life story
Magana ta gaskiya kyakkawar mace tayi.
Kashe mata kuɗi nake kamar ba gobe.
Banajin ɗuriyar kowa idan ba tata ba, ban sani ba ashe itace zata zamto sular ɗaureni na tsawon shekaru 25.
Bari kuji yadda labarin ya samo asali.......
""Wata ranace wadda bazan iya tunawa da sunan ranar ba.
Nafito daga gida, ranar ba wata damuwa a tattare dani balle ayi batun ƙunci.
Tafiya nake nima kai na bansan inda na dosa ba.
Na tsallaka titi kenan sai Allah ya kai idona kan wata haɗaɗɗiyar baby girl a yayin da take tsaye a kusa da wani restaurant.
Kallanta kawai nake ba tare da ta ankare da cewar idona a gareta yake ba.
Ji nayi kafata ta gurɗe a yayin dana taka wani totan masara wanda hakan ya kaini ga neman faɗuwa.
A yayin da idonta yazo gareni sai ji nayi tace "ayyah, sorry! Sannu.
Cikin yanayin mutuntawa na amsa ta hanyar cewa "yauwa nagode sannan naci gaba da tafiyata.
Har nasha kwana sai naji zuciyata ta ɗarsamin wani abun da nima kaina bansan me hakan ke nufiba.
Cikin gaggawa na juyo domin zuwa gareta.
Sai kuma nayi sa'a a yayin dana juyo domin zuwa gareta sai naga itama tasa kai domin tunkarar inda dare ya mata.
Haka naita bin bayanta kamar wani raƙumi da akala.
Allah cikin ikonsa bata tsaya ko inaba kuma bata hau wani abun hawaba har Allah yasa ta isa gida.
Duk da hakan dai ban tabbatar da cewar gudansu ta shiga ba har sai da na tambayi wani yaro ta hanyar cewa "kai wannan da ta shiga nan gidan meye sunanta?
Buɗar bakin yaron sai yace "Sunanta ZARAH amma bakuwace.
Bayan na koma gida sai tunanin zarah ya hanani sakewa badan komai ba sai dan kyawun surar da Allah ya mata.
Duk da cewar akwai tazara a tsakanin unguwar da zarah tazo da tamu unguwar hakan bai hanani kutsa kai na a gareta ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci har mu zama abokan juna ita kawata ni kuma abokinta.
Sakin jikin da zarah tayi dani ne ya bani damar cusa mata sha'awar son zama a garin bauchi domin tayi karatu.
Ranar monday itace ranar dana fara fita yawo tare da zarah.
Bayan mun dawo daga yawo a yayin da zata shiga gida sai naga tayimin kalar kallan nan da akewa lakabi da kallon maraici,
Wanda hakan yasani murmushi hade da cewa zarah ya naga kamar akwai wata yar damuwa a tattare dake?
Buɗar bakinta sai tace "kawai ina tunanin ranar rabuwarmu ne, saboda jibi zan koma gida wato kaduna kenan.
Sai nace "to amma zarah mezai hana ki roƙo abbanki domin ya nema miki admission a wannan garin namu saboda na fahimci kamar kinason zaman garin?
Ban sani ba ashe wannan shawarar danaba zarah ta ratsa zuciyarta.
Haka zarah ta matsantawa abbanta ta hanyar roƙonshi haɗe da bayyana tsantsar shagwaɓarta a gareshi domin yabarta tayi karatu a bauchi.
Sai kuwa zarah tayi sa'a mahaifinta ya amince da buƙatar da ta tunkareshi da ita.
Kwatsam rannan ina gida sai zarah tayi calling dina a waya.
Koda na amsa kiran bayan mungaisa, Sai take sanar dani cewar "burinta dai ya cika domin abbanta ya amince game da batun karatunta a jahar bauchi.
Zumbur na tashi zaune har hakan ya haifar da furgici ga yayata.
Buɗar bakina sai nace "zarah wace irin gudun mawa kike buƙata a gareni, game da zamanki a wannan jahar tamu?
Sai tace "kulawa haɗe da kyautatawa.
Cikin yanayin kwarin guiwa nace "Zan kula dake fiye da tunaninki.
Zan kuma kyautata miki fiye da hangen kowa.
Tun daga wannan ranar sai na zage dantse a fagen kulawa da zarah haɗe da kyautata mata.
•Sutturar zarah nine.
•Zarah batacin duk wani nau'in abincin da bai kwanta mata a rai ba, domin wurare da dama nake kai ta domin ta zaɓi kalar abincin da takesonci.
