new update
=> 1
Ameera yarinya mai hankali da sanin ya kamata ga ilimi da sakin fuska ga yara da manya.
To amma duk waɗannan halayan nata ba sune suke burgeni ba.
Kawai kyawun surarta ne yake mugun burgeni domin ita duniyace a fagen kyau.
Sai dai kuma ni ba gwani bane a fagen soyayya, haka ne yasa na ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da na iya gabatar da soyayyata a gareta ba.
Tsawon kimanin shekara 1 da rabi kenan da ajiye soyayyar ameera a raina.
Har wasa da dariya ne yake shiga tsakanina da Ameera amma hakan baisa na samu kwarin guiwar furta kalmar soyayya a gareta ba.
Kwatsam rannan ina tsaka da wanke motar mahaifina a ƙofar gida sai ƙanin ameera ya fito.
Buɗar bakina a yayin da nayi ido biyu dashi sai nace "Khalid ina Ameera?
Sai yace "tana gida tana cin abinci.
Bayan Khalid ya koma gida sai yace "anti ameera wai kizo inji yaya Abdul zai aikeki.
Koda ameera ta kalli Khalid sai tace "kaje kace bazanzo ba.
Bata sani ba ashe mahaifinta yanaji.
Bayan na gama wanke motar zan shiga gida kenan sai ji nayi Khalid yace "yaya Abdul wai Ameeran tace bazatazo ba.
Sai nayi dariya nace "to aini bacewa nayi ka kira ta ba.
Bayan nayi wanka a yayin da nake shirin fita wajan aiki sai yayata wato anti sadiya kenan tace kaje mahaifin Ameena yana son ganinka.
Nan take naji ƙirjina ya buga saboda banason kowa ya fahimci son ameera ne a raina.
Haka na shiga har cikin gidan su ameeran tare da mahaifin nata.
Gani ga ameera sai mahaifinta ya kalleta yace "ke dan ubanki wannan bai girmeki ba, ya za'ai ya kiraki zai aikeki ki aikamai da saƙon bazaki zo ba?
Nayi matuƙar mamakin ganin yadda mahaifinta ya bani socket haɗe da cewa "ka zanemin ita.
Na buɗa baki zanyi magana sai ya dakatar dani yace "wallahi idan baka daketaba to wannan socket ɗin sai ya tsutstsunke a jikinka.
Jin haka ne yasa naji a jikina cewar mahaifin nata zai iya zaneni da socket ɗin saboda mahaifin nata tsohon soja ne.
Da hannuna na zane wadda nakeso wanda hakan yasa nabar gidan fuskata cike da kunya.
Tun daga wannan ranar naji a raina cewar ba yadda za'ai na iya samun soyayyar Ameera domin ko hanya ce ta haɗani da ita ba batun gaisuwa a tsakaninmu balle har ayi batun wata magana a tsakaninmu.
A haka dai kullun sonta sai ƙara girma yake a zuciyata har akai matakin da nake bin samarinta cikin dare inayi masu mugun saran da zai iya nakasasu ko yai sular rabasu da rayuwarsu.
Akan ameera na kashe samari da dama kuma ba wanda yai zaton ni ke aikata haka.
Akwai wani dajin dake kusa da garin namu wanda hakan yasa duk ranar asabar ko lahadi muke shiga cikinsa domin cin yayan itatuwan dake dajin.
Misalin ƙarfe 10 na safiya na shirya ni da abokaina mu 4 mu shiga dajin.
A wannan ranar munyi yawo mai nisa sosai wanda hakan yasa muyi katari da wani gida a tsakiyar dajin.
Mu a tunaninmu irin gidan da malaman daji suyi zama a ciki ne.
Ganin yadda yana da ƙura su baibaye gidan ne yasa mu fahimci cewar ba sauran wasu masu rayuwa a gidan.
A ƙarshe sai mu yanke shawarar shiga ciki domin ganema idanunmu abubuwan dake ciki Ba tare da sanin cewar ashe gidan aljanu zamu shiga ba.
A yayin da mu ƙarasa bakin ƙofar gidan sai nayi ido biyu da wani ɗan ƙaramin littafi.
Cikin gaggawa nasa hannu na ɗauki littafin nasashi a aljihu na, sannan mu buɗe ƙofar gidan mu shiga.
Da shigarmu sai muyi arba da wata ƙaramar yarinya tana wasa da wani ƙatoton maciji.
Cikin yanayin firgici muyi waje da gudu, Allah cikin ikonsa ba abun da ya biyomu har mu isa gida.
To amma duk da haka sai da mu ɗauki watanni muna jinyar rashin lafiya.
Bayan mun samu sauƙi bamu sake marmarin komawa dajin da sunan yawo ba.
Ni har na manta da batun ƙaramin littafin da na ɗakko a lokacin da mu shiga dajin.
Kawai rannan ina cikin sharar ɗakina sai nayi ido biyu da littafin.
Sai dai kuma bani da ilimin da zan iya gane ko harafi ɗaya daga cikin abun da littafin ya ƙunsa.
Buƙatar sanin abun da littafin yake tattare dashine yasa na tunkari wani babban malamin gargajiya da littafin domin neman sani a game da littafin.
Koda malamin ya duba littafin sai yace "yaro a ina ka samu wannan littafin, domin wannan ba ƙaramin littafi bane kuma littafin bai shafemu ba domin wannan littafine da ya shafi aljanu.
Buɗar bakina sai nace "ai nasan littafi ne wanda ya shafi aljanu kawai ni dai buƙatata itace sanin abun da yake tattare da littafin.
Sai malamin yai wani ɗan murmushi sannan yace "ba wani abune yake tattare da wannan littafin ba illa ɗalasimai irin na aljanu, wato addu'o'in aljanu irin waɗanda manyan bokaye ke amfani dasu wajan neman biyan buƙata a wajan rafanai wato aljanu kenan.
Jin haka ne yasa na buƙaci malamin ya sauyamin zubin littafin zuwa yaren Hausa.
Da kyar na samu malamin ya amince abisa sharaɗin, zai yi ƙoƙarin sauyamin shafi ɗaya daga cikin littafin a naira miliyan 1 sannan zai riƙe littafin a matsayin mallakinsa.
Haka na amince da wannan sharaɗin abisa yaƙinin duk rintsi sai nasan yadda nayi littafin ya dawo gareni.
Sai da a ɗauki tsawon wata ɗaya sannan aikin sauya shafi ɗaya ya kammala.
Na ɗauka al'amarin wannan littafin wasane haka nayita karantashi cikin dare ba tare da sanin abun da zai iya faruwa ba.
A haka dai har bacci ya ɗaukeni zuwa can sai wata mummunar halitta ta bayyana a mafarkina shi ba mutun ba kuma ba abun na kirashi da dabba ba.
Halittar tana lulluɓe ne da wani mummunan baƙin mayafi ga kuma wata sarƙa jajawur kamar garwashin wuta rataye a wuyan halittar.
Matsowa halittar tayi kusa dani tace "munji kiranka kuma mun amsa, me kake buƙata a garemu?
Nan take na furta cewar kuɗi nake buƙata.
Sannan halittar ta sake tambayata cewar "bayan iyayanka wa kafi So.
Buɗar bakina sai nace "Ameera.
Sai aljanin ya ɓace ba tare da ya sake furta komai a gareni ba.
A cikin daran na tashi a tsorace bayan nayi wasu ƴan addu'o'i sannan na koma na kwanta.
A wannan ranar dai bani na farka ba sai musalin karfe 10 na safiya.
Sakkowar da zanyi daga kan gado sai nayi ido biyu da wasu manyan laidoji har guda 2 cike da kuɗi.
Ban taɓa ko sisin kobo daga kuɗin ba na rufe ɗakin nayi waje.
Fitowa ta daga gida kenan sai na hangi motar yan sanda a ƙofar gidan su ameera.
Ina nan tsaye a ƙofar gida sai yayata ta fito daga gida, koda tayi ido biyu dani sai tace yauwa dan Allah tai maka ka karɓomin madara da milo a shagon Sani.
Cikin hanzari nace "wai anti me yake faruwa a gidansu ameera naga motar yan sanda a ƙofar gidan?
Sai tace "kai dai bari kawai Ameera ce ake tunanin an saceta ko kuma ta ɓace.
Kuma iyayanta sunce jiya da musalin ƙarfe 1 na dare ta kamu da wani irin matsanancin ciwon ciki basuyi tunaninma zata rayu ba bayan mahaifin nata ya bata magani tasha sai bacci ya ɗauketa.
To shine da safiyar nan kuma a nemeta a rasa, bayan sun duba gaba ɗaya dakunan dake gidan basu ganta ba sai suyi tunanin ko tafitane basu sani ba.
Wani abun mamaki kuma ƙofar falon da ƙofar gidan duk a kulle mahaifin nata ya gansu wanda hakan yasa suyi tunanin cewar ba fita tayi ba kuma ba saceta ayi ba domin da fita tayi ko saceta ayi duk ƙofofi biyin za'a samesu ne a buɗe ba a kulle ba.
Bayan na dawo daga aiken da yayar tawa tamin sai naji a jikina cewar anya ɓacewar Ameera bashi da nasa ba da mafarkin da nayi kuwa!
Wannan tunanin da nayine yasa na fahimci cewar siyar da ameera nayi zuwa ga aljanu a mafarkin da nayi.
A wannan ranar na fitar da gaba ɗaya kuɗadan a motar mahaifina zuwa bayan gari ba tare da kowa ya sani ba.
Haka na tattarasu a waje ɗaya na banka masu wuta saboda zan iya aikata komai akan Ameera.
Saboda banyi tunanin da niyar cutarwa su buƙaci na bayyana masu sunan wanda nafi so ba.
Washe gari da daddare sai wannan aljanin ya sake zomin a cikin bacci na domin jin dalilin da yasa na ƙona kuɗin dana nema a garesu.
Sai na sanar dashi cewar saboda zan iya aikata komai akan Ameera, sannan na roƙeshi akan ya taimaka ya dawo da Ameera zuwa ga iyayenta.
Sai yace "zamu dawo da ita kamar yadda ka buƙata amma sai kayima Qur'anin dake ɗakinka fitsari sannan zamu biyama wannan buƙatar taka.
Sai nace "koda ace zaku salwantar da raina da na Ameera haɗe da rayukan iyayena to ba yadda za'ai na iya aikata wannan haramtacciyar buƙatar da ku nemi na aikata a game da Qur'anin da mahaliccinmu ya saukar a garemu.
Sai yace "to indai haka ne sai dai mu ɗauke ka a madadinta.
Jin haka ne yasa na amince ita ta rayu ni kuma suyi duk yadda suga dama dani.
Ban farka daga baccin da nake ba sai a wani ƙazamin kogon dutse.
A wannan wajanne naga gumakan mutane bila adadin ga kuma Ameera kwance a wani baƙin gado cikin wani mawuyacin hali domin batasan halin da take ciki ba balle ayi batun gane waɗan da suke tare da ita.
Ganin yadda na kiɗime a sakamakon ganin halin da Ameera ke ciki ne yasa su sanar dani cewar "ba wani abu ne yake damunta ba illah yunwa haɗe da ƙishin ruwa domin kwananta 2 ba tare da wani abu ya shiga cikin taba.
Burinsu kawai yunwa tayi ajalinta wanda hakan zai basu damar maidata gunkin da zasu riƙa yima bauta kamar yadda su maida sauran gumakan mutanan da na gani a kogon.
Wani aljanine ya busamin iskar bakinshi wanda hakan yasa na zube ƙasa ba tare da sanin halin da nake ciki ba.
Bayan an maida Ameera zuwa ga ahalinta sai ni kuma a maidani kan gadon da a kwantar da ita.
Kwanana ɗaya a wannan kogon sai wata aljana ta gudu dani zuwa wani ƙungurmin daji.
Bayan tayimin magani na farfaɗo daga mawuyacin halin da nake ciki.
Sai tace "me ya kaika shiga hurumin waɗanda kasan cewar sumfi ƙarfinka?
Cikin yanayin nadama mai tattare da sanyin jiki nace "dan Allah kuyi haƙuri karku cutar dani.
Sai tace "ban kawoka nan domin cutar da rayuwar kaba.
Na kawo ka nan ne domin ceton rayuwar ka.
Sai dai kuma banajin cewar waɗanda na kwatoka daga wajansu zasu iya barinka.
Amma idan har ka ɗaukarmin wani alƙawari guda ɗaya to bazan taɓa cutar dakai ba kuma bazan bari a cutar dakai ba.
