new update
=> 1
abun yana matuƙar bani mamaki haɗe da bani dariya musamman idan naji al'umma suna kuranta soyayya.
Abun har kunya yake bani musamman idan naga wani ya shiga ɓacin rai a dalilin soyayya.
Ban sani ba ashe nima soyayya ba mantawa tayi da shafin rayuwata ba.
Sai dai kuma soyayyar da ta tashi buɗe shafina sai ta buɗomin baƙin shafi wanda banma san ta ina zan fara sarrafa linzamin soyayyar ba.
Lokaci ɗaya khadeeja ta shiga zuciyata ko kuma ince ummey domin da wannan sunan a saba kiranta.
Duk da cewar unguwarmu ɗaya kuma layinmu ɗaya da ummey bamu cika yima juna magana ba, domin ni ko kaɗan banason raini ya shiga hanyata.
Sai bayan ummey ta ɗan tasa nima shekaruna sun ɗan ƙaru.
Sai na fahimci cewar ummey ba yarinya ce mai raini ba, kawai tsantsar alkunya ce a tattare da ita.
Haƙiƙa ummey tana da fasalinta na ƙyau dolene nasata a jerin masu ƙyan sura bawai dan zuciyata tana buƙatar kasancewa a tare da itaba.
Na tabbata duk wanda zaiyi ido biyu da ummey dolene ya yaba da kyawun halittar ta.
Ummey ba ta da wata abokiyar yawo wadda ta wuce anti zainab wato yayata kenan wannan al'amarin yana matuƙar burgeni ganin yadda zainab ta ɗauki ummey tamkar ƙawarta.
Ummey takan shiga gidanmu tayi duk abun da taga dama kamar yadda uauata zainab take gudanar da harkokinta a gidanmu.
Tabbas zuciyata tayi matuƙar kamuwa da son kasancewa a tare da ummey a matsayin wadda zata kasance uwar yayana.
Amma sai dai nakasa samun hanyar da zata kasance mafi sauƙi wajan cimma burina na samun tabbataccen wajan zama a zuciyar ummey.
To amma duk da cewar ummey yarinyace mai ƙananun shekaru ni kaina nasan ummey tafi ƙarfin ajina.
Ganin hakane yasa na nemi tausar zuciyata ta hanyar mantawa da ita.
Amma sai hakan yafi ƙarfina domin ako wace rana nakanyi ido biyu da ummey fiye da sau talatin kai banmasan iyakaba.
Kuma duk sanda zan ganta sai shauƙin sonta ya sake sabon toho a zuciyata.
Gaisuwace kawai take haɗani da ummey idan ba gaisuwa ba bazan iya cewa ga wata maganar datake haɗani da ummey ba.
Tabbas zuciyata tana matuƙar girmama ummey fiye da yadda take ganin girman anti zainab.
Amma sai dai zuciyar tawa ba ta da ikon fito da wannan girmamawar a fili ta yadda ummey zata fuskanta.
A wannan lokacin ne na fahimci girman soyayya.
A yayin da nabi duk wata hanyar da ta dace wajan mallakar numbar ummey sai na sayi sabon layin MTN.
Ako wace rana nakan tura ma Ummey saƙonnin jan hankali kamar sau ukku domin cimma burina wajan ganin na samu soyayyar ummey.
Sai da na ɗauki kimanin sati ukku ina aika mata da sakonni iri-iri, amma ban taba ganin replay ɗin ummey ba.
A karshe sai ummey tayimin wani furucin da ya sani kukan zuci ta hanyar dawo min da replay.
Da sassafe na ɗakko layin dana saba aika mata da saƙonni da ƙudirin aika mata da saƙon barka da safiya.
Koda na ɗora layin sai nayi arba da sakonta.
Cikin yanayin shauƙi mai tattare da farin ciki na buɗe saƙon.
Abun da tace shine "dan Allah dan Annabi idan kana ganin girman iyayenka kayi haƙuri ka dai na aikomin da saƙonnin messege.
Nan take naji duk ilahirin jikina ya mutu kamar wanda aima dukan kawo wuƙa.
Duk da haka dai ban haƙuraba.
A wannan lokacin ƙaramar wayace dani ƙirar nokia E72
Duk da cewar ba wani daɗin hawa social network zanji da ita ba, haka na buɗe sabon account a shafin facebook.
Da ɓoyayyan suna nayi amfani kafin kowa ya sanni dashi a yanzu wato Young Uzee kenan.
Ummey itace farkon wadda na fara aikama Request wato buƙatar kasancewa a matsayin abokinta kenan.
Sai da a ɗauki tsawon kwanaki 8 sannan na samu karɓuwa a matsayin frnd ɗinta.
Duk da hakan dai ban tsiraba domin bansan adadin maganar da na mata ba, amma shiru ba replay.
Har raina ya fara ƙuna sai na tuna ummeyfa kyakkyawace dolene al'umma suyi mata yawa ta hanyar aika mata da sakonni iri-iri wanda hakan zaisa taƙi tsayawa domin karanta saƙon kowa ɗaya bayan ɗaya.
Ganin hakane yasa na aika mata da saƙon da zai jawo hankalinta zuwa gareni.
Abun da nace shine {"haba malan sam wannan ba halin mutun nagari bane, kaji tsoran Allah ka rufe wannan account ɗin.
yanzu a matsayinka na musulmi meye amfanin buɗe account da sunan mace haɗe dasa hotan wadda bakasan ko waceceba?
Kaji tsoran Allah ka dai na amma kayi haƙuri idan na ɓatama rai"}
Bayan 7 minutes da aika mata da wannan sakon, sai replay ɗinta ya shigo wayata.
Abun da tace shine {"subhanallah dan Allah karkayi tunanin wannan account ɗin na wani ne to bana kowa bane face nawa kuma ni macece kuma hotan da ka gani a profile ba na kowa bane face nawa"}
Sai nayi mata replay nace {"dan Allah ummey kiyi haƙuri wallahi nasan wannan account ɗin naki ne banawani namiji ba kawai na rasa yadda zanyi ne wajan ganin kin kulani, a matsayina na friend ɗinki a kalla nayi miki magana tafi 20 ba tare da nayi ido biyu da replay ɗinki ba.
Ganin hakane yasa nayi miki wannan maganar, sai gashi kuma nayi sa'a kin kulani dan haka wallahi ko yanzu kiyi blocking ɗina bazan wani damu ba tunda har nayi nasarar magana da kyakkyawar mace kamarki"}
Na ɗauka zata faɗamin wata mummunar magana sannan tayi blocking ɗina, amma sai naga saɓanin haka.
Murmushi tayi tace {"humm"} ba tare da ta furta wata kalmaba.
Sai nace {"to amma ummey ko zan iya sanin abun da yasaki murmushi haka cikin ƙanƙanin lokaci a mai makon ki nuna ɓacin ranki a game da laifin da na miki?"}
Sai tace {"kawai salankane ya burgemi.}
Wannan ne yasa najawo hankalin ummey zuwa gareni.
Yanayin yadda nake chating da itane yasa ta matsu taji muryata wanda hakan yasa ta turomin da numbarta haɗe da cewa "dan Allah ka kirani ko kuma kayimin plashing domin na kiraka.
A wannan lokacin ne na fashinci cewar wannan hanyar bazata taɓa ɓullewa dani ba saboda muddun nayi kuskuran kiran ummey a waya to ba makawa saita ganeni ta hanyar jin muryata ni kuma hakane banaso saboda so nake sai munyi matuƙar shaƙuwa da juna sannan zan bijiro mata da ainashin ƙudirina a gareta.
Hakane yasa nayi forget ɗin facebook domin canza wata sabuwar hanyar wadda kuma nake kyautata zaton zata ɓulle dani.
Kwatsam wata ranar asabar da misalin ƙarfe 5:00 na yamma lokacin nayi wankana kamar yadda na saba.
Zan fita kenan sai nayi arba da mahaifina ayayin da ya shigo gida.
Wani kallo naga yamin haɗe da cewar "kasan yaune za'a fara aikin gyaran gidannan amma saboda tsabar wulaƙanci tun ɗazu nake nemanka ban samu ganinkaba, gudun karna ɓatawa masu aikin lokaci ne yasa na ɗaga aikin sai zuwa gobe saboda key ɗin ɗakin da'a aje simintin yana wajanka, dan haka maza kaje ka ɗakko key ɗin ka fito da gaba ɗaya buhunan simintin dake dakin waje.
Ba yadda na iya duk da cewar nayi wanka haka na buɗe ɗakin domin fara fito da buhunan simintin dake ɗakin.
Tabbas buhun siminti ba ƙaramin nauyi ne dashi ba saboda tun da nake ban taɓa ɗaukar buhun siminti ba sai a wannan lokacin.
A yayin dana ɗakko na farko daƙyar na iya fito dashi waje.
A yayin da ummey tazo wucewa ta kusa dani tare da anti zainab sai Allah ya jarabceni ta hanyar taka wani dutse wanda hakan yasa ƙafata ta zame, bansan lokacin da buhun simintin yaje ƙasaba koda ƙurar simintin ya ɗan buɗesu.
Cikin yanayin wasa ummey ta kalleni haɗe da cewa "kash daɗina da yaran zamani sun fiye gaggawa kasan ƙarfinka baikai ba taya zaka ɗauki buhun siminti, gashi har kana neman ɓatamu da ƙura.
Koda na ɗago kai na kalleta sai nayi dariya haɗe da cewar "zan ramane yarinya.
Tun daga wannan lokacin sai wasa ya fara shiga tsakanina da ummey.
=> 2
Haka naita nazarin hanyar da zata haifar da wasa a tsakanina da ummey amma kwata-kwata na rasa. Kwatsam wata rana ina zaune a falon gidanmu ranar banje ko inaba haka na tasa set light da kallo.
Sai naji ƙarar buɗe ƙofa dubawar da zanyi sai nayi ido biyu da ummey a yayin da ta shigo.
Bayan tayi sallama na amsa mata kanta tsaye ta wuce ɗakin anti zainab ko cikakkun mintina 3 da shigarta ba aiba sai ta fito da daga ɗakin.
Da zuwanta gareni kamar zata zauna a kusa dani sai tace "kaga ɗan komacan inason nayi kallone.
Kallonta kawai nayi tun daga sama har ƙasa sannan nace " ummey idan har na tashi rama wulaƙancin da kikemin to ba makawa sai kin koka dani.
Murmushi naga tayi sannan tace "au da yayar taka kake sa'insa, to dan Allah karka janye wannan ƙudirin naka mu fara daga yau.
Jin haka ne yasa na jinjina kai sannan na tashi na bata wuri.
A ƙalla an ɗaki kimanin sati ɗaya da faruwar haka.
Kwatsam da musalin karfe 8 na dare nazo wucewa a hanyata ta komawa gida a yayin da nazo dai-dai ƙofar gidan su ummey sai nayi ido biyu da ummey a yayin da take tsaye da wasu samari biyu.
Ganin hakane yasa naji kishi ya kamani wanda hakan yasa nayi matuƙar jin haushin ganin samarin a tare da ita.
Ganin hakane yasa nayi amfani da wannan damar wajan rama abunda tayimin alokacin da nake kallo a gida.
Da zuwana gida sai na shiga ɗakina na kwaso wasu tsofaffin maganin da wani doctor ya taɓa bani domin nima kai na na manta adadin daɗewarsu a tare dami.
Cikin yanayin ƙwarin guiwa na fito daga gida, da zuwana inda suke sai nayi sallama kamar yadda addinin musulunci ya tanadar mana.
Bayan na miƙa musu hannu mun gaisa sai nasa hannuna aljihu na fito da maganin da na ɗakko a ɗakina.
