Tuesday, August 13, 2024

ALƘAWARIN MACE compelet




=>1
new update

A duk lokacin da kaji mace ta ɗauki alwashin aikata mummunan abu a gareka to kar ka sake ka nemi jayayya da ita, kawai ka nemi tsari a tsakaninka da ita daga wajan mahaliccinmu saboda KAIDIN mace yafi ƙarfin tunanin wanda bai san wacece mace ba.
A wannan labarin ne zakuji yadda mace ta ɗauki alwashi aikata wani mummunan al'amari kuma ta aikata

__Misalin 12 na dare nahau online domin duba comment ɗin da members dina suyimin a dangane da labaran da nake bayarwa a group ɗina mai suna KOTUN MASOYA.
Bayan na gama yan dube-dubena zan sauka kenan sai naga message ya shigo.
Koda na duba sai naga ai macece tamin magana domin Zainab Zee nagani a user name dinta amma batasa hoto ba.
Abun da tace shine "Slm har yanzu bakayi bacci ba?
Fuskata a sake nace "Wslm ai indai kiga na kwanta bacci sai zuwa karfe 1.
Murmushi tayi haɗe da cewa "kodai nazo na tayaka kwana ne?
Cikin yanayin mamaki nace "ban fahimci abun da kike nufi ba?
A wannan lokacin bamuyi maganar da takai 5 minutes ba sai ji nayi tace "kana sex chat??
Murmushi kawai nayi haɗe da cewa "ashe kema kina ɗaya daga cikin mutanan da suke tattare da ɗabi'un dabbobi?
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai tace "Da kasan wadda kake magana da ita na tabbata ba dalilin da zaisa kayi ƙoƙarin dangantani da dabbobi.
Raina a ɓace naja wani dogwan tsaki nace "Mutswwwww!! Kefa a cikin dabbobinma kinkai maƙura a cikin karnuka irin waɗanda suke haushi cikin dare ba gaira ba dalili.
Ban sani ba ashe wannan furucin yai matuƙar fusatata wanda hakan yasa ta ƙuduri niyar afkani a chakwakiya.
Buɗar bakinta sai tace "Ni kuma nayima alƙawarin wallahi sai ka kwanta dani a zahirin ba'a sex chat ba, kuma sai nasa an ɗaureka badan komai ba sai dan buƙatar lalata rayuwarka sannan ta sauka daga online.
Nan take nikuma nayi Remove and Block ɗinta.
A ƙalla an samu kimanin wata 6 da faruwar wannan al'amarin wanda hakan yasa gaba ɗaya na manta da abun da ya faru a tsakanina da ZAINAB ZEE.
A sanadin labaran da nake bayarwa a facebook da WhatsApp ne ya haɗani da mutane da dama domin bazan iya iyakance mutanan da suke bibiyar labarai na ba.
(Musa Ibrahim) yana ɗaya daga cikin masu bibiyar labaraina amma kwata-kwata da haduwata dashi bamu ɗauki tsawon wata biyu ba.
Ba ranar da zanhau online ba tare da nayi chatting da Musa Ibrahim ba.
Kwatsam wata ranar asabar da misalin ƙarfe 8 na safiyar litinin sai naji kira ya shigo wayata koda na amsa kiran bayan mun gaisa sai yace "kana magana da abokinka Musa Ibrahim a facebook na ɗauki numbarka domin na kiraka mu gaisa.
Bayan mun gaisa sai yace "ga ƙanwata itama tana buƙatar gaisawa da kai.
Cikin yanayin girmamawa tace "salamu'alaikum ɗan uwa anwuni lafiya?
Cikin yanayin sakin fuska nace "lafiya ƙalau yar uwa yasu abba da mummy?
Murmushi tayi haɗe da cewa "sunanan lafiya ƙalau.
Dama yayana ne yake yawan bani labarinka kuma abun yana matuƙar burgeni wannan ne dalilin da yasa na buƙaci ya haɗani dakai domin na jinjinama.
Bayan kwana biyu da faruwar haka misalin ƙarfe 11 na ranar laraba lokacin bana tare da wayata sakamakon na barta a wajan chaji.
37 missed call nagani a yayin dana karɓi wayar daga wajan chaji.
Sai Kuma message guda 7.
Bayan na duba kiran da'amin sai kuma na shiga ɓangaran message.
Abun da na gani a message ɗin farko shine ("na kira wayarka har sau 7 amma baka amsaba ganin haka ne yasa nayi tunanin ko baka kusa da wayar ne.
Daga Haneefa ƙanwar Musa Ibrahim, kahuta lafiya.
Ban wani ɓata lokaci ba na kirata.
Koda ta amsa kiran bayan mun gaisa sai tace "kaga message ɗina kenan?
Buɗar bakina sai nace "ai message ɗin ne yai min jagora wajan gane wadda tamin kira har sau 6.
Wanda hakan yasa nayi gaggawar kiranta domin na bata haƙuri sakamakon rashin amsa kiranta ɗin da nayi akan lokaci.
Dariya naji tayi haɗe da cewa "ammafa kanada barkwanci.
Sannan ta ƙara da cewa "dama na buƙaci magana da kai ne domin neman wata alfarma a gareka.
Cikin yanayin mamaki nace "wace alfarma kuma kike nema a gareni?
Buɗar bakinta sai tace "dama yau na buɗe account a shafin Facebook shine nake buƙatar nima ka riƙa turomin da irin labaran da kake bayarwa.
Sai na ɗanyi dariya haɗe da cewa "indai dan wannan buƙatar ne to karkiji komai kawai abun da nake bukata a gareki shine user name ɗin daki buɗe account ɗin.
Sai tace "User name din shine Haneefa Ibrahim zakaga hotona ina riƙe da wasu yara biyu ɗaya mace daya namiji.
Tun daga wannan ranar sai kyakkyawar alaƙa ta fara shiga tsakanina da haneefa.
Lokaci-lokaci ina tura mata da labarai domin samar da farin ciki ga zuciyarta.
Kafin na farga har shaƙuwa ta shiga tsakanina da haneefa kuma gashi ba soyayya ce a tsakanina da ita ba.
A ranar dana sanar da ita cewar zan tafi makaranta Jahar Katsina sai da tasan yadda tayi ta canzamin ra'ayi ta hanyar marai-raicewa haɗe da bayyanamin tsantsar shagwaɓa duk dan buƙatar na karkata akalar karatuna izuwa jahar naija / minna wato jahar da take da zama kenan.
Ba yadda na iya haka nabi zaɓinta haɗe da roƙon Allah a domin yasa hakan shine mafi alkairin.
Nasamu kulawar da ban taɓa tunanin samun irinta daga haneefa ba.
Dukkanin wata buƙatar da zata tasomin komai girmanta sai haneefa ta kawarmin da ita yunwa bata samu masauki a zuciyata ba domin musamman haneefa take zuwa har inda nake domin tamin girki wani lokacin kuma tun daga gida take tahomin da abun da zanci.
Haneefa tana ɗaukata ta kaini har gidansu ba tare da tunanin komai ba.
Gidan nasu irin babban gidannan ne domin a mutanan gidan ba wanda zai nuna damuwarshi dan wani ya shiga da abokinshi.
Kai da ganin gidan haɗe da tufafin da haneefa take sawa kasan ba yar ƙananun mutane bace.
Nima kaina nasan da cewar wannan alaƙar tawa da haneefa tana gaf da juyewa izuwa soyayyar da kunnuwanmu bazasu taɓa jin kira ba.
Tun kafin soyayya ta kaiga bayyanuwa a tsakanina da haneefa sai yayanta wato Musa Ibrahim kenan ya sameni da buƙatar yin wata muhimmiyar magana dani.
Bayan mun gaisa sai yace "nazo gareka ne domin muyi wata muhimmiyar maga a matsayinka na abokina ba kuma wata magana bace illa maganar da ta shafi tsakaninka da ƙanwata haneefa dan Allah abokina ina mai roƙonka akan kar kayi ƙoƙarin yaudarar ƙanwata musamman a yayin da sonka yai nisa a zuciyarta.
Sannan ya ƙarara da cewa "ko kasan da a halin yanzu ba ta da wani muradin son kasancewa da wani a matsayin mijinta bayan kai dan haka idan har kasan babu batun auranta a shafin rayuwarka to kayi ƙoƙarin fita daga zuciyarta.
Idan kuma kana da niyar auranta to ni zan tsayama wajan ganin ta zama mallakinka domin bazan ɓoyema ba iyayenmu ko kuma ince abbana yana da matuƙar zafi.
Jin haka ne yasa na ɗan yi murmushi haɗe da cewa indai nine to baka da wata damuwa domin muradin ƙanwarka shine muradina idan har tana buƙatar kasancewa dani a matsayin mijinta to nima Ina muradin kasancewarta a matsayin matata, domin ba dalilin da zaisa na juyama buƙatar ƙanwarka baya.
A wannan ranar sai Allah ya jarafceni da matsanancin zazzabi.
Bayan nasha magani sai na kwanta bacci a ɗaki bani na farka ba sai misalin ƙarfe 3:30 na rana.
Buɗe idan da zanyi sai nayi ido biyu da haneefa zaune a kusa dani tanamin fifita.
Murmushi naga tayi haɗe da cewa "lallai kajima kana bacci sannan ta ƙara da cewa ya jikin naka?
Cikin yanayin mamaki nace "haneefa ya ai ki gane cewar bani da lafiya?
Buɗar bakinta sai tace "waɗannan maganin da na gani a kusa da kaine yasa nayi tunanin akwai rashin lafiya a tattare da kai wanda hakan yasa na taɓa fuskarka zafin da naji a yayin dana taɓa fuskarka ne ya tabbatarmin da cewar baka da lafiya, gudun karka shiga wani hali ne yasa na zauna a kusa dakai ina yima fifita.
Duk da cewa na samu sauƙi haka haneefa ta hanani zuwa ko ina.
Kuma ba ita tabar wajena ba har sai da 6 na yamma tayi.
Kafin ta tafi sai nayi mata wani furucin da ya jawo bayyanuwar ɓacin ranta sai dai kuma ni banyi mata furucin domin buƙatar haifar da damuwa ko ɓacin rai a tattare da ita ba.
Kawaifa cewa nayi "haneefa ki rage nuna damuwarki a gareni domin cikin ƙanƙanin lokaci Allah zai iya haifar da tazara mai nisan gaske a tsakanina dake musamman idan.......
Sai ta dakatar dani ta hanyar ɗaga hannunta haɗe da cewa dakata!!!!
Sannan tayi waje tana kuka.
Ganin haka ne yasa nayi mamakin faruwar haka.
Tun daga wannan ranar ban sake ganin haneefa ba har saida a ɗauki tsawon kwana biyu.
Misalin 11 na dare naji ana ƙwankwasa ƙofar ɗakina fargaba haɗe da tsoran da nake tattare dasu a zuciyata ne yasa naƙi buɗe ƙofar.
Sautin muryar haneefa naji tana kuka haɗe da cewa dan Allah ka taimaka ka buɗe ƙofar.
Jin haka ne yasa nayi gaggawar buɗe ƙofar domin ganin halin da take ciki.
Buɗe ƙofar kenan sai jinayi ta rungumeni tana kuka haɗe da cewa wallahi bazan iya rabuwa dakai na tsawon awa ɗaya ba saboda ina sonka.
Fuskata ba alamar wasa nace "bazaki iya rabuwa dani na tsawon awa ɗaya ba, amma taya ai ki iya nisanta kanki a gareni na tsawon kwana biyu?
Cikin yanayin bayyana damuwa tace "tunaninka, mafarkinka haɗe da fargabar yadda rayuwata zata kasance a yayin da idanuwana su daina ganinka kunnuwana su daina Jin kalamanka sune su hanani sakewa wanda hakan yasani zubar da hawayen da banyi zato ba.
Gudun kar zuciyata ta shiga mawuyacin hali ne yasa nazo gareka domin idanuwana su ganka kunnuwana suji sautin muryarka badan komai ba sai dan kawar da fargabar da nake tattare da ita.
Cikin yanayin alhini nace "kalamanki sun zarce nawa domin bani da kalaman da zan iya danganta nawa da naki kawai ni dai abun da zan iya cewa shine nima na kamu da haƙiƙanin ƙaunarki rabuwar da kiyi dani na tsawon kwana biyu ba kaɗan yasani a damuwa ba.
Wani kallo naga tamin haɗe da cewa "idan da gaske ne kashiga damuwa a dalilin nisanta kaina ɗin da nayi s gareka na tsawon waɗannan kwanakin meyasa ka kasa zuwa gareni kamar yadda ni na kawo kaina gareka a yanzu?
Kallanta nayi haɗe da cewa "gudun karki ɗauki mummunan mataki akaina ne yasa na kasa zuwa inda kike sakamakon ganin yadda ki rabu dani kina kuka.
Murmushi tayi haɗe da cewa "Dan Allah karka sake kawo batun aukuwar tazara komai ƙanƙantarta balle rabuwar da zata haifar da damuwa a gareni.
Tun daga wannan lokacin sai soyayya ta makantar damu amma duk da haka banyi sake da karatuna ba.
Maganar gaskiya soyayyar mutanan naija tasha banban da ta sauran jahohin da muke dasu a arewacin najeriya, domin soyayya ce irin ta amutu ta shiga tsakanina da haneefa.
A zahirin gaskiya indai har mutun ya mallaki kimanin 20 years ba tare da wasu alamu na hauka sun bayyana a tattare dashi ba to ba yadda za'ai ace baisan abun da ya dace dashi a fagen soyayya ba abun da nake nufi shine "dukkanin wani abu mai kyau ko mara kyau ya sani sai dai son ranshi ya ingizashi wajan biyema son zuciyarshi.
Nima son zuciyata ne yasa na biyema haneefa.
Haneefa tana riƙe hannuna aduk lokacin da taga dama bakuma ta jin kunyar kwanto jikinta a nawa jikin ko kuma ta rungumeni.
Haka ne yasa na ɗauki salon soyayyarta a matsayin baƙon al'amari a gareni.