Idan har kayimin alƙawarin bazaka taɓa auren wata ba bayan ni to zan kasance a tare dakai cikin baka kulawa.
Jin haka ne yasa na buƙaci ta bani abun da zanci domin kawar da yunwar dake damuna kafin na bata amsa.
Ba'a wani ɓata lokaci ba ta gabatarmin da yayan itatuwa kala-kala a gabana amma iya mangoro da gwaiba kaɗai na iya ci daga cikinsu.
Bayan hankalina ya ɗan dawo jikina sai na buƙaci jin maimaicin alƙawarin da takeson na ɗaukar mata.
Bayan ta sake maimaitawa kamar yadda na buƙaci ji daga bakinta sai nace "na ɗaukar miki alƙawarin duk lokacin da na buƙaci yin aure to ba wadda zan aura bayan ke, amma zanso kema ki ɗaukar min alƙawarin bazaki cutar dani ba kuma bazaki cutar da dukkanin waɗan da nake tarayya dasu ba kuma zanso ki kasance mai riƙon alƙawari a gareni.
Sai tace "na ɗauki dukkanin waɗannan alƙawarika kuma zan kasance mai riƙe su a zuciyata domin shigata addinin Musulunci ne ya koyar dani muhimmancin riƙe alƙawari.
Kafin ta maidani gida sai ta bani wani ɗan ƙaramin zobe tace na haɗiyeshi domin shine zai kasance garkuwa a gareni.
Bayan na samu nasarar komawa gida sai na fara tunanin taya za'ai a matsayina na ɗan adam nayi tarayya da aljana.
Tun daga lokacin da na dawo gida ban sake kula wata mace da sunan soyayya ba bawai dan inajin tsoran aljanar da na ɗaukarma alƙawari ba.
Kawai rannan ina cikin baccina mai daɗi sai naji ana tashina daga bacci ka tashi kaje kayi sallah da wata zazzakar murya.
Cikin gaggawa na buɗe ido a tsorace a nan ne fa nayi tozali da wata kyakkyawar mace ganin haka ne yasa naji a jikina cewar aljanar dana ɗaukar ma alƙawarice tazo gareni.
Na buɗa baki zanyi magana sai ta dakatar dani haɗe da cewa kaje kayi sallah kadawo.
=>2
Bayan an idar da sallar cikin gaggawa na fito daga masallacin badan komai ba sai dan buƙatar sake ganin kyakkyawar surar da aljanar tazo gareni da ita, a garin sauri har ina jefa ƙafata a kwata ko damuwa banyi ba haka naci gaba da tafiya.
Da shigata gida bayan na wanke ƙafar tawa sai na tasarma ɗakin nawa.
Ina buɗe ƙofar ɗakin sai nayi ido biyu da ita zaune a gefen gado na.
A wannan lokacin ne naji tsoro ya fara bugun zuciyata.
Ganin yadda na tsaya ina kallanta ne yasa tace "ka shigo mana.
Haka dai na shiga a tsorace na zauna gefe ɗaya ba tare da na iya furta ko kalma ɗaya a gareta ba saboda tun dama can ni ba gwani bane a fagen kula mata.
Ji nayi ta dafa kafaɗata haɗe da cewa "karka kasance mai yawaita yin shiru a gareni saboda akaf faɗin duniyar nan ba wanda nakeso fiye da kai, dan haka zanso ka kasance mai sakin jiki a gareni.
Buɗar bakina sai nace "kawai ji nake kamar wasa kike yimin a game da soyayyar da take shirin yin nisa a tsakanin zukatanmu, saboda kyawunki yakai mizanin da ya kamata ace sai masu manyan matsayine zasuyi rayuwa dake.
Cikin yanayin bayyana damuwa haɗe da tausasa murya tace "dan Allah karka sake ƙoƙarin kawo makamanciyar wannan maganar a tsakaninmu, kuma karka bari kwarjinina yasa ka kasa bayyana ɓacin ranka a game da kurakuran da zaka na aikata a game da addininmu na Musulunci ko wasu daga cikin al'adunku na yan Adam.
Zanso aduk lokacin da kaga na aikata wani abun da ya saɓama addini ko al'adarku kayi gaggawar gyaramin kuma ko durƙusawa zan iya yi domin neman yafiyarka, saboda nima so nake na riƙa gudanar da rayuwata a irin yadda kuke gudanar da taku rayuwar.
Sannan ta ƙara da cewa "idan ka amince zan riƙa kiranka da Sweetheart saboda a halin yanzu kai kaɗai nake gani naji daɗi a zuciyata, kai kuma zaka iya kirana da Aisha ko wani sunan da kaji yafi burgeka domin sunana A'isha.
Kuma zanso ka gabatar dani ga ahalinka a matsayin wadda kakeson ka aura saboda haka ne zai taimaka wajan bani tabbacin cewar zaka zamto miji a gareni saboda banason wani akasi ya gifta a tsakaninmu.
Ba tare da wata kwanakwana ba na amince da wannan buƙatar da ta nema a gareni, Nan take na buɗi baki nace indai wannance buƙatarki to karkiji komai in Allah ya amince zuwa gobe da musalin ƙarfe 3 na yamma zan gabatar dake a garesu, kuma zanso kizo da irin wannan suffar tamu ta yan adam domin banason kowa ya fahimci cewar ke ba mutun ɓace saboda zan gabatar dake a garesu ne a matsayin baƙuwar da tazo gareni tun daga Adamawa.
Bayan mun ɗan taɓa firarmu sannan ta ɓace.
A wannan ranar haka na damu kaina da tunanin cewar bai kamata na gabatar da aljana ga iyayena ba saboda gudun samun matsala.
Washe gari da safe sai na sanar da yayata cewar yau budurwata zata ziyarcemu dan Allah ko zaki iya sanar da umma saboda kunya nakeji.
Bayan saƙona ya isa kunnan iyayena sai yayar tawa ta bani 20 thousand tace na ƙara domin yi mata babbar tarbar.
Saida na gama kashe kuɗadan da na ƙimanta cewar zan kashe wajan haɗama aljana A'isha babbar tarba sai kuma na tuna da cewar sufa aljanu ba ruwansu da duk wani nau'in abincinmu na yan Adam.
Haka dai na fuske har Allah yai isowar Aljana A'isha.
Ina zaune tare da abokaina a wata majalissar dake kusa da gidanmu sai na hangi tahowar A'isha wanda hakan yasa na tashi domin tarbarta.
Da zuwana sai nasa hannu na karɓi jakar da take riƙe da ita.
Ganin hakane yasa gaba ɗaya hankalin abokan nawa ya karkato zuwa garemu.
Da isarmu gida bayan anyi mata sannu da zuwa haɗe da bangajiyar hanya sai kowa ya yaba da kyawun halittar da Allah ya mata, daga bisani kuma sai na kai mata abinci ɗakina.
Nayi matuƙar mamakin ganin yadda take ɗibar abincin tana kaiwa bakinta wanda hakan yasa na saki baki ina kallanta.
Ganin hakane yasa tayi murmushi haɗe da cewa "kar kayi mamaki domin ba cikina yake zuwa ba kawai kana ganin ina kaiwa bakine domin zan iya aikata komai dan rayuwata dakai tai ƙarko.
Bayan kimanin awa 1 da shigowarta gidan namu sai na fita waje tare da ita domin yawatawa.
Haka muyita yawanmu ba tare da kowa yagane cewar da aljana nake tafiya ba.
Bayan dare yayi sai a kaita ɗakin yayata domin yin bacci ba tare da anti sadiya tasan cewar da aljana zata kwana ba.
haka dai su kwana a ɗaki ɗaya a matsayin baƙuwa ba tare da yayar tawa tasan cewar da aljana ta kwana ba.
Ni kuma a raina ko damuwa banyi ba saboda na yadda da cewar bazata taɓa cutar da ahali na ba muddun bani na nemi faruwar haka daga gareta ba.
Bayan gari ya waye da musalin ƙarfe 10 na safiya sai muyi bankwana da ita.
Haka na ɗauki jakar da tazo da ita domin yi mata rakiya zuwa inda zata hau mota.
Har tabar gidan ba tare da kowa yasan cewar aljanace ta baƙuncesu ba.
A haka dai soyayyata da Aljana A'isha taci gaba da tafiya a tsakanin zukatanmu har a ɗauki kimanin watanni 7 ba tare da wata matsala ta shiga tsakanina da ita ba.
Sai dai kuma har izuwa wannan lokacin soyayyar Ameera bata disashe a zuciyata ba kuma banajin cewar zan iya haƙura a game da batun janye kai na a fagen soyayyar Ameera koda kuwa hakan zai iya zamtowa sular rasa rayuwata ne.
Soyayyar da nayi da Aljana A'isha ne yasa na samu kwarin guiwar iya tunkarar Ameera domin gabatar da soyayyata a gareta saboda a wancan lokacin bani da kwarewar da zan iya furta kalaman dasu dace wajan gabatar da kaina a matsayin wanda yake son Ameera.
Rannan ina zaune a wajan wani mai shayi sai mahaifin Ameera ya aikeni domin na karɓomai wasu takaddu a gida.
Da zuwana bayan nayi sallama kai tsaye na shiga gidan saboda gidan ba baƙon shigata bane.
Bayan na karɓi saƙon sai mahaifiyar Ameera tace "dan Allah Abdul ka tafi tare da Ameera daga can sai ka rakata wajan Doctor Musa domin ya mata treatment ɗin ciwon dake hannunta, yanzu ta yanke da wuƙa garin yanka kayan miya.
Cikin yanayin alhini nace "subhanallahi, ina Ameeran?
Sai mahaifiyar Ameeran tace "yanzu ta shige ɗaki a yayin da taji sallamarka.
Nan take mahaifiyar Ameeran ta kwalla mata kira wanda hakan yasa ta fito ranta a ɓace.
Ganin yadda jini yake zuba daga hannunta ne yasa nayi gaggawar fito da farin handkerchief ɗin dake aljihuna na ɗaure mata hannun.
Bayan na rakata zuwa wajan likitan da zai duba yankan dake hannun nata, a hanyarmu ta dawowa sai na cire duk wata fargabar dake zuciyata.
A yayin da muke cikin tafiya kawai sai na tsaya ba tare da na ƙara ko taku ɗaya ba, sannan na kalli Ameera haɗe da cewa "magana ta gaskiya Ameera a halin da nake ciki yanzu shekara 2 kenan da ajiye soyayyarki a zuciyata.
Kin mallaki dukkanin wasu muhimman abubuwan da ya kamata ɗan Adam ya mallakesu wajan tafiyar da rayuwarsa akan tsari, to amma ni kuma kyawun fuskarki ne yafi burgeni.
Sannan na sake kallanta nace "Ameera inasonki dan Allah ki taimaka ki samar da masaukin soyayyata a zuciyarki.
Ban tashi aune ba sai ji nayi Ameera ta tsunkeni da mari.
Ɗago kan da zanyi sai naji muryar Aljana A'isha a bayana a yayin da ta furta cewar "kin kyauta kuma kin burgeni.
=> 3
domin marin da kiyimai ne kaɗai ya ceci rayuwarki daga ƙudirin kasheki.
Jin haka ne yasa Ameera ta kalli A'isha haɗe da cewa ke kuma wacece, kuma meye naki na shiga maganar da ba ta shafeki ba?
Cikin gaggawa na dakatar da Ameera nace "A'a Ameera rabu da ita domin wannan maganace wadda ta shafi tsakanina da ita dan haka ki wuce kawai ki tafi.
Bayan tafiyar Ameera sai Aljana A'isha ta kalleni ranta a ɓace tace "yanzu har kana da gajeran tunanin da zakayi amfani dashi wajan yaudarata?
Jin haka ne yasa naja hannunta mu samu waje mu zauna.
Ganin yadda na kalleta ne yasa itama ta kalleni ba tare da ta sake furta wata magana ba wanda hakan yasa nayi murmushi haɗe da cewa "shifa wannan al'amarin da kiga ya faru a tsakanina da waccan yarinyar ɗabi'armuce kuma al'adarmuce ta yan adam, saboda mafi yawancinmu zukatanmu basu da juriya wajan haƙurin bayyana soyayya ga dukkanin wata macen da muga tana burgemu, dan haka wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa mahaliccinmu ya halatta mana auran mace 4 muddun zamu kasance masu adalci a garesu.