Koda na kalli ummey sai nace "ummey dama dazune anti zainab ta aikoni wajanki domin karbar saƙon da ta baki, sai kuma ayi rashin sa'a a wannan lokacin bakyajin daɗi sakamakon gudawar da take damunki wanda hakan yasa ban samu damar ganinki ba sakamakon a wannan lokacin kina toilet saboda gudawar ta matsa miki.
Shine abbanki ko kuma ince abbanmu ya aikeni domin siyo miki waɗannam maganin saboda yasan bakya shiri da allura.
A gaban samarin nata tamin wani kallo cikin yanayin ɓacin rai tace " kaga karka sake yimin irin wannan.
In banda tsabar wulaƙanci yaushe ne na kamu da wata rashin lafiya balle ayi batun gudawa, ina gudawarne zan ɗauki tsawon wannan lokacin a waje?
Koda naga alamun bazata karɓi maganin ba kai na tsaye na shiga gidan nasu. Sai dai kuma na ɗauki tsawan lokaci rabona da shiga gidan.
Da shigata sai nayi arba da mahaifinta a harabar gidan a yayin da yake alwala.
Bayan mun gaisa sai yace "yau kuma kai ne a gidan namu ai na ɗauka ka manta damu ne sai nayi dariya nace " abba ai ba yadda za'ai na manta daku nima kai na nasan ban kyautaba, yanzu nazo wucewa saina haɗu da ummey anan ƙofar gida shine take cewa "bani da mutunci kullun tana zuwa gidanmu amma ni banason zuwa gidansu hakane yasa na shigo domin wanke wannan laifin a idonta.
Sai yayi dariya haɗe da cewar aikon ta kyauta.
Haka na ƙarasa ciki na gaisa da mahaifiyar ummey sannan na fito.
Koda na dawo zuwaga ummey sai nace "ummey abba yace kije yanason ganinki.
Ba yadda ta iya haka tayi bankwana da samarin nata ranta a bace.
Bayan sun tafi sai nace "ummey ai bai kamata ki nuna ɓacin ranki a game da wannan ɗan ƙaramin wulaƙancin ba, saboda tun farko ke kice muzuba mugani.
Sai ta jinjina kai hade da cewa "tabbas kayimin wulaƙancin da yai matuƙar ƙonamin rai amma kasa a ranka muddun ina raye ba abun da zai hanani rama wannan cin mutuncin da kayi a gareni.
A dalilin faruwar wannan al'amarin sai da mu ɗauki tsawon wata ɗaya ba tare da mun sake yima juna maganaba.
Kwatsam wata rana zamu garin bauchi ɗaurin auran wani ƙanin mahaifiyata mutuncin da yake a tsakanin gidanmu da nasu ummey ne yasa ummey ta bimu zuwa bikin ashe raban za'a samu dai-daito a tsakanina da ummey ne.
A yayin da muna cikin tafiya sai nace da anti zainab "anti karfa ki manta da batun kuɗin da kice zaki cikamin domin siyan wayar da nake buƙatar siya?
Buɗar bakinta sai tace "karfa ka takuramin tunda nace zan baka kawai ka zuba ido mana.
Da isarmu sai na sake tambayarta batun kuɗin saboda na matsu naga wayar ta shiga hannuna.
Nan take ta hauni da masifa haɗe da cewa "ka bari saimun koma gida ganin haka ne yasa ummey ta nuna tausayawarta a gareni.
Koda ta kalleni sai tace "nawane cikon kuɗin da zata baka cikin yanayin ɓacin rai nace 20 thousands ne.
Sai ummey tayi dariya sannan tace "indai akan 20 thousands ne karka damu ni zan cikama.
Da yake akwai wani shagon saida wayoyin dana sani sai na tafi tare da ummey domin siyan wayar.
Da isarmu bayan anyi cinikin wayar akan naira dubu 170 sai ummey ta karɓi kuɗin dake hannuna ta cika naira dubu 20, sannan ta miƙawa mai shagon.
A wannan lokacin ne na fahimci cewar ummey rainamin hankali tayi domin ɗaukar fansar wulaƙancin da na mata a baya domin sunanta naji tace asa a resit ɗin wayar.
Haka na zuba ido a kammala komai a gaban idona sannan ta kalleni haɗe da cewa "nagode yayana gaskiya ka burgeni da ka sai min waya.
Cikin yanayin bayyana damuwa nace dan Allah ummey kiyi haƙuri nasan nayi kuskure amma daga yau ba yadda za'ai na sake aikata miki abun da zai haifar da ɓacin rai a tattare dake.
Murmushi naga tayi sannan tace "da zakayi haƙuri ka cire wannan wayar daga zuciyarka zaifiyema komai daɗi domin wahalar da kanka kawai kakeyi.
Koda taga alamun zan takura mata nan take ta damƙa wayar a hannun mai shagon haɗe da cewa "malan ka'ajemin wayarnan na tsawon wata biyu sannan ta damƙamai 2 thousands a matsayin kuɗin ajiya.
Inaji ina gani haka nayi bankwana da kuɗina ba tare da cikon burina ba.
Bama wannanne yafi damuna ba illa rashin sanin hanyar da zan ɓullo mata wajan ganin sakon zuciyata ya isa gareta a game da son da nake mata.
Amma duk da haka ban ja da baya ba haka muci gaba da yima junanmu wulaƙanci mai kama da rashin mutunci.
=> 3
Haka ummey ta riƙa yimin dariya domin tasan dolene raina ya ɓaci ganin yadda mu koma gida ba tare da ummey ta karɓi wayarba ne yasa na tabbatar da cewar eh lallai ba yadda za'ai ta bani wayar balle ayi batun dawowar kuɗina.
Duk da irin wannan ta'addancin da ummey tayi a gareni baisa taja da baya wajan ci gaba da yimin abuncda taga dama ba.
Bazan taɓa mantawa da wata ranar Monday ba, ranar mahaifiyata da mahaifina basanan sunyi wata tafiya zuwa garin kaduna haka na dawo gida a yunwace.
Koda na duba inda asaba ajemin abinci banga komaiba face emptying plate.
Ganin hakane yasa na shiga ɗakin anti zainab, cikin yanayin damuwa nace "wai anti baki girka mana komai ba ne?
Buɗar bakinta sai tace "an faɗama cewar ni baiwarkace da zan zauna domin yima girki?
Cikin yanayin sakin fuska nace "ammafa zainab baki da mutunci.
Wani mugun kallo naga tayimin haɗe da cewa "a ina kuma ka manta antin da zaka kira sunana kaitsaye ba girmamawa?
Buɗar bakina sai nace "ai idan har kiga yara suna kiran yayarsu da anti to na tabbata tana kyautata musu ne, ammake ko kaɗan wannan sunan bai cancanta da ke ba saboda bana samun kyautatawa daga gareki.
Koda naga alamun ranta ya ɓaci sai nace "haba antita dawasafa nake miki saboda nasan bazaki rasa ƴan kuɗin da zaki bani ba domin naje na samu ɗan abun da zanci.
Daƙyar na shawo kanta ta dauki Five hundred ta bani domin naje naci abinci.
Ba yadda na iya haka na karɓi kuɗin majalissarmu na tunkara domin nasan acan bazan rasa abun da zan siya ba da isata ko zama banyi ba nace da maryam mai shinkafa ta zubomin shinkafar two hundred haɗe da lemo coke mai sanyi.
Bayan ta kawo abincin ko faraci banyi ba sai abokina bangis yazo gareni a gaggauce, wayar dake hannunshi naga ya miƙomin haɗe da cewa wata yarinyace mai suna aisha takeson magana dakai.
Haka na tashi na koma gefe domin jin ko wacece.
Ban saniba ashe tun daga nesa ummey taga lokacin da'a kawomin abincin da zuwanta sai ta ɗauki abincin haɗe da coke ɗin ta damƙawa almajirai haɗe da cewa "ku karɓi sadaka, a yayin da nikuma inacan ina waya da yarinyar da bangis ya haɗani da ita.
Bayanin da naji daga bakin aisha wato wadda nayi waya da ita kenan ba kaɗan ya jefani a ruɗani ba.
Haka na dawo majalissar tamu domin cin abinci na.
Koda na duba naga ba abinci kuma ba coke sai na kalli bangi haɗe da sauran abokan nawa nace dasu "ina kuma abincin nawa yake?
Buɗar bakin bangis sai yace "gashican a hannun almajirai cikin yanayin bayyana ɓacin rai na daka musu tsawa!
Cikin yanayin dariya nuhu ya dafa kafaɗata haɗe da cewa "a'a abokina karkaga laifinsu domin ummey ce ta ɗauka da hannunta ta basu.
Jin hakane yasa na jinjina kai haɗe da cewa "ammafa haskiya yarinyar nan tafini wulaƙanci.
Ganin haka ne yasa bangis ya sai min wani abincin daga wajan maryam.
Inacin abincin ina tunanin maganar da aisha ta faɗamin bayan naba bangis wayar sannan na sanar dashi cewar "dan Allah ya tabbatar da cewar yayi saving ɗin numbar saboda ina buƙatar sake magana da ita.
Bayan kwana ukku da faruwar haka musalin karfe 5:00 na yamma lokacin ina zaune a ƙofar gida sai ummey tazo gareni kaida ganin fuskarta kasan akwai damuwa a tattare da ita.
Da zuwa ta sai ta zauna a kusa dani, koda naga idanuwanta duk sun canza daga yadda na saba ganinsu sai nace "amma ummey ban taɓa ganinki a irin wannan yanayin ba, ko zaki iya sanar dani abun da yake faruwa dake?
Sai tace "tabbas na aikatama laifi mafi muni domin abbana ya fasa wayar daka siya na kwacema.
Kuma wallahi ban hanaka wayar domin ta zama mallakinaba kawai na hanakane domin buƙatar gane shin soyayyar da kake min gaskiyace ko kuma ta wasa ce saboda tun daga lokacin da kake aikomin da saƙon message na gane cewar ba kowa bane yake aikomin da saƙon ba illah kai.
Cikin yanayin mamaki nace amma ummey taya ai ki iya gane cewar nine mai aikomiki da waɗannan saƙonnin?
=> 4
Sai tace "na gane haka ne tun wata ranar juma'a, lokacin ina zaune tare da zainab a falon gidanku koda zainab taji ƙarar horn ɗin motar abbanku cikin yanayin tsoro naga ta shiga ɗakinka da sauri.
Ganin hakane yasa nabi bayanta domin jin abun dake faruwa.
Cikin yanayin mamaki nace amma zainab lafiya kuwa naga kin shigo nan a tsorace?
Buɗar bakinta sai tace "wallahi tun ɗazu abba yakirani a waya domin na kaimai wasu takaddu kuma shaf na manta, nasan idan yai ido biyu dani sai nasha fada.
Da shigowar mahaifinku bayan yayi sallama sai ya fara ƙwallama zainab kira amma sai zainab tayi shiru ba tare da ta amsa kiran ba.
Allah cikin ikonsa sai kira ya shigo wayarta cikin yanayin furgici ta jefar da wayar saboda tsoran kar mahaifinku yaji ƙarar Ringtone ɗon wayar.
Haka wayar tayi watsa-watsa ba tare da sanin wake kiranta ba.
Ashe tuni karar wayar ya isa kunnan mahaifinku, a wannan ranar zainab tasha fada.
Bayan ya ya ɗauki abun da zai ɗauka ya fita, sai zainab tace "naje na ɗakko mata wayar da ta jefar a ɗakinka.
A tsakar ɗakin ka naga wayar batirin kuma haɗe da marfin wayar a karkashin gadonka na ɗakkosu amma Allah baisa naga Ɗin Card ɗin dake wayar ba.