Son da nake mata ne yasa na kasa ganin laifinta.
Kawai wata ranar asabar da misalin ƙarfe 5 na yamma bayan na dawo daga school fitowata daga wanka kenan sai haneefa ta shigo.
Yanayin kallon da tamin ne yasa na fahimci cewar akwai ƴar damuwa a tattare da ita.
Cikin yanayin sakin fuska nace "lafiya kuwa domin naga kamar akwai damuwa a tattare dake?
A sufane takalleni haɗe da cewa "nazo ne domin na sanar dakai gaskiyar dana daɗe ina ɓoyema.
Jin haka ne yasa na zauna a kusa da ita haɗe da "cewa wace gaskiya kuma kizo sanar dani?
Buɗar bakinta sai tace "Ina da miji.
Koda naji tayi wannan furucin cikin yanayin ɗaga murya na daka mata tsawa haɗe da cewa "ki tashi ki ɓacemin da gani.

Cikin yanayin sanyin jiki tace kar kayi gaggawar rabuwa dani ba tare dakaji dalilin da yasa na shiga rayuwarka ba?
Cikin yanayin ɓacin rai nace "wane dalili kike tattare dashi wanda ya wuce kwaɗayin bin maza.
Cikin yanayin kuka ta girgiza kai haɗe da cewa ni ba musulma bace.
Jin haka ne yasa nayi tunanin anya kuwa haneefa ba rainamin hankali take nemanyi ba.
Domin tasha ɗaukata ta kaini har gidansu me kuma zaisa ta sanar dani cewar ita ba musulma bace alhalin kuma iyayenta haɗe da sauran mutanan gidansu duk musulmai ne.
Idan kuma ita matar aurece taya za'ai yayanta ya barni naci gaba da kasancewa a tare da ita da sunan soyayya.
Ji nayi tace "nasan dole ne ka shiga ruɗani a dalilin jin wannan bayanin da nayima dan haka ka kwantar da hankalinka domin a yau ne zanyima cikakken bayanin dalilin da yasa haka ta faru a tsakanina dakai.
=> 2
Haka ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa "tabbas ni ba musulma bace kuma ahalinama ba musulmai ba ne.
A halin da nake ciki yanzu bani da wani burin da ya wuce zama cikakkiyar musulma.
Tun daga lokacin da na fara mallakar hankalin kaina na gane cewar addinin da iyayena suke ciki ba komai bane face ɓata.
Ban kuma tashi gane hakanba sai a lokacin dana tsunci kaina a matakin secondary.
Haƙiƙa makaranta itace kan gaba waja haɗa mutun da abokai masu yawan gaske.
Zuwana secondary ne ya haɗani da mutanan da banyi zaton haɗuwa da irinsu ba.
A school ɗin da nayi karatu ba'a ware class ɗin maza da na mata haka muke gwamutsuwa maza da mata mu zauna.
Kwatsam wata rana sai kiristocin da ke school ɗin su fara nuna ƙabilanci wanda hakan yasa idan an shiga class sai Musulmai su koma ɓangare ɗaya haka suma kiristocin zasu koma ɓangare ɗaya.
Ba kuma komai ne ya haddasa hakanba illah wata ƴar rigimar da ta faru a tsakanin musulmai da kiristocin.
Rigimar ta samo asali ne tun wata ranar Monday.
Aisha da Abdul suna da ya daga cikin ƴan class ɗin mu kuma sune musabbabin faruwar rabuwar kanmu.
Kasan harkar makaranta dolene a samu yan raining wayo.
Aisha tana zaune a wajan zamanta tana rubutu koda Abdul ya kyalla ido ya ganota cikin yanayin sakin fuska ya tashi daga wajan zamanshi zuwa inda Aisha take da zuwane da zuwanshi sai ya fisge biron da ke hannun A'isha haɗe da cewa "me yasa jiya bakizo school ba?
Cikin yanayin damuwa Aisha ta girgiza kai haɗe da cewa "bani birona, domin ba huruminka bane jin dalilin rashin zuwana school.
Cikin yanayin wasa Abdul yace "nikuma idan har bazaki sanar dani ba to ba yadda za'ai na baki wannan biron.
Ran Aisha a ɓace tace "Abdul banason irin wannan wasan kaga rubutu nakeyi dan haka ka bani birona.
Koda Aisha taga alamun ba yadda za'ai ya bata biron sai ta miƙe tsaye koda takai hannu domin fusgar bironta sai Abdul ya rike hannunta.
Bamu tashi aune ba sai jin saukar mari muyi a fuskar Abdul.
Nanfa Abdul ya dafe kumatunshi a kunyace.
Ganin haka ne yasa nan take wani christer ya watsama Aisha giya a fuska.
Ba iya musulmai ba hattamu kanmu kiristocin sai da muyi mamakin ganin yadda abun ya faru.
Nanfa musulman da ke class ɗin namu su yinƙuro akan sufa bazasu taɓa yadda ba wanda hakan yasa a fara doke-doke a tsakanin musulmai da kiristocin da ke class ɗin.
Ni kuma tuni nayi waje domin Allah bai haɗa jinina da giya ba duk da cewa ni ba musulma bace ko kadan banason warin giya.
Cikin gaggawa malaman dake school ɗin su dakatar da faɗan.
Koda malaman suji bayanin yadda faɗan ya samo asali.
Sai suyi yinƙurin ɗaukar mummunan mataki ga waɗan da su haddasa faɗan wato Abdul da John kiristan da ya watsama Aisha giya a fuska kenan.
Koda Aisha taji batun da hukumar makaranta tayi akan cewar dole ne sai iyayen Abdul da John sunji bayanin abun da ƴaƴansu su aikata haɗe da zartar da mummunan hukunci akansu sai Aisha tace "a'a idan ayi haka za'a iya samun matsala a school ɗin saboda idan abbana yaji wannan labarin hatta ku kanku malaman dake makarantar sai ta shafeku saboda dole ne a tuhumeku a game da sakaki wajan rashin kulawa da dokokin makaranta alhalin kuma mu mu san kuna iya bakin ƙoƙarinku wajan hana faruwar irin wannan saboda muma kanmu bamusan cewar a class ɗinmu akwai masu shigo da giya ba.
Kuma kaga yanzu saura kwana ukku ɗaliban da ke gaba damu su fara rubuta jarabawar fita ta WAEC da NECO dan haka bazanso su samu matsala a dalilina ba, saboda haka na haƙura.
Sai principal ɗin makarantar ya jinjina kai haɗe da cewa "tabbas kin cancanci a yaba miki domin kina da tarbiyyar da ba ko wace ya mace zata samu irinta a wannan lokacin ba uwa uba kuma gaki da hangen nesa.
Bayan an gargaɗi Abdul da John akan idan har a sake kamasu da wani laifi komai ƙanƙantarshi to ba makawa sai an koresu daga school ɗin kuma kora ta har abada.
Sannan a umarcemu damu koma mu zauna.
Sannan aba Aisha ruwa ta wanke fuskarta.
Ganin haka ne yasa kiristocin dake class ɗin su ware kansu suma musulmai su koma ɓangare ɗaya amma dukanmu muna a class ɗaya ne.
Da yake a kusa da wajan zamanmu John ya watsama Aisha giya sai wajan ya gagareni zama saboda banason warin giya wanda hakan yasa nayi ƙoƙarin canza wajan zama.
Abun yayi matuƙar bani mamakin ganin yadda yan uwana kiristoci su hanani wajan zama wanda hakan yasa su fara zagina haɗe da cewa yaza'ai ina kirista amma na riƙa kyamar giya.
Ganin haka ne yasa wata baiwar Allah mai suna ameena daga cikin musulman dake class ɗin ta matsamin na zauna a kusa da ita.
Ganin haka ne yasa kiristocin dake class ɗin su ƙauracemin ni kuma ko kaɗan ban wani damu ba.
Bayan hukumar school ɗin tamu tasa doka mai tsanani a game da duk wanda a kama da giya a school ɗin.
Sai na koma cikin ƴan uwana kiristoci a hankali dai sai al'amurana dasu ya koma dai-dai.
Har Allah ya kaimu lokacin da zamu rubuta exam wato jarabawar NECO da WAEC kenan.
A wannan lokacin ne Allah ya jarafci wasu daga cikinmu kuma a cikin waɗanda Allah ya jarafta hadani domin mu biyar ne mu rasa kuɗin da zamu zana jarabawar fita daga matakin secondary.
Kuma ni kaɗai ce kirista a cikin mutane biyar ɗin da basu da kuɗin zana jarabawar.
Daƙyar na samu dubu 10 daga wajan iyayena ganin haka ne yasa na yanke shawarar tunkarar ƴan uwana kiristocin dake class ɗin namu domin neman taimakon kudin da zan cika wajan ganin nayi ko iya NECO ne amma suƙi tallafamin duk wanda na tunkara da wannan buƙatar sai ya canzamin fuska haɗe da yimin furucin da zai ƙonamin rai.
A wannan lokacin ne na gane cewa musulunci addini ne mai sauƙi saɓanin addinin da nake ciki domin musulman dake class ɗin namu ne su biyamin kuɗin jarabawar NECO da WAEC ɗin da zamuyi ba tare da ko sisin kobona ba.
Tun daga wannan lokacin hankalina ya fara karkata zuwa addinin musulunci.
Koda kiristocin dake class ɗin namu suga alamun halayyata ta fara canzawa saɓanin yadda susanni sai su kai ƙarata zuwa ga iyayena.
Haka kawai bansan hawaba bansan saukaba mahaifina yamin shegen duka haɗe da gargaɗina akan karna kuskura na sake kula wasu musulmai idan kuma ba haka ba to raina sai yayi matuƙar ɓaci.
Kuma gashi ba mai ƙwatata a yayin da mahaifina yake dukana domin tun ina ƴar ƙarama mahaifiyata tabar duniya.
Sai ya kasance itama matar da mahaifina yake zaune tare da ita bana samun sauƙi a gareta.
Haka na ƙaraci kukana har bacci ya ɗaukeni ina cikin bacci sai nayi mafarkin mahaifiyata ta tasheni daga bacci.
Tashina kenan saita dafa kaina haɗe da cewa bazaki taɓa samun sassauci ba har sai kinbar wannan addinin da kike ciki izuwa addinin musulunci sannan ta ɓace firgigit na tashi daga bacci a tsorace.
Tun daga wannan ranar na daki ƙirjin fita daga addinin da nake domin komawa addinin musulunci.
Gudun karna shiga addinin musulunci ne yasa mahaifina yai gaggawar mallaka ma wani kirista ni a matsayin matarshi.
Duk da cewa banason wanda mahaifina ya mallakani a gareshi haka na ɓoye wannan ƙiyayyar a iya zuciyata saboda ina matuƙar tsoran mahaifina.
Neman mafita ne yasa na tuntuɓi abokinka Musa Ibrahim wanda kake ɗaukarshi a matsayin yayana.
Koda na sameshi bayan mun gaisa sai nace "musa bani da wani burin da ya wuce na kasance a wannan addinin naku na musulunci sai dai kuma akwai matsalar da nake gudu domin mahaifina ya bayar dani ga wani kirista a matsayin matarshi kuma idan har na kuskura nace zanbar wannan addinin da nake ciki to na tabbata kasheni iyayena zasuyi.
Koda musa yaji haka sai naga yayi shiru na ɗan wani lokaci zuwa can sai yace ""to yanzu ya kikeson ayi?
Cikin yanayin damuwa na kalli musa haɗe da cewa "rashin sanin yadda za'ayi ne ya kawoni gareka.
Jin jina kai naga yayi haɗe da cewa "to gaskiya bani da masaniyar yadda za'a ɓulloma wannan al'amarin amma akwai wani abokina dana haɗu dashi a facebook kuma na tabbata idan yaji halin da kike ciki zai iya taimaka miki fiye da tunaninki.
Cikin yanayin farin ciki nace "dan Allah musa ya za'ai ka haɗani dashi wallahi na matsu naga na fita daga wannan baƙin jahilcin.
Sai Musa ya girgiza kai haɗe da cewa "wannan ba al'amari ne na gaggawa ba domin abu ne wanda yake buƙatar bi a hankali.
Tun daga ranar da musa ya fara nunamin irin labaran da kake bayarwa a shafinka na Facebook mai suna KOTUN MASOYA na tabbatar da cewa zaka iya sharemin hawayena domin labaran da kake bayarwa masu ma'ana ne haɗe da nuna jajircewa wajan cimma wata manufa.
A yayin da musa ya haɗani da kai a waya ne naji kashiga raina wanda hakan yasa tunaninka ya hanani sakewa.
Soyayyar da nakema ce tasa na dage wajan canzama ra'ayin zuwa garin Katsina karatu.
Amincewar da kayi dani ne yasa ka biyema ra'ayina ka dawo da ƙudurin karatunka wannan jahar tawa ta Naija.
Gidan da na kaika a matsayin gidan iyayena ba gidanmu bane gidansu Musa ne.
Aduk lokacin da nayi kuskuran yin shiga irinta addinin musulunci ba karamin ƙalubale nake fuskanta daga iyayena ba.
Haka ne yasa bana yadda nayi wata shigar da ta shafi addinin musulunci sai a lokacin da zan tunkari inda kake saboda banason ka gane cewar ni ba musulma bace wanda hakan zai iya sawa na rasaka.
Ganin ba yadda za'ai burina ya cika ne muddun banyima bayanin gaskiyar abun da nake boyewa w gareka ne yasa nayima wannan bayanin.
Kalamanka sunyi matuƙar sani a yanayin da banajin cewar akwai dalilin da zai iya rabani dakai.
Dan Allah kataimakeni ka wargaza alaƙar da take a tsakanina da wanda mahaifina ya damƙani a gareshi.
Cikin yanayin tausayawa nace "meye sunanki?
Buɗar bakinta sai tace "sunana Merry.
Sai na jinjina kai haɗe da cewa "To gaskiya merry ba ni da wata hanyar da zan iya taimakonki shawara da ya zan iya baki idan har dagaske kina buƙatar kasancewa musulma dan haka me zai hana ki rabu da ahalinki? ni kuma nayi miki alƙawarin zan baki gudun mawa wajan cika miki wannan burin naki.
