soja mutun ne mai dakakkiyar zuciya wanda yake tafiyar da rayuwarsa cikin kwarin gwuiwa.
Soja shine wanda yake rabuwa da; Mahaifiyarsa, mahaifinsa, Matarsa, Ƴaƴansa, ƙannanshj ko yayyunsa haɗe da sauran danginsa.
Sannan shine wanda yake miƙa jikinsa domin bashi horo mai tsanani koda zai rasa ransa ne bazai taɓa nuna gazawarsa ba.
Soja shine wanda yake shiga surƙuƙun daji ko tsaunuka domin kare ƙasarsa haɗe da al'umar dake cikinta daga azzaluman mutane ko wata halittar dake shirin haifar da tashin hankali ko damuwa ga al'umar dake cikin ƙasarsa.
Cikakken soja shine wanda ba ruwanshi da ƙabilanci ko wariyar launin fata, mai aiki dan Allah aduk halin da zai tsunci kansa.
Allah kasa mu dace ka kuma kare mana ƙasarmu da al'umar dake cikinta.
0 comments:
Post a Comment