Wani littafin geography na gani a ƙasa koda na dagashi sai naga layin MTN ya faɗo ƙasa.
Ganin haka ne yasa na ɗauki Sim ɗin nasa a wayar saboda wayar irin ƙaramar nokiyar nance ina kunnata ta kawo.
Bayan na bata wayar sai tayi ƙoƙarin duba numbar da'a kirata kafin ta jefar da wayar amma bataga numbar kowaba sai numbata kaɗai ta gani a wayar.
Koda ta shiga ɓangaran message sai taga saƙonnin da ba ita ta turasuba.
Ganin haka ne yasa ta kalleni haɗe da cewa "ummey wannan ai ba layina bane, domin airtel nake amfani dashi ba MTN ba duk yadda ai wannan Aiki ɗin Faruq ne domin na tabbata waɗannan saƙonnin ba wanda zai turasu face shi.
Dariya naga tayi a yayin da ta kalleni sannan tace ummey yashe ku fara soyayya?
Cikin anayin mamaki na karɓi wayar domin dubawa.
Ganin saƙonnin ne ya tabbatarmin cewar kai ne kake aikomin da saƙonnin soyayya zuwa wayata..
A wannan ranarne na roƙi zainab domin karta nuna wata alamar da zatasa kagane mun duba Sim ɗin naka.
Sannan na roƙeta domin ta kauda kanta a game da dukkanin wani abun da zai riƙa faruwa a tsakanina da kai.
Haka naita yima abubuwan da nasan cewar zasusa ranka ya riƙa ɓaci domin auna mizanin soyayyar da kakemin a zuciyarka.
Haka ne ya tabbatarmin cewar lallai kana matuƙar sona a ƙarshe sai na yanke shawarar komawa Bauchi domin karɓoma wayarka.
Haka na tafi har Bauchi ba tare da kowa yasani ba domin ko mahaifiyata bata da masaniyar tafiyata balle mahaifina.
Bayan na sauka a Bauchi sai a samu akasi akasin da'a samu shine ban samu shagon a buɗe ba domin a kulle na sami shagon dayake ya rubuta numbar wayarshi a gaban shagon sai na kirashi a wayata.
Koda ya amsa kiran bayan mungaisa haɗe da sanar dashi dalilin kiranshi sai yace "gaskiya baya kusa domin yaje ɗaurin auran wani abokinshi ne haka na zauna zaman jiranshi har ya dawo domin sai misalin karfe 4 ya dawo.
Bansani ba ashe ran abbana yayi matuƙar ɓaci a sakamakon rashin ganina na tsawon wasu awanni.
In taƙaicema dai bani na dawo gidaba sai misalin karfe 8 na dare.
Da shigata falo sai nayi arba da mahaifina zaune a falo.
Ranshi a ɓace ya kalleni haɗe da cewa "ummey daga ina kike?
Sai nayi shiru ba tare da na bashi amsa ba saboda na tabbata idan na sanar dashi inda naje raina ba ƙaramin ɓaci zaiyi ba.
Gudun kar raina ya ɓaci ne yasa nayi mai ƙaryar cewar zainab na raka unguwa.
Ban tashi aune ba sai jin saukar mari naya haɗe da cewa "munafukar banza kawai, ni zaki rainama hankali a ƙalla na kira wayarki yafi a ƙirga amma sam bata shiga.
Muryata tana rawa Nace "abba wayar ba caji ne.
Jinai ya dakamin tsawa haɗe da cewa "ina wayar take?
Cikin rawar jiki nasa hannu a ƙaramar jakar dake hannuna domin fito da wayar tawa.
A wannan lokacin ne a samu akasi na fito da sabuwar wayar da ka siya.
Koda mahaifina yaga sabuwar waya a tattare dani sai yace " ummey a ina kuma ki samo wannan babbar wayar?
Cikin yanayin kiɗimewa nace "Abba wannan ba wayata bace bari na fitoma da tawa.
Wani kalar kallo naga yamin haɗe da cewa "a sanina wannan wayar mai tsadace dan haka kamar yadda nasan cewar bana baki kuɗin da zasu sa ki sayi wannan wayar haka nake da tabbacin bazaki samu kuɗin wannan wayar daga wajan mahaifiyarki ba.
Dan haka ki gaggauta sanar dani yadda ai ki samu kuɗin siyan wannan wayar.
Cikin yanayin kuka nace "wallahi abba ajiyarta abani.
Ban tashi auneba sai ji nayi ya buga wayar da ƙasa sannan ya nunani da yatsansa haɗe da cewa "ko wayar uban waye na sake ganinta a tattare dake to ba makawa sai na fasata.
Bayan ta gama bani wannan labarin sannan ta kalleni haɗe da cewa "bansan wane irin haƙuri zan baka a dalilin faruwar wannan al'amarin ba.
Jin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "haba ummey kefa tamkar ƙanwata na ɗaukeki dan haka zan iya sadaukar miki da komai nawa.
To amma sai dai kuma ummey akwai wani baƙon al'amarin da ya jefa zuciyata a ruɗani ko kuma ince sarƙaƙiya.
Kuma ina ganin muddun hakan ya kasance gaskiya to zuciyata zata iya cutuwa.
Cikin gaggawa ummey tace "dan Allah ko zaka iya sanar dani sarkakiyar zuciyarka ta tsunci kanta a ciki?
Sai nace "ummey akwai wata yarinya kokuma ince budurwa mai suna Aisha wadda ta kira wayar abokina bangis da buƙatar magana dani.
Bayan bangis ya kawomin wayar maganar da naji daga bakinta ba kaɗan ta girgizani ba.
Bayan mun gaisa sai tace dani "kai ɗan uwana ne dan haka bazan taɓa bari ka cutar da zuciyarka wajan faɗawa soyayya da wadda aure bazai taɓa kasancewa a tsakaninka da ita ba.
Dan haka ina mai tabbatarma cewar har abada ba aure a tsakaninka da wadda kake shirin faɗawa soyayya da ita wato ummey kenan, omin addinin musulunci yayi hani da haka na buɗe baki zanyi magana kenan sai ta yanke wayar.
Buƙatar sake yin magana da itane yasa tun a lokacin nayi ƙoƙarin kiranta amma sai kiran yaƙi shiga domin kashe wayar tayi.
Bayan na sanar da ummey wannan maganar sai na kalleta nace "babban abun da yake ɗauremin kai shine taya ai tasan akwai soyayyarki a tattare da ni, saboda ba wanda na taɓa sanar dashi cewar ina sonki.
Sannan kuma ita wacece sarkakiyar da nake ciki itace "shin dagaskene ba aure a tsakanina dake?
Sai ummey ta girgiza kai haɗe da cewa "meyasa kake ƙoƙarin haifarma zuciyarka da damuwa alhalin kafi kowa sanin cewar ba wata dangantakar da zata kawo batun hana aure a tsakanina da kai?
Dan haka kamar yadda na ɗauki wannan maganar a matsayin shirme zanso kaima kayi ƙoƙarin ɗaukarta a matsayin shirme.
=>5
Tun daga wannan ranar sai komai ya sauya a tsakanina da ummey.
Lokaci ɗaya ta janye kanta dangane da batun yawo tare da anti zainab sai ya zamto ba ta da wani abokin rakiyar da ya wuce ni.
Haka na riƙa nuna jin kunyar jerawa tare da ummey a matsayina na baƙon soyayya, rannan sai ummey ta kalleni tayi murmushi haɗe da cewa na fahimci kana matuƙar jin kunyar jerawa tare dani musamman a yayin dana buƙaci rakiyarka domin zuwa wani wajan.
To amma ni a ganina hakan ba wani abun kunya bane a matsayinmu na masoya.
Kuma ta wani ɓangaran ni tamkar ƙanwar nake a gareka saboda gidanmu da naku ya zama tamkar gida ɗaya musamman idan kayi la'akari da yadda iyayanmu suke mutunta junansu saboda ganin haka ne yasa nake aikata duk wani abun da naga dama a gidanku ba tare da ahalinka sun nuna wata damuwa a gareni ba.
Abun yana matuƙar bani haushi ganin yadda baka damu da zuwa gidanmu kamar yadda na maida gidanku tamkar gidanmu ba.
Zanso kaima kayi ƙoƙarin ɗaukar gidanmu tamkar naku gidan kamar yadda nakeson ka cire duk wata kunyar da take a tsakanina da kai.
Haka dai soyayyarmu taci gaba da bayyanuwa a idon kowa.
Ko wace safiya mukan turawa junanmu saƙon barka da safiya ta hanyar amfani da waya.
Idan dare yayi bama taɓa gajiyawa ba tare da munyi waya da juna ba.
Kwatsam wata rana ina tare da ummey da misalin ƙarfe 8:00 na dare ƙofar gidanmu sai naji kira ya shigo wayata.
Koda naga baƙuwar numba ban wani ɓata lokaci ba na amsa kiran.
Muryar mace naji ayayin da na kara wayar a kunnena wanda hakan yasa na gane ko wacece domin ba wata bace illa wadda takeson haifar da ruɗani a tsakanina da aisha wato wadda bangis ya taɓa haɗa i da ita muyi magana a kwanakin baya.
Buɗar bakinta sai tace "wato har yanzu kananan akan bakanka kenan, to bari kaji wallahi wahalar da kanka kawai kakeyi domin ummey bazata taɓa kasancewa a matsayin matarka ba.
Cikin yanayin ɓacin rai nace wallahi muddun nayi ido biyu dake ina mai tabbatar miki cewar sai kinyi raina kanki, saboda banga dalilin da zaisa ki riƙa ƙoƙarin haifar da ruɗani a game da rayuwata ba.
Dariya naji tayi haɗe da cewa "ai bansan zaka iya aikata haka a game dani ba, domin yanzu na wuce ta kusa daku nan take na sauke wayar daga kunnena na fara waige-waige domin tabbatar da maganarta.
Koda ummey taga ina waige-waige sai tace "lafiya kuwa, me kuma ya faru?
Cikin yanayin mamaki nace ummey kinga wata ta wuce tanan yanzu?
Sai tace "Eh akwai wadda ta wuce ta nan kusan tsayinta ɗaya dani tana sanye da wasu kaya ruwan madara haɗe da wani farin gyale.
Sai ummey ta kalleni tace "wai me yake faruwa?
Buɗar sai nace "itace ta sake kirana domin sake sanar dani cewar babu aure a tsakanina dake.
Jin haka ne yasa naga ummey tayi dariya sannan tace "ko wacece wannan to ba abun da zata ƙaru dashi face baƙin ciki haɗe da takaici domin bazamu taɓa rabuwa ba saboda na fahimci so take ta kawo ƙarshen alaƙata da kai.
A wannan lokacin haka mu ɗauki maganar a matsayin shirme.
Amma duk da haka na kasa cire zuciyata daga rudanin da Aisha ta haifar min ba.
A maimakon mutsaya muyi dogon bincike a game da yadda rayuwarmu ta samo asali, kawai sai muci gaba da soyayyarmu.
Ashe dai maganar Aisha tana kama da gaskiya.
A tsakanin iyayan ummey da iyayena mahaifiyatace ta fara gane cewar akwai soyayya a tsakanina da ummey.
Cikin dare da misalin ƙarfe 1:00 mahaifiyata ta shigo ɗakina.
Bayan ta tasheni daga bacci cikin yanayin mamaki nace "umma lafiya kuwa?
Sai tace "lafiya ƙalau nazo garekane da wata buƙata a matsayina na mahaifiyarka.
Cikin gaggawa nace "umma ki faɗi duk wata buƙatarki nayi miki alƙawarin zan biya miki ita domin nasan bazaki taɓa tunkarata da wata buƙatar da kisan cewar zatafi karfina ko ta cutar dani ba.