•Duk wanda ya nemi haifar da furgici ko ɓacin rai ga zarah tofa sai inda karfina ya ƙare.
•Suttura kalakala nake sai mata badan komaiba sai dan na faranta ranta.
•Ina kaita gidanmu aduk lokacin da ta buƙaci zuwa, wanda hakan yasa ahalina suyi matuƙar shaƙuwa da ita.
To amma kuma har kawo wannan lokacin na kasa bayyana soyayyata ga zarah.
Haka dai naci gaba da kyautata mata ba tare da nuna gajiyawa ba.
Kwatsam rannan sai naga abun da yai matuƙar ƙonamin rai a game da zarah.
Haƙiƙa ba kowane saurayine zai juri ganin wani a tare da wadda yakeso ba.
A yayin da nayi ido biyu da zarah zaune da wani suna fira ba kaɗan rai na ya ɓaci ba.
Haka dai na danne ɓacin ran dake cimin rai ta hanyar miƙawa saurayin nata hannu domin gaisawa.
Cikin yanayin shauƙi zarah ta gabatar dani ga saurayin nata a matsayin abokinta.
Sannan ta gabatar dashi a gareni a matsayin saurayinta, kuma muradin ranta.
Tun daga wannan lokacin gaba ɗaya duniyata ta sauya daga farin ciki zuwa baƙin ciki wanda hakan yasa na yanke shawarar haƙura da Zarah ta hanyar nisanta kai na a gareta.
To amma sai dai kuma na kasa gane cewar shin zarah yaudarata tayi ko kuma laifinane.
Haka dai nayita faman damun kai na da ƴan tunane-tunane a ƙarshema sai na yanke shawarar keta haddinta ta hanyar kwantawa da ita domin huce takaicina.
Buƙatar cika wannan muradin nawa ne yasa na ƙara take totir ɗin kyautata mata badan komai ba sai dan buƙatar ɓata tarbiyarta.
=> 2
A yayin dana sanar da wani abokina duk abun da ya faru a tsakanina da zarah wanda hakan yasa na ɗauki alwashin ɓata tarbiyyarta ko kaɗan bai bani goyan baya ba.
Haka ya nemi shawo kai na ta hanyar bani haƙuri haɗe da cewa abun duniya ba wani abune mai tasiri ba.
Kuma karka manta kana da ƙanne mata idan ma baka dasu to kana da yayyu mata.
Suma idan baka dasu kanada yan uwa.
Sannan kuma karka manta zakayi aure kahaifi yara.
Kuma na tabbata a waɗannan dana lissafi bazaka taɓason makamancin abun da kake shirin aikatawa ya faru da ɗaya daga cikinsu ba.
Amma duk da irin shawarar da abokin nawa ya bani baisa na janye wannan ƙudirin nawa ba.
Kafin faruwar wannan al'amarin bana taɓa iya kai hannuna zuwaga jikin zarah.
Amma a yayin dana duƙufa wajan ganin na ɓata tarbiyyarta nine hada riƙe hannunta.
Gaba-gaba dai har mu fara rungumar juna wanda hakan yasa na fara ɗaukar wasu matan a matsayin masu ƙarancin tunani.
Ban sani ba ashe zarah kar take kallona.
Haka nayi iya bakin ƙoƙarina domin cika wannan muradin nawa amma abun yaci tura.
Duk wani tarkon da zan kafawa zarah cikin ƙanƙanin lokaci take tsallakeshi.
Kwatsam rannan sai zarah ta fito fili domin sanar dani cewar itafa ba marar tunani bace kamar yadda nake ɗaukar kai na a matsayin marar hangen nesa.
Cikin yanayin mamaki nace zarah banfahimci mekike nufi da wannan kalamin ba.
Buɗar bakin Zarah sai tace "tun daga lokacin daka buƙaci kai ni ɗakin abokinka na fahimci akwai mummunan ƙudirin da kakeson zartarwa a gareni.
Koda naji wannan furucin daga bakinta sai nace "to amma zarah ai nasha kai ki ɗakunan abokai na haɗe da ɗakina kuma kin fita lafiya ba tare da wani abu ya faru dake ba.
me zai sa ki haifar da zargi a tsakanin zuciyarki da tawa zuciyar a yayin dana buƙaci kai ki ɗakin abokina, kuma ai a lokacin cemiki nayi kizo muje ki rakani domin duba lafiyar abokin nawa saboda a lokacin yana fama da rashin lafiya ne.