Idan kuma mun san cewar bazamu kasance masu adalci ga koda mace 1 ba to bai halatta mu aureta ba.
Tabbas na aikata kuskure saboda bai kamata ace na haɗa soyayyar mace biyu ba, kamata yai ace sai na fara cika alƙawarin dana ɗaukar miki a game da batun aure na da ke sannan nake da damar tunkarar wata mace da sunan soyayya har muyi aure saboda haɗa soyayyar mace 2 ko 3 alamace ta yaudara.
Sai tace "to amma tunda kasan haka me yasa ka tunkareta da batun soyayya bayan kuma kasan cewar ka ɗaukar min alƙawarin nice wadda zaka aure?
Koda naji haka sai nace "eh nasan cewar na ɗaukar miki alƙawarin kece wadda zan aura aduk lokacin da na tashi yin aure, amma ban ɗaukar miki alƙawarin cewar bazan ƙara wani auren bayan ke ba.
Sannan ban ɗaukar miki alƙawarin zan daina kula Ameera da sunan soyayya ba.
Idan har na fara auran Ameera shine ya zama yaudara.
Idan kuma na fara auranki sannan kuma na auri Ameera daga baya ba yadda za'ai a kira haka da sunan yaudara a tsakanina dake.
Dan haka ina nan da ƙudirin auranki kuma zanci gaba da neman soyayyar Ameera har zuwa lokacin da zancimma nasarar auranku ku biyu.
Buɗar bakin Aljana A'isha sai tace "nifa ba yadda za'ai na bari ka auri wata mace bayan ni saboda ni kadai ce wadda nake son na rayu da kai ba tare da wata ba, idan kuma ba haka ba to ina mai tabbatarma cewar zaka tsinci kanka a babbar damuwa.
Koda naji haka daga bakinta sai nace karfa ki manta ke da kanki ki ɗaukarmin alƙawarin bazaki cutar dani ba kuma bazaki cutar da dukkanin waɗanda nake tarayya da su ba.
Sannan ke da kanki ki buƙaci a duk lokacin da naga zaki aikata kuskure a game da addininmu na Musulunci ko wasu daga cikin al'adunmu na yan Adam to nayi gaggawar kawo gyara a gareki, dan haka hanani kula Ameera a matsayin wadda nakeson ƙara aure bayan na aureki kuskurane a addininmu da al'adarmu.
Jin haka ne yasa nan take Aljana A'isha ta ɓaci ba tare da ta ƙara furta komai a gareni ba.
A haka dai har a ɗauki tsawon wata ɗaya ba tare da na sake ganin Aljana A'isha ba kuma ba ta sake dawowa gareni koda a mafarki ba.
Ganin hakane yasa nayi tunanin cewar Aljana A'isha ta haƙura dani ne wanda hakan yasa ni kuma naci gaba da ƙoƙarin neman soyayyar Ameera ba tare da sanin cewar Aljana A'isha tana nan tana bibiyar duk wasu harkoki na ba.
Koda Aljana A'isha taga na dage wajan ganin cewar lallai sai na cusa soyayyata a zuciyar Ameera, kawai sai Aljana A'ishan ta shiga jikin Ameera bawai dan buƙatar ta cutar da rayuwar Ameera ba, kawai ta shiga jikinta ne domin buƙatar haifar da ruɗani a garemu.
Haka Ameera taci gaba da gudanar da harkokinta kamar yadda take gudanar da harkokinta kafin A'isha ta shiga jikinta.
Sai dai kuma dukkanin harkokin da Ameera take gudanarwa tana gudanar da sune ba tare da sanint ba saboda Aljana A'isha ta kawar da hankalinta kuma ba wanda ya fahimci haka domin ko iyayanta basu da masaniyar cewar aljanace take gudanar da dukkanin harkokin da Ameera take gudanarwa.
Ni kuma haka naci gaba da neman soyayyar Ameera amma taƙi amincewa.
Kawai rannan da musalin ƙarfe 3 na rana a yayin da na dawo gida domin cin abinci sai mahaifiyar Ameera tasa Khalid ya kirani wato kanin Ameera kenan.
Da shigata gidan bayan mun gaisa sai mahaifiyar Ameera tace "tun da safe Ameera ta kulle kanta a ɗaki tana kuka saboda mahaifinta ya hanata zuwa Jos wajan kawunta, shine nakeso ka taimaka ka ɓallemin ƙofar saboda bansan halin da take ciki ba.
A yayin da na ɓalle ƙofar sai nayi tozali da Ameera kwance a gado tana bacci ga kuma Earpiece a kunnanta.
Ganin hakane yasa na fahimci cewar wani abun take saurara a wayarta har tayi bacci wanda hakan yasa batajin duk wani kiran da mahaifiyar tata take mata a yayin da ta kulle ƙofar.
A nannefa hankalina ya karkata zuwaga kallan hotunan da ke maƙale a ko wane bangon dake ɗakin Ameera.
Ganin hotunan da nayi ne yasa na fahimci cewar ashe itama Ameera ta daɗe da kamuwa da haƙikanin so na domin hotuna na na gani har guda 4 a kowane bangon dake ɗakin.
Haka dai nabar gidan ba tare da Ameera ta tashi daga baccin da take ba kuma Allah baisa mahaifiyar Ameera ta kula da hotunan da na magani a ɗakin ba.
Ban sani ba ashe dai Aljana A'isha ce take son haifar da babban ruɗani a tattare da rayuwarmu saboda ko nima bani da masaniyar cewar Aljana A'isha ce ta shiga jikin Ameera.
Musalin ƙarfe 8 na dare sai na haɗu da Ameera a wani shagon dake unguwarmu.
Bayan ta fito daga shagon sai nabi bayanta, a yayin da naje daf da ita sai nace da ita "Ameera duk da cewar nasan akwai soyayyata a zuciyarki hakan bazai hanani neman izinin baki cikakkiyar kulawar da ta dace a yayin da mu tsinci kanmu a duniyar masoya ba.
Sannan na tareta ta hanyar shiga gabanta haɗe da cewa "dan Allah ko zaki iya bani damar baki kulawa a birnin masoya?
Nan take naga tayi wani ɗan murmushi sannan ta kalleni haɗe da cewa "waya sanar dakai cewar akwai soyayyarka a zuciyata?
Buɗar bakina sai nace hotunan dana gani a ɗakinki sune su bani tabbacin cewar kema kin daɗe da ajiye sona a taki zuciyar.
Cikin yanayin mamaki tace "kar dai kace kai ne wanda ka ɓalle min ƙofar ɗaki?
Sai nace "Eh! nine amma kiyi haƙuri gobe zansa azo a gyara miki.
Cikin yanayin damuwa tace "ni ba ɓalle ƙofar ko ganin hotan ne abun damuwa ba Allah yasa dai bakaga komai ba bayan hotunan.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "Eh na gankine lulluɓe da babban mayafi banda wannan banga komai ba.
Cikin yanayin kunya tasa hannuwanta biyu ta hankaɗeni sannan ta rufe fuska ta tasarma gida da sauri.
=> 4
Washe gari da sassafe sai Ameera ta aiko ƙaninta Khalid da rubutacciyar wasiƙa.
Ranar ina zaune a falo tare da mahaifina da mahaifiyata haɗe da anti sadiya.
Da shigowar Khalid sai ya miƙomin wasiƙar haɗe da cewa gashi inji anti Ameera kuka tace tana gaisheka.
Nan take naji kaina ya ɗauke wuta sai naji kamar na nutse ƙasa saboda tsabar kunya.
Cikin yanayin sanyin jiki na kalli mahaifina sannan na kalli anti sadiya, haka dai na karɓi wasiƙar a kunyace.
Ganin hakane yasa anti sadiya tayi murmushi haɗe da cewa "saurayin kusa da gidafa akwai naci, to ya kuma zakayi da soyayyar A'isha yar mutan Adamawa? Koda yake ban sani ba ko abba mata biyu zai aurama a rana ɗaya.
Cikin gaggawa nabar gidan ba tare da na tsaya sauraron zantukan da take furtawa a gareni ba.
Ina fitowa waje sai nayi arba da Ameera a ƙofar gida.
Cikin yanayin sakin fuska nace da ita "kin kyauta da kisa yaro ya bani wasiƙa a gaban su Abba wanda hakan yasa na fito cikin kunya.
Buɗar bakinta sai tace "au kai yanzu nan har kasan kunya? karfa ka manta ni na fika jin kunya a game da abu biyu da ka aikatamin.
Cikin yanayin alfahari nace "wane abu na taɓa aikata miki dahar kike iƙirarin cewar kinfini jin kunya?
Sai tace "abu na farko a matsayinka na wanda nake so kuma na kasa furtama cewar ina sonka haka mahaifina ya baka bulala ka zaneni a gaban mahaifiyata.
Abu na biyu kuma "kai ne wanda ka ɓalle ƙofar ɗakina kaga tsuraicina a lokacin da nake kwasar bacci domin a lokacin daka ɓalle ƙofar daga ni sai Pant da Breasier amma saboda ka raina min hankali cewa kayi ka ganni lulluɓe da wani babban mayafi, to dan Allah kai a naka tunanin akwai kunyar da tafi waɗannan abu biyun da su faru a tsakanina dakai.
Koda na kalleta sai nace "to kema in ban da abunki meye na dawo da abun da ya riga ya wuce, kawai yanzu ba abun da ya rage a garemu illa muci gaba da kwasar soyayya a tsakanin zukatanmu.
Amma kafin nan inason ki sanar dani abun da yake tattare da wannan wasiƙar da kisa Khalid ya kawo min domin ko buɗe ta banyi ba na fito daga gida.
Sai tace "na aiko da wasiƙar ne domin baka haƙuri a game da marinka da nayi a lokacin daka sanar dani cewar ka daɗe da aje soyayyata a zuciyarka ba tare daka sanar dani cewar kana sona ba.
Domin na marekane saboda jin haushin yadda kabar zuciyata ta daɗe tana cutuwa wajan yawaita tunaninka.
Cikin yanayin tausasa murya na kalli farafan idanunta haɗe da cewa "karki damu domin ke tawace na yafe miki.
Kuma zanso kema ki yafemin a game da dukanki da nayi haɗe da ganinki ɗin da nayi ba tare da wasu muhimman kaya ba.
Sai tace "na yafema a game da ganin da kamin amma batun yafiyar dukan da kamin a gaban mahaifina ya kamata ka nemi wannan yafiyar idan kuma ba haka ba to sai dai mu haƙura da juna.
Cikin yanayin mamaki nace "haba Ameera, yanzu kina nufin dolene sai na nemi yafiyarki a gaban mahaifinki sannan zamuci gaba da soyayya.
Sai tace "kwarai kuwa domin haka na rubuta a ƙarshen wasiƙar da naba Khalid ya kawoma.
Koda na duba wasiƙar sai naga eh lallai hakane a rubuce.
Haka Ameera ta kalleni haɗe da cewa karka sake ƙoƙarin bayyana shauƙin soyayyarka a gareni har sai ka sameni har gida domin bani haƙuri a gaban mahaifina da mahaifiyata saboda hakan zai taimaka wajan ƙara min ƙima a garesu, domin dukan da mahaifina yasa kayi a gareni tamkar zubar da mutunci ne a gareni saboda ko kaɗan banji daɗin abun da mahaifina yasa kamin ba domin hakan yasa na fahimci cewar ko bayan na aureka hakan zai rage ƙimata a gareka saboda haka kayi haƙuri a game da wannan buƙatar da na nema a gareka saboda hakane kaɗai zai sa mahaifina ya fahimci cewar abun da yasa ka aikata a gareni kuskurene saboda na sanar da Khalid cewar bazanzo ba ne a lokacin da ka aikoshi cewar nazo zaka aikeni domin gudun kar mahaifina ko mahaifiyata su fahimci soyayyace take shirin afkuwa a tsakaninmu saboda kasan mu mata bamason mahaifanmu suyi gaggawar gano cewar muna soyayya da wani a tashin farko, domin wallahi ban furta cewar bazanzo ba domin nuna raini ko isa a gareka ba.
Saboda kai mutun ne wanda ka isa ka aikeni duk inda kaga dama domin ina matuƙar ƙaunarka.
Waɗannan kalaman da Ameera tayi a gareni ne yasa naji sonta ya ƙara shiga zuciyata wanda hakan yasa naji ƙwalla sun fito daga idanuna.
Ganin ƙwallan da Ameera tayi a idanuna ne yasa nan take ta shige gida ba tare da ta sake furta komai a gareni ba.