Buɗar bakin mahaifiyata sai tace "wace alaƙace a tsakaninka da ummey?
Cikin yanayin kunya na sumkuyar da kaina ƙasa, na ɗauka jin abun da yake a tsakanina da ummey ne kaɗai buƙatar mahaifiyata a gareni.
Cikin yanayin kwarin guiwa nace "umma ba wani abu ne a tsakanina da ummey ba illa soyayya.
Sai tace "to indai har kanajin maganata a matsayina na mahaifiyarka zanso daga yau ka dakatar da batun soyayyar da take a tsakaninsa da ummey, sannan kuma karka bari ta fahimci cewar nice maƙasudin raba wannan soyayyar da take a tsakaninku balle wasu susan da faruwar haka domin ko yayarka zainab banason tasan da wannan maganar saboda banason abun da zaiyi sular daina shigowar ummey wannan gidan.
Cikin yanayin ruɗani nace "to amma umma ni a sanina mafi yawanci iyaye suna hana ƴaƴansu auran wadda sukesone saboda wasu dalilai ko wani babban dalili.
Amma sai gashi ke da kanki kin nemi na guji ummey ba tare da kin sanar dani dalilin hakanba kuma ta wani ɓangaran sai naga kamar ummey ba ta aikata wani laifin da zaisa ki nemi rabani da itaba saboda naga alamun kina matuƙar kaunarta wanda hakan yasa bakyason wani dalilin da zaisa ta daina shigowa gidannan.
Sannan na kalleta nace "dan Allah umma ki sanar dani abun da yake faruwa nayi miki alƙawarin bazan sanar da kowa ba?
Sai ta girgiza kai haɗe da cewa "na riga na ɗaukarwa mahaifinka da iyayan ummey alƙawarin bazan taɓa sanarma kowa wannan sirrin ba.
Dan haka kawai kayi haƙuri ka biyamin wannan buƙatar tawa ba tare da ka nemi jin komai daga bakinmu ko wajan iyayan ummey ba.
Jin haka ne yasa nan take hawaye ya kwaranyo daga idanuna.
Cikin yanayin kuka nace "umma karkisa zuciyata ta fara zarginki da aikata ba dai-dai ba.
Nan take mahaifiyata tasa hannunta ta share hawayen dake fuskata haɗe da cewa "ko kusa karka taɓa bari zuciyarka ta zargeni da batun saɓawa mahaliccinmu saboda ban taɓa aikata fasiƙanci kamar yadda kake tunani a halin yanzu ba.
Sanannan ta tashi tayi waje ta barni cikin ruɗani.
=> 6
Nan take mahaifiyata tasa hannu ta share hawayen dake fuskata haɗe da cewa "ko kusa karka taɓa bari zuciyarka ta zargeni da batun saɓawa mahaliccinmu saboda ban taɓa aikata fasiƙanci kamar yadda kake tunani a halin yanzu ba.
Sanannan ta tashi tayi waje ta barni cikin ruɗani.
A wannan ranar haka na kwana cikin ruɗani haɗe da matsanancin tunani washe gari da sassafe sai ummey ta shigo kamar yadda ta saba kanta tsaye ta shiga har ɗakina
A lokacin da ta shigo ina kwance amma idona biyu, duk da cewar ba wani annuri a tattare dani haka na ɗan saki fuskata.
Cikin yanayin sakin fuska nace "ummey kardai kice kinzo tashina daga bacci ne?
Murmushi naga tayi sannan tace "amma ya ai kasan abun da ya kawoni?
Buɗar bakina sai nace "ai saboda zukatanmu sun riga da sun zama ɗaya shine dalilin da yasa na fahimci haka.
Sai tace "kaga malan tashi kazo muje kayi breakfast domin akwai inda nakeson ka rakani.
Bayadda na iya haka na fito daga ɗaki amma ba'a son raina ba, saboda ko kaɗan banason abun da zai ɓatawa mahaifiyata rai saboda kar ummey ta fahimci na fara ja da baya da itane yasa na fito.
Haka ummey ta zauna a falo tare da Anti Zainab har na fito daga wank.
Zamana kenan a falo a yayin da nake cin abinci sai Ummey ta taso daga wajan anti zainab tazo ta zauna kusa dani tanamin irin kalar kallan da masoya sukewa junansu.
Bayan na kammala cin abinci sai na fita tare da ita domin rakata inda take son zuwa.
Bayan na dawo gida sai na fahimci cewar ran mahaifiyata yayi matuƙar ɓaci wanda hakan yasa na rasa hanyar da zanbi wajan ganin na cikawa mahaifiyata burinta a game da batun rabutun kawo ƙarshen soyayyata da ummey ba tare da ummey ta fahimci komai a game da al'amarin da nake ciki ba.
Duk da cewar nasan hakan ba abu ne mai yuwuwaba amma ko kaɗan zuciyata bata daina nazarin neman mafita ba.
Rana ɗaya nayi duk wani shirina na tafiya garin jigawa, amma sai dai kuma ina duba yiwuwar tafiyar da zanyi zan ɗauki dogon lokaci ba tare da na dawo gida ba domin bana tunanin cewar zan dawo har sai lokacin da ummey tayi aure.
Koda na sanar da iyayena batun tafiyata da ƙudirin bazan wuce sati daya ba.
Sai suyimin fatan alkairi haɗe da sa albarka a gareni.
Ummey har zubar da hawaye tayi a dalilin wannan tafiyar tawa inaji ina gani haka nayi bankwana da abar ƙaunata wadda ko tuntube batason taga nayi musamman a yayin da muke tafiya tare da juna.
Gashi dai tafiya nakeyi amma tunanin irin soyayyar da mukewa junanmu ne yake ta damun zuciyata wanda hakan yasa nakejin kamar na fasa tafiyar.
Gashi kuma bansan halin da ummey zata tsunci kanta a ciki ba, musamman a yayin da taji shiru ban dawoba.
Duk da irin wannan tunanin da zuciyata take ciki hakan bai hana nayi wannan tafiyar ba, badan komai ba sai dan buƙatar cikawa mahaifiyata burinta saboda kokaɗan banason mahaifiyata ta shiga damuwa a dalilina.
To amma sai dai kuma a zuciyata ba jahar jigawa nake da ƙudirin zuwaba domin jahar kebbi ce a zuciyata.
Da misalin ƙarfe 1 na dare na sauka a kebbi state.
Da saukata sai nayi calling ɗin wani abokina mai suna Kamal wanda na haɗu dashi a sanadin social network wato facebook kenan.
Ba'a wani ɗauki dogon lokaci ba Kamal yazo gareni, farin cikin haɗuwa da nine yasa ya saukeni a gidansu cikin karramawa.
A wannan ranar ne na sanar da Kamal duk abun da ya faru dani haɗe wanda hakan yai sular barowata gida.
Daga karshe kuma sai na sanar dashi cewar "bana muradin komawa gida har sai lokacin da ummey tayi aure.
Shiru naga yayi na ɗan wani lokaci zuwacan sai ya kalleni cikin yanayin tausayawa yace "tabbas kayi matuƙar burge ni tunda har ka zaɓi farantawa mahaifiyarka fiye da son zuciyarkk, dan haka zakaci gaba da zama a tare dani har zuwa lokacin da wannan burin naka zai cika.
Duk da cewar na nisanta da ummey amma hakan baisa muryar ummey ta nisanta da kunnena ba haka itama muryata bata nisanta da nata kunnan ba, saboda kullum ne sai sai ummey tayi calling ɗina haɗe da aikomin da saƙon text message.
Nanfa na rasa hanyar da zanbi wajan ganin haka ta daina faruwa a tsakanina da ummey.
Kwanana biyar da zuwa kebbi sai wata motar (kano line) tayi accident/haɗari a yayin da take gaf da fita daga cikin garin kebbi domin zuwa jahar kano.
Abun takaici domin duk jama'ar ciki basu rayu ba saboda mota ƙonewa tayi gaba ɗaya.
A fasinjojin dake motar ba wanda za'a iya shaida fuskarshi balle gangar jikinsa.
Ganin haka ne yasa na yanke shawarar yin amfani da wannan damar wajan ganin na ɓatar da rayuwata a idon ummey haɗe da iyayensu.
Ta wani ɓangaran kuma ina tunanin irin hawayan da iyayena haɗe da ummey zasu zubar musamman a yayin da saƙon mutuwata ya isa kunnansu.
Amma sai na tuna da wata karin maganar da naji wasu daga cikin hausawanmu suna yawan furtawa.
Wato "da ruwan ciki akanja na rijiya, domin kuwa sai an fuskanci wani ɓacin ran sannan ake samun wani farin cikin.
Bayan na tsara duk wani shirina tare da abokina Kamal, a ƙarshe sai na damƙa wayata a hannunshi.
A gaban idona Kamal ya miƙa wayar tawa a hannun ɗaya daga cikin jami'an Yan Sandan dake gudanar da bincike a wannan wajan hade da cewa "yallabai ina tunanin wannan wayar ɗaya daga cikin mutanan da wannan haɗarin ya auku dasu ne.
Ta hanyar wayar ne saƙon barina duniya ya isa kunnuwan iyayena, saboda a zahirin gaskiya wannan ita kaɗaice hanyar da zatasa ummey ta auri wani ba tare da ta fahimci komai a game da sirrin da iyayena haɗe da nata iyayan suke ɓoye mana ba.
=> 7
Duk da cewar abokina Kamala yasan cewar ina raye domin tare dashi mu tsara komai, hakan bai hanashi zuwa har jahar Kano sadakar ukkuna ba nadan komai ba sai dan buƙatar ya ganomin halin da iyayena suke ciki.
A ranar da kamal ya dawo gareni ne ya sanar dani maganar da ta ɗan kiɗimani.
Zama yayi a kusa dani ya kalleni haɗe da cewa "gaskiya abokina abun da mu aikata bai dace ba, domin saura kiris na bayyana gaskiyar abun da ya faru a game da batun ƙaryar da muyi ta cewar ka mutu.
Amanar da take a tsakanina da kaice tasa na kasa aikata haka bayadda na iya haka na baro jahar kano hankalina a tashe, sakamakon mawuyacin halin da naga ummey a ciki.
Cikin ƙanƙan lokaci naga ƙwalla sun bayyana a idanunshi.
Buɗar bakinshi sai yace "tabbas ummey tana matsanancin sonka saboda a yadda na samu labari tun daga lokacin da saƙon mutuwarka ya isa kunnanta ta yanke jiki ta faɗi sai da ta ɗauki dogon lokaci kafin ta farfaɗo daga dogon suman da tayi, kuma ba'anan al'amarin ya tsaya ba domin har barowata garesu ba ta iya furta kalmar komai, daka take zaune ba umm ba a'a.
Dan haka shawarar da zan baka a matsayina na abokinka itace "kawai ka komaga ummey saboda hakane kaɗai zai iya kawo sassauci ga rayuwar Ummey.
Cikin yanayin damuwa na kalli Kamal haɗe da cewa "tabbas nasan ko kaɗan ban kyautaba, amma inason kasan cewar ba yadda za'ai naso ganin abun da zai ɓatawa mahaifiyata rai a dalilina.
Duk da cewar taƙi sanar dani dalilinta na rabani da ummey hakan bazai taɓa sawa na kasa cika mata burinta ba, kuma inason kasan cewar duk inda tsanani yake to ka tabbata a kwai ranar da sassauci zaizo.
Dan haka ummey zata samu sauƙi domin Allah maji roƙon bayinsa ne.
Kimanin shekarata ɗaya da wata takwas a jahar kebbi tare da abokina kamal ba tare da ahalina sunsan cewar ina nan a raye ba.