Murmushi naga tayi haɗe da cewa "Abdul kenan, karkayi mamakin yadda ayi nagane cewar akwai ƙudirin da kakeson cimmawa a gareni.
saboda akwai wani sirrin da kowace mace take tattare dashi sai dai kuma ba kowace mace bace take iya saurin fahimtar wannan surrin.
Sannan ta ƙara da cewa "a wannan lokacin yanayin kallon da naga kana yimin haɗe da sauran wasu muhimman al'amuran dana gani a tattare dakai waɗanda bai dace nasanar dakaisu ba, sune su bani tabbacin cewar ba abun arziƙi kakeson zartarwa a gareni ba.
Haƙiƙa nasha binka zuwa wurare da dama domin har ɗakinka kasha kai ni ba tare da fargabar komai ba saboda a wadannan lokutan banga alamun cutarwa a tattare da kai ba.
Na buɗa baki zanyi magana sai ta dakatar dani ta hanyar cewa karka sake ka nemi kawo inkari a game da maganata.
Cikin yanayin nuna damuwa tace "Abdul ka kyautatamin fiye da yadda nake tunanin samun kulawarka.
Ka kula dani kamar yadda nake tunanin samun kulawa daga wajan iyayena.
Ina gabatar da dukkanin wata buƙatata a gareka ba tare da fargabar komai ba.
Duk da cewar Ina da dangi a wannan garin naku hakan baisa ka barni da yunwa ba.
Kana iya bakin ƙoƙarin ka wajan ƙawatani da sutturu kala-kala.
Kana kai ni duk inda na buƙaci zuwa ba tare da nuna gajiyawa ba.
A zamantakewata da kai ban kasance a ƙunci ko damuwa ba domin kai ne mai ƙoƙarin farantamin rai a duk lokacin da wata damuwa ta nemi halartar zuciyata.
Ban tashi aune ba sai ganin hawaye nayi daga idanun zarah cikin yanayin kuka tace "me yasa zaka boye buƙatar ka a gareni, meyasa bazaka fito fili ka sanar dani cewar kana buƙatar kadaituwa dani ba?
Sannan ta kalleni tace "Abdul a shirye nake wajan mallakama dukkanin wani abun da kake buƙata a gareni.
Buɗar bakina sai nace "tabbas maganarki gaskiyace domin a wannan ranar buƙatata itace na kwanta dake domin da ace kin amince da batun zuwa ɗakin abokina umar to da tuni komai ya faru a tsakanina dake.
Share hawayen dake fuskarta naga tayi haɗe da cewa "to wane laifin na aikata a gareka dahar kakeson kwantawa dani?
Yanzu idan kasamu labarin wani yana shirin aikata kalar abun da kake son aikatawa dani ga ƙanwarka wane irin ɓacin rai zakaji?
Meye amfanin aikata abun da zai kasance danasani ga rayuwarka tun a nan duniya har izuwa lahira?
Sannan tace "nasamu kulawar da bazan iya mantawa da itaba a gareka.
Ba wani abune yasa kaga na zubar da hawayena haɗe da zayyanoma irin kulawar dana samu a zamana dakai ba, sai dan buƙatar fito da gaskiyar mummunan ƙudirin dake tattare da zuciyarka.
Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci kafito da iskancinka haɗe da rashin kunyarka a fili.
Cikin yanayin nadama nace "zarah nasan na aikata kuskure amma ki yafemin kuma ki aminta dani a matsayin saurayinki saboda tun farkon ganina dake naji cewar sonki ya shiga rai na.
Buɗar bakinta sai tace "ai duk wata kimarka a gareni tagama zubewa tun da har kakeson tozartani ta hanyar zubar da mutuncina haɗe dana iyayena.
sannan ta ƙara da cewa "idan da ace son gaskiya kakemin da tun a farkon zuwanka gareni ya kamata ka gabatar da soyayyarka a gareni.
Sannan ta lalle i tace "Abdul wannan itace rana ta farko kuma ta ƙarshe dazan gargaɗeka akan cewar "karka sake ƙoƙarin alaƙanta kanka dani balle har ka kawo kanka gareni.
Jim kaɗan da tafiyarta sai na tura mata da text message kamar haka.
"""Gazawarki wajan ƙin karbar soyayyata tamkar nisanta kanki da muhimman takaddun da kike buƙatar mallaka a school ɗin da kike karatu ne.
Tun daga wannan lokacin sai saɓani ya shiga tsakaninmu idan na kirata a waya bata amsawa a ƙarshema in
Idan na kira numbarta ba ta shiga.
Idan na haɗu da ita a hanya ba ta sakarmin fuska balle ayi batun magana.
