuncin mahaifin abdul haɗe da ceton rayuwar jaririn da yake cikinta.
Washe gari bayan na tafi school sai a samu akasi ban dawo gida da wuri ba, koda merry taji shiru kuma gashi yunwa tayi mata matsanancin kamu kawai sai ta buɗe fridge ta ɗakko lemo Coke haɗe da Bread domin kawar da yunwar da take damunta.
Jim kaɗan da shan wannan lemon sai taji cikinta yana murɗa mata har a kai matakin da ta fara fita hayyacinta.
Shigowata gidan kenan sai na samu merry kwance a falo a wani irin mawuyacin hali.
Koda naga tana bleeding wato zubar da jini kenan cikin gaggawa nasa hannu na ɗauketa zuwa mota.
Bayan na sata a mota ban tsaya ko inaba sai a wani General Hospital.
Bayan merry ta samu sauƙi a yayin da takaddar result ɗin abun da ya faru da ita ta iso gareni nan take na tsunke merry da mari haɗe da cewa amma ke ba ƙaramar wawiya bace,ashe dama kinsha lemon ne domin ya kawar da cikin da kike ɗauke dashi?
Haka ta dafe fuskarta haɗe da cewar dan Allah kayi haƙuri bansha lemon domin buƙatar haka ta faru dani ba.
Nasha ne domin kawar da yunwar da nake tattare da ita sakamakon rashin dawowarka gareni da wuri.
Koda likitan yaji wannan bayanin daga bakin merry sai yace haba abokina ai ya kamata ka kasance mai uziri a gareta tunda ta tabbatarma da cewar batasan hakan zai faru da itaba.
Jim kadan da komawata gida sai Sister A'isha ta kirani a waya.
Bayan na amsa kiran ko kadan banyi tunanin jin furucin da A'isha tayi a gareni ba domin ko sallama banji tayi ba kawai ji nayi tace "tabbas kayi kuskure tunda ka bari mugun halinka ya bayyana a idon duniya.
Buɗar bakina a yayin da naji wannan furucin daga bakin A'isha sai nace.
Amma A'isha kinsan dawa kike magana kuwa?
Sai tace "waye kuwa banda Young Uzee sannan ta yanke wayar.
Ban sani ba ashe Abdul ne ya munafunceni ta hanyar gogamin baƙin fenti.
Ko 1 minute da kiran da A'isha taimin ba ai ba sai calling ɗin mahaifina ya shigo wayata.
Koda na amsa kiran cikin gaggawa yace duk inda kake a halin yanzu maza ka dawo gida idan ba haka ba zanyi matukar saɓama.
A wannan ranar na ɗauki hanyar Kano amma ba tare da merry ba.
15 thousands na damƙawa merry haɗe da ɗaukar mata alƙawarin bazan wuce 2 days ba zan dawo gareta.
Ban sani ba ashe gaggarumar matsala zan fuskanta a yayin dana halarci gida.
=> 6
Da isata gida ko zama banyiba sai abbana ya kalleni hade da cewa, ni zaka maida mutumin banza ko?
Buɗar bakina sai nace "subhanallahi" abba me kuma ya faru.
Cikin yanayin ɗaga murya yace "kaji munafikin banza.
To bari kaji muddun bakayi gaggawar fito masu da ƴarsu ba haɗe da yimin bayanin wanda yai mata ciki to wallahi sai nasa anci mutuncinka.
Haka na nuna kamar bansan abun da yake faruwa ba ta hanyar kallan mahaifiyata haɗe da cewa " umma wace yarinyarce ake zargina da batun ɗaukewa domin tun da nake a rayuwata ban taɓa tunanin kasancewar irin wannan al'amarin a gareni ba.
Dan Allah zanso kuyi gaggawar sanar dani yarinyar da ake alaƙanta wannan zargin a gareni?
Cikin yanayin ɗaga murya anti Aisha tace "karka raina mana wayo, kana nufin abokinka Abdul zai yima ƙarya ne? to idanma so kake kaji ko wacece to ba wata bace illa jeniffer wadda kuke kiranta da merry dan haka kayi gaggawar fito masu da ƴarsu tun kafin ranka ya ɓaci.
Haka na kalli abbana haɗe da A'isha nace "tabbas Abdul yayimin ƙazafin da bana tunanin cewar zan iya yafemai.
To amma duk da irin butulcin da Abdul yamin baisa na bayyana gaskiyar al'amarin ba domin haka mahaifin merry ya damƙani a hannun jami'an ƴan sanda domin gudanar da bincike a gareni.
Haka mahaifin mery ya sanar da ƴan sanda cewar bazai iya shara'a dani ba amma ya basu izinin suyimin duk abun da suga ya dace domin tono gaskiyar abun da yake faruwa.
A yayin da ake ganamin azaba sai da nayi ƙudirin faɗar gaskiya sai kuma na tuna da cewar idanfa har a samu merry a tare dani to ba makawa ni za'a ɗorama duk laifin abun da ya faru, haka ne yasa na gwammaci rasa rayuwata domin kare mutuncin gidanmu.
Kwanana huɗu a hannun jami'an ƴan sanda, dakyar na kuɓuta daga sharrin da'a nemi ɗoramin ta hanyar dagewa da roƙon mahaliccinmu.
To amma duk da haka mahaifina bai rangwantamin ba domin nasan ko kaɗan bashi da wasa haka shima mahaifina ya damƙani a hannun ƴan banga.
Abu kamar wasa na ɗauka bazan wuce kwana ɗayqva hannunsu ba amma nune har tsawon sati biyu tsare a hannunsu.
A wannan lokacin ba komai ne yakesani zubar da hawaye ba illa tunanin halin da merry take ciki a dalilin rashin komawata ba
Ranar da abbana ya bada umarnin sakina daƙar na shawo kanshi a game da batun komawata school.
Bayan fitowata nayi ƙudurin tunkarar Abdul domin jin dalilin da yasa ya nemi ɗoramin sharri sai kuma naga ai hakanma bashi da wani amfani a gareni.
A ranar da na koma kebbi ba inda na tsaya sai a gidan da nake zaune da merry.
Da shigata gidan sai na taradda merry zaune a falo kai da ganinta kasan tana cikin damuwa.
Koda tayi ido biyu dani cikin yanayin farin ciki ta taso zuwa gareni, haka ta rungumeni haɗe da nuna ɓacin ranta a sakamakon rashin cika mata alƙawarin da nayi na rashin dawowata gareta akan lokaci.
Ko kaɗan banga wani laifinta ba saboda bata da masaniyar halin dana tsinci kai na a yayin dana halarci gida domin banyi mata bayanin komai ba.
A ƙarshema haƙuri na bata haɗe da rarrashinta bayan kwana biyu da faruwar hakan sai na umarceta da ta shirya domin na maidata gida.
Buɗar bakinta sai tace "dan Allah kayi haƙuri ka barni domin na ɗan zauna tare da kai na ɗan wani lokaci domin idan ka maidani can jahar mukodi zasu maidani da zama wurin yayan mahaifina kuma ba ƙaramar wahala zansha acan ba domin tun ina ƴar ƙarama nake fuskantar wahala a garesu saboda tun ina ƴar ƙarama mahaifiyata da mahaifina subar duniya sakamakon haɗarin motar da ya faru dasu a hanyarsu ta dawowa gida daga Lagos.
Shi kuma wanda nake zaune a wajanshi ƙanin mahaifiyatane kuma ina fuskantar takurawa a tattare dashi.
Tabbas bama ni kaina ba duk wanda ya kalli fuskar merry a wannan lokacin dolene ya tausaya mata wanda hakan yasa ba yadda na iya haka na barta taci gaba da zama a tare dani.
Ko kaɗan ban taɓa tunanin shaƙuwa mai zata shiga tsakanina da merry ba.