Bayan gari ya waye da musalin ƙarfe 8 na safiya sai na shiga gidan su Ameera domin bata haƙuri kamar yadda ta nema a gareni.
Da shigata gidan bayan nayi sallama haka na durƙusa har ƙasa na gaishe da mahaifinta haɗe da mahaifiyarta ga kuma Ameera zaune a gefe ɗaya tana danna waya.
Cikin yanayin kunya na kalli mahaifin Ameera haɗe da cewa "Abba nazo ne domin naba Ameera haƙuri a game da dukan da kasa nayi mata yau kimanin watanni 8 kenan da faruwar haka.
Saboda tun daga lokacin da kasa na daketa shikenan ta dai na yimin magana domin ko gaisuwa ba ta haɗani da ita alhalin kuma kafin faruwar hakan har wasa da dariya ne yake shiga tsakanina da ita.
kuma a lokacin da ka umarceni da na daketa sai da nayi ƙoƙarin sanar da kai cewar ban aiko Khalid domin ya kira Ameera na aiketa ba.
Saboda a lokacin son Ameera nakeyi kamar nayi hauka amma Allah baisa na iya bayyana soyayyata a gareta ba wanda hakan yasa nake yawaita tunaninta ako da yaushe.
A ranar da kasa na daki Ameera lokacin ina wanke motar mahaifina ne a ƙofar gida sai naga Khalid ya fito daga gida ganin fitowarshi ne yasa na tambayeshi cewar "Khalid ina Ameera?
Buɗar bakinshi sai yace tana gida.
Shi kuma kawai yana zuwa gareta sai yace tazo injini zan aiketa alhalin ni kuma ban aikoshi domin ya kirata ba.
Sannan na kalli Ameera haɗe da cewa dan Allah Ameera kiyi haƙuri a game da abun da ya faru a tsakaninmu saboda duk hakan ya farune a bisa kuskure.
Buɗar bakin Ameera a yayin da ta gyara zama haɗe da aje wayar dake hannunta a gefe ɗaya sai tace "babu komai na yafema kuma nima banƙi zuwa gare ka a lokacin da Khalid ya sanar dani cewar nazo injika zaka aikeni domin rainaka ko nuna isa a gareka ba, kawai na furta cewar bazanzo ba ne saboda banason umma ko abba su fahimci cewar akwai wata alaƙar da ta shafi sonka a tattare da zuciyata.
Jin hakane yasa mahaifiyar Ameera tace "ah to ashe dai dukanku makafin soyayyane tunda har ku kasa furtama junanku soyayyar da take zukatanku gashi har hakan ya kusa ya nemi haifar da saɓani a tsakaninku, dan haka ya kamata ku godema abban naku saboda dukan da yasa kayi matane yai sular bayyanuwar wannan soyayyar taku.
Jin hakane yasa nan take Ameera tacewa mahaifinta "to Abba nagode sannan ta shige ɗaki tana irin dariyarnan mai bayyana alamun kunya.
Ganin hakane yasa nima nace "to Abba mungode sannan nima nayi waje a kunyace na barsu suna dariya.
Jim kaɗan da komawata gida sai naji messege ya shigo wayata.
Ina buɗe saƙon sai naga sunan Ameera a farko abun da tace a saƙon nata shine.
•Saƙo daga Ameera.
Tabbas kai cikakken masoyi ne kuma mai nuna tausayawa ga macen da kakeson ta zamto mallakinka.
Haƙiƙa ka kankaro ƙimata a idon mahaifina, domin wannan babbar jarumtace kayi a gareni.
Naga ƙwalla a idanunka a lokacin da nake sanar da kai irin ƙunar da naji a lokacin da mahaifina yasa ka zaneni wanda hakan yasa na fahimci cewar kai mutun ne wanda zaka kasance mai nuna tausayawa a gareni musamman bayan mun samu nasarar cimma burinmu na kasancewa ma'auratan juna.]
Tun daga wannan lokacin sai soyayyata da Ameera taci gaba da tafiya ba tare da wata matsala ta sake shiga tsakanin mu ba har Allah ya kaimu ga cimma nasarar auran juna.
Haka naci gaba da rayuwa da Ameera ba tare da sanin cewar da aljana A'isha ce a jikinta ba, alhalin ita Ameera batasanma duk wani abun da yake faruwa ba, saboda tun daga lokacin da aljana A'isha ta shiga jikin Ameera har izuwa lokacin da muyi aure bata fita daga jikinta ba.
A haka dai tafiyata da ameera taci gaba da tafiya har zuwa lokacin da Ameera ta samu juna biyu wato ciki kenan.
Kwatsam rannan da misalin ƙarfe 7:30 na safiya sai na tashi Ameera daga bacci ta hanyar cewa "baby na tashi ki haɗamin Tea saboda yau da wuri nakeson fita wajan aiki.
Cikin yanayin nauyin bacci tace "to kaje ka fito daga wankan tukuna.
Koda na fito daga wankan sai na sake ganin Ameera a kwance.
Ganin hakane yasa nayi yinƙurin sake tashinta domin ta haɗamin shayin da nake buƙata.
Nakai hannu zan taɓata kenan sai naji muryar Ameera a bayana a yayin da ta furta cewar "kar kayi gaggawar tashinta, saboda hakan zai iya haifar da matsala ga ƙwaƙwalwarta.
Fuskata cike da mamaki mai tattare da fargaba nayi gaggawar juyowa.
=> 5
Cikin yanayin ruɗani nace "Ameera ina kuma cikin da kike ɗauke dashi sannan kuma wannan wacece kwance a gado?
Sai tace "ni ba Ameera bace domin sunana A'isha, wadda take kwance kuma ameeran kace wadda na shiga jikinta.
Domin ba ta da sanin komai a game da soyayyar ka balle auran da yake a tsakaninku sannan kuma gata da ciki.
Jin haka ne yasa nace da ita "amma gaskiya kin cuceni, kin dagula dukkanin wani farin cikina.
Sai tace "ni ban cuceka ba rashin cika alƙawarin ka ne ya haifar da faruwar haka, saboda na nayi tunanin idan ka aure ni shi kenan bazaka ƙara wani auran ba.
Amma sai ka kawo min wasu tsare-tsaran banza da wofi ta hanyar cewa "ai ban ɗaukar miki alƙawarin zan daina soyayya da Ameera ba, kuma ban ɗaukar miki alƙawarin bazan ƙara wani auran bayan na aureki ba.
A ƙarshe kuma sai ka gabatarmin da wasu alƙawarikan da na ɗaukar ma akan cewar "na ɗaukar ma alƙawarin bazan cutar da kaiba kuma bazan cutar da waɗanda kake tarayya dasu ba.
Ganin ba yadda zanyi da kai ne yasa na ƙaurace ma ganin ka saboda a wannan lokacin raina ne yai matuƙar ɓaci.
Shine kai kuma da yake cikakken mayaudari ne kuma marar cika alƙawari sai kayi amfani da wannan damar wajan neman soyayyar Ameera.
Buƙatar gwada ƙarfin riƙe alƙawarinka ne yasa na shiga jikin Ameera kuma nasa ta karɓi soyayyarka.
Na ɗauka bayan ka samu soyayyar Ameera zaka buƙaci sake haɗuwa dani domin cika alƙawarin da yake a tsakanina da kai kafin ka auri Ameera, toamma ko tunanina sai ka daina yi har ka auri Ameera ba ka nuna wata alamar son sake haɗuwa dani ba.
Haka ta matso kusa dani haɗe da cewa "kayimin abun da ya kamata ace na cutar da kai saboda kai da kanka ka karya alƙawarin da yake a tsakani na da kai.
To amma duk da haka bazan cutar da kai ba saboda ina matuƙar sonka, dan haka ka rabuda Ameera domin ka aureni in yaso sai ka dawo da ita daga baya.
Jin haka ne yasa nayi shiru na ɗan wani lokaci zucan sai na kalli Aljana A'isha haɗe da cewa "Gaskiya bazan iya furta kalmar saki ga wadda nake aure ba, saboda mahaliccinmu ya hanemu da aikata haka ba tare da wani ƙwaƙƙwaran da lili a tsakaninka da wadda kake aure ba.
Saboda Ameera bata aikata laifin komai a gareni ba domin wannan al'amari ne da ya shafi tsakanina dake.
Bansan abun da A'isha tamin ba wanda hakan yasa nan take na zube ƙasa ba tare da sanina ba.
Muryar Ameera naji tana tashina daga bacci ta hanyar cewa "ka tashi kayi wanka kaci abinci karka makkarara domin har ƙarfe 10 tayi.
Buɗe idan da zanyi sai na tsinci kai na kwance a saman gado wanda hakan ya haifar da kokwanto mai tattare da mamaki a gareni.
Ɗaga hannun da zanyi kawai sai na tsunke Ameera da mari, saboda ni a nawa tunanin Aljana A'isha ce ta sake shiga jikin Ameera.
Ban sani ba ashe tun a lokacin da Ameera ta samu juna biyu Aljanar A'isha ta fita daga jikin Ameera, kawai ta bayyana a gareni ne domin ta haifar da ruɗani a tsakanina da Ameera.
Koda Ameera taga na tsunketa da mari sai al'amarina yai matuƙar bata mamaki wanda hakan yasa ta koma falo ta zauna tana kuka.
Bayan na gama shirye-shiryena sai nayi tafiyata wajan aiki ba tare da na furta komai a gareta ba.
A wannan ranar haka na wuni da tunanin yadda aljana A'isha ta ke neman haifar da tashin hankali a gareni.
Haka dai Ameera ta gama kukanta kuma ta share hawayen da ke fuskarta haɗe da tunanin cewar shifa dama zaman aure ya gaji haka sannan tasa ma ranta haƙuri a game da marin da nayi mata.
Bayan na dawo daga wajan aiki haka Ameera ta taho gareni domin tarbata kamar yadda ta saba.
Haka ta tunkaroni fuskarta a sake cike da annuri haɗe da furta kalmar Oyoyo sannu da zuwa My dear.
A wannan lokacin ne na sake tsunke Ameera da mari haɗe da cewa "Dan Allah ki taimaka ki fita daga jikin matata saboda har kawo wannan lokacin tunanina yana nan akan cewar Aljana A'isha ce take raina min hankali.
Jin wannan kalamin da nayi ne yasa Ameera ta dafe fuskarta ba tare da tace komai a gareni ba.
Bayan ta shiga ɗaki sai ta ɗauki hijab tasa sannan ta tasarma gidan iyayanta.
Da zuwanta gida sai ta sanar da mahaifinta cewar "nifa Abba tun a safiyar yau na kasa ganema al'amarin mijina, da safe ya mareni saboda na tasheshi daga bacci domin karya makkara a wajan aiki.
Haka yanzuma da ya dawo daga wajan aikin ya sake marina saboda nayi mai sannu da zuwa haɗe da furta cewar "dan Allah ki taimaka ki fita daga jikin matata.
Sannan ta kalli mahaifin nata haɗe da cewa "wannan kalamin da naji yayi ne yasa nakeji a rai na kamar aljanu ne suke son haifar da saɓani a tsakanina da mijina, domin wallahi tsoro nakeji kar naje ya illatani.
Nan take mahaifin Ameera ya kirani a waya da buƙatar ganina.
Da zuwana gidan bayan mungaisa sai yace "wai me yake farune a tsakaninka da Ameera?
Buɗar bakima sai nace "kawai ina ganin alamun akwai iskokai ne a tattare da ita saboda naga alamun duk wasu al'amuranta sun sauya kuma ina yawan ganin tana min gizo daga suffarta zuwa wata suffar.
Jin hakane yasa mahaifin Ameera yace "to indai hakane akwai matsalar shafar aljanu a tattare da Ameera ko kai kanka ko kuma a cikin gidan naku.
Saboda a kwanakin bayacan idan baka mantaba kayi wata tafiya zuwa jahar Nasarawa har ka ɗauki tsawon sati ɗaya acan.
Sai nace "kwarai na tuna domin yau kimanin watanni 6 kenan.
Sai yace "to bayan kwana ɗaya da tafiyarka sai Ameera tazo garemu cikin wani irin yanayi na mantuwa ko kuma ince ɗimuwa, saboda a lokacin ta nuna mana alamun cewar itafa ba ta da wata masaniyar cewar tayi aure.
Domin a lokacin da ta sameni cewa tayi "Abba Allah yasa dai wannan cikin da nake ɗauke dashi ba na shege bane, saboda wallahi bani da masaniyar yanda ai na samu wannan cikin da nake ɗauke dashi.