Koda na fahimci suna gaf da fara exam ɗin ƙarshen fita daga jami'a kawai sai na yanke shawarar tunkarar school ɗin da zarah take karatu domin bin hanyoyin dasu dace wajan dagula mata lissafi.
Haka na fitar da kuɗi masu tsoka domin cusa baƙi ciki a zuciyar zarah.
Bayan wani lokaci ayayin da takaddun karatun zarah su isa gareta sai ranta yai matuƙar ɓaci.
Kwatsam rannan da yamma Ina kwance a gida ranar banje ko inaba sai jin kukan zarah nayi ayayin da ta shigo gidanmu.
Fitowar da zanyi sai kuwa nayi arba da mahaifina ayayin da shima ya fito daga ɗaki.
Buɗar bakin zarah a yayin da tayi ido biyu da abbana sai tace "abba danka azzalumine.
Jinjina kai naga abbana yayi haɗe da cewa kwarai kuwa nima nasan da haka amma me ya faru a tsakaninku?
=> 3
Durƙusawa har kasa zarah tayi tana kuka haɗe da cewa "Dan Allah abba kayi haƙuri domin ko kaɗan banso sawoka a wannan matsalar da Abdul ya cusani a ciki ba.
Haka zarah ta kalli mahaifina tace "abba Abdul yasa an ɓatamin takadduna shaidar karatun da nayi.
Cikin gaggawa nayi ƙoƙarin taka mata burki ta hanyar cewa "yanzu duk irin kulawar dana baki ki rasa abun da zaki sakamin dashi sai sharri haɗe da ƙazafi?
Sannan na Kara da cewa "me na taɓa samu a gareki wanda ya danganci kyautatawa?
Abu ɗaya nasan na roƙeki itace soyayya Amma hanani kiyi haka ki damƙa zuciyarki ga wani wawa can.
Cikin yanayin ɓacin rai zarah tace "karka sake alakanta wanda nakeso da kalmar data danganci ɓatanci.
Domin kyautatawar da nayima ban samu kwatankwacinta a gareka ba.
Kai ne sular lalacewar karatuna tun a level 1.
Cikin yanayin dakewa nace "idan harke ba munafuka bace zanso kiyimin bayanin yadda ayi na zamto sular lalacewar karatunki?
Buɗar bakin zarah sai tace "idan baka mantaba a yayin da nake gaf da shiga level 2.
Ka taɓa zuwa dani nan gidan har mahaifiyarka tayima faɗa akan cewar ka fita yawo da motar abbanka ba tare daka nemi izinin ɗaukar motar ba.
Yanayin faɗan da ka tasarwa mahaifiyar taka a lokacin da takema faɗane yasa ranta yai matuƙar ɓaci wanda hakan yai sular tasowar larurar dake damunta.
Tun daga wannan lokacin naji gaba ɗaya na tsani kai na dahar na bari wata alaƙa ta shiga tsakanina da kai badan komaiba sai dan irin kunyatini ɗin da kayi a gaban mahaifiyarka saboda duk ɗan kirki bai dace ya rika yiwa mahaifiyarshi irin faɗan da kayi mata ba.
Fitarka daga gidan kenan sai nima na fito.
Fitowata kenan sai na tuna da cewar na manta wayata a kujerar danazauna.
Komawata kenan sai na taradda mahaifiyarka kwance a ƙasa wanda hakan yasa nayi tunanin hawan jinine ya kayar da ita.
Gudun kar a zargeni game da abun dake Shirin faruwa da mahaifiyarkane yasa nayi ƙoƙarin gaggawar barin gidan.
Sai kuma zuciyata ta shawarceni akan cewar bai dace nabar yar uwata musulma a wannan yanayin ba.
Cikin gaggawa na ɗakko key ɗin motar daka dawo da ita domin kai ta asibiti.
Da zuwanmu asibitin tun kafin a fara duba lafiyarta nayi ƙoƙarin kiran numbarka amma numbar taƙi shiga.
Gudun kar wani zargi ya hau kai na ayayin da likitocin da suke duba mahaifiyarka su kasa ceto rayuwartane yasa na sanar dasu cewar babu sanayya a tsakanina da mahaifiyar taka domin a hanyata ta dawowa daga school na haɗu da ita a wannan yanayin.
Buɗar bakin likitan sai yace "to magana ta gaskiya taimakon da kiyi yayi dai-dai saboda haka akeson kowane dan adam ya kasance mai taimako haɗe da tausayawa.
To amma kuma wannan zamanin namu ya riga ya canza wasu muhimman sharuddan da addininmu na musulunci yazo dasu.