Mukanci abinci tare, mu fita yawo tare, domin ba yadda za'ai merry taci abinci ba tare dani ba idan kuma dare yayi wajan kwananta daban haka nima nawa wajan kwanan daban.
Saboda jin daɗin kasancewarmu a tare ne yasa itama na nema mata admission a school ɗin da nake karatu.
Saboda gudun kar rabuwa ta gifta tsakanina da ita ne yasa na daki ƙirjin son kasancewarta a matsayin matata badan komai ba sai dan kareta daga afkawa a cikin ɓacinran danginta domin addininmu na musulunci bai hanemu da auran wadda ba musulma ba.
Tun ina level 2 ita kuma merry tana level 1 giyar soyayyar merry ta ruɗeni ta hanyar ɗaukar alwashin auranta.
Duk da cewar nasan mahaifina yanada tsats-tsauran ra'ayi kuma bawai na manta da abun da ya faru dani a baya ba hakan bai hanani ƙudirin afkawa a fagen soyayyar merry ba.
Da misalin ƙarfe 3:30 na rana a yayin da nake cin abinci tare da merry.
Buɗar bakina a yayin da na kalleta sai nace "merry kinajin idan har na bayyana cewar zan aureki domin baki kulawar da ta dace na tsawon rayuwarmu zaki amince?
Kanta tsaye tace a'a.
Cikin yanayin mamaki nace amma merry me yasa zaki ƙi amincewa da wannan ƙudirin nawa?
Sai tace "saboda kai musulmine kuma hakan zai iya haifar da gaggarumar matsala a tsakanina da dangina..
Haka na kalleta nace merry a shirye nake wajan rabuwa da duk dangina muddun su nemi hanani auranki.
Sannan na ƙara da cewa nasan kinasona fiye da yadda nake tunani me yasa bazaki iya kwatar yancinki ta hanyar juyama duk wanda ya nemi haifarma rayuwarki da ɓacin rai.
To bari kiji yanzu kin girma dan haka yanzu ne ya dace kisan hanyar da zakibi wajan ganin kin samarwa rayuwarki da tabbatacciyar rayuwa mai ƴanci saɓanin wadda ki tsinci kanki a baya.
Muddun zan iya rabuwa da dangina akanki to ke meyasa bazaki iya aikata haka a kaina ba.
Haka merry ta kalleni haɗe da cewa "wane daliline zaisa ka iya rabuwa da ahalinka a dalilina?
Kaina tsaye nace merry soyayya ba ƙarya bace domin ta samo asali ne tun farkon kafa duniya.
Kuma ai auranki bai saɓawa addininmu na musulunci ba.
Sai tayi shiru na ɗan wani lokaci daga bisani kuma sai ta kalleni sannan ta riƙe hannuna haɗe da cewa "na amince zan aureka amma dan Allah ka riƙeni amana karka bari a cutar dani.
Haka na dafa kafaɗarta fuskanta ba alamar wasa nace "nayi miki alƙawarin koda ace danginkine bazan taɓa barin su cutar min dake ba.
Koda naga hawaye a fuskarta sai nasa hannuna na share mata sannan na kalleta haɗe da cewa "karki kuskura ki sake zubar da hawaye.
Washe gari da misalin ƙarfe 11:00am mu ɗauki hanyar gida.
A haka dai har na kammala karatuna ba tare da kowa yasan merry tana a tare dani ba.
Domin bayan soyayya ta shiga tsakanina da merry Sai da na aikama Abdul da messege ɗin gargaɗi zuwa wayarshi.
=> 7
Sannu a hankali har itama merry ta kammala nata karatun wanda hakan yasa na tunkari gida tare da merry.
Da misalin ƙarfe 9 na shiga gida tare da merry ƙanwata Fareeda na gani zaune tana kallo a falo gefe ɗaya kuma anti ameenace kwance tana bacci.
Cikin yanayin murna fareeda ta taso da sauri zuwa garemu haɗe da furta kalmar oyoyo, sannu da zuwa yayana.
Haka ta rungumeni fuskarta cike da murna.
Koda ta haɗa ido da merry sai tace "wacece kuma wannan nake gani kamar merry?
Buɗar bakina dai nace kwarai kuwa itace domin ba kama kike gani ba.
Sai tace "to amma yaya baka tsoran faɗan abba da har zaka shigo tare da ita alhalin kasan abun da ya faru da kai a dalilinta?
Haka na samu wuri na zauna ba tare da yimata wani dogon zance ba.
Zamanmu kenan sai anti ameena ta farka daga bacci.
Koda tayi ido biyu da merry a tare dani, cikin yanayin izza tace "kai yaushe ka dawo, kuma wacece wannan?
Buɗar bakina sai nace "ban jima da shigowa ba, wannan kuma ba wata bace illah merry.
Wani banzan kallo naga tamin mai tattare da rainin wayo.
Sannan tace "meye alaƙarka da ita, sannan meye dalilinka na shigo da ita gidannan?
Haka nayi banza da ita ba tare da na sake furta kalmar komai a gareta ba.
Cikin yanayin ɗaga murya tace " da kaifa nake magana idan kuma baka bani amsar tambayata ba to ba shakka sai ranka ya ɓaci a gidan nan.
Koda abbana yaji ɗaga muryar anti ameena cikin gaggawa ya fito daga ɗaki domin ganin abun da ke faruwa.
Koda naga anti Aisha itama ta fito daga ɗaki sai naji tsoro ya daki zuciyata domin nasan bata da wasa ko kaɗan.
Haka dai na dake ta hanyar ɓoye duk wata fargabar da nake tattare da ita a zuciyata.
Buɗar bakin mahaifina sai yace "kai yaushe ka dawo?
Koda na kalleshi sai nace "abba saukata kenan.
Wannan kuma wacece?
Abba Merry ce.
Meye alaƙarka da ita?
Abba alaƙata da ita bazata wuce mutunci haɗe da tausayawa ba.
Meye dalilim kawota nan gidan?
Na kawota ne domin gabatar da ita a matsayin wadda nakeson ta kasance matata.
Nanfa naga tsantsar mamaki a tattare da anti Aisha haɗe da ameena.
Haka abbana ya jinjina kai sannan yace "to batun cikin da yake tattare da itafa?
Bani da wata alaƙa da cikin da ta samu domin ɗaya daga cikin abokaina ne yake da alaka dashi.
Gudun kar asirin gidansu ya tonu ne kamar yadda nima banason mutuncin gidanmu ya zube yasa na tafi tare da ita makarantar da nake karatu da ƙudurin bayan munje can zansa a zubar da cikin da take ɗauke dashi ba tare da kowa yasan abun da ya faru ba.
Tsoran kar na saɓawa mahaliccinmu ne yasa na janye ƙudurin zubar da cikin da take ɗauke dashi ta hanyar ɗaukar haƙurin zama tare da ita har zuwa lokacin da zata haifi abun da take ɗauke dashi wanda hakan zai bani damar miƙa abun da ta haifa a gidan marayu.
Sai kuma ayi rashin sa'a bayan na tafi school na barta a gida a bisa tunanin cewar bazan ɗauki wani dogon lokaci ba zan dawo gareta sai a samu akasi a a lokacin ban dawo gareta da wuri ba har yunwa ta addabeta wanda hakan yasa ta buɗe fridge ta sha lemon da yai sular zubewar cikin da take ɗauke dashi.
Bayan ta samu lafiya sai na yanke shawarar maidata wajan iyayanta.
A wannan lokacin ne ta sanar dani cewar iyayenta sun jima da barin duniya sakamakon haɗarin motar da ya rutsa dasu a hanyarsu ta dawowa gida daga Lagos, wanda hakan yasa ta roƙeni akan cewar na barta taci gaba da zama tare dani saboda tana yawan fuskantar tashin hankali a wajan waɗanda suke riƙe da ita.