Sai tace "karfa kamanta idan har nayi wannan yinƙurin to ba makawa sai iyayena sunga bayana saboda shirkarsu tafi ƙarfin tunaninka.
Koda naji wannan batun daga bakinta sai nace "to gaskiya a halin yanzu bansan hanyar da zamubi ba.
Matsowa tayi kusa dani haɗe da cewa ni nasan hanyar da zamubi ammafa sai dai hanyar zatayima tsauri kuma ina da tabbacin indai mubi wannan hanyar to ba makawa sai burina ya cika.
Cikin gaggawa nace wannan wace hanyace?
Buɗar bakinta sai tace "bai zama lallai ka amince da shawarar da zan bayar ba.
Matsawa nayi kusa da ita nace "akan buƙatarki ta kasance musulma zan iya sadaukar da raina domin cika miki burinki dan haka ki gaggauta sanar dani wannan shawarar.
Kallona naga tayi sannan tayi ƙas da kanta haɗe da cewa "a al'adar ƙabilarmu da zaran anyiwa mace miji to idan har wanda ya kasance a matsayin mijinta ya kamata da wani a matsayin suna aikata aikin da bai dace ba.
To mijin nata zai rabu da ita ahalintama zasu rabu da ita wanda hakan zaisa su koreta daga gida.
Wannan hanyar ita kaɗaice zata rabani da wanda yake riƙe dani a matsayin matarshi, kuma itace zata rabani da iyayena ba tare da sunyi ƙoƙarin cutar da ni ba.
Cikin yanayin mamaki nace "to amma taya kike tunanin zamu samu wanda zai zartar da wannan aikin?
Buɗar bakinta sai tace "kai ne wanda zaka jagoranci kawo ƙarshen zamana da iyayena kuma nayima alƙawarin bazan bari wani abu ya shiga tsakanina da kai ba, kawai da zaran na dai-daici lokacin da mijin nawa yake gaf da dawowa gida to ni kuma zan kiraka a waya.
A yayin da zai shigo gidan to kai Kuma sai ka fito daga ɗakin nawa a matsayin wanda ya kwanta dani.
Cikin yanayin dariya nace "lallai kin rainamin hankali taya kike tunanin zan amince da wannan gurguwar shawarar taki.
Nan take ta riƙe hannuna tana kuka haɗe da cewa "Dan Allah ka taimakamin kamar yadda Allah ya taimakeka ka kasance a ɗaya daga cikin musulmai, me zai hana nima kayi jahadin taimakona?
Kuruciyar da nake tattare da ita ne yasa na biyewa merry domin cika mata burinta.
Washe gari da misalin ƙarfe 9:20pm merry ta kirani a waya.
Jim kaɗan da zuwana gidan da take da zama sai ta jani zuwa ɗaki.
Da shigata ɗakin sai mery ta samu nasarar sokamin allurar da tayi nasarar jefani a bacci.
Kafin baccin ya ɗaukeni haka tayi tsurara ta hanyar cire kayan dake jikinta.
Haka tabi duk wasu hanyoyin da take ganin sun dace wajan tayar da hankalina.
Bayan ta gama tayar da hankalina inaji ina gani haka ta cire kayan da nake sanye dasu ba tare da na iya dakatar da ita ba saboda a wannan lokacin duk ilahirin jikina ya gama mutuwa.
Buɗe idon da zanyi sai na tsunci kaina a wani baƙon yanayi domin ganin jikina nayi duk ya ɓaci da ƙazanta.
A wannan lokacin ne takaici ya hana i furta komai a gareta wanda hakan yasa naji na tsani kaina.
Cikin yanayin ta kaici na buɗa baki zanyi mata magana kenan sai naji sallama wanda hakan yasa nan take naji ƙirjina ya buga.
Sallamar da naji anyi ne tayi matuƙar tsoratani wanda hakan yasa na shiga kokwanto koda na hada ido da merry sai naga tayi murmushin da ya ƙara afkani a ruɗani.
A yayin da nake ƙoƙarin mayar da kayana sai mijin ta ya kamani a matsayin kwanton da ya kwanta da matar aure.
=> 3
Ita kuma a wannan lokacin ba abun da takeyi face kuka.
Ganin haka ne yasa nayi shiru ba tare dana iya furta komai ba.
Nan take mutumin dake gabana ya kalli merry haɗe da cewa "Zainab kin cuceni Allah ya isa tsakanina dake.
Fuskata cike da ruɗani na nunata da yatsana haɗe da cewa "dama ke musulmace har kimin ƙaryar cewa sunanki merry?
Furucin da naji tayi ne ya ƙara jefa ƙwaƙwalwata a ruɗani.
Haka ta durƙusa a gaban mijinta tana zubar da hawaye tace "dan Allah mijina kayi haƙuri wallahi ba yadda zanyine domin wannan mutumin da kake gani yayi matuƙar addabar rayuwata dan haka bazan taɓa ganin laifinka ba musamman idan kace zaka dauki matakin wannan babban laifin damu aikata amma zanso na fara baka labarin yadda ai har hakan ta faru kafin ka zartar da duk wani abun da kaga dama a garemu.
Haka ta ɗago kai ta kalleni sannan ta kalli mijinta haɗe da cewa "tun kimanin watanni biyu dasu wuce a ranar wata litinin da misalin ƙarfe 3:30 na rana lokacin baka gida sai naji zazzaɗi yana neman takuramin ganin haka ne yasa nayi gaggawar shan magani.
To amma duk da cewar nasha maganin banji wani rangwame a game da zazzaɓin da nake tattare dashi ba.
Koda naji jiri ya fara ɗaukata sai nayi ƙoƙarin kiran wayarka sai kuma ayi rashin sa'a da na duba wayar sai naga ba network.
Ganin haka ne yasa na ɗauki mota domin zuwa asibiti fitata daga gida kenan sai naji amai ya tasomin cikin gaggawa na fito daga motar da nake tuƙawa bansan lokacin dana yanke jiki na faɗi ƙasa a yayin da nake aman ba.
Ban tashi tsuntar kaina ako inaba sai a gadan asibiti.
Misalin ƙarfe 6 na yamma a sallameni daga asibitin.

A yayin da take cikin bayar da wannan jawabin sai ta kalli mijin nata sannan haɗe da nunani da yatsanta sannan tace "wannan shine ya kaini asibitin kuma shiya dawo dani har gida.
Da shigowarmu falo sai yabuɗe maganin da'a bani daga asibitin haka ya ɗibo wasu ƙwayoyin magani da hannunshi ya bani haɗe da cewa kisha wadannan yanzu.
Jim kaɗan da shan maganin gaba ɗaya sai narasa inda hankalina yake.
Bansani ba ashe maganin bacci ya bani.
Bani na farkaba sai misalin ƙarfe 9 na dare haka na tsinci kaina cikin wani baƙon yanayi domin a tsurara na tsinci kaina.
A wannan lokacin ba kaɗan nayi kukan baƙin cikin abun da ya aikatamin ba.
Gudun karka rabudani a yayin da ka gane haka ta faru dani ne yasa nayi ƙoƙarin ɓoye wannan surrin.
Koda na duba wayata sai naga missed calls ɗinka har 7.
Haka na ɓoye damuwar da nake ciki na kiraka bayan ka amsa kiran sai kace "ɗazu na kira wayarki amma banji kin amsa ba.
Cikin yanayin shagwaɓa nace "dan Allah kayi haƙuri lokacin ina kitchen Ina dafama abun da zakaci ban Kuma fito ba har sai da na kammala girkin.
Da fitowata kuma ko ɗaki ban shigaba kai tsaye na wuce toilet domin yin wanka.
A wannan ranarban bari kasan abun da ya faru dani ba.
Na ɗauka shikenan abun ya wuce to ashe akwai sauran matsala a gaba.
Kimanin kwana biyar da faruwar haka sai naji kira ya shigo wayata koda na duba sai naga baƙuwar number.
Bayan na amsa kiran sai naji ance zainab ya jikin naki?
Cikin yanayin mamaki nace "Dan Allah ko zan iya sanin dawa nake magana?
Buɗar bakinshi sai yace "wanda ya kaiki asibiti ne a lokacin da baki da lafiya yau kwana biyar kenan dasu wuce.
A wannan lokacin ba furucin da ya fara fita bakina sai tsinuwa haɗe da furta kalmar Allah ya isa a tsakanina dashi.
Kawai sai ji nayi naji ya dakamin tsawa haɗe da cewa "ban kiraki domin buƙatar ji wasu ƙazaman kalaman bakinki ba.
Na kiraki ne domin sanar dake cewar auranki yana gaf da mutuwa, dan haka yanzu zan turo miki da wani Vedio dan haka abun da zan sanar dake bayan kin kalli Vedion shine zai hana isar Vedion wayar mijinki.
Cikin yanayin kuka tace bayan naga Vedion da ya turomin sai al'amarin yai matuƙar kiɗimani domin Vedion kwantawar da yayi dani alokacin da ya bani maganin bacci nagani.
Haka ne yasa nayi gaggawar kiranshi domin roƙonshi akan ya share vedion.
Dariya naji yayi a yayin dana buƙaci ya share vedion haɗe da cewa "tabbas zan share vedion kamar yadda ki buƙata amma sai abun da ya faru a tsakanina dake ya sake maimaita kansa.
Cikin yanayin ruɗani nace "ban fahimci abun da kake nufi ba?
Ko kunya babu a tattare dashe ya bayyana mummunar buƙatarshi ta sake kwantawa kaina.
Ƙiri-ƙiri yace "idan kiga na share vedion da na ɗauka ba tare da ya isa wayar mijinki ba to sai na sake kwantawa dake a ɗakin da na kwanta dake a kwanakin baya.
Ganin ba yadda za'ai ya haƙura ne yasa na amince da wannan buƙatar tashi domin banason abun da zai kawo rabuwa a tsakanina da kai.
Bayadda banyi dashi ba domin naje har inda yake domin na biyamai buƙatarshi amma yaƙi domin cewa yayi "gadan da mijina yake kwantawa dani yafi daɗin hutawa.
Ban sani ba ashe rabon asirina ya tonu ne wanda a ƙarshe gashi ka kamani tare dashi a yayin da ya gama biyan buƙatarshi.
=> 4
Wannan shiryayyen ƙazafin da naji ya fita daga bakin Zainab ba kaɗan yasani a ruɗani gami da mamaki ba.
Ganin bani da wata hanyar da zan iya kare kainane yasa nayi ƙoƙarin guduwa domin ceton rayuwata.
Ban tashi auneba sai jin saukar ƙarfe nayi a kaina wanda hakan yasa nayi wanwar a ƙasa.
A yayin da hankalina zai dawo gareni sai na tsunci kaina a hannun jami'an ƴan sanda.
Na tabbata idan har iyayena su samu labarin abun da ya faru dani to ransu sai yayi matuƙar ɓaci wanda hakan zaisa a ƙarshe kuma mutuncin gidanmu ya zube a idon al'ummar dasu sanmu domin bani da wata hanyar da zata iya kareni daga wannan babban laifin da'ake tuhumata dashi.
Gudun karna ɓata mutuncin gidanmu ne yasa nayi gaggawar amsa laifin da ake tuhumata dashi a kotu haɗe da yima kotu bayanin cewar banida kowa domin ni kaɗai ne ɗa a wajan iyayena kuma Allah ya masu rasuwa a sakamakon haɗarin motar da ya afku dasu tun shekara 4 dasu wuce.
Sannan na roƙi kotu da tamin sassauci a danga ne da hukuncin da za'a zartar akaina.
A wannan ranar a zartarmin da hukuncin ɗaurin shekara 7 haɗe da aiki mai tsanani.
Bansan lokacin da hawaye ya zubo daga idanuna ba domin na tabbata iyayena haɗe da sauran ƴan uwana sai sunyi matuƙar shiga damuwar rashin ganina a dalilin waɗannan shekarun da'a ɗibarmin.
Amma ba yadda na iya saboda wannan ita kaɗaice hanyar da nake da ita wajan kare mutuncin iyayena.
Nan take mijin Zainab yabata takaddar saki biyu.
Watana ɗaya a gidan yari sai ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan yarin ya kirani haɗe da sanar dani cewar an kawomin ziyara ne.
Cikin yanayin mamaki a raina nace "waye kuma zai kawomin ziyara alhalin gaba ɗaya dangina ba wanda yasan abun da ya faru dani da har zaisa wani yai ƙoƙarin kawomin ziyara.
Ban sani ba ashe zainab ce tazo ganina.
Duk da cewa raina yai matuƙar ɓaci a yayin da nayi ido biyu da ita haka na taushi zuciyata domin jin dalilin zuwanta gareni.
Ko gaisawa bamuyi ba tace "nazo ne domin sanar da kai koni wacece domin na fahimci har kawo yanzu baka gane wacece ni ba.
Raina a ɓace nace "wacece ke wadda ta wuce banza wofi matacciyar jaka a gefen titi wadda batasan mutuncin addinin taba.
Wani mugun kallo naga tamin haɗe da cewa "kalamanka suna neman zarce ƙa'ida kuma sanin kanka ne kaidina yazarce tunaninka.
Dan haka idan baso kake na ƙara ingizaka a wata masifar ba to kaja bakinka kayi shiru domin jin abun da nazo sanar da kai.
Kuma ai wannan ba laifina ba ne kai kaja duk wannan abun da ya faru a tsakani na da kai.
Idan baka mantaba a cikin friends ɗinka na Facebook akwai wata mai suna Zainab Zee.
Wadda kayi rigima da ita ayayin da tayima magana akan batun sex chat.
Cikin yanayin mamaki nace "ashe dama kece? Wannan Zainab Zee ɗin tabbas kin cika mahaukaciya.
Jin haka ne yasa naga tayi wata ƴar dariya sannan tace "waya faɗama sunana zainab Aisha shine ainashin sunana ko kuma kace UMMEY domin dashi mahaifiyata ta saba kirana.