Koda naji haka sai nace da ita "A'a cikin da kike ɗauke dashi ba na shege bane domin ta hanyar aure ki sameshi.
Buɗar bakinta sai tace "Abba kardai kace Abdul shine wanda yake aurena saboda auranma bani da masaniyar kasancewa a cikinshi, saboda kafin na baro wani gida anan kusa naga hotunana a tare da Abdul maƙale a jikin bango.
Koda naji haka sai nace "anya Ameera ƙwaƙwalwarki ba ta samu matsala ba kuwa?
Saboda ke da kanki ki bayyana mana cewar Abdul kikeso, kuma haka kuci gaba da soyayyarku har kuyi aure kuma gaki da ciki domin gidan da kice kinga hotunanki tare da abdul shine gidan da mijinki yake zaune dake.
Ganin halin da take cikine yasa a lokacin na kiraka a waya domin sanar dakai cewar zaman Ameera ita kaɗai a gidanka yana bata tsoro dan haka zata zauna a tare damu har zuwa lokacin da zaka dawo.
Saboda a wannan lokacin banason kowa yasan halin da ake ciki wanda hakan yasa na kaita asibiti domin duba lafiyar ƙwaƙwalwarts.
Bayan anyi yan gwaje-gwaje sai a sanar dani cewar ƙwaƙwalwarta lafiya ƙalau take amma sai dai alamu sun nuna cewar ƙwaƙwalwar tata ta ɗan samu cushewa ne a wasu watannin da suka gabata amma a halin da take ciki yanzu ƙwaƙwalwarta lafiya ƙalau take.
A ƙarshe sai su rubuta mana wani maganin da zan siyo mata domin ta riƙa sha, kuma a lokacin ne su bamu masaniyar cewar tana ɗauke da juna biyu.
Haka dai mahaifin Ameera ya dai-daita tsakanina da Ameera ya kuma sa ayi mana saukar Qur'ani har 7 a garemu da kuma gidan da muke ciki badan komai ba sai dan buƙatar mu zauna lafiya cikin kwanciyar hankali, ammafa duk da haka ban gama gamsuwa da cewar babu aljana A'isha a tatare da Ameera ba.
Tun daga wannan lokacin wani ruɗani bai sake shiga tsakani na da Ameera ba har zuwa lokacin da ta haifi abun da ke cikinta, kuma a wannan lokacin sai Allah ya albarkacemu da samun yan biyu mace da namiji.
Bayan kimanin wata ɗaya da samuwar haihuwar yan biyu a garemu sai Aljana A'isha ta sake ziyartarmu da suffa irin ta matata Ameera wanda hakan ya haifar da ruɗanin kasa gane wacece Ameeran gaske kuma wacece ta ƙarya.
Da sassafe na tashi daga bacci sai nayi ido biyu da Ameena a yayin da take zaune a gaban mirror tana kwalliya, ga kuma jarirai a gefe suna ƙamshi wanda hakan yasa na fahimci cewar suma tuni ayi masu wanka.
Buɗar bakina sai nace "amma Ameera wannan wane irin wulaƙanci ne, yanzu fisabilillahi shine kina ganina sai bacci nake amma kiƙi ki tasheni da wuri?
Koda ta juyo ta kalleni sai tace "nifa tsoro naji domin kar ka sake marina.
Bayan na fito daga wanka a yayin da na gama shirina sai na sameta a falo zaune tana zaman jirana domin nazo muci abinci a wannan lokacin su kuma jariran suna ɗaki suna bacci.
Zamana kenan a kusa da Ameera ga kuma abinci a gaban mu sai Ameera ta kalleni haɗe da cewa "yaufa sai dai kayi haƙuri domin babu batun fara shan Lipton kafin cin abinci saboda yanzu na duba naga ashe tuni Lipton ɗin ya ƙare.
Nan take na miƙe haɗe da cewa aikon kinsan ba yadda za'ai na fara cin abincin nan ba tare da na fara shan Lipton ba dan haka yanzu zanje na karɓoshi a shagon dake nan kusa.
Bayan na dawo sai na samu Ameera a ɗaki tare da jariranmu.
Haka nasa hannu na ɗauki ɗaya itama ta ɗauki ɗaya mu fito daga ɗakin tare.
Fitowarmu daga ɗakin nenan sai kuma nayi ido biyu da Ameera a yayin da ta fito daga kitchen hannunta riƙe da flask.
Ganin hakane yasa ameera ta sakiflask ɗin dake hannunta.
Haka itama Ameeran da na fito tare da ita ta tsorata wanda hakan yasa ta nanne a jikina.
=> 6
A wannan lokacin ne nima na shiga ruɗanin kasa gane ameeran gaske da kuma wadda ba ta gaske ba, saboda a wannan lokacin ni kaina bazan iya gane asalin matata ba.
Ganin yadda dukkanninsu su bayyana tsantsar tsoro ne yasa na kalli Ameeran da na fito tare da ita daga ɗaki haɗe da cewa karkitsorata bazata cutar dake ba.
Sannan itama Ameeran da ta fito daga kitchen na kalleta haɗe da cewa "ki kwantar da hankalinki karki tsorata domin ba abun da zata aikata miki.
Jin haka ne yasa wadda ta fito daga kitchen ta kalleni cikin yanayin tsoro haɗe da cewa "ba ruwana da wani batun bazata cutar dani ba, kawai ka karɓar min ɗana daga hannunta saboda ganinshi a tare da ita tamkar yinƙurin rabani da numfashi na ne.
Buɗar bakin wadda na fito tare da ita daga ɗakin sai tace "ƙarya kike munafukar banza wallahi nafi ƙarfin ki shigar da ruɗani a tsakanina da mijina.
Ganin yadda ruɗani yake neman shiga tsakaninmu ne yasa na karɓi jaririn dake hannun wadda na fito tare da ita daga ɗakin.
Sannan na kallesu haɗe da cewa "muje mu zauna domin warware wannan matsalar.
Bayan mun samu waje mun zauna sai na kallesu haɗe da cewa "duk da cewar nasan akwai wadda tasan zahirin yadda wannan al'amarin ya samo asali hakan bazai sa nayi ƙasa aguiwa wajan sake furta farkon faruwar wannan matsalar ba.
Haka na kallesu nace "wannan matsalar ta samo asali ne tun wata ranar da yawonmu ya kaimu cikin dajin da yake kusa da wannan garin namu.
A dajin ne mu haɗu da gidan aljanu har nayi sa'ar mallakar wani ɗan ƙaramin littafi.
A sanadin littafin ne duk wannan matsalar ta faru a tsakaninmu, saboda a ranar da na riƙa karanta wani sashe daga cikin abun da littafin ya ƙunsa wata mummunar halittata ta bayyana a mafarkina domin tambayata abun da nake buƙata.
A wannan lokacin ban furta komai ba face buƙatar kuɗi.
Jin haka ne yasa mummunar halittar ta tambayeni cewar "bayan iyayena wa nafi so.
A wannan lokacin ba wadda nakeso fiye da Ameera wanda hakan yasa na ambaci sunanta, saboda ni a nawa tunanin halittar zata tai makamin ne wajan sawa Ameera ta ƙaunaceni kamar yadda nake ƙaunarta saboda a wannan lokacin kasa furta mata cewar inasonta nayi.
Kuma a wannan lokacin banajin cewar zan iya haƙura da ita wanda hakan yasa na riƙa bin wasu daga cikin samarinta ina kashewa ta hanyar amfani da wata tsohuwar wuƙar da mahaifina ya gada tun zamanin wani kakanshi.
Da wuƙar na riƙa amfani wajan raunata samarin dake zuwa wajan Ameera fira wasu sun mutu wasu kuma sunanan a raye.
Bayan na furtama wannan halittar cewar "Ameera ce wadda nafi ƙauna bayan iyayena kawai sai halittar ta ɓace.
Bayan gari ya waye sai naga kuɗi masu yawa a ɗakina wanda hakan yasa nayi gaggawar rufe ɗakin sannan na fita waje ba tare da kowa yasan da batun kuɗin ba.
Fitowata daga gidan kenan sai na samu labarin ɓacewar Ameera, bayanin yadda ɓacewar Ameera ya kasance ne yasa na fahimci cewar nine sular duk wani abun da yake shirin faruwa da Ameera domin a wannan lokacin ji nayi a raina cewar siyar da Ameera nayi a mafarkin da nayi.
Ganin haka ne yasa naje bayan gari na ƙone kuɗin gaba ɗaya wanda hakan yasa a dalilin ƙona kuɗin na cimma nasarar zuwa inda aljanun suke tsare da Ameera.
Ƙaunar da nakema Ameera ne yasa na zaɓi su maidata zuwa ga iyayanta sai su riƙeni a madadinta.
Wata aljanace ta ceci rayuwata ta hanyar guduwa dani zuwa wani daji wanda hakan yai sular afkuwar alƙawarin aure a tsakani na da ita har tayimin alƙawarin bazata cutar dani ba kuma bazata cutar da waɗanda nake tare dasu ba.
Sannan na kallesu haɗe da cewa "aljanar da na ɗaukarma alƙawarin aurece ta zo gareni domin haifar da ruɗani a game da matar da nake aure domin itace a ɗaya daga cikinku.
Miƙewa naga ɗaya daga cikinsu tayi haɗe da cewa "tabbas na dawo garekane domin buƙatar nemawa ƴaƴana lafiya a game da illatasu ɗin da kayi da tsohuwar wuƙar da ka gadarwa kanka tun zamanin kakanninka saboda waɗanda kake iƙirarin cewar ka kashesu ba mutuwa suyi ba suna nan da ransu domin ƴaƴana ne suke zuwa wajanta fira asuffar mutane kuma sun rigaka kamuwa da haƙiƙanin soyayyar ta.
Da ace ka riƙemin alƙawarin fara aurena da tuni ƴaƴana sun samu lafiya saboda ban shiga rayuwarka domin buƙatar cutar da kai ba, domin abu biyu ne zasu zamto sular samuwar lafiyar ƴaƴana.
Wuƙar da kayi amfani da ita wajan illata ƴaƴana tana da matuƙar haɗari a garemu Aljana.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "da ace ka yadda ka aureni a matsayin matarka ta farko to za'ayi amfani da ƙasar wajan da'a ɗaura auran namu ne domin yima ƴaƴana maganin a game da illatasu ɗin da kayi.
Koda naji haka sai nace da ita "to amma me yasa kiƙi sanar dani gaskiyar wannan buƙatar taki?
Sannan kuma ai da ace kinyi tunani bai kamata ace kin nemi soyayyata a lokacin da ki ceci rayuwata daga hannun aljanun dasu sace Ameera ba domin a wannan lokacin kamata yayi ki ƙyaleni sai bayan kin maidani gida sannan daga baya sai kizo gareni da suffa irin tamu ta yan adam wanda hakan zai baki damar sace zuciyata da kyakkyawar suffar da zakizo gareni da ita har ki cimma nasarar aurena domin nemawa ƴaƴanki lafiya.
Matsowa tayi kusa dani haɗe da cewa "kowane magani akwai dokokinsa.
Dan haka dokar maganin da zan nemawa ƴaƴana "dolene sai kasan cewar Aljana zaka aura saboda dokar maganin ba ta yadda da cewar nazo gareka da suffar da zaka kasa gane cewar Aljana zaka aura ba, to amma bayan Kasan cewar Aljana zaka aura to zan iya zuwa gareka da dukkanin wata suffar da naga dama.
Sannan dolene ya zamto nice matarka ta farko.
Sannan kuma dokar maganin ba ta yadda na sanar dakai cewar zan aureka ne domin buƙatar nemawa ƴaƴana magani a game da illar da kayi masu ba, wannan shine dalilin da yasa ban sanar da kai komai a game da shiga rayuwarka da nayi ba.
Koda naji haka sai nace "to yanzu meye mafita tun da batun aure na dake a halin yanzu bazai zamto sular samuwar lafiyar ƴaƴanki ba?
Sai tace "a halin da ake ciki yanzu dolene sai dai ka sadaukar da rayuwarka ta hanyar bamu jininka ko jinin wani daga cikin ƴaƴan da ka haifa domin ayi amfani da jinin wajan nema masu magani kuma har wuƙar da kayi amfani da ita wajan illatasu ake buƙata saboda da ita ne za'ayi amfani wajan fitar da jinin wanda za'ayi amfani da jinin nashi.