Ba yadda na iya haka naci gaba da zama a tare da ita har shakuwa ta shiga tsakanina da ita wanda hakan yasa naji ya dace ta zama matata domin hakan bai saɓawa addininmu na musulunci ba.
Sannan na kalli abbana haɗe da cewa wannan shine dalilin da yasa na kawota gareku a matsayin wadda nakeson ta kasance uwar yayana.
Buɗar bakin abbana sai yace "to bari kaji ko bayan ba raina baka isa ka auri wannan yarinyar ba.
Idan kuma ka nemi bijirewa maganata to bani ba kai.
Haka na kalli abbana nace "abba banajin cewar zan iya rabuwa da merry saboda na riga na ɗaukar mata alƙawarin kasancewa a tare da ita idan har na karya wannan alƙawarin to ba shakka nayi ma addininmu na musulunci zagon ƙasa, dan haka na gwammaci rasa rayuwata a maimakon rabuwa da merry domin banajin cewar zan iya rabuwa da ita muddun ina a raye.
Buɗar bakin abbana sai yace "to zaka iya fitarmin daga gida kuma na yafeka a matsayin ɗana baka da gadona nima bani da gadonka.
Haka na kalli yayyina da kuma ƙanwata fareeda sannan na kalli abban haɗe da cewa abba zanso kayimin wata alfarma guda ɗaya ka barni na gana da mahaifiyata kafin na bar gidannan.
Buɗar bakinshi sai yace zaka iya binta can kaduna domin taje bikin ƙaninta abubakar.
Dan haka karka sa tsammanin sake dawowa gidannan da sunan ganawa da wani ko wata
Har na juya zan fita sai ya umarceni dana bashi key ɗin gidanshi haɗe da na motar da ya bani.
A daran nabar gidan mahaifina tare da merry.
Haka merry tayi iya yinta domin na rabu da ita na koma zuwa ga iyayena amma naƙi.
Tun a wannan ranar duniya ta fara juyamin baya.
Sai gashi wanda ya saba wadaƙa da kuɗi ne yake roƙon wajan kwana.
Haka nabi abokaina ɗaya bayan ɗaya domin roƙonsu wajan da zamu kwana kafin gari ya waye amma sam-sam sai suƙi amincewa dani.
A ƙarshe sai na yanke shawarar tunkarar babban makiyina wato Abdul kenan.
Da yake ɗakin Abdul a ƙofar gida yake shakuwar da take tsakanina dashi ne yasa kai na tsaye nake shiga ɗakinshi ba tare da neman izini ba.
Tabbas abun yayi matuƙar bani mamaki haɗe da takaici a yayin dana shiga ɗakin Abdul.
Domin a wannan lokacin ne nayi tozali da Abdul tare da sister A'isha suna aikata fasiƙanci.
A kunyace nayi gaggawar fitowa daga ɗakin.
Koda Abdul ya fito daga ɗakin sai ya tsinkeni da mari.
A wannan lokacin banyi wani mamakin ganin yadda abdul ya mareni ba domin murmushi ne kawai ya bayyana a fuskata ba tare dana furta kalmar komai a gareshi ba.
Haka naja hannun merry muyi gaba wanda hakan yasa na fahimci dalilin da yasa Abdul yai min ƙazafi.
A wannan lokacin ne tunanina ya bani cewar Abdul ya nemi yimin sharri ne domin buƙatar samun nasarar rabani da sister A'isha sakamakon ginin yadda soyayya take neman shiga tsakanina da ita wanda hakan zai bashi damar shiga rayuwarta domin ya ɓata rayuwarta.
A wannan ranar dai a ɗakin wani abokina ɗin da ban ɗaukeshi a bakin komai ba mu kwana a bisa yaƙinin zuwa safiya zanbar garin tare da merry.
=> 8
Taƙamar akwai wasu yan kuɗaɗe a tattare dani ne yasa na yanke shawarar barin garin gaba ɗaya tare da merry.
Ko ƙarasa wayewa garin baiyi na mu nufi tashar mota domin a wannan lokacin ko sallar asubahi ban samu nayi ba .
Da shigarmu tasha sai naji ƴan kamasho haɗe da sauran yaran mota sunata ƙoƙarin neman fasinja haka naji sunata ambato sunayan garuruwa amma banji sunan garin jos ba domin can nake da muradin zuwa koda naji wani ya ambaci garin bauchi cikin gaggawa muhau motar.
Da misalin ƙarfe 1 mu sauka a bauchi daga nan kuma sai muhau wata motar zuwa garin Jos.
Hakika ba kaɗan na haɗu da jarafta ba domin a wannan ranar dai a lojin mu kwana.
Bayan gari ya waye sai na fara fafitikar nema mana hayar ɗaki.
Haka na karɓa mana wani ɗaki na tsawon wata ukku akan kuɗi #4500.
Akwana a tashi dai mune har tsawon 4 months ba tare da mun sake waiwayar gida ba.
Haka merry ta kasance tamkar ƴar uwata ta jini wadda bana ƙaunar ganin abun da zai kasance ɓacin rai a tattare da ita.
Ba yadda za'ai merry ta kwanta bacci ba tare da taga na kwanta ba, da zaran taga bacci ya fara ɗaukata haka zatazo ta zauna kusa dani ta riƙa shafa kaina har sai taga bacci ya ɗaukeni haka zata jawo mayafi ta lullubeni domin gudun kar sanyi yai min illa sannan itama zata samu wuri ta kwanta.
Lokaci ɗaya naga kuɗin da nake tare dasu suna neman ƙarewa a yayin dana duba account ɗina sai naga saura 45 thousands.
Ganin haka ne yasa nayi gaggawar biyan kuɗin hayar dakinmu na tsawon shekara ɗaya.
In taƙaice muku dai a yayin da kuɗin da suke tare dani naga sun tafi ƙarewa sai na nemi koyama rayuwata cin abinci marar daɗi saɓanin wanda na sabaci a gidanmu.
Ranar dana sake duba kuɗin da nake tattare dasu a account ɗin a sai naga saura 5760.
Bansan lokacin dana fara zubar da hawaye ba domin nasan wahalace take shirin tunkaroni.
Bayan gari ya waye sai na fahimci cewar abar ƙaunata tana buƙatar abun da zataci.
Koda na kalleta sai nace "my sister kijirani yanzu zanje domin kawo miki abun da zakici.
Haka tayi murmushi sanan ta amsamin da to.
Da zuwana shagon wani inyamuri sai na sayi garin kwaki gwangwani ɗaya haɗe da sugar ta 100 sannan na buƙaci ya bani abun da zanjiƙa domin nasha.
Haka nasha garin ni kaɗai ba tare da na ƙoshi ba sannan na wuce wajan mai shayi.
Haka nasa a haɗamin shayi da biredi haɗe da soyayyan kwai guda biyu.
Bayan an gama haɗamin sai na tasarma inda merry take.
Da zuwana sai na kalleta fuskata cike da annuri nace " my dear, kiyi haƙuri nabarki cikin kaɗaici ko.
Murmushi tayi sannan tace "ai koda baka kusa dani to zukatanmu suna tare da juna.
Bayan na miƙa mata abun dana taho mata dashi.
Tana buɗewa sai naga ta kalleni ranta a ɓace.
Nan take naga tayi jifa da abincin dana siyo mata waje wanda hakan yai sular hassalani.
Cikin gaggawa na zare belt ɗin dake wandona da ƙudurin yi mata shegen duka.
Can naji zuciyata tace "kaikon me zaijama dukan wadda kakeso kuma kodama ba budurwarka bace yana da kyau kai mata uziri a matsayinta na wadda ba musulma ba.