Buɗar bakina sai nace "to amma ya ai naji mijinki ya kiraki da Zainab?
Sai tace "ai hakan duk a cikin shirina ne domin ba mijina ba ne ataƙaicema ban taɓa yin aure ba domin tun daga lokacin daka furtamin baƙaƙen maganganu akan na buƙaci muyi sex chat na ƙuduri niyar shiryama gadar zare ta hanyar yima zagon ƙasa.
Musa Ibrahim shine wanda na fara ba kuɗi domin ya shiga rayuwarka wanda hakan zai bashi damar haɗani da kai a matsayin ƙanwarshi.
A lokacin da ya haɗani da kaine nabi duk wata hanyar da ta dace wajan ganin na cusama sona a cikin zuciyarka alhalin kuma ni nasan bason gaskiya nake ma ba.
A yayin dana fahimci kayi nisa a so sai na sanar da kai cewar ni ba musulma bace haɗe da baka wasu labaran da basu faru dani ba.
A ƙarshe kuma sai na buƙaci ka taimakeni.
Tausayawarka akaina ne yasa ka biyemin ta hanyar karɓar uzirina wanda a ƙarshe buƙatata ta biya sannan tayi dariya haɗe da cewa dama nayima alƙawarin sai ka kwanta Sani a zahiri haɗe da alƙawarin ɗaureka dan haka ina mai shawartarka akan cewar kaji tsoran kaidin mace.
Koda naji wannan batun daga bakinta sai na jinjina kai haɗe da cewa tabbas mahaifiyarki tayi asarar haihuwa sannan na tashi na bata waje.
Allah cikin ikonsa watana 7 da kwana 4 a gidan yarin sai gwamnatin jahar Naija takai ziyara gidan yarin da ake tsare damu.
Ina ɗaya daga cikin waɗanda ayima alfarma haɗe da wasu mutane bakwai.
A yayin da na samu fitowa daga gidan yarin sai naga duniya tamin haske.
Tabbas makarantace musabbabin zamana a Naija amma a yayin dana fito daga gidan yarin sai ya kasance bani da wani burin da ya wuce na haɗu da iyayena misalin ƙarfe 6 na yamma na isa jahata ta KANO.
Shigata gida kenan tun a bakin "gate" naji mahaifina ya dakamin tsawa haɗe da cewa "me kuma ya dawo da kai?
Ban iya furta kalmar komai ba har sai da naje gabanshi, haka na durƙusa har ƙasa nace "abba nasan.......
Sai ya dakatar dani ba tare da ya bari na ƙarasa maganar dake bakina ba sannan yace "kimanin 8 months kenan rabanmu da ganinka idan mun kira wayarka bata shiga ganin haka ne yasa naje har makarantar da kake karatu domin ganinka amma ban samu labarin komai a tattare dakai ba.
Ran mahaifina a ɓace yace "wato so kake ka koma mutumin banza ta hanyar zama ɗan duniya ko?
Cikin yanayin damuwa nace "haba abba ai tarbiyyar da na samu a gareku bazata taɓa barin na kasance ɗan duniya ba.
Sannan na ɗari kai na kalleshi haɗe da cewa "abba hannun miyagun muta ne mutsinci kanmu ni da wasu abokaina su biyu.
Cikin dare muna kwance lokacin bamu rufe ƙofa ba saboda a ranar ana fama da zafi mai tsananin gaske.
Tashin da zamuyi saimu tsinci kanmu a wani ɗakin da hankalinmu bai gamsu dashi ba saboda yanayin ɗakin damu gani ne ya tabbatar mana cewar hannun yan mafia mushiga.
Ni kaɗai ne na samu damar kuɓuta daga hannunsu.
Jin haka ne yasa mahaifina yace "to Allah ya ƙara kiyayewa.
A wannan ranar dai ƙanwata da mahaifiyata ba kaɗan suyi farin cikin dawowata gida ba.
Haka ƴan uwa da abokan arziƙi suyita zuwa domin jajantamin a game da abun da ya faru alhalin kuma ba gaskiyar labarin abun da ya faru da ni na sanar dasu ba.
Ganin haka ne yasa na yanke shawarar cigaba da karatuna a jahata ta KANO.
Bayan wasu ƴan kwanaki lokacin bana gida sai mahaifiyata ta kirani a waya.
Da buƙatar duk inda nake to nayi gaggawar zuwa gida tana son ganina.
A gaggauce na dawo gida domin cika umarnin mahaifiyata.
Da shigata gida sai na tarar da cewar ashe baƙi muyi domin ƙanwar mahaifina ce yazo bayan na gaisa da ƙanwar mahaifin nawa.
Nan take ta bayyana ɓacin ranta a dangane da rashin zumuncin da nake tattare dashi a rayuwata.
Kuma ko kaɗan banga laifinta ba domin na ɗauki dogon lokaci raban da naje garin Jos balle ayi batun zuwa inda take wasu lokutan kuma idan tazo gidanmu bata samun damar haɗuwa dani domin yawona yafi ƙarfin tunanin kowa.
Na buɗa baki zanyi magana kenan sai ganin Zainab nayi ta fito daga ɗakin mahaifiyata.
Cikin yanayin alhini mu kurawa junanmu ido fuskokinmu cike da mamaki.
Buɗar bakina sai nace "Zainab!!!!
Sai mahaifiyata tace "Zainab ko dai Aisha sannan tace "me ya faru, naga kunayima juna kallon mamaki mai tattare da ruɗani?
Cikin yanayin sanyin jiki nace "umma ina fatan dai wannan ba ta shafi ahalina ko wasu daga cikin dangina ba?
Buɗar bakin mahaifiyata sai tace "aikon A'isha ƴar uwarkace ta jini domin ƴar ƙanwar mahaifinka ce ga mahaifiyartanan kuma zaune a kusa da kai.
Nanfa ƙanwar mahaifina ta kalli Aisha sannan ta kalleni haɗe da cewa "wai me yake faruwa ne?
Na buɗa baki zanyi magana sai Aisha ta rigani cikin yanayin bayyana damuwa tace "umma dama na haɗu dashi a jahar naija ne sai rashin sani yasa muɗanyi wata rigima wanda hakan yasa na ɗaga hannu na mareshi bansani ba ashe yayana na mara.
Dariya naji mahaifiyata tayi haɗe da cewa ai hakanma yayi dai-dai kunga tun daga yau sai ku gane cewar zumunci ba ƙaramin abu bane domin ba abun wasa ba ne na tabbata a tsakanin ke dashi da ace akwai mai zumunci da hakan bazai taɓa faruwa a tsakanin ku ba.
Sannan mahaifiyar tawa ta kalli ƙanwar mahaifina haɗe da cewa "yanzu ki kalli yaran nan tun yana ɗan ƙarami nake ƙoƙarin koya mai zumunci amma sam yaƙi tun yana kimanin 8 years rabanshi da garin Jos.
Jinjina kai ƙanwar mahaifina tayi haɗe da cewa "ai daga shi har ita duk mutanan banza ne domin basusan mutunci ba saboda a tsakaninsu ba wani mai zumunci.
Domin itama wannan yarinyar da kike gani ko kaɗan bata damu da dangintaba gwaramashi ya taɓa zuwa inda nake amma ita wannan shine zuwanta na farko.
Sannan ƙanwar mahaifin nawa tace "kunga ni bama wannan maganarce ta kawoni ba domin so nake na koma gida a yau.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "gobe nake saran zan wuce ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji tun ɗazu naso na koma sai mahaifiyarka tace ya kamata na tsaya domin na gaisa da kai.
Kuma babban dalilin zuwana shine "kawo A'isha domin ta zauna anan har zuwa lokacin da zan dawo saboda mahaifinta mai yawan tafiye-tafiye ne hakan zaisa a kasa samun wanda zai kula da ita saboda A'isha yarinya ce marar jin magana.
Dan Allah ku kula da ita domin ba ta da wani banbanci da ƴan gidannan kuma zanso ku zartar mata da duk wani hukuncin da ya dace a yayin da ta aikata ba dai-dai ba.
=> 5
Bayan tafiyar mahaifiyar Aisha ina kwance a ɗakina sai Aisha ta shigo.
Jikinta a sanyaye ta zauna kusa dani.
Yanayin ɓacin ran da ta gani a tattare dani ne yasa ta zubar da hawaye haɗe da cewa "wallahi" nasan akaf faɗin duniyar nan ba wanda ya taɓa aikatama kwatan-kwacin rashin mutuncin da nayima.
Dan haka kasancewata na ƴar uwarka ba zai hanaka rama cin mutuncin da nayima ba.
Nayi da nasanin kasancewata a raye da har nayima ɗan uwana ƙazafin da ba wanda zai iya yimai makamancinsa.
Cikin yanayin ɓacin rai nace "Allah bai haliccemu domin mu kasance masu ɗaukar fansa ba.
Babban abun takaici a rayuwata shine "kasancewar arniya wadda ba musulma ba a cikin ahalina.
Haka na kalleta nace "halayyarki, shigarki, ɗabi'arki, tunaninki, makircinki, zafin ranki. Duk basu da wani banbanci dana kafurai.
Kina da halayyar da tasha banban da ta musulmai zafin ranki ne yake ingizaki wajan rama duk abun da wani ya aikata miki alhalin kuma haƙuri shine maudu'in duk wani musulmi.
Kuɗi sune suke ruɗarki wajan aikata duk wani abun da kiga dama.
A halin yanzu baki da wani banbanci da arna domin na tabbata ko salla baki damu da ita ba.
Tabbas fuskarki tanada kyawun kallanda ba wanda zaiso ya kauda kansa daga kallanta mai hankali da tunani ne kaɗai zai iya nisanta kanshi a gareki saboda bakiyi kama da musulmai ba domin ba karamar wahala mutun zaisha ba musamman idan ya buƙaci kasancewa a tare da ke.
Fuskarta A'isha cike da hawaye tace "haƙiƙa bazan yima musu a game da dukkanin abun da naji ka faɗa ba domin babu ƙarya a maganarka.
Nana take ta kwantar da kanta a jikina tana kuka haɗe da cewa "wallahi ba laifina bane domin tun daga iyayena nayi rashin wannan tarbiyyar.
Abba da Umma koda yaushe wajan aiki suke tafiya ranar asabar da lahadi ne kawai umma take zama a gida domin ita babbar likitace a garin Jos.
Abba bashi da lokacin zama a gida domin harkokin kasuwancinshi sunshamai kai.
Kuma basa fita ba tare da sun bani kuɗin da zasusa najini tamkar wata sarauniya ba domin har mota abba ya bani domin na riƙa hawa.
Duk inda naga damar shiga a garin Jos kaina tsaye nake sa kai.
Wannan damar ce ta bani ikon zartar da duk wani abun da naga dama musamman idan wani ya shiga gonata.
Zan iya aikata duk wani abun da naga dama amma banda abu biyu.
Shan kayan maye haɗe da bin maza, kai kaɗaine mutumin da nasan cewar na taɓa kwantawa dashi kuma na aikata haka ne domin buƙatar tabbatar ma cewar nafi ƙarfin tunaninka.
Ba kuma komai ne yasa nake gudun waɗannan abu biyun ba sai dan gudun karsu ɓata kyawun da nake tattare dashi badan hakaba da ba abun da zaisa na juya masu baya.
Haka ne yasa idan dare yayi bani da wani aikin da ya wuce hawa Social Network badan komaiba sai dan haɗuwa da mutanan da zanyi sex chat dasu a ƙarshema sai sex chat ya daina burgeni wanda hakan yasa na koma sex call.
A sanadin "sex chat" da "sex call" na samu kuɗin da ni kaina banyi tunanin samunsu ba.
Hatta motar da mahaifina ya saimin ta isa ta tsorata duk wasu mutanan kirki da suke da niyar tunkarata hatta ƙawayenama shakkata sukeyi wanda hakan yake hana su fitowa fili domin faɗamin gaskiya.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa dan Allah ka faɗamin ta wace hanya kake tunanin tarbiyya zata samu gurbin zama a tattare dani.
Dan Allah zanso ka kasance malami a gareni wanda zai koyar dani darasin rayuwa.
Bansan meye mutunci ba balle ayi batun adalci.
Bansan meye haƙuriba balle ayi batun yafiya.
Idanunta suna zubar da hawaye tace "dan Allah yayana kayafemin ka kuma yimin uziri a game da abun da ya faru a tsakanina da kai.
Zan kuma cigaba da zama anan gidan tare da kai har izuwa lokacin da zanyi aure badan komai ba sai dan buƙatar na koyi darasin rayuwa a gareka.

__Duk da cewa A'isha ta dawo gidanmu hakan baisa na saki jiki da itaba domin abar tsoroce a gareni harkarta daban nima tawa harkar daban.
Tanayin duk wani abun da zaisa hankalina ya karkata zuwa gareta amma hakan bai taɓa sa ra'ayina ya karkata izuwa gareta ba.
Kimanin kwana biyar da zuwan A'isha gidanmu.
Kwatsam rannan ina zaune a shagon wani abokina sai ƙanwata khadeeja ta kirani a waya.
Bayan na amsa kiran sai take sanar dani cewar "wayar A'isha ta ɓata a shagon wani mai chajin da yake unguwarmu.
Tun kafin na ƙarasa wajan sai naji Aisha tana ɗaya murya haɗe da cewa "wallahi ba inda zata har sai anfito mata da wayarta.
Da zuwana sai na daka mata tsawa haɗe da cewa "idan na sake jin irin wannan furucin daga bakinki sai ranki yai matuƙar ɓaci.
Sannan na kalli Khadeeja haɗe da cewa "yimin bayanin abun da yake faruwa?
Buɗar bakinta sai tace "ɗazu ne da yamma munfito daga gida zamu gidan anti (maryam) sai A'isha ta kalleni haɗe da cewa "gashi wayata ba wadataccen chaji kuma gashi akwai muhimmin abun da nakeson nayi da ita zuwa anjima.
Sai nace "to tunda bamuyi nisa da gida ba ki koma kisata a chaji mana.