Jin haka ne yasa matata hafsat tayi matuƙar tsorata wanda hakan yasa na fahimci cewar ba ta son rabuwa da ɗaya daga cikinmu.
Na buɗa baki zanyi magana sai matar tawa ta dakatar dani.
Haka Ameera ta kalleni haɗe da dafa kafaɗata sannan tace "ko kaɗan bazan iya jure ganin yadda za kayi nesa dani ta hanyar sadaukar da rayuwar ka ba.
Dan haka na baka dama ka bayar da ɗaya daga cikin jariran da muka haifa domin a zauna lafiya.
Inaji ina gani haka Ameera ta miƙa ɗaya daga cikin jariran da muka haifa ba tare da ta tsaya dubawa domin ganin mace zata bayar ko namiji saboda a wannan lokacin idanunta cike suke da hawaye.
Bayan aljanar ta karɓi ɗaya daga cikin jariran sai tayi min ishara da cewar zuwa gobe zata dawo domin karɓar wuƙar da nayi amfani da ita wajan illata ƴaƴanta sannan ta ɓace tare da jaririn.
A wannan ranar haka mu wuni tamkar wasu marasa lafiya, kuma gashi bamu da wata amsar da zamu iya sanar da Ahalina da Ahalin Ameera musamman a yayin da su nemi ganin ɗayan jaririn da mu salwantar.
Kwatsam cikin dare a yayin da muke kwance a ɗaki cikin damuwa ba tare da ɗaya daga cikinmu ya runtsa ba.
A yayin da na duba agogo sai naga ƙarfe 6 saura minti 11 wanda hakan yasa na fahimci cewar gari ya kusa wayewa.
Jim kaɗan da duba agogon sai muji ana kwankwasa ƙofar ɗakin da kuke kwance.
Buɗar bakin Ameera sai tace "ka manta baka rufe ƙofar falo ba ko?
Koda na kalleta sai nace "da ƙofar falon da ta gidan duk ba wadda ban rufe ba.
Bayan na sauka daga gadon da muke kwance sai nayi addu'a sannan na buɗe ƙofar domin ganin ko waye.
A wannan lokacin ne na sake yin ido biyu da Aljana A'isha a suffa irin wadda ta saba zuwa gareni tun a wancan lokacin.
Buɗar bakim Aljana A'isha a yayin da muyi ido biyu da juna sai tace "yanzu ƙarfe 6 na safiya nazone domin karɓar wuƙar da muyi magana a jiya da safe.
Ganin yadda raina ya sake ɓaci ne yasa tayi murmushi haɗe da cewa "taya kake tunanin cewar zan iya cutar da ƙaramin jaririn da baisan komai ba, sannan taimin nuni dashi a yayin da yake kwance a falo haɗe da cewa "gashican yana hutawa a falo.
Sannan ta ɓace haɗe da cewa na barku lafiya.
=> 7
Tun daga wannan lokacin sai na samu kwanciyar hankali haɗe da natsuwa wanda hakan yasa naci gaba da rayuwa a tare da Ameera cikin jin daɗi da wal-wala.
Kwatsam bayan wani ɗan taƙai taccan lokaci da rabuwar mu da aljana Aisha, sai wannan mummunar halittar da ta taɓa zomin a mafarki tun kafin haɗuwata da aljana A'isha ta sake zuwa garemu riƙe da wata wuƙa.
A wannan lokacin ne nayi matuƙar tsorata domin nasan da ƙudirin ɗaukar fansar kuɗinsu da na ƙona aljanin ya sake dawowa gareni.
Sai dai kuma a wannan lokacin dani da Ameera sai mu kasa motsawa ko ina domin ceton rayuwarmu.
A yayin da aljanin ya matso daf damu sai ya sokawa Ameera wuƙar dake hannunsa sannan ya kalleni haɗe da furta cewar "ka dawo mana da littafin mu.
Ganin yadda jini yake zuba daga jikin ameera ne yasa nayi matuƙar razana.
Kawai sai ji nayi an ɗakamin duka haɗe da kwaramin ruwa mai sanyi a jikina wanda hakan yasa cikin gaggawa na tashi daga bacci a tsorace.
Juyo fuskar da zanyi kawai sai naga anti sadiya tsaye a gabana hannunta riƙe da kofin ruwa.
Cikin yanayin ƙasaita haɗe da bayyana ɓacin rai tace ka tashi kaji tun ɗazu abba yake kiranka amma saboda tsabar wulaƙanci ka wani kwanta sai kwasar bacci kake gashi har ƙarfe 10 ta kusa.
A wannan lokacin ne na fahimci cewar mafarki nayi a game da dukkanin wata cakwakiyar da na tsinci kai na a ciki.
Ganin haka ne yasa nayi ma yayar tawa wani mummunan kallo haɗe da furta cewar amma gaskiya duk duniya bani da wani babban maƙiyi sama dake, wallahi na gwammaci a barni naci gaba da gudanar da rayuwata a wannan mafarkin fiye da a tasheni.
Ba yadda na iya haka nayi waje domin amsa kiran mahaifina.
Da fitowata bayan na wanke fuskata domin a wannan ranar ko sallar asuba ban samuyi ba.
Sai mahaifin nawa ya bani key ɗin motarshi haɗe da wasu takaddu yace"naje na kaima Alhaji Adamu wato abokin kasuwancinshi kwanan.
Haka na fito daga gida raina a ɓace.
Fitowata daga gida kenan sai naga maifiyar Ameera ta fito daga gida ɗauke da Ameera ranga-ranga jikinta duk ya ɓaci da jini.
Ganin haka ne ya jefa zuciyata a ruɗani wanda hakan yasa na taka burkin motar da nake ciki ba tare da naci gaba da tafiya ba.
Cikin gaggawa na fito daga motar na karɓi ameera daga hannun mahaifiyarta.
Har mu isa asibitin mahaifiyar ameera bata daina kuka haɗe da sumbatun cewar Ameera karki mutu ki barni.
Ni kuma a wannan lokacin bakina ba abun da yake furtawa sai kalmar "innalillahi-wa'inna-ilaihi-raji'un.
A haka dai har mu isa asibitin.
Bayan mun ƙarasa asibiti a yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarta daga gargarar mutuwa sai mahaifiyar Ameera take bayar da rahoton cewar "bayan ameera ta gama breakfast sai ta koma ɗaki ta kwanta, saboda a wannan lokacin ta sanar dani cewar tana jin alamun zazzabi yana neman saukar mata.
Ganin hakane yasa na shiga ɗaki na kawo mata magani tasha sannan takoma ta kwanta.
Bata jima da komawa ɗakin ba domin ko mintuna 30 da komawarta ba ai ba sai naji ta ƙwalla ƙara.
Cikin gaggawa naje gareta domin ganin abun da ke faruwa.
Da shigata dakin sai na ganta kwance cikin jini.
Ganin haka ne yasa nayi gaggawar ɗaukkota domin kawota asibiti.
Bayan mahaifiyar Ameera tayi wannan jawabin ban bar asibitin ba har sai da a samu nasarar yimata ɗinki a wajan da a soketa dawuƙar domin wuƙar ba ta illata wani abu daga cikin nata ba.
Ita kuma a wannan lokacin batasan halin da take ciki ba sakamakon allurar baccin da likitocin suyi mata.
Bayan na isar da saƙon mahaifina sai na zarce wajan wani abokina mai suna Faruq.
Koda na samu faruq a yayin da muke zaune a ɗakinshi sai nace "faruq ina cikin wata babbar matsala.
Amma kafin na fara sanar dakai halin da nake ciki ina buƙatar ka fara cireni daga wani kokwantan da nake ciki.
Buɗar bakina a yayin dana kalleshi sai nace "dan Allah ameeran da gidansu yake kusa da namu gidan ta taɓa yin aure ko bata taɓa yi ba.
Jin wannan tambayar ne yasa faruq yai wata ƴar dariya haɗe da cewa "amma gaskiya ka rainamin hankali, to amsar tambayarka itace "ameera bata taɓa yin aure ba.
Sannan ya kalleni haɗe da cewa "amma me yasa kamin wannan tambayar.
Nan take na gyara zama haɗe da cewa "mafarki nayi na shiga wannan dajin namu tare abokaina kuma ciki hada kai.
A dajin ne mu haɗu da wani gidan aljanu har na samu nasarar tsuntar wani littafi.
A dalilin karanta wani sashe daga cikin littafin ne wata mummunar halitta ta bayyana a mafarkina domin tambayata abun da nake da buƙata.
Bayan na furta cewar kuɗi nake da buƙata sai halittar ta nemi sanin abun da nafiso bayan iyayena.
Nan take na furta sunan ameera saboda itace wadda nafiso bayan iyayena.......
Haka dai nayimai bayanin komai kamar yadda kuji bayanin abun da ya faru a baya har izuwa lokacin da na kai ameera asibiti domin ban ɓoyemai komai ba.
Jin haka ne yasa faruq yai matuƙar bayyana tsoranshi a game da wannan babban al'amarin.
Sannan ya kalleni haɗe da cewa "a halin da muke ciki yanzu ya zama wajibi a garemu mu dage da addu'a.
Sannan kar ka kuskura kayi gaggawar sanar da kowa wannan maganar koda kuwa mahaifiyarkace.
Mataki na 3 ya zama wajibi a gareka kayi gaggawar yanke duk wata alaƙar da take a tsakaninka da ameera saboda hakan zai iya taimakawa wajan ceton rayuwarta.
Abun na 4 kuma muyi ƙoƙarin nemo masu littafinsu mu kuma mayar masu dashi inda yake, ammafa ina mai gargaɗinka akan cewar karka kuskura wannan maganar ta shiga kunnan kowa saboda hakan zai iya sawa a kalleka da wata mummunar manufar da zata iya sawa a yankema hukuncin da bakayi zato ba.
Buɗar bakina sai nace "to ta wace hanya kake tunanin cewar zamu iya samo littafin alhalin na sanar da kai cewar duk wannan al'amarin ya faru ne a mafarki, sukar ameera da wuƙa ne kawai ya bayyana a zahiri.
Jin haka ne yasa yai shiru na ɗan wani lokaci.
Koda ya ɗago kai ya kalleni sai yace "to amma shi malamin da kaba littafin domin ya juyamashi izuwa harshen hausa bazaka iya ganeshi a zahiri ba?
Cikin yanayin damuwa nace "ganeshi a zahiri ba abune wanda nake jin cewar zai samu yiwuwa a gareni ba.
Buɗar bakin faruq sai yace "to tunda har sukar ameera da wuƙa ya bayyana a zahiri, zata iya yiwuwa idan mu duba ɗakinka mu iya samun coping ɗin takaddar da malamin da ka sanar dani cewar ya baka.
Wannan tunanin da Faruq yayi ne yasa nayi gaggawar miƙewa tsaye wanda hakan yasa mu tasarma gidan namu tare.
Da shigarmu ɗakin ina janyo shimfiɗar gadon da nake kwanciya sai muyi ido biyu da littafin haɗe coping ɗin takaddar da malamin ya bani wanda hakan yasa naji a jikina cewar malamin da na haɗu dashi a mafarkin da nayi ba mutun bane.
Cikin gaggawa faruq yasa hannu ya ɗauki coping ɗin takaddar ya buɗe ta.
Cikin hanzari ya kalleni haɗe da cewa ba komaifa a wannan takaddar.
Koda na duba naga eh lallai haka ne cikin gaggawa na buɗe ainashin littafin da ayi coping ɗin daga cikinsa.
Bayan na buɗe littafin sai na kalli faruq haɗe da cewa "shimafa ba komai a cikinsa.
Duk da cewar mun tabbatar da cewar ba komai a wannan littafin hakan bai hanamu ƙoƙarin gano gidan da na ɗauki littafin a dokar dajin ba.
Sai da muyi tafiya mai nisan gaske domin maida littafin saboda a mafarkin da nayi ina iya tuna wasu daga cikin hanyoyin da mubi wajan shiga dajin.
A yayin da muzo kan wata mararrabar hanyoyi 3 sai na kasa gane takamaiman hanyar da ya kamata mubi domin zuwa gidan.
Ganin haka ne yasa faruq yai murmushi sannan ya nuna wata hanya daga cikin hanyoyin haɗe da cewa "tabbas idan mubi wannan hanyar to zata kaimu izuwa ga wani tsohon gidan da wasu ma'aikata su taɓa zama a cikinsa domin na daɗe da sanin wannan gidan.