Amma sai dai har kawo wannan lokacin ummey batayi aure ba, domin bata kula kowa.
Kwatsam wata rana sai abokina kamal yazomin da wani labari wanda yai matuƙar sani a farin ciki.
A yayin dana sake turashi jahar kano domin ya jiyomin ko kuma ince ya ganomin abun dake faruwa a tattare da ahalina haɗe da abar ƙaunata wato ummey sai yazomin da labarin ansama ummey rana haɗe da yayata zainab wanda za'ayi bikinsu a ranar 27 ga wata mai kamawa.
Tabbas ba kaɗan naji daɗin wannan albishirin ba.
Sai dai kuma na tabbata ummey zatayi aura ne ba'a son ranta ba.
Jahar kebbi sai da ta kasance tamkar mahaifata domin ba abun da na rasa a tattare da abokina kamal, haka ne yasa kamal yai matuƙar damuwa a yayin da nake shirin komawa gida.
Bayan sati biyu da bikin anti zainab haɗe da ummey sai na ɗauki hanyar kano.
Sai dai kuma na tabbata sai ahalina haɗe da waɗanda su Sanni sun shiga rudani musamman a yayin da suyi ido biyu da ni.
Kuma dole ne su nemi jin yadda ai na kasance a raye.
Tun a mota nake nazarin hanyar da zanbi amma sai kaina ya kulle.
Har na shiga kano zuciyata bata daina saƙe-saƙen amsar da zanba iyayena musamman idan su nemi sanin yadda ai haka ta faru dani ba.
Tare mu sauka mota da wata baiwar Allah, harna juya zan tafi.
Sai naji tace "dan Allah malan ɗan tsaya mana.
Koda ta ƙaraso gareni sai tace "dan Allah malan ni baƙuwace a wannan garin kuma gashi dare yayi shine nakeson ka taimakamin da aran wayarka domin na kira wadda nazo wajanta saboda wayar tawa tun a mota cajinta ya ƙare.
Cikin yanayin tausayawa na miƙa mata wayar.
Haka tayita trying ɗin numbar amma bata samu shigaba.
Ganin hakane yasa duk tabi ta kidime.
Wani yanayin kallan da naga tayimin ne yasa na fahci cewar tana cikin damuwa.
Bayan ta bani wayar, cikin yanayin sakin fuska nace "na fahimci kamar a kwai damuwa a tattare da ke, amma idan bazaki damu ba me zai hana na kaiki gidanmu ki kwana kinga idan gari ya waye saiki kirata domin ku haɗu.
Cikin sanyin murya tace "to shikenan nagode.
Tun kafin mu ƙarasa gidan namu sai na nemi sanin sunanta haɗe da sanin garin da ta fito.
Buɗar bakinta sai tace "ai sunana ba wani mai wahala bane, domin sunana Aisha kuma ni yar asalin jahar taraba ce.
Batun dalilin zuwana kano kuma wannan labari ne mai matuƙar tsayi haɗe da ban tausayi amma a halin yanzu ba abun da nake buƙata fiye da abincin da zan ba cikina, saboda ina matuƙar jin yunwa.
Dan haka idan Allah yasa mu wayi gari lafiya zan baka cikakken labarina haɗe da dalilin zuwana kano domin bazan ragema ko ɗaya daga cikin labarina ba.
Jin haka ne yasa nayi murmushi sannan muci gaba da tafiya.
Gaba ɗaya har na manta da kalubalan na nake ciki a game da tunanin yadda iyayena zasuyi mamakin ganina a raye domin sai bayan na tura ƙofar gidanmu sannan na tuna.
Ji nayi ƙirjina yayi wata irin bugawa amma ko kaɗan ban bari Aisha ta fahimci komai a tattare dani ba.
Da shigarmu gidan koda mahaifiyata tayi ido biyu dani a yayin da nayi sallama sai ji nayi ta zafga salati sannan ta mike a tsorace.
Cikin yanayin ruɗani tace "waye wannan Allah yasa dai ba mafarki nakeyi ba.
Saboda jin daɗin ganin mahaifiyata da nayi a wannan lokacin nan take naji hawaye ya zubo daga idanuna.
Buɗar bakina sai nace "umma tabbas ɗanki ne ya dawo gareki domin ba mutuwa nayi ba kamar yadda kuke tunani.
Kawai nayi haka ne domin bani da wani burin da ya wuce na faranta miki rai.
Wannan ne dalilin da yasa nabar gida domin cika miki burin ki.
Cikin yanayin mamaki tace "wane irin buri ne kakeson cikamin wanda har zaisa kabar gida?
Kasan irin ƙunar da muji a yayin da mu samu labarin cewar kabar duniya kuwa?
Haka muyita zubar da hawayanmu akanka bamu sani ba ashe ba sonmu kakeyiba, kawai zubar hawayanmu kake son gani.
Nan take na durƙusa har ƙasa ina mai kukan baƙin ciki.
Haka na ɗago kai na kalli mahaifiyata nace "dan Allah umma ki yafemin nasan na aikata kuskure kawai na aikata haka ne domin cika miki burinki.
Ta buɗa baki zatai magana sai nace "a'a umma nasan maganar da zakimin bazata wuce neman sanin burin da nakeson cika miki ba, saboda nasan yanzu kin manta da alfarmar daki nema a wajena a game da batun rabuwa da ummey wadda nake matuƙar so to amma sai dai son da nake miki ya zarce nata.
Koda mahaifiyata taji wannan batun sai ta riƙe baki.
Cikin yanayin kuka tace "tabbas na cuceka kuma bana tunanin Allah zai yafemin a game da wannan al'amarin da ya faru.
Jin haka ne yasa nan take na miƙe tsaye haɗe da cewa "haba umma kefa mahaifiyatace wadda take da ikon sani duk wani abun da taga dama muddun bai saɓawa addinin musulunci ba.
Kuma ina da tabbacin cewar sirrin da kike boyewa bai saɓawa addinin musulunci ba.
Dan haka zanso ki manta da wannan al'amarin, tunda Allah yasa ummey tayi aure bani da wani farin cikin daya wuce haka.
Sai mahaifiyata ta shafa kai na tace " Allah yama albarka.
Koda na kalli Aisha sai nace "au dan Allah Aisha kiyi haƙuri alhinin da muke ciki ne yasa na manta da ke.
Murmushi naga tayi sannan tace "kar kaji komai domin nima nayi matuƙar tausaya muku.
Bayan nayiwa mahaifiyata bayanin komai a game da zuwan aisha gidanmu sai a kaita ɗaki a kuma bata abinci bayan na fito sai nace "umma wai ina abba yaje ne naga tun da nazo ban samu ganinshi ba?
Sai tace "aikon abbanka yana jahar katsina yau kwananshi biyu a can amma gobe nakesa ran dawowarshi haka na zauna kusa da mahaifiyata ina cin abinci.
Sai tace "yau ne zan bayyanama sirrin dana daɗe ina ɓoyewa a zuciyata badan komai ba sai dan ina da tabbacin bazaka sanarma kowa ba saboda na yadda da kai kuma bani da kowa yanzu a kusa dani wanda ya wuce ka tunda yayarka zainab ta riga da tayi aure.
Haka na gyara zama domin jin sirrin da mahaifiyata ta daɗe tana ɓoyewa a zuciyarta.
=> 8
Sai mahaifiyata tace "sanin kankane mahaifin ummey abokin mahaifinka ne, ita kuma mahaifiyar ummey kawatace.
Haka ne yasa mukasance tamkar yan uwan juna sai dai kuma tun daga lokacin da Allah yasa abokin mahaifin naka yayi aure har kawo yanzu basu taɓa samun haihuwa ba.
Koda naji haka cikin yanayin mamaki nace "to amma umma ita kuma ummey fa, kar dai kice ba yarsu bace?
Sai tace "ummey yarsuce amma ba wadda su haifa da cikinsu ba, saboda wannan al'amarin yasamo asaline tun wata ranar da Allah ya albarkaci mahaifiyar ummey da samun ciki a dai-dai lokacin da nima nake dauke da juna biyu.
Tsakar dare misalin ƙarfe 2 lokacin kowa yayi bacci sai haihuwa tazomin haihuwata kenan sai abokin mahaifinka yazo mana da batun hajiya ameena ta haihu amma ɗan baizo da raiba.
Ganin damuwar da suke cikine a game da rashin samun haihuwa yasa mu ɗauki ɗaya daga cikin yayan damu haifa mu sadaukar masu domin ƴaƴa biyu na haifa a wannan lokacin.
Ba'ayi cikakken wata ɗaya da faruwar wannan al'amarin ba sai Allah ya ɗauke ran hafsat saboda a wannan lokacin canza masu suna muyi a matsayinsu na Hasana da Usaina.
Sannan ta lalle i haɗe da cewa "wannan shine dalilin da yasa na shiga tsakaninka da ummey saboda ita ƙanwarkace ta jini kuma tabbas kayi matuƙar dabara gami da hangen nesa da har ka nisancemu na tsawon wannan lokacin.
Dan haka zan kasance mai yima addu'ar samun nasarar duniya da lahira.
A wannan ranar haka na kwana cikin farin ciki haɗe da kwanciyar hankali bayan gari ya waye sai nayi alwallah na tafi masallaci.
A wannan safiyar da naje masallaci mutane da dama sunyi mamakin sake ganina a raye wanda hakan yasa a dameni da tambayoyin yadda ai haka ta kasance amma sai naƙi sanar dasu gaskiya domin ce masu nakeyi "haɗarin motane ya faru damu wanda hakan yai sular haifar da matsalar mancewa da duk wani abun da ya shafi rayuwa na lokaci mai tsawo.
Bayan na koma gida shiru har wajan karfe 9 banga fitowar baƙuwar da na sauketa a gidanmu ba wato Aisha kenan.
Ganin hakane yasa na shiga ɗakin domin dubawa ganin halin da Aisha take ciki ne yai matuƙar kidimani wanda hakan yasa kafafuwana su kasa ɗaukata bansan lokacin dana zauna kasa haɗe da zafga salati ba, domin a wannan lokacin ban samu Aisha a raye ba.
A yayin da nayi ido biyu da gawar Aisha nayi matuƙar shiga ruɗani.
Bayan jami'an tsaro sun gudanar da bincike sai su gane cewar bamu da hannu wajan mutuwar Aisha wanda hakan yasa su sallamemu ba tare da an wahalar damu ba.
Sakamakon rashin sanin iyayanta da kuma danginta ne yasa ayi jana'idarta a gidanmu dawowarmu daga maƙabarta kenan sai nayi kacibus da ummey a ƙofar gidanmu.
Duk da cewar ummey tayi aure haka ta tunkaroni fuskarta cike da mamaki, da zuwanta sai ta rike hannuna sannan ta fashe da kuka haɗe da cewa "yayana wallahi ji nake kamar mafarki nakeyi, dan Allah dagaske kai ɗin ne kuwa?
Kuma taya ai hakan ta faru dakai?
Cikin yanayin tausayawa nace "ummey zan sanar dake komai domin bazan taɓa barinki a cikin ruɗani ba.
Amma inason ki tabbarmin cewar zaki riƙe wannan sirrin kuma bazaki taɓa bari kowa yasan da wannan sirrin da zan sanar dake ba, domin ko iyayankima bana buƙatar susan kinji wannan sirrin balle wasu daban.
Amatsayin ummey na ƙanwata ta jini haka nasa hannuna na share hawayan dake fuskarta.
Sannan nace da ita "amma wannan sirrin bazai yuwu na sanar dake a yanzuba saboda gudun sa'idon al'umma, dan haka ki bari sai Allah ya kaimu zuwa gobe.