Sai tace "gaskiya tunda har mun riga mun fito bazan koma ba.
Sai nace to ki bada ita a shagon can mana kinga kafin mu dawo taɗan samu chaji.
Da zuwanmu saimu samu mai chajin zaune a ƙofar shagon yana alwallah zai wuce masallaci.
Koda mu bashi wayar sai "nace ya rubuta "Khadeeja" a wayar saboda duk chajin da zamu bashi indai wanda ya shafi na gidanmu ne to bama karɓar card / number haka mubashi wayar muwuce.
Shine yanzu munzo karɓar wayar amma ba'a gantaba to amma yace yana tunanin mantawa yai da wayar a wajan da yai alwallah domin a lokacin ajeta yai a gefenshi.
Ita kuma A'isha ta turje akan ko sama da ƙasa zata haɗe dole ne sai an fito mata da wayarta saboda layin dake wayar yana da matukar muhimmanci a gareta.
Ganin haka ne yasa mai chajin ya tambayeta kuɗin wayar domin ya biyata.
Cikin yanayin faɗa tace "itafa ba wani kuɗin da za'a biyata kawai a fito mata da wayarta.
Koda naga ya matsanta wajan neman sanin kuɗin wayar sai na sanar dashi gaskiyar yadda a sayi wayar domin 185 thousands a sayi wayar kuma ko sati biyu da siyan wayar ba aiba domin kwana ukku da siyan wayar A'isha tazo nan garin.
__Bayan na gama jin komai sai na kalli mai chajin cikin yanayin sakin fuska nace "malan Abdul zaman tare wani abu ne.
Kamar yadda kake kyautatama al'umar dake zuwa gareka a dangane da wannan harkar kasuwancin naka wanda hakan yasa duk mutanan unguwar nan suke yabawa da kyautatawar da suke samu a gareks dan haka karkaji komai idan Allah yasa anganta shikenan idan kuma ba'a gantaba anyafema.
Har A'isha ta buɗa baki zatayi magana sai na daka mata tsawa haɗe da cewa maza ku wuce gida.
Ba yadda ta iya haka ta tafi gida tare da Khadeeja ranta a ɓace.
Bayan na koma gida sai mahaifiyata take tuhumata akan yaza'ai a ɓatarma A'isha waya sannan naje na shashantar da maganar ta hanyar cewa anyafe.
Haka na zauna kusa da mahaifiyar tawa ga kuma A'isha zaune a gefa ɗaya nace "mummy ba abun da yake isar rai sai haƙuri.
Me zaisa akan abun duniya mu manta da adalcin da addininmu na musulunci yace mu kasance tattare dashi a zukatanmu.
Hakafa muzo duniya ba tare da komai ba kyau tata alaƙar da take a tsakaninmu da muta ne tana ɗaya daga cikin hanyar da zatasa musamu babban rabo a rana gobe ƙiyama.
Kuma ai bamu rasa kuɗin da za'a siya mata wata ba dan haka bai kamata mu takurama mai ƙaramin ƙarfiba.
Jin haka ne yasa mahaifiyata aita jinjina kai haɗe da cewa "to Allah ya kiyaye gaba.
Washe gari da misalin ƙarfe 8 na safiya ina zaune ni kaɗai a falo kafin na fita harkokin dake gabana.
Sai (Ameena) ta shigo gidan namu.
Tabbas Ameena yarinya ce mai matuƙar kamunkai ga ladabi da biyayya.
Kyawun surar da take dashi ne yasa samari suke dafifin zuwa gareta.
Gudun kar a ɓata tarbiyyar da take tattare da ita ne yasa mahaifinta yake bata tsats-tsauran tsaro.
Cikin yanayin sakin fuska mu gaisa sannan tace "yaya Faruq, anan gidan naku akwai wata baƙuwa mai suna A'isha?
Sai na kalleta haɗe da cewa kwarai kuwa ko kinzo wajan tane?
Sai tace Eh!! Inason ganinta ne.
Cikin yanayin isa na kwallama A'isha kira.
Bayan ta fito daga ɗaki sun gaisa sai Ameena tasa hannu cikin karamar jakar da take rataye da ita ta ciro waya sannan ta miƙawa A'isha haɗe da cewa dama wayarki na kawo miki.
Ji kake tasss!!!! A'isha ta ɗauke Ameena da mari haɗe da cewa "dama kece ki saci wayar tawa?
=>6
Marin da A'isha tayiwa Ameena ba kaɗan ya girgizani ba wanda hakan yasa na tashi a fusace domin zartar da mummunan hukunci a gareta.
Koda Ameena taga na tashi a fusace sai tace "a'a rabuda ita karkayi mata komai.
Cikin yanayi ɓacin rai nace "taya za'ai kice na rabu da ita na ɗaga hannu zan mareta sai Ameena ta riƙe hannuna haɗe da cewa idan har ka daketa akan wannan abun da ta min bazan taɓa yafema ba.
Muna cikin wannan hayaniyar sai mahaifiyata ta fito daga kitchen Koda ta ganmu tsaye cirko-cirko sai tace "me kuma ya faru naketa jin hayaniya?
Cikin gaggawa Ameena tace "a'a umma ba abun da ya faru.
Cikin yanayi sakin fuska mahaifiyata tace "Ameena yau kuma kece a gidan namu lallai yau babbar ranace a garemu domin an ɗauki dogon lokaci rabona da ganin ki a wannan gidan.
Haka Ameena ta ɓoye ɓacin ran dake ranta ta hanyar bayyana murmushi haɗe da cewa wallahi umma kinsan abbana baya barina ina yawo shiyasa kiga na daɗe ban shigo ba.
Wannan zuwanma da kiga nayi saida nayima umma bayanin dalilin fitowar tawa sannan ta barni na fito saboda wayar A'isha ce da na tsunta nakawo mata.
Cikin yanayin bayyana farin ciki mahaifiyata tace "ikon Allah kenan ya kuma ai kigane wayar ta A'isha ce?
Sai Ameena tace "jiya ne da daddare muna sauri zamu islamiya ni da kanwata Nusaiba.
Koda muzo gaf da shagon Abdul mai chaji sai Nusaiba tace "anti kinga wata waya a can kuma ga dukkan alama wani ne ya manta da ita a wajan.
Har mun wuce zamu tafi sai nace "khai!! Nusaiba idan mu wuce mubar wayarcan bamuyi adalci ba saboda zata iya yiwuwa ta faɗa hannun wanda fitowarta sai ankai ruwa rana.
Wannan tunanin da nayi ne yasa na umarci Nusaiba da taje ta ɗakko wayar domin taimakawa mai ita.
Kuma na tabbata badan Nusaiba taga lokacin da wayar ta kawo haske a screen ɗin ta ba da ba yadda za'ai wannan wayar tazo hannunmu saboda saura kaɗan wayar ta mutu saboda wayar bata da chaji a lokacin domin tun kafin mu ƙarasa islamiyar wayar ta ɗauke.
A hanyarmu ta dawowa gida Nusaiba tace "yanzu anti bakya tunanin idan muyiwa umma ko Abba batun tsintar wayarnan zasu iya yimana faɗa.
Koda naji wannan maganar daga bakin Nusaiba sai nayi shiru na ɗan wani lokaci zuwa can sai nace "tabbas zasu iya yi mana faɗa musamman ma abba zai iya yin tunanin cewar wani saurayin ne ya siyamin ita sannan na kalli Ameera nace "ko munje gida karki bari suji komai a game da batun tsintar wayar ni nasan hanyar dazanbi wajan ganin wayar ta koma hannun mai ita.
A wannan daran na cire Sim card ɗin dake wayar nasa a tawa wayar domin kiran ɗaya daga cikin numbobin dake layin.
Bayan nasa sim card ɗin a wayar tawa sai na shiga ɓangaran numbobin dake layin domin duba numbar da ta dace nakira.
Ina cikin dubawa sai naga wata number mai ɗauke da sunan (My lovely Dad) Wanda hakan yasa nayi tunanin numbar mahaifin mai wayarce.
Nan take na tura calling ba'a wani ɓata lokaci ba a amsa kiran.
Bayan ya amsa kiran sai naji yace "salamu alaikum (my douter) har yanzu bakiyi bacci bane?
Cikin yanayin girmamawa nace "wa'alaikasalam, Amma ba wadda kake tunani bace ta kiraka, domin nima tsintar wayar nayi ɗazu.
Sunan da na gani a numbar taka ne yasa nayi tunanin kai ne mahaifin mai wayar.
Wannan ne dalilin da yasa na kiraka domin naji yadda za'ai wayar ta koma hannun mai ita.
Cikin yanayin farin ciki yace toke a ina kike?
Bayan na bashi full address ɗina sai yace "to gaskiya ni a halin yanzu ni ina garin Jos itama kuma mai wayar ƴar garin Jos ce amma yanzu tana kano.
Koda ya faɗamin address ɗin inda take sai nayi dariya haɗe da cewa ai wannan address ɗin daka bani jinake kamar address ɗin gidanmu ka faɗamin domin tsakanin gidan da mai wayar take da namu gidan baifi gida biyar ba.
Cikin yanayin mamaki yace "ikon Allah kenan to yanzu ya za'ai kenan?
Sai nace haba abba karkaji komai idan Allah ya tashemu lafiya gobe da safe zankai mata wayar.
Haka yamin godiya sosai.
Bayan tayi mana wannan bayanin sai ta kalli mahaifiyata haɗe da cewa "wannan shine dalilin da yasa na gane wayar A'isha ce.
Koda A'isha taji haka cikin yanayin kunya taba Ameena haƙuri haɗe da yi mata godiya.
Raina a ɓace na buɗa baki zanyi magana sai Ameena ta dakatar dani ta hanyar ƙyaramin ido domin bata son mahaifiyata tasan abun da ya faru.
Ba yadda na iya haka naja bakina nayi shiru badan rai na yaso ba, amma duk da haka ban fasa yima A'isha kallon banza ba.
Misalin ƙarfe 8 na dare ina zaune tare da abokaina muna firarmu a game da al'amuran da suka shafi yau da kulkun sai abun da ya faru a tsakanin A'isha da Ameena ya faɗomin a rai.
Sai nayi shiru haɗe da tunanin ya kamata nayi tattaki har gidansu Ameena domin na ba ta haƙuri a game da abun da ya faru a tsakaninta da A'isha.
Cikin gaggawa na miƙe har da ya daga cikin abokan nawa yana cewa lafiya kuwa kayi irin wannan tashin kamar wani mai gudawa?
Sai nayi dariya haɗe da cewa "bazaku gane ba kujirani ina dawowa yanzu.
Da zuwana ƙofar gidan su khadeeja sai nayi kaciɓus da ƙanwarta a yayin da zata shiga gida.
Sai na dakatar da ita ta hanyar kiranta nace "Nusaiba ɗan tsaya
Koda tayi ido biyu dani sai tace "yaya Faruwa kai ne a ƙofar gidan namu?
Cikin yanayin sakin fuska nace "to abun mamaki ne? Kinga je kiyimin sallama da Ameena.
Cikin yanayin mamaki ta jinjina kai haɗe da cewa "lallaima wato haka za'ayi ko? Sannan ta juya ta tafi.
Haka na saki baki na bita da kallo sakamakon rashin fahimtar abun da wannan furucin nata yake nufi.
Jim kaɗan da shigarta saiga khadeeja ta fito cikin yanayin natsuwa kai da kaga tafiyarta kasan akwai kunya a tattare da ita.
Da zuwanta gareni bayan mun gaisa sai tayi shiru ba tare da ta sake furta komai ba.
Ganin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "tabbas rashin mutuncin da'a miki a gidanmu ba kaɗan ya ƙonamin raiba wanda hakan yasa nayi matuƙar jin haushin kaina sakamakon kasa ɗaukar miki fansar abun da a miki ɗin da nayi.
Cikin yanayin damuwa nace "duk da cewa nasan bazaki taɓa mantawa da wannan abun da ya faru ba hakan bazaisa na kasa baki haƙuri ba {dan Allah Ameena kiyi haƙuri kuma kar hakan yasa ki dai na ganin gidanmu da mutunci}.
Kallona naga tayi sannan tace "ko kaɗan banso ka tunkareni da wannan maganar ba, yanzu idan asamu akasi na daki ƙanwata sai hakan yasa ta tsani gidanmu?
Sai na girgiza kai haɗe da cewa "a'a.
Sai tace to gidanku tamkar gidanmu na ɗaukeshi dan haka ba abun da zaisa naji na tsani wani daga ahalinku balle gidanku.
A yayin da muke cikin wannan maganar sai ga mahaifinta ya dawo a mota.
Dawowar mahaifinta ne yasa na fahimci zuwana gareta zai iya haifar da matsala a gareta domin alamun tsoro nagani a tattare da ita.
Ganin haka ne yasa na tuna da cewar mahaifintafa baya bari tana fitowa kamar sauran mata.
Zuge Glass naga yayi sannan ya kirata.
Cikin yanayin alhini ta kalleni haɗe da cewa "abbana yana kirana.
Da zuwanta ko cikakken 1 minute batai ba ta dawo gareni fuskarta cike da annuri tace "abbana yace mushiga ciki.
=> 7
Koda na kalleta sai nayi murmushi haɗe da cewa "ai tunda mungaisa ba sai na shiga ciki ba.
Jin haka ne yasa tamin wani kallo haɗe da cewa to ai baka gaisa da umma ba.
Wannan furucin da naji tayi ne yasa ba yadda na iya haka mushiga gidan tare.
Da shigata gidan bayan nagaisa da mahaifiyarta haɗe da mahaifinta sai mahaifin nata yace "wato saboda tsabar wulaƙanci kazo har gidan naku shine zakaƙi shigowa sai dai katsaya a waje ko?
Cikin yanayin kunya na sunkuyar da kai na ƙasa haɗe da yin wata yar dariya.
Ganin yadda su barni dagani sai kAmeena a falo ne yasa nashiga ruɗani domin bansan abun da hakan yake nufi ba.
Shirun da Ameena taga nayi ne yasa ta ɗanyi murmushi haɗe da cewa "umma da abba duk tunaninsu soyayya ce a tsakanina dakai.