Jin haka ne yasa na bashi kwarin gwiwar tunkarar gidan ta hanyar cewa "muje gidan domin zata iya yiwuwa gidan ne.
A yayin da muke cikin tafiya sai na hangi gidan daga nesa wanda hakan yasa na kalli faruq haɗe da cewa "tabbas wancan gidan ne na gani a mafarkin da ya faru dani.
Haka faruq ya jani har izuwa ƙofar wannan gidan ba tare da wata farga a tattare dashi ba.
Ganin yadda faruq yake ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan ne yasa na kalleshi fuskata cike da fargaba mai tattare da tsoro nace "A'a faruq ba a ciki na samu littafin ba, a bakin ƙofar nan na ganshi dan haka mu aje masu kayansu kawai mu tafi.
Koda faruq ya kalleni sai yace "me kuma kake tsoro bayan wahala, kana tunanin cewar akwai aduk wahalar duniya akwai wadda ta wuce mutuwa ne?
Dan haka har ciki zamu shiga domin mu basu kayansu cikin girmamawa.
Kuma kamar yadda ka ɗaukar masu littafinsu a bisa kuskure ka kuma dawo masu da littafinsu kamar yadda su buƙata, idan su cutar dakai a yayin da kazo basu littafin nasu ya kake tunanin zata kasance a rana gobe ƙiyama.
Idan dawo masu da littafin ya zamto silar mutuwarmu shikenan alhakin mu ya rataya a wuyansu.
Nan take faruq yasa hannu ya buɗe ƙofar.
=> 8
Ganin yadda faruq ya buɗe ƙofar ne yasa a wannan lokacin na sallama rayuwata saboda na gama ji a jikina cewar sai mun baƙunci lahira.
Haka baru ya riƙe hannuna mu shiga har cikin gidan.
Sai dai kuma a wannan lokacin ba muga kowa ba.
Nan take faruq ya damƙa littafin a hannuna haɗe da cewa "je ka aje masu kayansu a kan wancan dutsen.
Haka na aje littafin a tsorace sannan muyi waje.
Bayan mun fito sai najini sakayau kamar wanda ya fito daga kurkukun da ya kwashi shekaru a cikinsa.
Ganin yadda faruq ya nuna wannan jarumtar ne yasa nayi matuƙar jinjina mai haɗe da bashi babban matsayi a zuciyata domin ya taka duk wasu matakan da ya kamata a kirashi da aboki na kwarai.
Bayan mun koma gida sai faruq ya sake gargaɗina akan cewar "dan Allah na fita harkar Ameera domin akwai kyawawan ƴan mata bila'adadin waɗan da sufita kyau da komai.
Tun daga wannan lokacin sai na ƙudiri niyar cire ameera daga zuciyata.
Bayan ameera ta samu sauki sai tazo har gida tare da mahaifiyarta domin yimin godiya a game da taimakon kaita asibitin da nayi alhalin kuma basu da masaniyar cewar nine saular faruwar wannan matsalar a game da Ameera.
Haka jami'an ƴan sanda suyi iya bakin ƙoƙarinsu wajan gano wanda ya shiga har gidan ya soki ameera da wuƙa amma su rasa har su gaji su haƙora.
Sai dai kuma a mafi yawan lokuta zuciyata tana yawaita tunanin ameera wanda hakan yasa ako wace rana nake bin duk wata hanyar da zatasa nayi ido biyu da ameera koda sau ɗaya ne.
To amma kuma har kawo wannan lokacin ameera bata da sanin komai a game da soyayyarta ɗin da take a zuciyata domin duk abun da ya faru a tsakanina da ita ya faru ne a mafarki.
Haka dai naci gaba da roƙon Allah domin ya haɗani da wadda tafi ameera kyau.
Kwatsam wata rana sai ƙaddara ko kuma ince tsautsayi ya haɗani da wata baiwar Allah mai suna Husna.
Habib muhammad abokina ne wanda na haɗu dashi a sanadin facebook.
Na haɗu da Habeeb tun kimanin shekaru 4 da suka gabata.
Ba ranar da bama chat da junanmu haka zalika kullun sai munyi waya da junanmu sabo da yana matuƙar jin daɗin karanta labaran da nake posting a Facebook haɗe da Whatsapp.
To amma duk da irin wannan daɗewar da muyi Allah baisa mun taɓa haɗuwa da junanmu a zahiri ba domin shi yana cikin garin Abuja da zama ni kuma ina jahar kano.
Kwatsam wata ranar juma'a sai habeeb ya kirani a waya.
Bayan mun gaisa sai yake sanar dani cewa an tsayar da ranar da ranar bikinshi da wata budurwarshi mai suna humaira wadda yake yawan bani labari a game da kyawawan halayanta.
Tun ana saura kwana biyu bikin habeeb.
Da sassafe bayan nayi breakfast fuskata cike da annuri na ɗauki hanyar Abuja.
amma kafin na tafi saida anti Sadiya ta gargaɗeni ta hanyar cewa "dan Allah ƙanina kayi tafiya ta natsuwa domin karka cutar da rayuwar ka musamman a yayin da kake tuƙi.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "karki damu anti, in Allah ya amince bazanyi watsi da wannan nasihar taki ba.
A ranar dana fara haɗuwa da habeeb ne na tabbatar da cewar akwai mutanan kirki a facebook.
Domin habeeb yamin tarba ta mutunci wadda koni kaina iya gwargwadon abun da zan iya yi kenan.
Haka habeeb ya zagaya dani cikin garin abuja sosai saboda wannan ranar ne zuwana na farko garin Abuja.
Bayan an ɗaura auran habeeb da husna a garki local gov't da.
Zuwa ƙarfe 4:00 Kuma sai mu wuce wani babban gidan wasan dake garin abuja domin a wannan ranar ne a shirya wata gaggarumar dinner.
Ban saniba ashe a wannan ranar ne zan haɗu da wata ƙaddara ko kuma ince sanadi.
Da isarmu gidan da za'a gudanar da wannan wasan cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da mutane mata da maza.
Tun daga lokacin da na rabuda Ameera Allah baisa na sake haɗuwa da wata macen da naji cewar ta kwanta min a raiba.
Kwatsam a wajan taron sai naga yarinyar da tayi matuƙar kwantamin a rai.
A yayin da nake zaune ina ɗan tattaɓa wayata waigawar da zanyi sai na haɗa ido da wata baiwar Allah, gata kyakkyawa kuma haɗaɗɗiya.
Koda na hada ido da ita sai nayi sauri na juyo fuskata, gashi kuma zuciyata tana buƙatar na sake kallon kyakkyawar surarta amma kwarjininta ya hana na sake waigawa.
Ganin haka ne yasa nan take na shiga camerar wayata da ƙudirin ɗaukar hotona haɗe da nata hotan.
Haka na ɗaga wayar sama na mana selpy!
Buɗar bakinta sai tace "haba malan wannan wane irin shirme ne, ya zaka ɗauki hotona ba tare da izinina ba?
Cikin yanayin ƙarfin hali mai tattare da ƙasaita na juya a fusace haɗe da cewa "ke dalla malama hotanki ɗin banza me zanyi da hotanki da har zanyi ƙoƙarin ɗaukar ki hoto da wayata?
Sai naja wani dogon tsaki Mtwsssss! Haɗe da cewa "wawiya kawai.
Ganin haka ne yasa ta kalleni tun daga sama har ƙasa sannan ta jinjina kai haɗe da cewa "to wallahi idan har bakayi gaggawar goge hotan daka ɗauka ba to ina mai tabbatarma cewar ranka sai yayi mugun ɓaci.
Duk da cewar barazanar da tayi a gareni ta ɗan bani tsoro hakan bai hanani sake ɗaukarta hota ba, kai tsaye na sake shiga camera na ɗauketa hotona har guda ukku.
Sai wani daga gefan mu ya taso yana dariya.
Da zuwanshi sai ya dafa kafaɗata haɗe da cewa "haba abokina ai irin wannan bai kamaceka ba.
Domin a matsayinka na ɗa namiji ita kuma mace zaman lafiya ne ya kamaceku a wannan taran.
Domin Allah ya la'anci duk wani mai son haddasa tashin hankali.
Kuma kaga idan wanda ya gayyaceka wannan taran yaganka ko yaji labarin abun daka aikata na tabbata bazaiji daɗi ba.
Koda naji haka sai nace "gaskiya ne abokina kuma nagode a game da wannan shawarar daka bani.
Nan take na shiga camera na share duk ilashirin hotunan dana dauketa sannan na bata haƙuri a game da kuskuran dana aikata.
Zuwacan bayan mun zauna sai na ciro kuɗi daga aljihuna na miƙa mata haɗe da cewa "dan Allah dan jeki nan waje ki siyomin lemo haɗe da biscuits.
Murmushi naga tayi sannan ta karɓi kuɗin.
Buɓar bakin a yayin da ta miƙe tsaye sai tace "to ai sai kazo muje domin ka rakani ko.
Koda naji haka sai nayi wani ɗan murmushi haɗe da cewa "to idan na rakaki meye amfanin aiken naki, sannan kuma idan mun tafi tare a matsayina na ɗan rako wazakiba abun da'a aikeki siyowa?
Sai tayi dariya haɗe da cewa "gaskiya kacika wayo wallahi.
Har ta juya zata tafi sai nima nabi bayanta mu tafi tare.
Muna cikin tafiya sai tace "aini ban ɗauka haka kake da sauƙin kai ba, gashi cikin ƙanƙanin lokaci har mun zamto kamar yan uwan juna.
Sai nace "ai a lokacin da kimin barazana sai da nayi matuƙar tsorata, kawai ƙarfin hali ne yasa nasake ɗaukarki hotan, domin a wannan lokacin da'ace naga ma'aikata kamar guda biyu zuwa ukku to da bazan tsaya wani boye-boye ba kawai guduwa zanyi.
Sai tayi dariya haɗe da cewa "ai ba yadda za'ai na haɗa wani da ma'aikata domin da kainama zan iya ɗaukar mataki.
Sai nace "to Allah ya rufa asiri.
Da isarmu sai nace "to abamu lemo guda biyu haɗe da biscuits.
Sai tace "a'a ni bana buƙatar komai domin aƙoshe nake.
Jin haka ne yasa nace "a'a karfa kiyiwa kanki rowa, gwara ki zabi abun da ranki yake da buƙata.
Sai tace "wallahi ba abun da nake da buƙata.
Bayan mun dawo mun zauna inashan lemona muna fira.
A haka dai har na kaiga tambayar sunanta wanda hakan yasa tayi murmushi haɗe da cewa "sunana husna.
A wannan lokacin ne husana tayi matuƙar bani mamaki kokuma ince ta jefani a ruɗani, domin a lokacin dana buɗa baki domin sanar da ita sunana sai ta dakatar dani ta hanyar cewa "basai ka sanar dani komai a game da kai ba.
Koda ta ɗago kai ta kalleni sai tace "Abdul ko?
Cikin yanayin mamaki nace husna a ina kuma kisanni?
Sai tace "a'a karkayimin wannan tambayar domin nan gaba na tabbata zaka gane koni wacece lokacin da zamu rabu sai na bukaci muyi exchange ɗin number domin mu riƙa gaisawa da juna.
Sai tayi shiru na ɗan wani lokaci zuwacan sai ta kalleni haɗe da cewa "tabbas nikaina naji daɗin haɗuwa dakai amma gaskiya ni bani da wata numbar dazan iya baka.
Amma dan Allah kayi haƙuri domin nasan zuwa nan gaba zamu sake haɗuwa inaji ina gani haka husna ta tafi ta barni cikin ruɗani.
=> 9
Bayan an gama taron a ranar da na koma gida.
Kwatsam da yamma sai naji kira ya shigo wayata koda na duba sai naga baƙuwar number ganin haka ne yasa na amsa kiran domin jin ko waye.
Bayan na amsa kiran a yayin da na kara wayar a kunne na sai naji muryar mace.
Bayan mun gaisa sai nace "amma dan Allah kiyi haƙuri domin ban gane ko dawa nake magana ba?
Jin haka ne yasa tayi murmushi haɗe da cewa husnace wadda ka haɗu da ita a bikin da kaje garin Abuja.
Cikin yanayin mamaki haɗe da sakin fuska nace "Husna a ina kuma ki samu numbata domin gaskiya nayi mamakin ganin yadda ki kirani a dai dai lokacin da nake buƙatar sake haɗuwa dake.