Cikin yanayin mamaki ummey ta ɗago kanta ta kalleni.
Haɗe da cewa "wane sa'ido kuma kake gudu karfa ka manta ni takace ta tsawon har abada domin dakai kaɗai zan iya rayuwa.
Buɗar bakina sai nace "ummey koda ace bakiyi aureba to ba yadda za'ai ki taba kasancewa matata.
Nan take naga wani sabon hawaye ya faso daga idanun ummey cikin yanayin kuka tace "idan auran da nayi ne zaisa kayi tunanin ƙin kasancewata a matsayin mallakinka to kasa a ranka wannan auran nawa tamkar na yanke igiyarshi ne, saboda tun da nayi aure har kawo yanzu ban taɓa barin wanda ya aureni ya kwanta dani ba, sau ɗaya ya taɓa riƙe hannuna wanda hakan yasa na tsunka mai mari.
Sannan ta juya ta tafi tana kuka wanda hakan yasa al'ummar dake wajan hankalinsu ya dawo garemu.
Haka na shiga gida fuskata cike da damuwa.
Kwatsam cikin dare da misalin ƙarfe 10:30 lokacin ina kwance a ɗakina bamu kaiga rufe gidaba sai ji nayi an tasheni daga bacci.
Juyowar da zanyi sai nayi ido biyu da ummey zaune a kusa dani.
=> 9
Nabuɗa baki zanyi magana sai naga ta miƙomin wata farar takadda wanda hakan yasa na karɓi takaddar domin ganin abun da ke cikinta.
Koda na duba sai naga saki ɗaya ɗauke da sunan ummey.
Ganin haka ne yasa na fahimci cewar ummey kashe auranta tayi.
Cikin yanayin takaici haɗe da nuna ɓacin rai nayi mata wani kallo haɗe da cewa "haba ummey me yasa ki aikata haka?
Buɗar bakinta sai tace "akanka ba abun da bazan iya aikatawa ba, sannan ta ƙara da cewa "kawaifa durƙusawa nayi har ƙasa idanuwana suna zubar da hawaye na rike ƙafarshi haɗe da cewa " dan Allah dan Annabi ka dubi girman iyayanka ka bani takaddar saki, saboda aikata haka na kaɗai zai kawo zaman lafiya a tsakanina dakai dan haka ka gaggauta bani takaddar saki a yau idan ba haka ba to wallahi sai na haddasama babban tashin hankali a tattare da rayuwarka.
Buɗar bakinshi sai yace "amma ummey wane laifi na aikata miki da har kike neman takaddar saki a gareni?
Sai nace "baka aikatamin laifin komai ba amma zanso kasan da cewar "tunda wanda nake ƙauna ya dawo to bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba muddun bai zama mallakina ba.
Dan haka ina mai roƙonka akan cewar ka gaggauta bani takaddar da zata zamto shaidar rabuwata da kai saboda hakan shine zaifi kasancewa zaman lafiya a tattare da kai.
Sai yayi murmushi sannan yace "tun daga lokacin da ya samu labarin dawowarka yaji a jikinshi haka zata iya faruwa dan haka shi maison zaman lafiyane kuma mai son ganin farin ciki a tattare dani.
Wannanne dalilin da yasa ya rubuta takaddar saki a gareni.
Bayan ta gama yimin wannan jawabin, raina a ɓace nace "amma ummey kin aikata kuskure.
Domin ke ƙanwatace ta jini wadda mahaifiyata ta haifeku a matsayin yan biyu da cikinta.
Nan take na fara bata labarin duk yadda ayi haka ta faru tun daga lokacin da mahaifiyata ta haifesu har zuwa lokacin danabar gida domin cikawa mahaifiyata burinta.
To amma duk da cewar nayi ma ummey bayanin komai hakan baisa ummey ta amince da bayanin da taji daga bakina ba.
Nan take ta miƙe tsaye haɗe da cewa "karka fake da wannan hanyar a matsayin hanyar da zata baka damar yaudarata, saboda idan har ka gujeni to zuciyata bazata taɓa yafema ba.
Ganin yadda tayi waje tana kuka ne yasa nabi bayanta domin gudun kar iyayanta su fahimci abun da yake faruwa.
Fitowata daga ɗaki kenan sai kuma nayi Arba da Aisha zaune a falo.
Cikin yanayin firgici nace "aisha!!!!!!
Jin haka ne yasa ummey ta juyo fuskarta da sauri ba tare da ta ƙara ko taki ɗaya ba.
A tsorace na ƙarasa kusa da Aisha, cikin yanayin ruɗani nace "aisha a iya sanina da kuma tunanin mutuwa ba ƙarya bace, amma hakan yana neman sake ganinki a raye yana neman jefa zuciyata a ruɗani.
Murmushi naga tayi! Sannan tace "waya faɗama cewar na mutu?
Alhalin kai da kanka ka rakani har tashar motoci nahau mota domin zuwa jahar jigawa.
Jin haka ne yasa nayi shiru na ɗan wani lokaci, zuwa can sai na kalleta nace "tabbas naga haka amma a mafarki.
Sai tace "ba mafarki kayi ba domin azahiri hakan ya faru.
Fitowar mahaifiyata daga ɗaki kenan.
Sai na kalli mahaifiyar tawa nace "umma kinga aisha wai ba mutuwa tayi ba.
Cikin yanayin mamaki mahaifiyata ta kalleni tace "to kai a ina kasamu labarin ta mutu, kaifa ka rakata har tashar mota domin hawa motar da zata kaita jigawa.
Nan take na kalli ummey haɗe da cewa "ummey anya acikin hankalina nake kuwa, tabbas idan har maganar da aisha tayi gaskiyace to ba shakka ƙwaƙwalwata ta samu taɓuwa.
Buɗar bakin ummey sai tace "ita kuma wannan aishar wacece kuma meye alaƙarka da ita?
Nan take na shiga bata labari.
Sai nace "motace ta haɗani da ita tun daga jahar kebbi da misalin 12 na dare mu sauka haka ne yasa ta nemi taimakon aran wayata domin kiran wadda tazo wajanta amma sai wayar taƙi shiga.
Ganin yadda tayi matuƙar shiga damuwa ne yasa na kawota nan gidan da niyar idan Allah yasa gari ya waye sai ta kira wadda tazo wajan nata.
Tun a hanya na nemi sanin sunanta da garin da take haɗe da dalilin zuwanta wannan jahar tu ta Kano.
Cewa tayi aisha ne sunanta batun dalilin zuwanta kano kuma labari ne mai tsayi haɗe da ban tausayi wanda hakan yasa ta buƙaci nayi haƙuri zuwa safiya saboda a wannan lokacin tana matuƙar jin yunwa hade da bacci.
Da isarmu gida cikin yanayin farin ciki nagaisa da mahaifiyata sannan na kaiwa aisha abinci.
Kawai da misalin karfe 8 na safiya ina shiga ɗakin da'aba aisha a matsayin masauki sai nayi ido biyu da gawarta.
Ga kuma abincin dana kawo mata koci batayi ba hakane yasa jami'an yansanda su gudanar da bincike akaina hade da iyayena
Jin haka ne yasa mahaifiyata ta matso kusa dani sannan ta dafa kafaɗata haɗe da cewa " to indai hakane ba shakka akwai matsala a tattare da kai domin duk wannan batun da kayi bai faru anan gidan ba, kawai abun da na sani shine kazo da Aisha gidannan washe gari da safe kuma ka rakata ta hau mota zuwa jahar jigawa.
Buɗar bakina sai nace "to amma umma meya maƙasudin dawowarta gidannan?
Sai mahaifiyata tace " ai dama ta sanar da kai cewar kwana ɗaya zatayi acan sannan ta dawo gareka, saboda ka ɗaukar mata alƙawarin zaka aureta a sakamakon tausaya mata ɗin da kayi a dalilin jin labarin da ta baka.
=>10
Koda naji haka nan take na samu waje na zauna jikina a sanyaye haka na kalli Aisha da Ummey haɗe da mahaifiyata sannan nace "tabbas ina cikin ruɗani, domin bansan wani labarin da A'isha ta bani ba balle alƙawarin da ake iƙirarin cewar na ɗaukar mata.
Dan haka ba wani alƙawarin aure a tsakanina da ita.
Sai aisha tace "ikon Allah! Yanzu kana nufin harka manta da duk labarin dana baka?
Cikin yanayin kiɗimewa nace "aisha nifa bansan wani labarin daki baniba.
Sannan na kalli mahaifiyata nace "to amma umma shi kuma jawabin da kiyimin akan cewar ummey ƙanwatace ta jini shima baki da masaniyar komai akansa kenan?
Jin haka ne yasa ta kalleni fuskarta cike da mamaki!
Shiru naga tayi na ɗan wani lokaci sannan ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa "tabbas banyi wannan maganar da kaiba, amma a ina kasamu wannan labarin?
Koda naji wannan batun daga bakin mahaifiyata nan take naji kaina yayi wata irin bugawa sakamakon ganin yadda nake neman komawa zararre alhalin kuma ni nasan a cikin hayyacina nake.
Ganin haka ne yasa ummey tayi tunanin kawai so nake na juya mata baya ta hanyar kame-kamen hanyoyin da zasu kawo rabuwata da ita wanda hakan yasa tayi waje tana kuka.
Jim kaɗan da fitar ummey sai Allah yai dawowar mahaifina daga tafiyar da yayi.
Kamar dai yadda mahaifiyata tayi mamakin sake ganina a raye haka shima wannan mamakin haɗe da ruɗani ya bayyana a fuskarshi.
A wannan lokacin sai rudanin da nake ciki ya hanani bayyana farin cikin sake haɗuwa da mahaifina, domin ba abun da ya fara fitowa bakina illah neman sanin alaƙar da take a tsakanina da ummey.
Buɗar bakina sai nace "abba wace alaƙace a tsakanina da ummey?
Jin fitowar wannan tambayar daga bakina ne yasa naga mahaifina ya kalli mahaifiyata sannan ya kalleni haɗe da cewa "wace ummey kuma?
Matsawa nayi kusa dashi haɗe da cewa "abba a halin yanzu ina cikin ruɗanin da bawanda zai iya cireni a kaf faɗin duniyarnan bayan kai da kuma mahaifiyata.
Dan haka yanayin kallan da naga kayiwa mahaifiyata ya tabbatarmin cewar akwai wani abun da kuke ɓoyewa a tsakanina da ummey.
Haka na durƙusa har ƙasa ina mai zubar da hawaye nace "umma sanin kanki ne ni mai son ganin farin ciki ne a tattare daku, saboda buƙatar ganin farin ciki a tattare da ke ne yasa nabar gida na tsawon wani lokaci badan komai ba sai dan buƙatar ganin na cika umarnin daki bani ba tare da nayi kuskure ba domin ko mahaifina ban nemi sanin komai a gareshi haka nabar gida domin cika umarninki.
Ji nayi abbana yace "bakai kankaba nima kai na a cikin ruɗani nake, saboda gaba ɗaya na kasa fahimtar inda wannan maganar taka ta dosa.
Na buɗa baki zanyi magana sai mahaifiyata ta dakatar dani ta hanyar cewa "a'a nice wadda zanyi mai bayanin komai dangane da wannan al'amarin.
Ɗakin mahaifina mu shiga gani ga mahaifiyata haɗe da mahaifina.
Sai mahaifiyata ta kalli mahaifina tace "soyayyace ta shiga tsakanin wannan yaran da ummey.
Gudun kar soyayyar tasu tayi nisa ne yasa na buƙaci ya janye kanshi daga batun kula ummey da sunan soyayya, sannan na sanar dashi cewar "amma banason rabuwar da zasuyi ta zamto sular dai na shigowar ummey gidan nan saboda ganin yadda take gudanar da al'amuranta a gidannan ba kaɗan nakejin daɗi ba.