Amma kar hakan yasa ka damu zuciyarka domin ni tamkar ƙanwa nake a gareka.
Sai dai kuma tun da nake a rayuwata ban taɓa jin farin ciki irin na wannan ranar ba.
Saboda wannan shine karo na farko ko kuma ince rana ta farko da na taɓa tsayawa da wani a yayin da yasa ayi sallama dani domin duk wanda zaizo abbana ko mahaifiyata basa taɓa barina naje gareshi.
Sai gashi a lokacin daka aiko Ameera domin ta kirani mahaifiyata ce tace natashi naje.
Wallahi jinayi gaba ɗaya jikina yai wani iri saboda bansaba tsayawa da kowa ba.
Jin haka ne yasa na kalleta haɗe da cewa "haƙiƙa duk wanda ya sameki a matsayin wadda zata kasance uwar yayansa yayi babbar sa'a domin iyayenki sun baki tarbiyyar da dole ne ayi alfahari dake.
Abu kamar wasa sai kalaman khadeeja suyiwa zuciyata tasiri wanda hakan yasa tunaninta yai nisa a zuciyata wanda hakan yasa a ƙarshe na yanke shawarar neman soyayyar Ameena.
Buƙatar kasancewar Ameena a shafin rayuwata ne yasa na aikamata da wasiƙa kamar haka.
{{Amincin Allah ya tabbata a gareki.
Zanso kafin ki kaiga karanta dalilin rubuto wannan wasiƙar kifara yin murmushi murmushinki shine zai taimaka wajan bani tabbacin samun abun da nake da buƙata a gareki.
Murmushinki alokacin da na jera tare dake a yayin da zan shiga gidanku ya bani tabbacin zaki kula da duk wanda ya mallakeki a matsayin mata.
Haƙurinki ne ya bani tabbacin duk wanda ya aureki bazai taɓa samun ɓaci rai a dalilinki ba sai dai idan ya kasance shiɗin mai son zuciya ne.
Alkunyarki haɗe da lafazinki sun isa su bada tabbacin akwai tarbiyya a tattare dake.
Dabadan kinfi ƙarfin ajinaba da ba abun da zai hana a fafata dani a fagen sonki sai dai kuma gashi gobe zan tafi makaranta tare da A'isha amma dan Allah zanso ace gobe da misalin ƙarfe 8 na safiya kizo domin kiga tafiyarmu saboda hakan zai yi matuƙar sani a farin ciki.
Bayan gari ya waye har mu gama shirinmu banga Ameena tazo ba koda na duba agogo naga 8:20 gaba ɗaya sai na cire rai da ganin Ameena.
A yayin da nake tsaka da tunanin Ameena sai mahaifina ya fito daga ɗaki hannunshi riƙe da key ɗin mota.
Koda ya kalleni sai yace "maza ku ɗakko kayanku.
Haka na shiga ɗaki domin ɗakko kayan da na shirya tafiya dasu.
Fitowata daga ɗaki kenan sai Ameena ta shigo.
Cikin yanayin sakin fuska mu gaisa sannan ta karɓi jakar da nake riƙe da ita.
Cikin yanayin sanyin jiki ta fita da jakar ta samin ita a mota.
Bayan na ƙarasa kusa da motar sai ameena ta kalleni fuskarta cike da damuwa ba tare da ta iya cewa komai a gareni ba.
Ganin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "to Ameena zamu tafi zanso kiyi mana fatan alkhairi.
Cikin yanayin kunya tayi ƙas da kanta haɗe da cewa "to yayana Allah ya kaiku lafiya ya kuma tsarki daga sharrin halitta Allah kuma ya baku ilimi mai amfani zanso kuma ka kula da kanka kamar yadda zan kulama da kai na.
Bayan mun isa garin Katsina sai mahaifina ya saukemu a gidan da ya karɓar mana haya wanda zai zamto masauki a garemu kenan.
Washe gari da sassafe bayan nayi wanka a yayin dana buɗe jakata sai nayi ido biyu da hotunan Ameena haɗe da wata wasiƙa wanda hakan yasa farin ciki a gareni.
Bayan na duba hotunan sannan na buɗe wasiƙar domin karanta abun da ke cikinta.
Abun da na gani a wasiƙar shine "Naji dukkanin kalaman ka a game da wasiƙar daka aikomin wanda hakan yasa na fahimci abun da kake nufi.
Amma sai dai kuma an samu akasi domin akwai amanar soyayyar wani a gareni, dan haka ina mai baka haƙuri a game da rashin cimma wannan burin naka a gareni amma idan da zaka karɓi shawarata da ka nemi soyayyar A'isha domin naga alamun tana matsanancin son ka.
Tun daga wannan ranar nayi ƙoƙarin kawar da soyayyar Ameena daga zuciyata amma sai dai kuma nakasa cire tunaninta daga zuciyata.
Ba yadda na iya haka dai makauniyar soyayya ta sake shiga tsakanina da A'isha.
Kwatsam rannan da misalin ƙarfe 12 na rana bayan na fita yawo tare da A'isha sai naji kira ya shigo wayata.
Koda na duba sai naga ai ƙanwata ce take kira na.
Koda na amsa kiran bayan nayi sallama sai naji tace "haba yaya wannan wace irin rayuwa ce ya zaka cutar da wadda muke da kusanci da ita to bari kaji wallahi saƙon mutuwar Ameena yana gaf da isowa gareka sannan ta yanke wayar.
Jin haka ne yasa na tuhumi kaina da kaine ta hanyar cewa "to meye kuma a tsakanina da Ameena da har ake neman dangantani da batun mutuwarta.
Shirun da A'isha taga nayi ne yasa ta nemi jin abun da ke faruwa koda na sanar da ita abun da khadeeja ta sanar dani sai ta jinjina kai haɗe da cewa "to bari kaji idanma sonka takeyi tun wuri gwara ta janye kanta daga mafarkin kasancewarka a tare da ita, idan kuma ba haka ba to wallahi zata aikata kuskure mafi muni a rayuwarta.
Cikin yanayin mamaki nace "haba A'isha wannan wane irin banzan furuci ne idanma sona ɗin takeyi ai ba haramun ba ne dan na aureta.
Jin haka ne yasa A'isha ta kalleni haɗe da cewa to wallahi zan iya aikata ko mene ne domin ganin haka ba ta faru ba, sannan taja wani dogon tsaki ta fice daga motar.
Haka dai na koma masaukinmu ba tare da A'isha ba.
Ganin yadda a ɗauki tsawon awa ɗaya da rabi ba tare danasa Aisha a idona ba ne yasa nayi tunanin A'isha kano ta wuce kuma hakan zai iya haifarmin da babbar matsala.
Cikin gaggawa nima na ɗauki hanyar kano.
Ƙarfe 6 na isa gida, da shigata gida ko gaisawa ban kaigayi da mahaifiyata ba sai mahaifina ya ɗaukeni da mari haɗe da cewa "mutumin banza kawai yanzu har ni zaka wulaƙanta a garinnan.
Wato kai ga ɗan rainin hankali , haka ka ɗauki ƙafa kaje har gidan abokina domin neman soyayyar yarinyarshi bayan ta aminta da kai daga baya kuma sai ka janye kanka a gareta ko?
Cikin yanayin alhini nace "abba wallahi bansan komai a dangane da wannan batun ba.
Cikin yanayin ɗaga murya mahaifina yace "kena nufin ƙarya akema bakaje gidansu ba kenan?
Buɗar baki na sai nace "tabbas naje gidansu amma....
Nan take mahaifina ya dakatar dani haɗe da cewa "maza ka fita kaje ka sameta a asibitin da take kwance domin tabbatar mata da cewar zaka aureta.
Ba yadda na iya haka nayi waje domin tunkarar inda Ameena take.
A yayin da nayi ido biyu da Ameena kwance a gadan asibiti ba ƙaramin tausaya mata nayi ba.
Ciki yanayin alhini tace "yayana kataimaki rayuwata bazan iya jure rashin kaba.
Buɗar bakina sai nace "amma ameena ya zakimin haka, karfa ki manta ke da kanki ki sanar dani cewar akwai wanda kikeso, kuma ya kikeson nayi a game da soyayyar wadda ki bani shawara akan cewar na nemi soyayyarta?
Kallona tayi haɗe da cewa "bani da masaniyar komai a dangane da wannan maganar domin wasiƙar da nasa a jakarka wasiƙa ce ta amincewar soyayyata a gareka.
Daga baya kuma sai ka aikomin da wasiƙar da ta sani zubar da hawaye kuma ka haɗo da ainashin wasiƙar dana rubutama.
Cikin yanayin mamaki nace "a"a Ameena ni ban aiko miki da wata wasiƙa ba Kuma wasiƙar dana gani a jakata tasha banban da wasiƙar amincewar soyayya domin wasiƙa ce ta nuna rashin samun nasara ga wanda ya nemi tayin soyayyar wata.
Wata jaka naga ta nunamin haɗe da cewa "idan ka duba cikin jakarcan zakaga wasiƙar dana rubutama wadda kabayar a dawomin da ita haɗe da wadda ka rubutomin domin wata macece ta kawomin wasiƙar kuma cewa tayi kai ne ka bata da hannunka domin ta kawomin.
Koda na duba wasiƙar sai na kalli Ameena haɗe da cewa "tabbas wannan aikin A'isha ne.
Zama nayi a kusa da Ameena haɗe da cewa "idan har a kaina ne ki kamu da wannan rashin lafiyar to kisa a ranki tamkar kin warke domin daga yau nazama mallakinki.
Da komawata gida sai nayi arba da A'isha zaune a falo tare da iyaye na.
Aisha ba ta tashi auneba sai taji saukar mari a fuskarta.
Cikin yanayin mamaki mahaifina yace "me tama zaka mata irin wannnan marin?
Nan take na miƙawa A'isha wasiƙun da na ɗakko a jakar Ameena.
Rai na a ɓace nace "waya aikama Ameena waɗan nan wasiƙun?
Nan take ta fashe da kuka haɗe da cewa "wato sai da kagama cin moriyata sannan zaka wulaƙantani a lokacin da kasan bani da wani jigon da ya wuce kai?
Nayima duk abun da ka buƙata a gareni.
Kaga tsuraicina a lokacin da bani da niyar raba jikina da sutturar da nake sanye dasu.
Ka kwanta dani ba'a son raina ba alokacin da sha'awarka ta taso.
Kawai saboda naƙi amincewa da batun zubar da cikin da kayimin shine zaka ɓullo da wadannan hanyoyin domin nisanta kanka dani?
Bani kainaba hatta iyayena sai da su girgiza a yayin da suji fitar waɗan nan kalaman daga bakin A'isha wanda hakan yasa naga mahaifina yamin wani bahagon kallo.
=> 8
Cikin yanayin tashin hankali naji mahaifina ya furta kalmar "innalillahi-wa'inna ilaishi raji'un"
Jin haka ne yasa na kalli A'isha a tsorace haɗe da cewa "a munanan kalaman dana sani ba wata kalmar da zan iya dangantaki da ita saboda duk wasu kalaman da zan furta a gareki su kansu tsoranki sukeji.
Kin tarwatsa rayuwata bakibarni nayi karatuba baki barni nazauna lafiya da iyayena ba.
Sannan na kalli mahaifina nace "abba a maganar A'isha a kwai gaskiya a ciki amma ƙarya ita tafi yawa a kalamanta.
Ida nuwana suna zubar da hawaye nace da mahaifina "na fara haɗuwa da A'isha ne tun a social network wato facebook kenan.
Domin a wannan lokacin a tsakanin ni da ita ba wanda yasan cewar mu ƴan uwan juna ne.
Da kalaman batsa ta fara tunkarata a yayin dana haɗu da ita a facebook wanda hakan yasa naji haushi har ta kaiga na furta mata munanan kalamai.
Jin haushin haka ne yasa ta shiryamin gadar zare ta hanyar ba wani kuɗi domin ya zama abokina.
A yayin da abotarmu tayi nisa sai ya haɗani da A'isha a matsayin ƙanwarshi domin mu gaisa.
Ita kuma sai tayi amfani da wannan damar wajan bijiromin da batun soyayya wanda hakan yasa ta canza ra'ayin zuwana makarata jahar katsina izuwa jahar naija/minna.
Haka dai muci gaba da soyayyarmu domin har gidansu take kaini kafin na gano gaskiyar al'amarin kenan.
Sai da soyayyarmu tayi nisa kwatsam sai ta sanar dani cewar itafa tana da miji.
Ganin yadda rai na ya ɓaci ne yasa ta sanar dani cewa ita ba musulma bace.
Kuma tabbas maganarta taso tayi kama da hakan domin a kwai ranar da ta taɓa yin wata shiga wadda ba wanda zai ganta har yai tunanin dangantata da hausawa balle ayi batun musulunci.
A yayin da ta sanar dani cewa ita ba musulma bace saita
ƙara da cewa "amma ba ta da wani burin da ya wuce son zama musulma.
Haka dai na gama ba iyayena labarin komai kamar yadda na baku labarin abun da ya faru a tsakani na da ita tun acan baya.
Sannan na kalli mahaifina haɗe da cewa sai dai kuma a halin da nake ciki yanzu bansan dalilin da yasa takeson shiga tsakanina daku ba.
Jin jina kai tayi sannan ta nunani da yatsanta haɗe da cewa "amma gaskiya ba tsoran Allah a tattare dakai.
Tabbas a facebook na fara haɗuwa da kai tun kanayumin maganganun batsa ina kaucema har takaiga na saba da jinkalaman banza daga bakinka wanda hakan yasa duk daran da zaizo ya wuce muddun banyi sex chat da kai ba to banajin daɗin rayuwata.
A hankali dai har abun ya gama bimin jiki wanda hakan yasa yake tafiyayya tun daga nan kano har garin jos badan komai ba sai dan yayi amfani dani.
Hotel mai tsada yake kaini domin yaji daɗin aikata duk abun da yaso dani.