Wasu daga taimako za'a ruftasu a komarda fitarsu sai yadda Allah yaso.
Shiru naga yayi na ɗan wani lokaci zuwacan sai yace "to yanzu ke yar nan garince?
Sai nace "A'a ni yar garin kadunace karatune ya kawoni wannan jahar.
Sai yace "babu damuwa zaki iya tafiya inyaso zuwa anjima sai ki dawo domin duba lafiyarta.
Duk da hakan dai ban tafiba har saida na ɗauki tsawon awa 1 da rabi 30 a asibitin.
A yayin da naga alamun mahaifiyarka ta fara samun sauƙi.
Banbar asibitin ba har sai da na biya kuɗin maganin da ayiwa mahaifiyarka.
Sannan na damka key ɗin motar a hannun likitan a wannan lokacin ne likitan ya karbi numbata nima na karɓi tashi numbar.
Kimanin 30 minutes da barina asibitin sai likitan ya kirani a waya domin sanar dani cewar "Allah yayima wadda nakai asibin rasuwa wato ita mahaifiyar taka kenan.
A hanyata ta dawowa zuwa asibitin sai na haɗu da wasu yan iskan gari su kwace wayata haɗe da kuɗin da abbana ya bani domin biyan kuɗin exam ɗin da zamu fara alokacin.
Haka likitan ya haɗa report ɗin ƙarya domin kareni daga zargin abun da zai iya ƙuntatamin ta hanyar sanar daku cewar "ita mahaifiyar takace takai kanta asibitin domin ceton rayuwarta.
Amma duk da irin babban rashin da kayi baisa naga alamun wata shiryuwa a tattare da kai ba haka ka riƙa bijiromin da wasu al'amuran dasu riƙa ɗauremin kai wanda har hakan yasa na fara nazarin janye kaina a gareka.
To amma kuma a wannan lokacin sai na hangi cewar idan na janye kai na a gareka bansan inda zan samu kuɗin dazan biya jarabawar da zamuyi ba saboda iyayena ba wasu masu ƙarfi bane kuma tunkararsu da buƙatar wasu kuɗin ba ƙaramar matsala zai haifarmin ba, domin kai ne sular zamana a wannan jahar kuma ka ɗauki alwashin kyautatamin haɗe da bani kulawa.
A yayin dana bijiroma da buƙatar waɗannan kuɗin har kimanin 75 thousands cewa kayi "zaka bani amma sai mundawo daga inda kakeson na rakaka.
A lokacin daka sanar dani inda kakeson na rakaka gaba ɗaya sai naji rashin yarda ya shiga zuciyata.
Haka zarah ta kalli mahaifina haɗe da cewa "abba danka so yake ya kwanta dani.
Saboda naƙi amincewa da wannan haramtacciyar buƙatar tashine yasa a ɓatamin takadduna.
Burina baiwuce nayi karatu na samu aikin da zan iya kyautatawa ahalina ba domin kare mutuncinsu haɗe da nawa mutuncin sai gashi lokaci ɗaya ɗanka ya haramtamin wannan mafarkin nawa.
Jin haka ne yasa mahaifina yasa a fito ma Zarah da ainashin takaddun shaidar kammala karatun ta.
Sannan ya ƙara mata da kuɗi har kimanin miliyan 3.
Tun daga wannan lokacin na kkkudiri niyar hana zarah sakewa wanda hakan yasa na shiga yima samarin ta ɗauki ɗai-ɗai.
Duk saurayin da zai ɓullo da ƙudirin auren zarah to ba makawa sai naga bayanshi.
A ranar da mahaifina ya gano cewar ni nake aikata kisan kai ga samarin zarah ya gabatar da kanshi a matsayin wanda yakeson auran zarah.
Bayan mahaifina ya samu nasarar auran zarah sai kuma yasa a kamani kai tsaye a wuce dani gidan yari ba tare da an gabatar dani a kotu ko hannun ƴan sanda ba.
Sai da na ɗauki tsawon shekaru 25 tsare a gidan yari sannan mahaifina yasa a fito dani.
Bayan mahaifina yasa an fito dani sai ya buɗemin wani katafare shagon saida shaddoji da atamfofi, sannan ya gargaɗeni akan cewar karna sake shiga gidanshi kar kuma na sake alaƙanta kaina a gareshi domin yayi hand over dani.
Tun daga wannan lokacin sai na gane cewar na aikata laifi mafi muni a rayuwata wanda hakan yasa na dage da riƙon Allah domin ya sassauta azabar da zaiyimin a rana gobe ƙiyama.
THE END
0 comments:
Post a Comment