Ganin yadda na nemi shiga tsakaninsu ne yasa ya buƙaci jin dalilin da zaisa na rabasu.
Alƙawarin dana ɗauka akan cewar ba wanda zaiji wannan surrin ne yasa naƙi sanar dashi batun komai.
Buƙatar cika umarnin dana bashi ne yasa ya ƙirƙiri tafiyar da zai ɗauki dogon lokaci ba tare da ya sake waiwayar inda muke ba, a ƙarshe sai saƙon mutuwarshi ya iso garemu alhalin kuma ba mutuwa yayi ba ya aikata haka ne duk dan buƙatar cikamin burkina wajan ganin ya cire son da ummey take mai a zuciyarta.
Bai kuma tashi dawowa ba har sai da ummey tayi aure.
Koda mahaifina yaji wannan bayanin sai naga ya jinjina kai haɗe da cewa "tabbas wannan al'amari ne mai rikitarwa.
Kuma wannan hanyar dakabi dan ganin ka cika mana burinmu itace tafi dacewa dan haka ba wani abun da zamuce a gare face fatan alkairi.
Sannan kuma inamai baka haƙurin rashin sanin wannan sirrin da yake zukatanmu, saboda alƙawari mu ɗauka akan cewar bazamu sanar da kowa ba.
Cikin hanzari mahaifiyata tace "to ai ya riga yasan komai kuma babban abun da ya ɗauremin kai shine yadda ayi har yasan cewar ummey ƙanwarshice ta jini.
Jin haka ne yasa cikin gaggawa na miƙe tsaye fuskata cike da mamaki nace "umma ashe dai gaskiya ne ummey ƙanwatace ta jini kenan?
Nan take mahaifiyata ta jinjina kai haɗe da cewa "kwarai kuwa ummey ƙanwarkace ta jini domin ba yadda za'ai aure ya shiga tsakaninka da ita.
Sannan ta ƙara da cewa "to amma taya ayi ka samu labarin cewa ummey ƙanwarkace alhalin ba wanda yama bayani a tsakanin ni da mahaifinka?
Cikin yanayin mamaki nace "umma kefa ki faɗamin komai tun a jiya lokacin ina cin abinci a kusa da ke, domin ke da kanku ki sanar dani cewar "ummey ƴarkice wadda ki haifeta tare da hafsat a matsayin yan biyu.
Ganin yadda abokin mahaifina haɗe da matarshi su shiga damuwa a dalilin rasuwar jaririn da su haifa ne yasa ku mallaka UMMEY a garesu badan kimai ba sai dan duba da yadda su ɗauki dogon lokaci ba tare da sun samu haihuwaba.
Ba'a ɗauki wasu dogwayen kwanaki ba sai Allah ya ɗauke ran hafsat wato ƴar uwar ummey kenan.
A yayin da mahaifiyata ta gama jin wannan jawabin nawa sai tace "tabbas akwai matsala a tattare da kai domin ko kaɗan banyima bayanin komai a tattare da wannan surrin ba.
Duk da cewa wannan al'amari ne ba ɗan ƙarami ba, haka nayi ƙoƙarin mantawa da wannan batun.
Bayan gari ya waye nayi wanka fitowata daga gida kenan da ƙudurin yawatawa cikin gari.
Sai Aisha ta biyo bayana.
Koda na haɗa ido da ita sai tace "ya kuma zaka tafi ka barni alhalin kuma kayimin alƙawarin bazaka taɓa nisanta kanka dani ba.
Kallanta kawai nayi haɗe da cewa "nifa bansan komai a dangane da rayuwarki ba, balle har kiyi ƙoƙarin kawo batun ɗaukar alƙawari a tsakanina dake.
Jin haka ne yasa nan take naga fuskar Aisha ta canza ta hanyar bayyana ɓacin rai.
Har ta juya da ƙudirin komawa sai na dakatar da ita ta hanyar cewa "da zaki taimaka ki bani cikakken labarinki zata iya yiwuwa hakan ya taimaka wajan rage ruɗanin da nake ciki.
Hawaye nagani a fuskarta a yayin da ta juyo zuwa gareni.
Ganin haka ne yasa nayi murmushi haɗe da cewa "haba Aisha meye kuma na zubar da hawaye a game da wannan maganar?
Buɗar bakinta sai tace "maganar gaskiya banyima halacci ba amma kayi haƙuri domin bani da wata hanyar da ta dace nabi wadda ta wuce wannan hanyar.
Cikin yanayin ɓacin rai nace "Aisha a halin yanzu bana buƙatar sakejin duk wata maganar da zatayi sular sake afkani a cikin ruɗani.
Dan haka duk wata maganar da zata fito bakinki zanso kiyita wara-wara yadda zan fashimci inda maganar ta dosa.
Hannuna naga ta riƙe zuwa wani kebabben wajan dake kusa damu.
Bayan mun zauna sai tace "tabbas nice sular haifar da duk wani ruɗanin daka tsinci kanka a ciki.
Kuma ba komai ne ya haifar da hakan ba illah ƙaunarka ɗin da take a zuciyata.
Azahirin gaskiya inasonka kamar yadda na aje kaunarka a zuciyata.
Amma dan Allah zanso kafin na sanar dakai koni wacece kasanar dani, shin kaima kanajin sona a zuciyarka koda kaɗan ne?
Jin haka ne yasa na ɗago kai nalleta hade da cewa "ai shi so a zuci yake samun masauki, kuma zanso ki gane wani abu dangane da batun SO.
Duk girman abu haɗe da ƙasaitarsa ko kyawunsa ba yadda za'ai ya samu masauki a sansanin zuciyar koma waye muddun zuciyarsa batayi na'am dashi ba.
Wani abun mamaki kuma sai kiga ɗan abu ƙarami ya haifar da soyayya ga zuciyar wasu.
Tabbas kina da kyawun da ya zarce na ummey domin ke kyakkyawace to amma hakan bazai taɓa sawa na ɗaukeki a matsayin wadda tafi ummey ba.
Koda naga ta ɗan ɓata rai sai nace "hakan bawai yana nufin cewar bana sonki ba domin tun tuni zuciyata ta alkinta sonki a cikinta.
Kuma hakan ya samo asali ne a sakamakon tausayawar da nagani a tattare dake.
Gyara zama tayi sannan ta kalleni haɗe da cewa "dan Allah kar kaji tsorona domin ba yadda za'ai na cutar da rayuwarka.
Kallanta nayi haɗe da cewa "ki faɗi duk wani abun dake ranki kanki tsaye.
Ban tashi auneba sai jin saukar mari nayi a fuskata.
Juyo fuskar da zanyi sai nayi ido biyu da ummey tsaye a gabana.
=> 11
Cikin yanayin fusata ummey tace "kai azzalimine macuci wanda baisan darajar kansaba.
Haƙiƙa wannan da kake tare da ita tafini kyawun fuska.
Dan haka bazanga laifinka ba dan kayi watsi dani ta hanyar maye gurbin soyayyata da ta wannan wawiyar.
Amma ka tabbatar da cewar ba yanda za'ai na bari ka ƙulla wata alaƙar da ta shafi soyayya da wata har sai ka kwashe gubar soyayyar daka shayar dani wadda ta daskare a zuciyata.
Sannan zaka samu damar kula wata ya mace, domin ba wanda nake jin cewar zai iya dakatar dani akan abun da zan iya aikatawa a gareka saboda gubar daka shayar dani ta doɗe duk wasu hanyoyin dasu dace shawara mai amfani ta isa kunnena.
Jin haka ne yasa ran Aisha yai matuƙar ɓaci.
Cikin yanayin bayyana ɓacin rai Aisha tace "haba ummey wannan ai halayyace irin ta marasa hankali da tunani ya za'ai kawa dan kinyi ido biyu damu zaune zaki ɗaga hannu ki mareshi?
Cikin yanayin ɗaga murya na dakama Aisha tsawa haɗe da cewa "karki sake danganta ummey a sahun marasa hankali, domin bazan taɓa jurar ganin bacin ranta ba.
Tsawar dana daka mata ne yasa ranta ya ɓaci, wanda hakan yasa nan take naji kai na yana sarawa kamar wanda yai karo da bango.
Cikin ƙanƙanin lokaci naji duk ilahirin jikina ya ɗauki zafi.
Ganin hakane yasa nayi gaggawar shiga gida.
Da shigata falo sai na yanke jiki na faɗi.
Sai da na ɗauki tsawon lokaci kafin mahaifiyata ta ankara dani.
A yayin da mahaifiyata tayi ido biyu dani sai ta rugo zuwa gareni.
Koda taga alamun suma nayi sai tayi gaggawar ɗakko ruwa a fridge ta yayyafamin har ta fara kuka a yayin da taga naƙi motsawa.
Miƙewar da zatayi sai taji nayi tari haɗe da jan wani dogon numfashi.
Cikin gaggawa a garzaya dani zuwa asibiti.
Tsawon kwana biyu na ɗauka kwance a gadon asibiti kafin na iya gane waɗanda ke kusa dani.
Da mahaifiyata na fara haɗa ido sai kuma abokina ANAS zaune a kusa dani.
A yayin dana haɗa ido da ummey sai naji kirjina yai wata irin bugawa.
Saboda nasan dolene a samu matsala, domin ko kaɗan banason ganin ummey a cikin damuwa ko ɓacin rai.
Sai dai kuma bani da masaniyar dalilin faruwar wannan rashin lafiyar tawa.
Na ɗauka ummey zata nisanta dani amma sai al'amarin ya sake rikicewa haka sona yaci gaba da sake sabon toho a zuciyar ummey, wanda hakan yasa ummey ta turje akan batun ba wanda zata zauna dashi a matsayin miji idan bani ba, saboda har kawo wannan lokacin ita ummey bata yadda da cewar ita ƙanwatace ta jini ba, su kuma iyayena haɗe da nata iyayan wato waɗan da suke riƙe da ita a matsayin ƴarsu sunƙi fitowa fili domin wayar mata da kai.
Tun daga lokacin da'a dawo dani daga asibiti ummey bata da wata sakewar da ta wuce ta ganta a tare dani.
Ganin hakane yasa nace da ita "ummey yaushe zaki koma gidan mijinki?
Buɗar bakinta sai tace "amma me yasa ka zaɓi kamin wannan tambayar saɓanin wadda nayi tunanin fitowarta daga bakinka, domin ba abun da nakeson ji daga bakinka face batun aurena da kai?
Fuskata ba alamar wasa nace da ita "amsar tambayar dana miki nakesonji daga bakinki.
Cikin yanayin damuwa tace "Ba rana balle wata saboda kai ne zaɓina.
Koda naji haka sai nace "to bari kiji tarayyata da ke bazata taɓa yiwuwa ba balle ayi batun aure, dan haka shawarar da nakeson baki a matsayina na ɗan uwanki itace "ki koma ga mijinki saboda wannan ita kaɗaice hanyar da zata iya ɓullewa dake.
Cikin yanayin alhini tace "meyasa kake son dangantani da batun ni yar uwarkace amatsayin hanyar da zata haifar da rabuwa a tsakaninmu?
Haka ta kalleni tana kuka tace "me yasa zaka juyamin baya a lokacin da sonka ya makantar dani ta hanyar daina ganin duk wata hanyar da zata kawo batun rabuwata da kai?
Ganin halin da ummey take ciki ne yasa na yanke shawarar wayar mata da kai a game da gaskiyar abun da iyayenmu suke boye mana.
Buɗar bakina sai nace "ummey sanin kanki ne tun kafin ki kamu da sona narigaki kamuwa da haƙiƙanin launarki.