Gudun kar ku san halin da yake ciki ne yasa aranar da yaje garin Jos yake dawowa gida a ranar.
Yana sane ya canza ƙudirin zuwa jahar katsina makaranta saboda yasan jahar Naija itace jahar da tafi dacewa dashi a jahohinmu na arewa wajan gudanar da duk wani iskancinshi ba tare da wani yasamai ido ba.
Buƙatar ya riƙa kwantawa dani ne yasa ya huremin kunne wajan biyoshi jahar naija kuma idan naje jahar naija ina ɗaukar sati ba tare dana koma wajan iyayena ba.
Haka mahaifina ya ƙaraci dukana har ya gaji ya barni.
A yayin da mahaifiyata zata tafi aikin hajji saita kawoni nan domin ku kula dani saboda tasan idan tabarni acan lalacewar sai tafi haka saboda mahaifina ba mazauni bane.
Bansani ba ashe da ɗan uwana na jini nake aikata aikin da bai dace ba.
Kuma duk hakan ya samo asali ne a sakamakon rashin zumuncin da yake a tsakaninmu.
Haka muyita yima junanmu kallan kallo a yayin da muyi ido biyu da juna saboda bamuyi tunanin mu ƴan uwan juna ba ne.
Nayi ƙoƙarin mu kawar da wannan mummunar ɗabi'ar da take a tsakaninmu amma yaƙi domin ko a cikin gidan nan yasha rungumata ya sumbaceni ya kuma kwanta dani aduk lokacin da yaso.
A lokacin da ya fahimci ina matuƙar jin tsoran kar asirinmu ya tonu sai ya ɓullo da batun mu wuce jahar katsina makaranta.
Ganin kar wannan ɗabi'ar tamu tayinisa ta yadda zaku fahimci halin da muke ciki ne yasa na bashi shawarar muyi aure amma yaƙi amincewa domin har marina sai da yayi a lokacin da na bashi wannan shawarar.
Ba yadda na iya haka na amince da wannan buƙatar tashi saboda yayi matuƙar mutuwa a kaina.
A ranar da zamu tafi jahar katsina sai ameena ta shigo domin taga tafiyarmu.
A lokacin da ta karɓi jakarshi sai shikuma ya koma ɗaki domin ɗakko sauran kayan dake ɗakin nashi.
Ina kallonta ta zuge jakarshi tasa hotanta haɗe da wasiƙa a ciki alhalin kuma ita batasan ina kallonta ba.
Tana fitowa daga falo sai nikuma na karɓi jakar sannan ta koma domin ɗakko wasu kayan.
A wannan lokacin ne na zare abun da tasa a jakar ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin gaggawa na shiga ɗakina domin karanta abun da ta rubuta a wasiƙar.
Koda na karanta wasiƙar nan take na yagi paper nayi mata wasiƙar da ranta zaiyi matuƙar ɓaci a matsayin shi ya rubuta
A yayin da take tsaka da ba iyayenta wannan labarin sai ta kalleni haɗe da cewa "idan baka mantaba a yayin damu fito daga gida muna cikin tafiya a mota a yayin da muzo kusa da gidan su Sameera na buƙaci abba ya tsaya domin buƙatar naba Sameera wani saƙo, to a wannan lokacin da na shiga gidan sai na ba Sameera wasiƙar da na rubuta na kuma sanar da ita cewar a kwai wata mai suna Fadeela zatazo domin kaɓar wasiƙar a wajanta.
Fadeela ƙawata ce wadda nayi kartu da ita a garin jos amma ita yar Kano ce haka ta taso tun daga hotoro ta karɓi wasiƙar dana rubuta da hannuna takaima Ameena.
Bayan mun isa jahar katsina a lokacin da ka shiga toilet domin yin wanka sai na rubuta wasiƙar da zatasa ka manta da batun Ameena wanda hakan zai sa ka riƙeni a matsayin wadda zaka aura haka na haɗa da hotunan nata nasa a jakarka amatsayin ita ta rubuto wasiƙar.
Tun da mu isa garin katsina ba ranar da baka kwantawa dani haka ne yasa nayi yinƙurin komawa wajan iyayena amma sai ya riƙeni yana kuka domin karna tafi na barshi.
Ba kuma komai nake guduba illah zubewar mutuncin iyayenmu musamman a yayin da na ɗauki juna biyu.
Sai gashi duk abun da nake gudu ya faru tunda har na ɗauki ciki a dalilin kwantawar da yake yawan yi da ni.

Bayan ta gama ɗaureni da waɗan nan manyan sharrikan nata sai ta kwanta a jikin mahaifiyata tana kuka haɗe da roƙonta ta hanyar cewa "dan Allah ayi gaggawar yimana aure tun kafin cikin da nake ɗauke dashi ya fito fili domin wallahi banason azubar dashi.
Jin haka ne yasa mahaifina yace "kinga bari kuka in Allah ya amince acikin satin nan za'a ɗaura auranku kuma ba wanda ya isa yayi batun zubar da cikin da kike ɗauke dashi.
Na buɗa baki zanyi magana sai mahaifina ya jefeni da takalmi.
Ba yadda na iya haka nayi waje cikin yanayin damuwa.
Fitowata daga gida kenan sai Nusaiba kanwar Ameena tazo gareni a gaggauce tana kuka.
Cikin yanayin kuka tace "Ameera tabar duniya tana kiran sunanka.
Jin haka ne yasa na tunkari asibitin da'a kwantar da Ameera.
Da zuwana sai na taradda ita tana numfashi sama-sama ashe dogon suma tayi wanda hakan yasa a cire tsammaninta.
Koda taji muryata a yayin da nayi sallama cikin yanayin mawuyacin hali ta riƙa kiran sunana tana kuka wanda hakan yasa nima kai na na zubar da hawaye.
Haka na zauna a kusa da ita ta wanda hakan yasa ta riƙe hannuna tana cewa "yayana zafi nakeji a cikin zuciyata dan Allah karka tafi ka barni saura mintuna kaɗan nabar duniya domin banajin cewar zan iya cigaba da rayuwa domin a halin yanzu bani da burin da ya wuce nabar duniya a yayin da nake riƙe da hannun masoyina.
Na buɗe baki zanyi magana sai naji taja wani dogon numfashi haɗe da furta kalmar shahada.
Inaji ina gani haka Ameena tabar duniya riƙe da hannuna.
=> 9
Haka iyayan ameena haɗe da sauran al'ummar gari suyita jifata da mugayen kalamai a bisa tunanin cewar nine musabbabin jefa rayuwar Ameena a mawuyacin halin da yai sular rasa rayuwarta.
Kasancewar A'isha a tattare dani ba ƙaramin tashin hankali ya zamewa rayuwata ba wanda hakan yasa na zubar da hawayen da bansan iyakarsa ba.
Na tabbata duk wanda ya karanci halayyar A'isha indai mai hankali da tunani ne bazaiso ya zauna da ita koda na tsawon minti ɗaya ba balle ayi batun aure a tsakaninsu.
To amma ni ba yadda na iya dole na ko naƙi ko naso sai A'isha tazama matata domin ta wannan hanyar ne kaɗai zan iya kare mutuncin iyayena nakuma rama cin mutuncin da tayimin.
Idan na kwanta har matsuwa nake gari ya waye saboda ɓacinran da nake ciki bana samun sakewa.
Kwatsam da sassafe ko breakfast banyi ba na fita daga gida har na kai bakin gate sai A'isha ta dakatar dani ta hanyar kirana.
Haka nayi banza da ita fitowata kenan sai jinayi ta riƙe hannuna sannan ta tsaya a gabana ko alamar tsoro babu a tattare da ita tace "nifa ko kaɗan babu niyar aure a tattare dani yanzu.
Sannan ta kalleni haɗe da cewa "nayima alƙawarin muddun ka sake kwantawa dani na rana ɗaya to ina mai tabbatarma cewar zanbi duk wata hanyar da ta dace wajan lalata wannan auren namu da za'ayi zan kuma wankeka daga ƙazafin da nayima kuma bazaka sake afkawa a kaidina ba.
Idan kuma har kabari ayi aurena da kai to zaka tsunci kanka a mawuyacin halin da baka taɓa tunanin kasancewar irinshi a rayuwarka ba.
Koda naji haka sai na kalleta haɗe da cewa "ai kinyi gaggawar toshe duk wata hanyar da wannan ƙudirin naki zai cika domin bani da wani burin da ya wuce na kare mutuncin iyayena dan haka tunda har kiriga ki bayyanama iyayena abun da na daɗe ina kare kaina daga afkawa cikinsa to babu sauran wani tsoran da zaisa na sake biye ma halayyarki da har zan aikata zina dake.
Kuma kona aureki zan zauna dake ne a matsayin matata amma ba yadda za'ai na kusanceci saboda nasan ke mazinaciya ce wadda take mallaka kanta ga wasu wanda har hakan yai sular samar da juna biyu a tattare dake.

Buɗar bakinta sai tace "idan har ni mazinaciya ce to kaima babban mazinaci ne tunda ka taɓa kwantawa dani.
Jin haka ne hasa nayi murmushi haɗe da cewa "Ni nasan ko a lahira Allah bazai kamani da laifin aikata Zina da ke ba saboda sanin kankine fyaɗe kiyimin sannan na juya nayi tafiyata.
Bayan anyi aurena da A'isha a ranar damu tare a sabon gidan da mahaifina ya mallakamin tun kafin na furta kalmar komai a gareta sai ta durƙusa a gabana haɗe da cews "dan Allah kayi haƙuri a game da ƙazafin da nayima akan batun cikin da nace ina ɗauke dashi domin tun da nake a rayuwata ban taɓa kusantar wani namiji ba sai kai kaɗai kawai nayi haka ne saboda bani da wata hanyar da zanbi dan ganin nazama matarka.
A wannan lokacin ban aminta da wannan furucin nataba har saida mu halarci asibiti.
Koda a tabbatarmin da cewar bata da juna biyu sai nayi shiru na ɗan wani lokaci zuwacan sai na kalleta haɗe da cewa ke ƙanwata ce ta jini amma karki damu kawai zanso ki ɗan ƙauracemin na ƴan wasu kwanaki.
Duk da cewar an ɗaura aurena da ita ban yarda na kwana tare da ita ba.
Ina zaune a falo tazo ta zauna kusa dani fuskarta cike da damuwa tace "yau kwana ukku kenan da ɗaura auranmu amma kaƙi sakin jiki dani kuma ai katabbatar da cewa bana ɗauke da juna biyu dan Allah....
Saina dakatar da ita ba tare dana gamajin abun dake bakintaba ta hanyar cewa "dakata banason jin wasu kalaman dasu danganci abun da ya shafi rayuwar damu bari a baya.
Misalin ƙarfe 3 na rana wayata tai ringing koda na amsa kiran sai na furta kalmar "innalillahi-wa'inna-ilaihi-raji'un" wanda hakan yasa A'isha ta nemi jin abun da ya faru.
Buɗar bakina sai nace "mahaifinki ne yai Accident kuma ga dukkan alamu.... Sai nayi shiru ba tare dana ƙarasa ba.
Nan take ta kwanta a ƙasa tana kuka haka na lallaɓata muhau mota zuwa garin jos.
Da shigarmu falo sai tayi kaciɓus da mahaifinta zaune a falo cikin yanayin alhini mai tattare da mamaki tace "abba!! Sannan ta ruga zuwa gareshi haka ta kwanta a jikinshi tana kuka haɗe da cewa dama abba ba Accident kayi ba?
Buɗar bakina sai nace "tabbas mahaifinki ba haɗarin da ya faru dashi kawai nayi haka ne domin nakawoki garesu.
Nan take na kalli iyayenta nace "abba dan Allah kuyi haƙuri domin an ɗaura aurena da A'isha ba tare da saninku ba.
Ba kuma komai ne yasa hakan ta faru ba sai dan wata ƴar matsalar da ta faru a tsakanina da A'isha wanda a yanzu zanyi maku bayanin komai a dangane da abun da ya faru a tsakanina da ita.
Nan take nayi masu bayanin komai kamar yadda nayiwa iyayena bayanin abun da ya faru.
Nanfa itama ta sake maimaita abun da ta fadama iyayena.
Koda nasakejin ta furta cewar tana ɗauke da juna biyu wanda take da tabbacin ni nayi mata shi cikin yanayin kwarin guiwa nace idan har aje asibiti a tabbatar da cewa tana ɗauke da ciki to na yadda da duk maganar dana fada ƙarya ce, maganar da ta faɗa itace gaskiya.
Bayan mun halarci wani asibitin dake garin Jos ba kaɗan kai na ya ɗaure ba domin a yayin da likitan da ya auna A'isha ya tabbatar mana da cewar tana ɗauke da juna biyu abun ya banu mamaki.
Haka A'isha ta kalli mahaifinta tana kuka haɗe da cewa "ba yadda baiyi ba domin na zubar da cikin amma naƙi haka ya takuramin har saida ya kaini wani ƙaramin asibiti domin zubar da cikin da nake ɗauke dashi gudun karna salwantar da rayuwar ɗan dake cikina ne yasa na biya likitan kuɗi masu yawa domin kar ya zubar da cikin na kuma umarceshi da ya sanar dashi cewa ya zubar da cikin alhalin kuma ba'a zubar da cikin ba.
Duk ya shirya maku wannan ƙaryar ne saboda yana tunanin cikin anzubar dashi.
Nan take mahaifinta yamin wani kallo haɗe da cewa kuwuce muje gida.
=> 10
Da isarmu gida sai mahaifin A'isha ya kalleni haɗe da cewa "yanzu abun da kayi ka kyauta kenan?
Fuskata cike da damuwa na kalli A'isha sannan na kalli mahaifinta nace "abba kuyi haƙuri kuma kamar yadda ku kasance iyayena to ba abun da zaisa nayi ƙasa a guiwa wajan kare mutuncinku duk da cewar akwai sarƙaƙiya mai tsauri a tsakanina da A'isha hakan bazaisa na wulaƙantata ba dan haka zan riƙeta a matsayin matata na kuma ba ta duk wata kulawar da ta dace kamar yadda addinin musulunci ya tanadar mana.