Cikin yanayin tusasa murya tace"karkayi wani mamaki domin a wajan yaya Habeeb na samu numbarka saboda na daɗe da saninka saboda yana yawan bani labarinka domin har hotunanka nake gani a facebook ɗinshi.
Kuma dan Allah zanso kayi haƙuri a game da abun da ya faru a game da hotunana ɗin da nasa ka share kawai nayima barazana ne domin buƙatar samun kusanci da zuciyarka.
Fuskata cike da mamaki nace yanzu kina nufin ke ƙanwar Habeeb ce?
Sai tace kwarai kuwa ni ƙanwar habeeb ce, amma dan Allah zanso ka faɗamin gaskiya a game da wata tambayar da zanyima yanzu.
Koda naji haka sai nace "kiyi duk wata tambayarki a gareni in Allah ya amince zan baki amsa dai-dai gwargwadon abun da na sani.
Sai tace "dan Allah ko zan iya sanin dalilin da yasa ka ɗauki hotona a wajan taron bikin yayana.
Nan take na bata amsa ba tare da jin wata kunya ba.
Buɗar bakina sai nace "kawai na ɗauki hotanki ne saboda fuskar ki tana da matuƙar kyau.
Sai tace "to gaskiya bayan tafiyarka na sanar da yayana duk abun da ya faru a tsakanina da kai wanda hakan yasa yai dariya haɗe da cewa "nasan abokina bazai taɓa ɗaukar hotanki da wata mummunar manufa ba domin zata iya yiwuwa ya ɗauki hotanki ne kawai saboda yaga kinyi mai.
Sannan yayan nawa ya sanar dani cewar "wallahi idan har ki samu Abdul a matsayin wanda yake son ki to na tabbata tun a soyayyarku zaki gane cewa zaki samu ingantacciyar kulawa saboda na yadda da Abdul ɗari bida ɗari domin shine sular canza mummunar halayyar daku sani a tattare da ni.
Duk wani abun da zakiga ina aikatawa na mutunci ko Alkhairi haɗe da sakin fuskata ga kowa shine sular ɗorani a waɗannan hanyoyin.
Sannan a ƙarshe sai ya shawarceni akan ta hanyar cewa "ki dage domin ki samu soyayyar Abdul domin hakan babbar nasarace a gareki.
Jin irin yabon da yayana yayi a gareka ne yasa nan take naji hawaye ya zubo daga idanuna.
To amma kuma sai na kasa gane shin hawayen nadamar abun da na aikatama ne ko kuma hawayen son kasancewa a tare dakaine.
Dan Allah ko zaka iya sanar dani dalilin zubar hawayen daga fuskata.
Buɗar bakina sai nace "Ni a tawa fahimtar kin zubar da hawaye ne domin buƙatar zukatanmu su kasance a tare da juna.
Cikin yanayin murmushi tace "to sai dai kuma ban san ko taka zuciyar zata iya amincewa domin ƙulla alaƙa da zuciyar da bata san hanyar da akebi domin dasa soyayya a tsakanin zukata biyu ba?
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "idan kiba ɗayar zuciyar dama zata iya janki zuwa birnin masoya domin karantar dake kokai a game da al'amarin da ya shafi soyayya.
Sai tayi dariya haɗe da cewa to na bata dama.
Tun daga wannan lokacin sai soyayya ta shiga tsakanina da husna har a kaiga tsayar da ranar auranmu.
Ana irin saura wata ɗaya da wasu kwanaki bikin aurena da husna.
Misalin ƙarfe 9:30 na dare a yayin da nake kwance a ɗakina sai naji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakina.
Koda ma buɗe ƙofar sai naga anti sadiya tsaye a ƙofar ɗakin nawa ga kuma Ameera zaune a falo.
Buɗar bakin anti sadiya sai tace "ameera ce take son magana da kai.
Nan take naji ƙirjina ya buga wanda hakan yasa naji a jikina cewar akwai matsala.
Koda naga Ameera ta kasa buɗa baki domin sanar dani abun da yake tafe da ita.
Sai nayi murmushi haɗe da cewa "me yake faruwa naga kinyi shiru, kodai mu fita waje ne?
Sai ta kalleni haɗe da cewa "muje wajan saboda maganar da nake tafe da ita mushimmiyace.
Da fitowarmu sai mu samu waje mu zauna a compound ɗin gidanmu.
Haka Ameera ta kalleni fuskarta cike da damuwa haɗe da cewa "ɗazu ne ina kwance a ɗakina da rana sai nayi mafarkin na samu ciki ba tare da nayi aure ba.
Sai naji tsoron kar na shiga wani hali musamman a yayin da iyayena su gano cewar ina ɗauke da ciki wanda hakan yasa nayi tafiyayya domin zuwa asibitin da za'a zubar min dashi.
Ina cikin tafiya a hanya sai na haɗu da wani mutun.
Bayan ya tsayar dani sai ya gargaɗini ta hanyar cewa "karki kuskura ki zubar da cikin da kike ɗauke dashi idan ba hakaba to mutuwa zakiyi.
Bayan na farka daga baccin a tsorace sai nayi wasu ƴan addu'o'i sannan na fito daga ɗakin.
Jim kaɗan kuma bayan naci abinci sai naji zuciyata tana tashi wanda hakan yasa na shiga toilet nayi aman ba tare da mahaifiyata ko maihaifina sun sani ba domin kai kaɗai ne nake tunanin cewar zaka iya taimakamin wajan samamin mafita ba tare da kowa ya sani ba.
Buɗar bakina sai nace "to amma a garin ya ai ki bari haka ta faru dake.
Koda ta ɗago kai ta kalleni sai tace "tun da nake a rayuwata ba wani ɗa namijin da ya taɓa kusantata kawai ni dai ina tsoran kar wannan mafarkin nawa ya zama gaske kamar yadda sukata da wuƙa ya kasance a zahiri.
Buɗar bakina a yayin da na kalleta sai nace "kina nufin sukarki da wuƙar da ayi a watannin da su wuce kinga hakan a mafarki sannan ya faru dake a zahiri?
Sai tace "kwarai kuwa domin nashayin munanan mafarkai kuma kaine mai cetona a munanan mafarkan da nakeyi.
Jin hakane yasa na sanar da ita cewar "to indai haka ne bana cire tsammanin samuwar ciki a tattare dake kuma wannan ba aikin kowa bane face aikin aljanu.
Nan take na kalleta haɗe da cewa"duk da cewar ɗaya daga cikin abokaina ya gargaɗeni akan cewar karna sanar da kowa sirrin da yake a tsakanina dashi hakan bazai hanani fayyace miki gaskiyar yadda ai wannan matsalar ta samo asali ba.
Nan take na shiga bata labari kamar haka.....
Koda na kalleta sai nace "maganar gaskiya ameera na daɗe da kamuwa da haƙiƙanin sonki.
To amma kuma a wannan lokacin sai na kasa samun ƙwarin Guiwarr tunkararki domin sanar dake soyayyar dake zuciyata har a samu akasin da mahaifinki yasa na dakeki da socket abisa kuskuran da ya faru a tsakaninmu.
A dalilin wannan kuskuran ne yasa naji cewar ba yadda zavi na iya samun soyayyarki.
Kwatsam sai yawo ya kaimu dajin da ke kusa da wannan garin namu wanda hakan ya kaini ga tsuntar wani littafi.......
Haka dai itama na fayyace mata komai har izuwa lokacin da'a soketa da wuƙa.
Sannan na kalleta haɗe da cewa "kuskuran da'a samu har kema ki shiga wannan matsalar shine, sunanki ɗin da na ambata ne yasa kema ki shiga wannan matsalar saboda banyi tunanin cutar dake za'ayi ba domin nayi tunanin taimakamin zasuyi wajan ganin cewar na samu nasarar samun soyayyarki.
Dan haka cikin da kiyi mafarkin cewar kin samu bana raba ɗayan biyu akwaishi a tattare daki.
Amma dan....
Sai ta dakatar dani ta hanyar rufe bakina da hannunta haɗe da cewa "A'a karka bani haƙuri domin baka aikata laifin komai ba, kawai ni dai a halin yanzu mafita nake nema.
Buɗar bakina sai nace "mafita ɗaya ce zata hana tonuwar wannan sirrin saboda zubar da cikin zai iya haifar da sanadin rasa rayuwarki kamar yadda ki gani a mafarkin da kiyi.
Haka ta ɗago kai ta kalleni idanunta cike da ƙwalla haɗe da cewa "mecece mafitar?
Sai nayi shiru na ɗan wani lokaci, zuwacan sai na kalleta haɗe da cewa mafitar itace "aure a tsakanin ni dake.
Kuma gashi ansa ranar aurena da Husna ƴar garin Abuja, saboda haka hanya ɗaya ce zata iya sawa aurena dake ya samu yiwuwa cikin gaggawa ba tare da kowa yasan halin da muke ciki ba?
Buɗar bakinta a yayin da ta kalleni sai tace "wace hanya ce?
Koda na kalleta sai nace "zuwa gobe da safe ki shigar da ƙarata zuwa kotu wanda hakan zai baki damar sanar da kotu cewar yau dararki nayi a game da batun soyayya a matsayin waɗanda su kwashi tsawon shekaru 3 suna soyayya.
Sannan sai ki sanar da kotu cewar "muddun nayi kuskuran auran wata mace ba ke ba to ba makawa sai kin kashe wadda na aura sannan sai kin bankawa gidana haɗe da na iyayena wuta.
Sannan kuma karki sake wani ko wasu su nemi baki haƙuri har zuciyarki tayi sanyi kawai ki turken akan lallai sai na aureki.
Bayan Ameera ta gabatar dani a kotu sai ta bi wannan tsarin da na ɗorata a kai.
Ganin yadda ameera ta turje ne yasa bamu rabu a kotun ba har saida alƙali ya ba iyayena haɗe da iyayan Ameera umarnin ɗaura mana aure a cikin sati ɗaya.
Bayan aurena da Ameera, kwatsam bayan wata safiyar asabar sai a kirani da wata baƙuwar number.
Koda na amsa kiran sai naji muryar mace "bayan mun gaisa sai tace "na fito waje tana son ganina.
Fitowata waje kenan sai nayi idon biyu da aljana A'isha tsaye a ƙofar gidan da nake zaune da Ameera.
Ban wani ji tsoro ba haka na ƙarasa gareta bayan mun gaisa.
Sai tace "tabbas na yaba da ƙoƙarinka domin haka ne yasa na dawo gareka domin sanar da kai cewar ba yadda za'ai ka samu kwanciyar hankali muddun ba mayar masu da littafinsu kayi ba saboda wanda ka mayar tare da abokinka ba komai a cikinsa.
Nan take ta bani wani littafin haɗe da cewa "wannan shine asalin littafinsu domin ni na tafi dashi.
Dan haka zuwa gobe kayi gaggawar mayar masu da kayansu wanda hakan zai samar da kwanciyar hankali a tsakaninka da matarka haɗe da sauran danginka.
Har ta juya zata tafi sai nace "amma dan Allah idan bazaki damu ba ko zaki iya sanar dani yadda ai ameera ta samu ciki?
Jin haka ne yasa A'isha ta matso daf dani haɗe da cewa "idan baka manta ba ka taɓa yin mafarkin ka auri ameera har ku haifi ƴaƴa biyu a mafarkin da kayi?
Sai nace "kwarai kuwa ban manta ba domin ba yadda zai na iya mantawa da wannan mafarkin.
Sai tace "to bayan yayarka ta tasheka daga bacci a wane yanayi ka samu sutturar da kake sanye dasu?
Cikin yanayin kunya nace "tabbas naga kayan da nake sanye dasu sun ɓaci da ƙazanta.
Sai A'isha tace "to da wannan ƙazantar aljanun da littafinsu suke hannunka suyi amfani wajan sa matashi a mahaifarta wanda hakan ya bata damar samun ciki domin ba wani abu ne yasa su soketa da wuƙa ba illah buƙatar samata ƙazantar da ka fitar a mahaifarta.
Bayan na karɓi littafin washe gari da sassafe na ɗauki hanyar mayar da littafin ni kaɗai.
Bayan kimanin watanni 2 da faruwar wannan al'amarin sai Ameera ta shawarceni akan cewar "na auri husuna saboda tana matuƙar jin tsoran zama a gida ita kaɗai musamman idan na tafi wajan aiki.
Kimanin watanni 6 da aurena da husna sai Ameera ta haifi ɗa namiji.
Alhamdulillah.
The End
0 comments:
Post a Comment