Haka na durƙusa a gabanta nace "merry sonki ɗin da nakeyi bazai bari naga za'a cutarmin dake ba balle ni da kaina na nemi cutar dake, amma wannan abincin daki watsarmin ji nakeyi tamkar abincin dana saba ci a wajan mahaifiyata ki watsar.
Haka ta riƙe hannuna tana mai zubar da hawaye tace "me yasa kake ƙoƙarin banbanta matsayinka da nawa, taya zakaje kasha gari sannan ni kuma ka kawomin abinci mai rai da lafiya?
Sannan ta ƙara da cewa a lokacin da nayi ido biyu da kai kana shan wannan garin ba tare da ka ganni ba ji nayi tamkar na kashe kai na domin ka huta da irin wahalar da kakesha a dalilina.
Babban abu takaicina shine kawo wannan abincin da kayi a gareni saɓanin abun da kai kaci.
Koda naji wannan batun daga bakin merry nan take na riƙe hannunta inamai zubar da hawaye.
Buɗar bakinta sai tace "kayimin komai a rayuwata, riƙon alƙawarika haɗe da tausayawarka da kuma imaninka ne yasa na yadda da cewar addinin musulunci gaskiya ne dan haka ina mai tabbatarma cewar a yau zan musulunta.
=> 9
Cikin yanayin mamaki na shafa fuskarta sannan na dafa kafaɗarta haɗe da cewa "anya ke dince kuwa sannan abun da kunnuwana suji kin furta da gaske ne har cikin zuciyarki?
Kwantawa tayi a jikina tana mai cewa bani da abun da zan iya biyanka dashi fiye da shiga musulunci saboda banason rabuwa da kai.
A wannan lokacin ne naji ko kaɗan banason ganin abun da zai kawo ƙarshen zamana da merry wanda hakan yasa naƙi tunkarar al'umma domin su ba ta kalmar shahada.
A wannan ranar na koyar da merry yadda zatayi wankan tsarki. Daga bisani kuma na koyar da ita yadda ake alwallah haka mu zauna a tsakar ɗakin da muke kwana gani gata a yayin da muke kallon juna.
Buɗar bakina sai nace "merry yanzu ne zaki shiga musulunci ta hanyar karbar kalmar shahada haɗe da karbar duk abun da addinin musulunci ya umarcemu damu aikata ko karmu aikata.
Kalmar Shahada ita ce "La'ilaha illal-laah" (Ma’ana Babu abin bauta da gaskiya sai Allah) "wa anna Muhammadar Rasulullah" (kuma Annabi Muhammad (S.A.W.) Manzon Allah ne), ga wanda ya faɗi wannan kalma kuma yai imani da ita to ya Musulunta (ma’ana ya miƙa wuya izuwa ga addinin Allah wato (Musulunci). Bayan ta furta kalmar shahada kamar yadda na koyar da ita sai nace "Amma faɗin wannan kalma da baki baya isarwa mutum, har sai ya cika sharuɗɗanta kamar haka
1) ILIMI:-
Ma’ana dole ki nemi ilimin sanin haƙiƙanin ma’anar Kalmar, kamar yadda Allah(S.W.T.) Ya faɗi a cikin Al-Qur’ani Maigirma.
Sannan ba yadda za'ai mutum ya yiwa Allah wata bauta face yana da ilimin sanin yadda ake yinta, haka mutum Musulmi ba zai yi magan aa game da Allah ko abin da ya shafi Addininsa ba face mutum yana da sanin abun a ilmance.
2) YAQINI:-
Ma’ana yarda da kuma barin kwokwanto a game da lamarin Allah da kuma addininsa haɗe da jingina lamari zuwa gareshi ba tare da jin wani ɗar-ɗar a zuciya ba.
3) QABUL:-
Ma’ana amsar ko karɓar duk wani abun da Allah Yace ayi ko yace a bari gaba ɗaya, ba tare da mutum yasa son zuciya a game da addinin Ubangiji ba.
4) AL-INQIYAD:-
Ma’ana miƙa wuya, idan ace miƙa wuya shine ki bada kanki gaba ɗaya ga Allah, duk abin da Allah Yace ko Manzonsa (S.A.W.) Yace to bake ba jayayya dole ki yarda kibi,koda kina aikata wani abu idan ace Allah ya hana, to dole ki hanu ki miƙa wuya, ki gujewa son zuciya.
5) AL-SIDQ:-
Ma’ana gaskatawa, kishiyar munafurci ko ƙaryatawa, ya zama wajibi dukkanin wani musulmi ya gujewa munafinci a tsakaninsa da addinin Allah.
6) IKLASI:-
Ma’ana yi ko aikata wani aiki domin Allah, yana da kyau Musulmi ya kasance mai bin dukkanin wani abun da ya shafi addinin Allah, kuma ya yi shi da zuciya ɗaya, haɗe da Iklasi (ma’ana yi dan Allah) ba tare da ya sanyawa zuciyarsa kishiyar hakan ba,
ya guji Riya (yi don mutane) ko neman yabo da sauransu.
7) MUHABBAH:-
Ma’ana soyayya, dole mutumin da ya aminta da Kalmar shahada ya so Allah sama da komai, sannan duk abin da mutum zai so ya so wannan abun domin Allah, haka in zai ƙi shi to ya ƙishi dan Allah.
Manzon Allah (S.A.W.) Yace: Duk wanda yake son ya samu ɗandɗanon Imani to yaso mutum ba don komai ba sai dan Allah.
8) KAFURCEWA ƊAGUTI:-
Ma’ana ƙin duk wata bauta bayan bautar Allah, dole mutum Musulmi ya gujewa duk wani abun da zai zamto kishiyar Allah.
Misali: Annabawa, Mala’iku, Gumaka, Shehunnai, Waliyai, Shaiɗanu da suransu, da dukkanin wata halitta dole ne mutun musulmi ya gujewa bauta a garesu.
9) IMANI DA KUMA KAUNAR MANZON ALLAH (S.A.W.)
Dole ne duk wanda ya yarda da Kalmar Shahada yayi imani da Manzon Allah (S.A.W.), Ya gaskatashi, ya kuma so shi fiye da kowa da komai a rayuwarsa, ya bi koyarwarsa, ya hanu da haninsa.
Duk wanda ya ji baya son Annabi (S.A.W.) ba shida imani, kuma dole son ya kasance fiye da son komai a rayuwar mutum.
10) TABBATA:-
Dole mutum musulmi yayi riƙo da Kalmar Shahada da dukkan sharuɗanta har zuwa lokacin da zai koma ga Allah, wanda yayi haka shi ne ya rabauta.
Haka na ɗauki alƙawarin koyar da merry duk wani abun da ya dace ta koya a game da addinin musulunci dai-dai da abun dana sani.
A ƙarshe kuma na kalleta nace "wane suna kike buƙatar ya kasance sunanki domin yana da kyau ki chanza suna daga merry zuwa wani sunan irin namu na musulunci.
Haka ta kalleni sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa haɗe da cewa "MARYAM nake buƙata ya kasance sunana.
Tun daga wannan ranar ta tashi daga merry zuwa maryam.
Ganin ta musulunta ne yasa na ƙuduri niyar komawa zuwa ga mahaifina saboda ni a nawa tunanin ya guji kasancewata a tare da ita ne saboda ita ba musulma bace.
Ta bakin masu iya magana, Ashe akwai sauran rina a kaba.
Cikin yanayin taƙama hade da cire duk wata fargabar dake zuciyata nayi bankwana da garin jos ta hanyar komawa gida tare da abar ƙaunata.
Da misalin ƙarfe 4:00pm mu shiga jahar kano ba wanda hakan yasa ba inda naci burki sai a harabar gidanmu.
Da shigata gida sai mahaifina yasa mai gadi yai ram dani.