Duk da irin wannan kalamin da nayiwa mahaifin A'isha baisa ya kalleni da mutunci ba haka yariƙa furta munanan kalamai a gareni.
A gaban idona kuma ya zazzagi mahaifina a waya wanda hakan yasani zubar da kwalla.
Cikin dare nabar garin jos tare da matata A'isha sanin muhimmancin aure ne yasa natsaya a hanya domin nasai mata abin da zataci saboda na lura akwai alamun buƙatar abinci a tattare da ita.
Tun kafin na ƙarasa wajan masu abincin na laluba aljihuna banji wallet a tattare dani ba wanda hakan yasa nayi gaggawar komawa motar domin dubawa.
Ganin ban ganta a motar ba ne yasa nayi tunanin cewar faɗuwa tayi.
Da yake da waya biyu nake amfani babba da ƙarama saina ɗauki ƙaramar na tunkari wajan masu abincin da ƙudirin neman taimako.
Da zuwana bayan nayi sallama mun gaisa sai nace "baiwar Allah ina buƙatar taimako ne idan da hali kuma bazaki takura ba domin ina tare da matata ne kuma gashi tanajin yunwa shine nake buƙatar abinci domin na bata taci kuma gashi ba kuɗi a tattare dani dan Allah ki taimaka ki riƙe wannan wayar tawa a matsayin abincin da zaki bata taci.
Bayan ta karɓi wayar sai naga ta jinjina kai haɗe da cewa "ba damuwa.
Haka na kira matar tawa wato A'isha kenan domin tazo abata abinci taci.
Damuwar da nake tattare da ita ne yasa naji bana buƙatar wani abinci.
Ni a fara kawoma abincin kafin a kawoma A'isha.
Buɗar bakina sai nace "ni bana buƙatar abinci ruwa kawai nakeson a taimakamin dashi domin nasha wanda hakan yasa ana A'isha abincin ni kuma a kawomin ruwan da zansha.
Bayan A'isha ta kammala cin abincin sai nayiwa mai abinci godiya sannan mu tashi da niyar wucewa.
Nan take mai abincin ta tsayar dani koda ta ƙaraso gareni sai tace "bawan Allah ka sadaukar da wayarka domin buƙatar kare haƙƙin matarka daga azaftuwar yunwar da take damunta alhalin kuma wayar daka bayar ta ninka kuɗin abincin dataci.
Sannan tace "tabbas kai mutun ne mai adalci sannan ta kalli A'isha haɗe da cewa "baiwar Allah kiriƙe mijinki da muhimmanci domin samun kamarshi zaiyi matuƙar wahala sannan ta miƙomin wayar haɗe da cewa "karɓi wayarka nayafema kuɗin abincin da taci.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "baiwar Allah kalaminkima kaɗai ya cancanci na mallaka miki abun da yafi ƙarfin wannan wayar dan haka zanso ki riƙeta domin taimakon da kimin yafi ƙarfin wannan wayar a gareni, dan haka ki riƙeta kodan ki riƙa tunawa damu.
Haka dai mu rabu muna yima juna godiya.
Misalin ƙarfe 3 na dare mu isa gida a yayin dana sauka domin buɗe gate sai naga itama A'isha ta sauka.
Buɗar bakina sai nace "ya kuma zaki sauka? ki bari mushiga tare mana.
Haka ta durƙusa a gabana tana kuka haɗe da cewa dan Allah mijina kayi haƙuri ka yafemin cutarwar da nayima yafiyarka itace zata bani damar shiga gidanka itace kuma zata bani ikon kallona a matsayin matarka.
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai nace "tashi ki koma mota!!
Koda mu shiga falo sai ta riƙe hannuna tana kuka haɗe da kwantowa a jikina tana mai roƙona domin na yafe mata.
Haka na dafa kafaɗarta haɗe da cewa "dan Allah A'isha ki daina kukan nan ki sanifa alƙawari na ɗaukarwa iyayenki akan cewar zan kasance mai kulawa dake ta hanyar kaucema duk wani abun da zai haifar da damuwa ko ɓacin rai a tattare dake.
Zanso ki gane cewa yanzu rayuwar da muke ciki ta banbanta da wadda mu bari a baya.
Domin zaman aure ba zama ne kamar na aboki da aboki ko ƙawa da ƙawa ba.
Domin zaman aure zama ne irin wanda akeson ya kasance zama na tsawon har abada ba tare da rabuwa ta shig tsakanin ma'aurata ba.
Kuma hakan bazai taɓa yiwuwa ba har sai ansa.
=Haƙuri.
=Kyautatawa.
=Kawaici.
=Yafiya.
To amma mafi yawancin muta ne suna kasa yima junansu uziri musamman a yayin da wani akasi ya gifta a tsakaninsu da abokan zamansu.
Sannan na kalli aisha haɗe da cewa karki manta ke a matsayin ƙanwata kike koda ace babu aure a tsakanina dake to ba yadda za'ai na iya ɗaukar fansar abun da ki aikatamin saboda tun kafin na haɗu dake nasan cewar kaidin mace ya zarce tunanin duk wani ɗa namiji.
Kuma ba wani abu ne yasa kiga nayi ƙoƙarin fahimtar da iyayena haɗe da iyayenki gaskiyar abun da ya faru a tsakanina dake ba, sai dan ƙoƙarin kare mutuncina a garesu ba wai dan ɗaukar fansa ba.
Kuma ita ɗaukar fansa al'adace wadda ta samo asali daga yahudawa marasa tawakali dan haka bazanso na kasance mai ƙoƙarin ɗaukar fansa ba, domin haƙuri manzon Allah yai mana koyi dashi.
Saboda haka zanriƙeki da mutunci haɗe da kyautatawa na tsawon har abada ɗan da zaki haifa kuma zan riƙeshi a matsayin ɗana.
Haka ta kwantar da kanta a kirjina cikin yanayin kuka tace "kai ne mutumin daka fara kwantawa dani domin ban taɓa mallaka kai na ga wani ba domin cikin dana sanar da iyayenmu cewar ina dauke dashi wallahi, wallahi, wallahi ƙarya ne.
Gwajin da'amin na farko a yayin da kakaini asibiti wanda a tabbatarma da cewar bana ɗauke da ciki shine gaskiya.
Gwaji na biyun da'amin a garin jos wanda a tabbatama iyayena cewar ina ɗauke da juna biyu ƙarya ne domin kuɗi na turama likitan da ya aunani ta account ɗinshi domin buƙatar ya bayar da tabbacin cewar ina ɗauke da ciki.
Tsayawar damuyi a wajan mai abincin da ke garin Jos ne yasa na gane kuskurena.
Haka tana kuka tana cewa "dan Allah ka yafemin kaji mijina?
Cikin yanayin tausasa murya na dafa kafaɗarta haɗe da cewa "A'isha karki sake zubar da hawaye a game da wannan al'amarin domin na yafe miki.
Sai ta jinjina kai haɗe da cewa "to nagode mijina.
Tun daga wannan ranar na ɗauki alwashin mantawa da duk wani abun da A'isha ta aikata a gareni
Kwatsam da safe ina zaune a falo sai ganin shigowar jami'an ƴan sanda nayi tare da mahaifina.
Na buɗa baki zanyi magana sai mahaifina ya dakamin tsawa haɗe da cewa idan har ka sake ka furta wata magana to sai na tsinema ba yadda na iya haka naja bakina nayi shiru.
A gaban A'isha asamin ankwa da ƙudirin wucewa dani zuwa station.
=> 11
Ganin haka ne yasa aisha tayi gaggawar durƙusawa a gaban mahaifina domin roƙonshi akan ya kyaleni.
Cikin yanayin ɗaga murya yace "ba yadda za'ai na bari wannan mutumin banzan ya zubarmin da mutunci a faɗin duniyarnan.
Koda A'isha taga haka sai tace "A'a abba ko kaɗan bashi da laifi.
Domin.... Raina a ɓace nace "A'a A'isha a matsayina na mijinki ina mai umartarki da kirki kuskura kiyi ƙoƙarin furta wata magana.
Jin haka ne yasa ta kalleni idanunsa suna zubar da hawaye haɗe da cewa dan Allah kayi haƙuri domin fito da wannan gaskiyar itace zata samar da kwanciyar hankali ga rayuwata koda kuwa faɗar gaskiyar ce zata kawo ƙarshen rabuwata da kai.
Haka mahaifina ya kalli A'isha haɗe da cewa "Yanzu ke har kin manta da irin cin mutuncin da yai miki.
To yana da kyau kiyi tunanin cewar ƙoƙarin kare mutuncinki haɗe dana iyayanki ne yasa mu tilastamai akan saiya aureki da badan hakaba daba yadda za'ai nabari ya aureki saboda ke ba tsararsa bace domin shi baisan mutuncinmu haɗe da na sauran danginsa ba wanda har hakan yasa ya aikata abun kunya a gareki.
Na aurar dake a gareshine ba tare da sanin iyayenki ba saboda banason hakan yai sular ɓacin ransu domin hakan zai iya haifarda saɓani a tsakaninmu da iyayenki.
Amma saboda shi ba ɗan mutunci bane har sai da ya ɗaukeki zuwa ga mahaifanki domin ya zubar mana da mutunci kuma buƙatarshi ta biya tun da har mahaifinki ya kirani a waya domin sauke baƙin cikinshi ta hanyar zagina.
Haka ne yasa nayi ƙudirin zartarmai da mummunan hukunci ta hanyar dangantashi da gidan yari.
Cikin yanayin kuka A'isha tace "ba wadda ta cancanci hukunci face ni.
Sannan ta nunani haɗe da cewa "abba na koyi darasi da dama ta hanyar haɗuwata da wannan yayan nawa duk da irin azabar dana ganamai ta hanyar shiryamai mugayen makirci haɗe da ƙazafi baisa ya gujeni ba.
Haka ta share hawayen dake fuskarta ta kalli mahaifina haɗe da cewa "abba nayi rantsuwa da Allah a a game da abun da ya faru a tsakanina da wannan yayan nawa duk abun da na sanar daku ƙarya ne domin maganarshi itace gaskiya.
Cikin yanayin mamaki mahaifina yace "anya A'isha kina cikin hankalinki kuwa? Yanzu ashe har ƙaunarshi zatayi nisa a cikin zuciyarki wanda hakan zaisa kiyi ƙoƙarin kareshi ta hanyar ɗorama kanki laifi?
Haka A'isha ta kalli mahaifina tace "abba duk da cewar ni mace ce na tabbata a tsakanin mata da maza ba wanda ya kai mace iya makirci.
Halaccin da ya nunamin ne ya tabbatarmin da cewar na aikata kuskure mai ɗinbin yawa a rayuwata.
Sannan tace "abba na cancanci duk wani hukuncin da ya dace a zartarmin kodan hakan ya zama darasi ga rayuwar mutanan da zasu samu wannan labarin.
Koda jami'an ƴan sanda suji haka sai babban cikinsu yace "alhamdulillah tunda gaskiya ta bayyana saiki wuce muje station domin gabatar dake a gaban alƙali wanda hakan zai bada damar zartar miki da hukuncin da ya dace.
Koda naga alamun dagaske yake sai nace "ba yadda za'ai na bari a zartar da wani hukunci ga matata domin sai na amince da wannan maganar tata sannan za'a hukuntata dan haka ba itace da laifiba nine da laifi.
Ni na cutar da ita ta hanyar ɓata rayuwarta wanda har hakan yasa iyayena su aurar da ita a gareni sai gashi kuma Allah cikin ikonsa muna zaune cikin kwanciyar hankali da natsuwa wanda har itama kanta take mamakin faruwar hakan.
Domin buƙatar kasancewata a farin ciki da walwala ne yasa take ƙoƙarin juya laifin dana aikata izuwa gareta.
Dan haka ba dalilin da zaisa na bari a cutarmin da ita.
Haka Aisha ta dafa kafaɗata haɗe da cewa "me yasa kake ƙoƙarin aikata kuskure?
Karfa ka manta ita kanta gangar jikinka idan ka cutar da ita da gangan sai Allah ya maku shisabi a rana gobe ƙiyama.
Dan Allah zanso ka kauda kanka a game da duk wani hukuncin da za'a zartar a gareni domin haka ne zaisa na samu rabo a duniya da lahira.
Na buɗa baki zanyi magana sai ɗaya daga cikin jami'in ƴan sandan yai murmushi haɗe da cewa "tabbas na fahimci irin soyayyar da take a tsakaninku kuma tabbas hakan ya burgeni ganin yadda kuke ƙoƙarin kare mutuncin junanku.
Dan haka zamu rabudaku ne abisa tsoran kar soyayyar da take a tsakaninku ta samu tangarɗa amma zanso kuci gaba da gudanar da soyayyarku kamar yadda kuke tafiyar da ita a yanzu.
Sannan ya kalli mahaifina haɗe da cewa "dan Allah alhaji zanso ka kauda kanka a dangane da wannan al'amarin da ya faru domin ya riga da ya wuce kawai kuyi masu addu'ar zaman lafiya tun da Allah yasa sun gane kuskuransu kuma sun aminta da juna.
Bayan tafiyarsu sai A'isha ta kwanta a jikina tana kuka tana cewa haba yayana me yasa ka hana a zartar da hukuncin da ya dace dani.
Buɗar bakina sai nace "ai muddun ina raye ba yadda za'ai nabari ki shiga wani ƙangin da zai haifar da damuwa a gareki.
Ni dai fatana shine muci gaba da nunama juna soyayya fiye da wadda muke ciki a yanzu.
Wani kallo naga tamin irin na masoya sannan ta lumshe ido haɗe da cewa "ina ƙaunarka domin kai abun alfahari ne a gareni.

Alhamdullah

To yan uwa da abokan arziki anan zan dakata da wannan labarin sai kuma mun sake haɗuwa a wani sabon labarin da zan gabatar maku nan bada jimawa ba domin samar da farin ciki ga zukatanku.

The End
Rubutu Daya Gabata
Rubutu Na Gaba

Mawallafi:

0 comments: