Idan ka koyar da mace darasin abu 5 to
Zaka iya lanƙwasa zuciyarta duk ta yadda
kaga dama.
1 haƙuri.
2 tausayi.
3 tawakali.
4 riƙo da addini.
5 muhimmancin riƙe alƙawarin.
KAR KA KASANCE MAI YAWAN KWAƊAYIN ABUN HANNUN MATARKA
Wai shin ko kasan kwaɗayin abun hannun
Macen da kake tarayya da ita yana haifar
da matsaloli 3.
1 wulaƙanci.
2 rashin yadda.
3 zaka kasance marar daraja a gareta.
ABU 3 ZASU IYA BAKI DAMAR LANƘWASA ZUCIYAR WANDA KIKE TARAYYA DASHI
Ko kinsan abu 3 zasu iya baki damar lanƙwasa
zuciyar wanda kike tarayya dashi?
1 haƙuri.
2 ladabi.
3 biyayya.
KA KASANCE MAI ADALCI
Idan ka tsaya kayi tunanin cewar kaine
sular nisanta wadda ka aura da Mahaifiyarta
Mahaifinta haɗe da sauran danginta wannan
kaɗai ya isa yasa kaji tausayinta haɗe da
yi mata uziri a game da kurakuran da take
aikatawa a gareka.
RASHIN LAFIYAR MATARKA
Aduk lokacin da ya kasance
matarke bata da lafiya to a wann
Likacin tana bukatar muhimmiyar
Kulawarka.
Kayi kokari ka bata kulawarka
Komai kankantar ta.
Mahaifinta ko mahaifiyarta hade
da sauran danginta basu da wata
muhimmiyar kulawar da zasu bata
Wadda tafi kulawarka a gareta.....
KA KASANCE MAI HAƘURI
Ya kai ɗan uwana ka kasance mai
haƙuri da juriya a game da
dukkanin wani ɓacin ran da zaka
riƙa fuskanta a game da macen da
kake tarayya da ita, saboda ako
wane lokaci ita mace mai buƙatar
uzirice.
KI KASANCE MAI KULAWA
Yake yar uwata ko kinsan cewar
mafi yawancin lokuta kulawarki
kaɗan take yiwa mijinki, kawai
yana bayyana murmushinsa a
gareki ne domin boye damuwarsa.
KAR KA KASANCE MAI SAURIN DLƊAUKAR MATAKI
Ya kai ɗan uwana a duk likacin da
matarka ta aikata laifi ko kuskure
a gareka, to kar kayi ƙoƙarin saurin ɗaukar
fansa a gareta kayi amfani da
tunaninka haɗe da hangen nesanka
wajan tausar zuciyarka saboda
mafi yawancin lokuta shaidan ne
yake ingiza matanmu wajan aikata
laifi a garemu.
KI KASANCE MAI GO DIYA
Rashin sanin muhimmanci
zamantakewar aure ne kesawa
mace ta kasa bayyana farin cikinta
haɗe da godiya ga mijinta musamman a
likacin da mijinta yai abun burgewa
a gareta.
HA'INCI
Wai shin ko kunsan ha'inci shine jigon duk
wani rikicin da ake samu a tsakanin
ma'aurata?
Ƙarya da Yaudara haɗe da Zalunci basu da
Wani tushen da ya wuce ha'inci.
KARKI KASANCE MAI HA'INTAR MIJINKI
Karki kasance mai ha'intar mijinki a game
da kuɗi ko kayan abinci.
Idan ya kyautata miki ki kasance mai
godiya a gareshi domin zata iya yiwuwa
shima a cikin wani ƙangi yake.
KAR KA RIKA SA MATARKA YAWAN ZUBAR DA HAWAYE
Kar ka bari halayyar matarka ya riƙa ingiza
zuciyar ka wajan yawan sata zubar da
hawaye, saboda su mata tamkar ƙananan
yaran da ake raino suke.
Idan ta tambayeka abu, muddun kana da
halin bata to ka bata.
Idan baka dashi to karka hauta da faɗa
domin idan kayi ƙoƙarin rarrashin ta to zata
haƙura.
KARKI KASANCE MAI GIRMAN KAI
A duk lokacin da kiga mijinki yai fushi a
game da wata yar matsalar da ta faru a
tsakaninku.
To ki cire girman kai ki durƙusa
har ƙasa haɗe da dafa cinyarshi ko kuma
ki zauna kusa dashi haɗe da dafa kafaɗarshi
sannan kice dan Allah kayi haƙuri a game
da abun da ya faru.
Ina mai tabbatar miki cewar hakan zai
taimaka wajan ƙara shigar dake a zuciyarsa
sannan kuma zai rage yawan faɗan da yake
miki.
KA KASANCE MAI RARRASHIN MATARKA
A duk lokacin da kaga matarka ta zubar da
hawaye a yayin da wata yar matsalar da ta
faru a tsakaninku koda itace bata da gaskiya
to ka cire girman kai ka rarrasheta muddun
kaga tayi murmushi ko ta saki fuskanta to
a wannan lokacin zataji sonka ya kara
shiga zuciyarta.
Saboda wata macen idan a ɓata mata
rai har ya kaiga ta zubar da hawaye to idan
kaga ta zauna ita kaɗai tai shiru to mafi
akasari sumfi yin tunanin abu biyu
1 tsohon saurayinta.
2 tunanin iyayenta.
KAR KA KASANCE MAI YAWAN SHIDIMA GA MACE
Kar ka kasance mai yiwa matarka shidimar
da bata cancanta ba kuma bata zama
wajibi a gareka ba, saboda a ƙoƙarin ka
sata a farin ciki zaka iya jefa kanka a
katafaren ƙunci da damuwa.
saboda mafi yawancin matan da ake yima
shidimar da bata cancanta ba sumfi
bijirowa mazajensu da bukatun banza da
wofi idan kuma baka biya masu ba kaima
kasan sauran.
KARKA RIƘA BARIN MATARKA A CIKIN DAMUWA
Yawancin mata suna amfani da yin shiru
wajen nuna damuwa. Ya kamata ka gane
duk lokacin da kaga yawan shirun matarka
ko budurwar ka yayi yawa, to tabbas
akwai abun da yake damunta.
Kar kace laifinta ne, meyasa bata fito
ta faɗa ba?! A'a ba haka ake mu'amala
da mace ba, Kamar yadda zakaga Jariri
yaita tsandara KUKA akasa fahimtar
abun da ke damunsa, to haka Mace take.
Meya kamata kayi? Tunda kasan Yin
shiru ba ɗabi'ar ta bane tun farko!
hakan ya nuna akwai abinda ke
damunta kenan,
A wannnan lokacin yana da kyau
kayi Amfani da Lafuza masu gamsar
da zuciya, idan matarka ce ka kama
hannunta ka jawo ta jikinka, kace wai
ya akayi ne naga duk kin canja?
Me a miki? Shin na ɓata miki rai ne?
kodai wanine ya taba min ke haka dai
zakayi amfani da kalamai
masu daɗi wajen shawo kanta.
a wannnan lokacin wata hawaye zatayi.
Wata murmushi zatayi.
Wata shiru zata ƙarayi.
Kada kayi fushi aduk halin da ta kasance.
Saboda ita kaɗai tasan irin daɗin da take ji a
wannan lokacin. saboda ta samu abunda
take so. wasu sunfi so a damu dasu a nuna
masu soyayya. Shiyasa suke kuka ko
babu abinda ayi musu. Kawai so suke
a lallashe su.
0 comments:
Post a Comment