Haka abbana yazo gaba ranshi a ɓace yace "me yasa kakeson tozartani a idon duniya?
Tun daga ranar da kazo da wannan yarinyar gidannan da sunan wadda zaka aura iyayenta susamu tabbacin cewar kaine ka gudu da ita.
Kuma cikin da take ɗauke dashi kai ne kayi matashi haka ne yasa iyayanta sukai ƙarata kotu.
A halin da ake ciki yanzu saura kwana ukku daga cikin kwanakin da kotu ta bani akan cewar duk inda kake na nemoka domin damƙaka a hannun jami'an tsaro.
Haka mahaifina ya kalleni fuskarshi cike da hawaye ya kirani da fasiki wanda hakan yasa aduk lokacin da na tuna da wannan kalmar ba kaɗan nake zubar da hawaye ba.
Inaji ina gani haka mahaifina ya kira jami'an ƴan sanda domin su tafi dani.
Koda naga ana ƙoƙarin damƙa Maryam a hannun danginta cikin yanayin ɗaga murya nace "abba tafa musulunta.
Ban saniba ashe wannan furucin da dangin maryam suji nayi ba kaɗan zai jefa maryam a babban haɗari ba.
Haka mahaifina ya tsinkeni da mari haɗe da cewa "ni zakayima wannan wasan kwaikwayon.
To bari kaji duk wani rainin hankalinka na gama saninshi.
Haka kotu ta yankemin hukuncin ɗaurin watanni huɗu haɗe da aiki mai tsanani ba tare da an ɗauki maganata da muhimmanci ba.
Ni nasan maryam bazata taɓa samun kwanciyar hankali a dalilin rabamu na tsawon wannan lokacin Sa'a ɗibarmin ba.
To amma abun dana sani shine duk sanda Allah yai fitowata to ba makawa sai na ɗauke maryam na tsawon har abada ba tare da dangina ko nata dangin sun sake jin ɗuriyarmu ba.
Ban saniba ashe wannan shine ƙarshen rabuwata da maryam.
Bayan adadin watannin da'a ɗibarmin sun ƙare, sai a sallameni.
Burin kowa ne mazaunin gidan yari idan ya samu nasarar fita bazai wuce ya fara ganawa da ahalinsa ba.
Ni kuma burina a wannan lokacin bai wuce ganin na haɗu da maryam.
A ranar da za'a sallameni daga tsarewar da amin haka masu kulawa damu a gidan yarin su damƙamin kayan sawata haɗa da wallet ɗina sai kuma ATM ɗina haɗe da wayata.
Cikin gaggawa na karɓi wayar haɗe da ƙoƙarin kunnata ban sani ba ashe tuni batirin wayar ya ɗauke wuta sakamakon daɗewar da yayi ba tare da an chazashi ba.
Bayan na fita daga gidan yarin sai na miƙa wayar a wajan wani mai chaji.
Haka na zauna a wajan mai chajin har tsawon 30 minutes ba tare da naje ko inaba.
Koda na fahimci cewar batir ɗin ya ɗan samu chaji sai na kunna wayar.
Bayan na kunna wayar da message ɗin maryam na fara tozali wanda hakan yasa na fara duba kwanan watan data aiko da messege ɗin.
A kwanan watan da na duba ne yasa na gane cewar maryam ta aiko da saƙon ne tun bayan kwana ukku da zuwana gidan yarin da ake tsare dani.
Amma sai dai kuma message ɗin ba kaɗan ya dugunzuma zuciyata ba domin a sauƙin nata cewa tayi;
__Yayana kayimin halacci mafi girma a rayuwata amma sai gashi zanbar duniya ba tare da na cikama burinka na aurena ba, saboda al'adar iyayena itace duk wanda ya fita daga addininmu ta hanyar shiga wani addinin to ba makawa kasheshi za'ayi ta hanyar bada jininshi ga dodon da akema tsafi.
Babban farin cikina shine zan mutu a matsayin musulma dan haka zan kasance mai alfahari da kai tun anan duniya har izuwa lahira.
Sannan kuma inayima fatan alkairi haɗe da fatan samun masoyiya ta gari amma ina mai shawartarka da akan cewar ko ka tashi aure to karka taɓa wuce ƙawata wato sister A'isha domin tanasonka tsakani da Allah.
Koda naji wannan batun nan take naji jiri yana neman ɗaukata.
Lokaci ɗaya naga bana iya banbance abun dake gabana.
Buɗe idon da zanyi sai na tsinci kaina kwance a gadan asibiti.
A wannan lokacin ba abun da yake fitowa daga bakina face sunan maryam.
Bayan wani ɗan lokaci sannan hankalina ya fara dawowa jikina sai na fara tunanin dalilin da yasa maryam take son na juya soyayyata zuwaga sister A'isha.
=> 10
Haka dai na rungumi ƙaddarar rabuwa da maryam badan inaso ba.
Nine har tsawon sati biyu gaba ɗaya na rasa abun dake min daɗi domin ko abinci ma inaci ne badan zuciyata tanaso ba.
Tun daga wannan ranar na maida hankalina ga mahaliccinmu ta hanyar daina yawan banza.
Bana zuwa ko ina muddun kaga na fita to masallaci zani.
Sai ya zamto nine koda yaushe cikin roƙawa maryam samun hasken kabari daga mahaliccinmu.
Fitowata daga masallaci kenan bayan an idar da sallar magriba a yayin da nake kan hanyata ta komawa gida sai nayi kacibus da sister A'isha.
Koda na haɗa ido da ita sai nayi ƙasa da kaina domin ko kaɗan banason abun da zai haɗani da ita balle har muyi wata magana.
Ganin yadda naƙi maida hankalina a gareta ne yasa ta tareni ta hanyar shiga gabana.
A yayin da nake ƙoƙarin kauce mata kawai sai ji nayi ta riƙe hannuna.
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai na kalleta haɗe da cewa "meye kuma na riƙemin hannu, a matsayinki na mace bakisan Allah yai hani da hakanba?
Cikin yanayin mamaki tace " ikon Allah yayana yaushe kuma ka musulunta, yanzu har ka manta da lokacin da kake taɓa jikina ba tare da tuna Allah ba?
Haka na kalleta tun daga sama har ƙasa nace "to ai a wancan lokacin na aikata haka ne a lokacin da son zuciyata yafi ƙarfin tunani a, amma yanzu Allah yasa na gane abun da na aikata a baya ba komai bane face shirmen iska.
Kuma karki manta da cewar ba wasu bane suyi sular ɗorani a wannan hanyar face ke da sauran abokan tafiyar tawa.
Dan haka ina mai shawartarki da kiyi gaggawar komawa izuwa ga hanyar da ta dace ta hanyar daina wannan shashancin da kikeyi a tare dasu abdul.
Koda ta kalleii sai tace "wane shashanci kuma muke aikatawa?
Jin wannan tambayar da tayi a gareni ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "au ke yanzu kina nufin bake na gani tare da Abdul a ɗakinshi kuna aikata fasiƙanci ba?
Cikin yanayin mamaki ta riƙe baki haɗe da cewa "innalillahi-wa'inna-ilaihi-raji'un" yayana ashe dama kaima kaga wannan lokacin?
Sai nayi tsaki sannan na juya da ƙudirin tafiya.
Nan take ta dakatar dani ta hanyar cewa "kayiwa Allah da manzonsa katsaya ka saurareni.
Koda naji tayi wannan furucin ba yadda na iya haka na juyo gareta.
Haka ta kalleni sannan tace " tunda Allah yasa ka tafi makaranta kafin wannan al'amarin ya faru da kai sai Abdul ya fara nuna alamun soyayya a gareni.
Ni kuma a wannan lokacin ba shine a gabana ba domin a wannan lokacin ba wanda nakejin zan iya damƙawa ragamar mulkin zuciyata face kai.
Koda naga alamun Abdul yana neman takuramin sai na fito fili na sanar dashi cewar "kaga Abdul nifa ba wanda nakeso illa babban yaya.
A wannan likacin dariya kawai naga yayi sannan ya juya ya tafi ya barni.
Ganin haka ne yasa na fashimci cewar akwai wani abun da yakeson ƙullawa a zuciyarshi.
Bayan kwana biyu da faruwar haka sai na samu labarin cewar kayima merry ciki.
Sannan na samu labarin cewar tsoran kar kowa ya sani ne yasa ka tafi tare da ita makaranta.
A wannan lokacin ne naji na tsani son kasancewata a tare da kai wanda hakan yasa na kiraka a waya na faɗama maganar da bata dace ba.
Sannan na yanke shawarar karɗar soyayyar babban maƙiyinmu wato Abdul kenan.
A yayin da soyayyarmu ta fara nisa, sai Abdul ya fashimci cewar idan har ya nemi kwantawa dani ta hanyar tunkarata face to face ba yadda za'ai na amince kawai sai ya sanar dani cewar bashi da lafiya ta hanyar aikomin da sakon text messege a waya wanda hakan yasa naje gareshi cikin gaggawa.
Bayan naje gareshi sai abun ya bani mamaki domin a wannan lokacin ganinshi nayi zaune a ɗakin nashi yana cin abinci.
Koda naga alamun ba wata rashin lafiya a tattare dashi sai nace "haba Abdul harfa kasa na tsorata meyasa kakeson razana zuciyata ta hanyar yimin ƙaryar baka da lafiya?
Sai yace "toke inbanda abunki ina lafiya ga zuciyar da batayi ido biyu da abar ƙaunarta ba.
Sannan ya ƙara da cewa kawai na kiraki ne domin kizo muci abinci tare.
Saka makon a wannnan lokacin banajin marmarin komai ne yasa na nemi turjewa ta hanyar ƙin cin abincin.
Koda naga ranshi yana neman ɓaci ba yadda na iya haka na zauna muci abincin tare.
Haka na riƙa cin abincina haɗe da shan drink ɗin da Abdul ya aje a kusa dani.
Ban sani ba ashe akwai kwayar bacci a drink ɗin da nakesha wanda hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci na rasa inda nake domin bacci ne ya ɗaukeni.
A wannan lokacin bani na farka ba sai misalin ƙarfe 4 na dare.
Ganin yadda na tsinci kaina a wani mummunan yanayi ne yasa na kalli Abdul fuskata cike da hawaye.
Haka na nunashi da yatsana haɗe da yimai Allah ya isa sannan na roƙi mahaliccinmu da buƙatar ya fara yimai azaba mai tsanani tun a nan duniya.
Kawai sai naga yayi dariya sannan yace "an faɗa miki cewar ni na wasa ne ai tun dama can wannan ƙudurin nakeson cikawa shine dalilin da yasa nayima wanda kikeso sharri badan komai ba sai dan buƙatar ki dawo da soyayyar da kike nuna mai a garenk.
Cikin yanayin takaici na kalleshi nace " kana nufin sharri kayimai kenan?
Nan take ya bani amsa ta hanyar cewa kwarai kuwa.
Sannan kuma cikin da ake zargin yayiwa merry to ba kowa ne ya mata ba illa ni.
Kuma ya tafi da ita makaranta ne domin buƙatar ya rufamin asiri, sai kuma ayi rashin sa'a ni kuma bansan menene mutunci ba balle ayi batun halacci.
Sai sister A'isha tace "tun daga wannan lokacin na fashimci cewar Abdul ba komai bane face dabba a cikin al'umma, a wannan daran na fita daga ɗakin abdun na tasarma gida.
Da zuwana ƙofar gida sai nayi kira mai gadin gidan namu a waya domin ya buɗemin ƙofa.
Bayan mai gadin ya buɗe ƙofar sai nayimai worning akan cewar karya kuskura mahaifina ko mahaifiyata susan cewar sai cikin dare na dawo gida.
Bayan sister A'isha ta gama bani wannan labarin sai ta kalleni haɗe da cewa "tabbas kayiwa merry halacci, kuma ka cika mutun nagari.
A yayin da na kalleta sai nace "bani nayiwa merry halacci ba itace tamin halacci tunda har ta miƙa wuyanta izuwa ga addinin musulunci kuma tayi sa'a tunda har ta bar duniya a matsayin musulma.
Cikin yanayin sanyin jiki mai tattare da mamaki sister A'isha tace "kana nufin merry ta musulunta.
Sai nace "kwarai kuwa domin ni na musuluntar da ita wanda hakan ya bani damar canza mata suna daga merry zuwa Maryam.
Sai Aisha tace "to amma naji kamar a bayaninka kace tabar duniya?
Nan take na nuna mata text ɗin da ta turo zuwa wayata.
Hakika ba kaɗan sister A'isha ta nuna baƙin cikin abun da ya faru da maryam ba.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "shin kanajin cewar zaka iya amincewa da shawarar da ta baka a game da batun soyayya dani kuwa?
Jin haka ne yasa nayi murmushi sannan nace "me zai hana ai bazan taɓa gujema shawararta ba.
Tun daga wannan ranar mu fara kallon junanmu a matsayin masoya.
Sai dai kuma duk da cewar A'isha tana matuƙar nunamin tsantsar soyayya hakan baisa na manta da soyayyar da ke wakana a tsakanina da maryam ba wanda hakan yasa a duk lokacin dana tuna da maryam sai naji kirjina yayi wata irin bugawa wanda hakan yake sawa nake ji a raina cewar akwai sauran wani abun da yake shirin sake faruwa dani....
=> 11
Kwatsam wata rana ina zaune a falon gidanmu domin a wannan ranar bani da aikin komai sai tunanin maryam ya faɗo a zuciyata.
Yanayin bugawar da naji ƙirjina yayi ne yasa nayi gaggawar dafe ƙirjin nawa.
Haka na kwanta akan kujera domin a wannan lokacin jinayi duk ilashirin jikina ya mutu.
Inaji ina gani wayata tana ringing!! Amma na kasa yunkurawa domin amsa kiran saboda ba'a kusa da wayar nake ba.
Koda naga anti Aisha ta fito daga ɗaki a yayin da ta take shirin fita, cikin yanayin sanyin murya nace "dan Allah anyi ɗan miƙomin wayata a ɗaki.
Jin haka ne yasa ta kalleni haɗe da cewa "baka da lafiyane?
Gudun karta gano abun da yake damuna ne yasa nayi mata ƙarya ta hanyar cewa "zazzabi ne yake neman kamani.
Bayan ta bani wayar har ta juya zata shiga ɗakinta domin ɗakkomin magani sai kira ya sake shigowa wayar tawa.
Da yake baƙuwar number na gani nan take nayi gaggawar amsa kiran.
Koda na kara wayar a kunnena sai naji muryar Maryam a yayin da tayi sallama.
Ko amsa sallamar banyi ba cikin yanayin kuɓutar baki nace "merry au Maryam ashe dama kina raye?
Cikin yanayin damuwa tace "yayana ina raye ban mutuba kuma a yanzu haka ina cikin wani mawuyacin hali domin banagida...
Ban tashi aune ba sai ji nayu anti Aisha ta fusge wayar ba tare da naji inda maryam take ba.
Nan take na durƙusa har ƙasa haɗe da riƙon anyi A'isha domin ta taimaka ta bani wayar amma sai taƙi bani wayar.
Koda naga tana neman buɗe wayar domin cire Sim card ɗin dake wayar.
Nan take na miƙe tsaye naci kwalarta haɗe da cewa "ba abun da bazan iya aikatawa ba a game da gaskiyata a.
A dalilin haka ne mu fara kokawa a ƙarshe sai ta samu nasarar bugani da ƙasa.
Inaji ina gani ta jefa wayar haɗe da Sim card ɗin a toilet.
A yayin da ta sanar da mahaifinmu abun da ya faru.
Sai mahaifin namu ya kalleni fuskarshi cike da ɓacin rai yace "wallahi kafi ƙarfina ba abun da zance a gareka face Allah ya shiryamin kai.
Tun daga wannan ranar naji bani da wani babban makiyin da ya wuce yayata A'isha.
Haka na riƙa ji a raina cewar hikenan Maryam ta rasa numbata kamar yadda nima na rasa tata numbar.
A wannan ranar nayi ƙoƙarin sawa amin (welcome back).
Bayan na bayar da duk wani abun da ya dace a game da Welcome back ɗin sai a sanar dani cewar sai zuwa sati mai zuwa sannan komai zai kammala.
A yayin da naji wannan furucin daga bakin mai Welcome Back ɗin sai naji tamkar welcome back ɗin bashi da wani amfani a gareni domin a wannan lokacin so nake na haɗu da maryam cikin gaggawa.
A wannan ranar dai haka na kwana cikin tunanin yadda zan samu haɗuwa da maryam.
Gari yana wayewa ko breakfast ban samu nayi ba haka na kammala duk wani shirina domin barin barin gida.
Koda mahaifiyata taga sai gaggawa nakeyi sai tace "wai ina zaka ne naga sai gaggawa kake?
Cikin girmamawa nace "umma maryam itace farin cikina itace kwanciyar hankalina dan haka ba yadda za'ayi na barta a cikin tashin hankali.
Koda mahaifina yaji haka sai yace "wai wacece maryam ɗin nan?
Nan take nace "abba ba wata bace maryam illa merry wadda ta canza sunanta a lokacin da ta karɓi musulunci.
Haka mahaifina ya miƙi tsaye haɗe da cewa "duk da cewar ta musulunta to ba yadda za'ai na bari ka auri abokiyar fasiƙancinka.
Na buɗa baki zanyi magana sai ya daka min tsawa haɗe da cewa "bana buƙatar jin komai daga bakina.
Haka nasa hannu na ɗauki jakata haɗe da cewa "banajin cewar akwai dalilin da zai hanani auran maryam sannan nayi waje.
A yayin da nake cikin tafiya a gefen titi domin tunkarar inda zan hau mota sai a samu akasi wata mota tayi packing a kusa dani.
Haka direban dake tuƙa motar ya fito waje.
Da fitowarshi bayan mun gaisa sai yace tafiya zakayi ne?
Cikin yanayin sakin fuska nace eh amma tafiyar tawa ba wata mai nisa nace domin a Suleja nakeson zuwa.
Jin haka ne yasa yai murmushi haɗe da cewa "ai muma akan hanya muke domin Abuja zamu shiga, nan take ya buɗemin mota na shiga.
Shigata motar kenan sai naji ƙirjina yayi bugawar da nima kaina na kasa gane dalilin faruwar hakan.
Ban sani ba ashe motar ƴa kidnafin nahau ban tashi tsintar kai na a ko inaba sai a wani katafaren gida wanda ni kai na bansan ko a wace jaha yake ba.
A haka na kwashi tsawon kwanaki a wannan gidan ba tare da sun zartar da mummunan ƙudirinsu a garemu ba.
A gaban idona sun halaka mutanan da bansan adadinsu ba.
A wannan lokacin ba abun da nakeyi face addu'a.
A ranar dasu sanar dani cewar zuwa gobe zan bar duniya ta hanyar yankani kamar yadda naga sun raba sauran mutanen dasu kawo gidan da duniya.
Sai ɗaya daga cikin masu gadin gidan yazo gareni.
Haka ya tambayeni cewar amma kai mutumin kano ne ko?
Cikin yanayin damuwa na bashi amsa ta hanyar cewa eh!
Nan take naga ya jinjina kai sannan yai shiru na ɗan wani lokaci.
Koda ya ɗago kai ya kalleni sai yace "tabbas mutanan kano sunyi min halacci ba ɗan kaɗanba.
Dan haka jin daɗin haka ne zaisa na ceci rayuwarka domin nasan ba makawa zuwa gobe zasu rabaka da duniya, gashi yau watanka ɗaya da kwana huɗu dan haka zuwa anjima idan dare yayi zan buɗeka.
A kwai wata katanga a nan baya zan taimakeka wajan haurawa domin ceton rayuwarka.
A wannan daran na kuɓuta daga sharrinsu ta hanyar taimakon wannan mai gadin.
Yanayin tsarin garin ne yasa na fahinci cewar a cikin garin Abuja nake.
Gashi ba waya a hannuna balle ayi batun kuɗi domin ATM ɗina haɗe da wallet ɗina duk suna hannunsu.
Ganin haka ne yasa na yanke shawarar neman taimakon aron waya domin kiran sister A'isha badan komai ba sai dan buƙa tare ta turomin da ƴan kuɗin da zasu kaini Bayelsa saboda inaji a jikina cewar maryam tana bayelsa saboda ta taɓa sanar dani cewar tana da ƴan uwa a bayelsa.
Haka dai na ƙarasa wajan wani mai shayi da zuwana bayan mungaisa sai na sanar dashi duk abun da ya faru dani sannan na nemi ya bani aron wayarshi domin na kira gida.
Bayan ya bani aran wayar nan take nayi calling ɗin sister A'isha.
A yayin da sister aisha taji muryata cikin yanayin mamaki tace "yayana ina kuma kashiga tsawon kwanakin nan ka barmu cikin damuwa ni da maryam.
Cikin yanayin mamaki nace A'isha kardai kice Maryam tana tare dake?
Sai tace "gata kuyi magana.
A yayin da naji muryar maryam ta sauka a kunnena saboda murna sai na rasa abun da zance.
Kawai sai naji tace "yayana amma dai kana cikin ƙoshin lafiya ko?
Sai nace "haba kedai bari kawai domin ba karamar jarabtace ta sameni ba amma idan nazo zakiji bayanin komai daga bakina.
Bayan A'isha ta turo min da kuɗi motar da zasu maidani gida ta account ɗin mai shayin sai jin daɗin hakan yasa naba mai shayin kyautar dubu 2 a cikin kuɗin da ta turomin.
Bayan na koma gida ba inda na tsaya sai a ƙofar gidan su sister A'isha.
Bayan na samu haɗuwa dasu a yayin da mu gaisa sai na kalli Maryam cikin yanayin farin ciki nace "maryam....
Sai tace "dakata nasan dukkanmu munsha wahala amma duk da haka dai kai ne jarimi a cikinmu domin na tabbata wahalar dakasha ko kwatarta bansha ba domin waje ɗaya ne zan iyacewa nasha wahala mai matuƙar ƙuna saboda a lokacin da ƙanin mahaifiyata ya ɗaukeni daga wannan jahar ta zuwa jahar mukodi a wannan ranar ne na ƙara tabbatar da cewar addinin musulunci yana da matuƙar sauƙi domin ko kaɗan ban ɗauka kasheni za'suyi ba.
A wani ɗaki su hankaɗani sannan su garkamini da wani kwado haɗe da yimin bayanin cewar tunda na shiga musulunci to dodon da sukema tsafi zasu ba jinina.
Haka su riƙa azaftar dani da yunwa a wannan lokacin haka nayi ta ƙoƙarin kiran wayarka amma bata shiga ganin chajin da yake wayar ya kusan ƙarwa ne yasa na yanke shawarar turoma da saƙon halin da nake ciki badan komai ba sai dan karka wahalar da zuciyarka wajan tunanin sake haɗuwa dani.
Kwatsam cikin dare sai Allah ya taimakeni wasu ɓarayi ko kuma ince ƴan fashi su shigo gidan.
Bayan sun kwantar da mutanan dake gidan gaba ɗaya haɗe da dukansu sai wasu su shiga ɗakunan dake gidan domin neman abun da ya kawosu.
Koda suga ɗakin da nake ciki a kulle da kwado sai su umarcesu dasu buɗe ɗakin domin su bincika.
A yayin da a buɗe ɗakin sai ɗaya daga cikinsu ya shiga koda ya haska tocilar dake hannunshi sai yai ido biyu dani.
A wani mawuyacin hali cikin ƙarfin hali na buɗe bakina haɗe da cewa "dan Allah ku taimaka ku fitar dani daga gidannan domin kasheni zasuyi.
Bayan ya fito dani daga ɗakin sai babban cikinsu ya kalleni haɗe da cewa "meki aikata da zasu kasheki?
Sai nace "saboda nabar addinin d nake ciki ta hanyar shiga addinin musulunci.
Nan take yace tashi ki fita ki tafi duk inda kiga dama.
Har naje bakin ƙofa sai babban nasu yace dakata domin yana da kyau kiga irin hukuncin da ya dace a zartar masu.
A gaban idona ƴan fashin su kashesu ta hanyar harbinsu da bindiga.
A wannan daran nabar gidan ina cikin tafiya banmasan inda nake dosa ba kawai sai na taka wata kwalba a ƙafata.
Zafin da naji ne yasa na kwalla ƙara wanda hakan yasa wani bawan Allah ya fito domin ganin abun da yake faruwa.
=> 12
A yayin da mutumin ya tsinceni a wannan mawuyacin halin sai ya ɗaukeni zuwa wani asibitin da yake a unguwar abun ya faru dani.
Sai da na ɗauki tsawon wata ɗaya a gidan mutumin.
Kasancewar shima musulmi ne yasa na bashi labarin yadda rayuwata ta kasance.
Buƙatar cigaba da kasancewa a tare da kai ne yasa na yanke shawarar dawowa kano sai kuma ayi rashin sa'a a ranar dana dawo na samu labarin kaima a wannan ranar kabar garin kano domin neman inda nake.
Jin haka ne yasa gaba ɗaya na rasa inda zan tunkara domin neman masauki sister A'isha ce kaɗai ta bani masauki a matsayina na yar uwarta mace kuma musulma.
Bayan ta gama bani wannan labarin sai ta kalleni idanunta cike da hawaye haɗe da cewa "kayimin halacci a rayuwata, sai dai kuma bansan wanda zai ɗaura aurena da kai ba.
Kuma gashi sister A'isha ma tana matuƙar sonka.
Haka nasa hannu na share hawayen dake fuskarta haɗe da cewa "kar kuji komai muddun zaku zauna lafiya a yayin daku zama matana to ba abun da zai hanani aurenku.
Bayan na basu labarin halin da na tsunci kai na a yayin dana tafi neman maryam.
Sai sister A'isha tace "to amma yanzu baka gudun samun matsala a yayin da abbanka ya ganka tare da maryam?
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "haba A'isha ai komai yazo ƙarshe.
Nan take na umarci sister A'isha da ta wuce gida.
Haka ta wuce ba tare da tambayata dalilin hakan ba.
Ni kuma a wannan lokacin na tunkari gidan su abokina Abdul.
A wannan lokacin sai da maryam tayi mamakin ganin yadda na tunkari gidansu Abdul tare da ita wanda hakan yasa tun a hanya take tambayata ina zamu.
Haka nayi shiru ba tare dana bata amsar tambayar da tayi a gareni ba har mu isa ƙofar gidan su Abdul.
A yayin da na tura ƙofar gidan nasu da ƙudirin shiga gidan sai nayi kaciɓus da Abdul a yayin da zai fito daga gidan.
Haka abdul ya kalleni haɗe da cewa "me kuma ya kawoku wajena?
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "ba wajanka muzoba domin nazo wajan mahaifinka ne.
Cikin yanayin sanyin jiki yace "dan Allah abokina kar kuyimin haka wallahi nasan bankyautamaba.
Fuskata cike da mamaki nace "haba Abdul nifa nazo wajan mahaifinka ne domin buƙatar kawo gyara a tsakanina da mahaifina saboda idan ba haka ba ina tunanin ba yadda za'ai na samu damar auran maryam.
Koda yaji haka sai yace "wacece kuma maryam?
Sai nace "ba wata bace illa merry domin tuni ta musulunta.
A yayin da muke cikin wannan maganar sai Allah yai fitowar mahaifin nashi.
Ba yadda Abdul ya iya haka ya barmu mu ƙarasa zuwa ga mahaifin nashi.
Bayan mungaisa sai nace "haƙiƙa kai babban malamine a wannan garin namu domin haka ne yasa nake ɗaukarka tamkar mahaifina domin ina ɗaukarka da muhimmanci wanda hakan yasa bazan iya barin mutuncinka ya samu nakasu a gaban idona ba.
Sai gashi kuma na samu saɓani da mahaifina haɗe da shiga matsanan ciyar wahala a dalilin ƙoƙarin kare mutuncinka ɗin da ɗanka ko kuma ince abokina Abdul yai ƙoƙarin zubarwa.
A gaban Abdul haɗe da maryam na fara yiwa mahaifin Abdul bayanin komai tun daga lokacin da merry ko kuma ince maryam ta kirani a waya domin neman taimako alokacin da take ɗauke da cikin da Abdul yai mata har izuwa lokacin da sister A'isha ta taimaketa ta hanyar ba ta masauki.
Amma ban bayar da labarin abun da ya far a tsakaninshi da sister A'isha ba domin shima labarin abun da ya faru a tsakaninsu da maryam na bayar da shi ne domin buƙatar kawo gyara a tsakanina da mahaifina.
A nan take mahaifin Abdul ya kalli Abdul haɗe da cewa "amma kaikon Allah......
Cikin gaggawa nace "a'a abba idan ka la'anceshi baka kyauta ba kawai addu'a ya kamata kariƙa yimai.
Sai mahaifin Abdul ya fashe da kuka yana mai yimin godiya haɗe da roƙona kan cewar karna bari kowa yasan da wannan sirrin.
A wannan ranar mahaifin Abdul ya samu mahaifina har gida yamai bayanin komai a ƙarshe kuma yace idan ka nemi gudun wannan ɗan naka ina mai tabbatarma cewar sai kayi danasani domin ɗanka bashi da laifin komai a taƙaicema kai ne ka aikata laifi a gareshi domin bakayimai uziri ba.
Nan take mahaifin Abdul ya kalleni haɗe da cewa "muddun kunason junanku to kushirya sati me zuwa zan ɗaura muku aure kuma ni zan ɗauki nauyin komai.
Sannan kuma na mallakama ɗaya daga cikin gidajena kazabi wanda yaima.
Kuma na baka dama ka nemi mahaifin A'isha idan har ya amince zai baka auranta to itama zan ɗauki nauyin bikin naku.
Haka naje gaban mahaifina na durƙusa har ƙasa inamai bashi haƙuri a game da abun da ya faru.
Sai yace "kar kaji komai domin wannan laifinane domin da ace nayima uziri kamar yadda malan ya faɗa da duk haka ba ta faru daku ba.
A wannan ranar dai ba kaɗan naji daɗi ba domin shima mahaifin sister A'isha bai nuna wata tirjiya ba haka ya amince dani a matsayin wanda zai auri A'isha.
Alhamdullah
The EndSai maryam tace a wannan daran nabar gidan ina cikin tafiya banmasan inda nake dosa ba kawai sai na taka wata kwalba a ƙafata.
Zafin da naji ne yasa na kwalla ƙara wanda hakan yasa wani bawan Allah ya fito domin ganin abun da yake faruwa.