Tabbas kafin zuwan wannan lokacin ba kaɗan nakejin shauƙin sonki a zuciyarsa ba, amma a halin yanzi idan akwai abun da zai iya kasancewa danasani ga rayuwata to bazai taɓa wuce faruwar soyayya a tsakanina dake ba.
Kallanta nayi haɗe da cewa "ummey kefa ƙanwatace ta jini wadda mahaifiyata ta haifeku a matsayin yan biyu abokiyar haihuwarki itace hafsat wadda Allah yaima rasuwa tun bata wuce wata ɗaya da haihuwa ba.
Tun da nake a rayuwata ban taɓa tunanin durƙusawa a gaban wata ƴa mace da sunan roƙon wata alfarma a tattare da ita ba.
Amma sai gashi nine na durƙusa har ƙasa a gaban ƙanwata domin roƙonta.
Koda na durƙusa a gaban ummey sai nace "dan Allah ummey ki taimaka ki rufa mana asiri ta hanyar janye batun soyayyar da take a tsakanina dake ki.
Kuma zanso kiyi ƙoƙarin riƙe wannan surrin a iya zuciyarki ta hanyar ƙin sanar da kowa wannan surrin.
Sannan zanso kikasance mai ƙoƙarin samawa zuciyarki haƙurin zama da wadanda suke riƙe dake a matsayin yarsu ta hanyar cigaba da ɗaukarsu a matsayin iyayenki waɗanda su haifeki.
A ƙarshe kuma ina mai roƙonki daki koma ga ainahin mijinki domin ba aure a tsakanina dake.
Nan take naga fuskar ummey ta canza sannan ta share hawayen dake fuskarta ta fita daga ɗakina.
Ban saniba ashe wajan mahaifiyarmu ta tafi.
Koda ummey ta samu mahaifiyar tamu sai tace "umma me yasa ke da abba ku zaɓi kuyi watsi da kyautar da Allah ya baku ta hanyar damƙata ga wasu?
Umma bansan irin azaftar dake ɗin da nayi alokacin da ina cikin mahaifarki ba wanda hakan zaisa kiyi sadaka dani ga waɗanda ko dangantakar jini bamu haɗa dasu ba.
Gashi a dalilin faruwar haka zuciyata tana neman cutuwa.
Abu na farko nayi rashin ingantacciyar tarbiyyar da ta dace na samu daga gareku.
Abu na biyu a dalilin rashin sanin wannan sirrin daku daɗe kuna ɓoyewa har zuciyata ta kamu da son kasancewa da yayana wanda nake jini ɗaya dashi a matsayin matarshi.
Nan take ummey ta durƙusa har ƙasa cikin yanayin kuka tace "dan Allah umma ku taimaka ku dawo dani gida?
Ina zaune a ɗakina cikin yanayin damuwa sai naji karar buɗe ƙofa.
Dago kan da zanyi sai nayi ido biyu da AISHA.
Buɗar bakin Aisha sai tace "yanzu kana tunanin abun daka aikata kayi dai-dai kenan?
Buɗar bakina sai nace "waike wacece?
Kuma wace alaƙace a tsakanina dake da har kike yima rayuwata shish-shigi akan abun da bai shafeki ba?
Murmushi tayi hade da cewa "zaka iya tunawa da wani ƘADANGARAN da abokinka yayi ƙoƙarin kashewa yau kimanin shekara 14 kenan da faruwar hakan?
Cikin yanayin ruɗani mai tattare da mamaki nace "shi wannan ƙadangaran shine ya addabi rayuwata na tsawon waɗannan shekarun naji kin ambata.
Haka ne yasa bana buƙatar jin duk wani labarin da ya shafi ƙadangare balle ganinshi ido da ido.
Wannan al'amarin ya samo asali ne tun ina ɗan kimanin shekara 8 lokacin muna zuwa makarantar primary.
Aduk lokacin damu halarci makaranta bani da wani sukunin da ya wuce maida hankalin riƙe koda abu biyu ne daga cikin abun da malamanmu su koyar damu saboda hakane yake bani kwarin guiwar samun kyaututtuka daga wajan mahaifina haɗe da mahaifiyata, domin ako wace ranar dana halarci school mahaifiyatace take fara tambayata abun da'a koyar damu idan mahaifina ya dawo shima sai ya ɗora da nashi tambayoyin.
Mahaifina haɗe da mahaifiyata suna matuƙar alfahari dani ganin yadda nake ƙoƙarin zuwa makaranta.
Sai dai kuma a zaman takewar rayuwa dolene kaci karo da mutane biyu wato mutanan banza da kuma na kirki.
Abokan banza ne suyi sular canza halayyata izuwa halayyar da suke ciki.
Tun ina jin tsoran kasancewa a tare dasu har na kai matakin da nake sakin jikina a cikinsu.
Da zaran mun halarci school bama ɗaukar awa ɗaya ba tare damun tafi bayan gari yawon banza ba.
Tafiya mukeyi mai nisa domin zuwa lambun ɗaya daga cikin abokanmu badan komai ba sai dan buƙatar shan gwaiba, rake, mangoro, kashu, da dai suransu.
Kafin mahaifina ya ankara tuni wannan yawon banzan yayi ƙarfi a zuciyata ta yadda sai ankai ruwa rana kafin a iya cimma nasarar dakatar da cigaba da faruwar wannan yawon a tattare dani.
Tabbas ni nasan cewa mahaifina yana matuƙar sona amma duk da hakan bai hanashi yimin shegen duka ba domin bansan adadin dukan da nasha a dalilin yawace yawacen banza ba.
Sai dai kuma akwai wata ɗabi'ar da nake tattare da ita wadda hakan yasa nake yawan samun matsala da abokan da nake tafiya yawo dasu.
Wannan dabi'ar tawa ta samo asaline tun wata ranar Monday kafin halayyata ta samu nakasu ta hanyar yawace yawacen banza.
Misalin ƙarfe 8 na safiyar Monday na fito daga gida a gaggauce ko karyawa ban samu damar yi ba domin gudun kar a dakeni a makaranta saboda nima kai na nasan a wannan ranar a makke nake.
Har nayi nisa sai kular abincin da nake riƙe da ita hannunta ya fita nan take taliyar dake ciki tayi watsa-watsa.
Tabbas nayi mamakin ganin yadda ƙadangaru su tasa abincin a gaba.
Ban bar wajan ba har sai da su cinye abincin tas.
Duk da cewa ayunwace nake haka na tafi makaranta ba tare da bayyana wata damuwa ba, saboda a cikin littattafaina akwai wata naira hamsin ɗin dana daɗe da ajewa.
Haka nayi haƙuri har a tashemu break sannan na samu abun da zanci.
Tun daga wannan ranar na ƙudiri niyar cigaba da tallafama ƙadangaru.
Ako wace rana bana taɓa rasa yan kuɗaɗan kashewa daga mahaifina ko mahaifiyata wani lokacin kuna yayata zainab nake tunkara da buƙatar ta bani kuɗin da zan ɗan kashe.
Ta waɗannan hanyoyin nake samun ƴan kuɗaɗan da nake siyan taliya domin ciyar da ƙadangaru.
Tafiyayya nakeyi zuwa wani kango domin kaiwa ƙadangaru abinci badan komai ba sai dan kar al'umma su samin ido.
Saboda abun yana burgeni musamman idan naga sun duƙufa wajan cin taliyar da nake kai masu.
Gaba ɗaya sai wannan al'amarin ya zamemin kamar wani bangare na rayuwata wanda idan ban aikatashi ba to ba yadda za'ai naji daɗi a rayuwata.
Haka nayita gudanar da wannan aikin ba tare da kowa ya sani ba, domin a wannan lokacin bani da wasu abokai na musamman.
A yayin da halayyata ta samu canjine ta hanyar samun abokan banza sai wannan dabi'ar tawa ta fito fili.
Amma ba kowa ne ya sani ba domin iya abokaina ne kaɗai susan da wannan dabi'ar tawa.
A yayin da nakai kimanin 10 years sai na tsayar da lokacin da zan riƙa kai masu abinci wato taliya kenan.
Misalin karfe 7:30 na safiya nake zuwa ɗakin abokina ANAS domin dafa taliyar da zankai masu.
Zuwa misalin karfe 2 na rana kuma bayan an idar da sallar Azahar kuɗi nake cirewa daga aljihuna domin siyan taliyar da zan kai masu.
Da zaran naga yamma tana neman yi haka zan sake siyan wata taliyar na aje masu idan magariba ta tunkaro sai naje na kai masu.
Abun ba kaɗan yake bani dariya ba ganin yanda ƙadangarun suyi ƙiba kuma ni ba ma'abocin cin ƙadangare ba balle na riƙa yankawa inaci.
Duk yawon da zanyi da abokaina bana taɓa yin sake wajan kai masu abinci akan lokaci.
Idan har nasan zanyi tafiyar da zata haifar da rashin kai masu abinci akan lokaci to ba makawa sai naje garesu domin basu haƙuri.
Da zaran sunji sallamata sai su rugo zuwa gareni.
Abun da nake cewa a garesu idan zanyi tafiya shine "kuyi haƙuri saboda yau zanyi wata ƴar tafiya kuma ina tunanin hakan zai iya haifar da rashin kawo maku abinci da wuri.
Haka zasuyita gyaɗa kai haɗe da buda baki ba tare da nasan abun da suke faɗa ba.
Idan kuma a samu akasi wani uzirin ya hanani kai masu abincin akan lokaci haka zan basu haƙuri haɗe da sanar dasu dalilin faruwar hakan.
Ganin yadda wannan al'amarin ya game jikina ne yasa abokaina suke nuna ɓacin ransu wanda a ƙarshe suyi yunƙurin kashe ƙadangarun gaba ɗaya ta hanyar sa masu guba a taliya.
Amma sai Allah da ikonsa yasa ƙadangarun suƙi cin taliyar da abokan nawa su kai masu.
A majalissa da muke zama ne a samu akasin da ya haifarmin da tsanar ƙadangaru a gareni.
Muna cikin zamanmu sai NUHU ya kira wata mai gyaɗa.
A gabanmu ya siyi gyaɗar 20 naira ya kuma murjeta a gaban idonmu da ƙudurin cinyeta shi kaɗai.
Ganin hakane yasa na nace akan cewar dole sai naci gyaɗar.
Cikin yanayin wasa muyita kokawa har mu fita daga majalissar tamu ta hanyar yin tafiya mai ɗan tazara duk a cikin kokawa.
Ba yadda ya iya haka ya buƙaci na buɗe hannuna domin ya zubamin gyaɗar.
Wajan zubamin gyaɗar ne a samu akasi gyaɗar ta zuba a ƙasa.
Ganin haka ne yasa wani ƙadangare ya rugo a guje ya ɗauki ɗaya daga cikin gyaɗar da ta zuba a ƙasa ya haɗiye.
Nan take naga ran NUHU yai matuƙar ɓaci wanda hakan yasa yayi ƙoƙarin kashe ƙadangaran.
Haka yabi ƙadangaran a guje domin ganin bayanshi sai Allah ya taimaki ƙadangaran ya afka wani rami to ashe dai ƙadangaran bai sha ba, domin ramin ba wani mai nisa bane.
A gaban idona nuhu ya zura hannu ya kamo ƙadangaran da hannunshi.
Ganin yanda Nuhu yake ƙoƙarin kashe ƙadangaran ne yasa nayi ƙoƙarin dakatar dashi amma sai hakan bai yuwu ba domin buga ƙadangaran yayi a ƙasa.
Anan take ƙadangaran ya riƙa kumbura kamar wanda ake hurama iska.
Haka naja abokina mu tafi tun a hanya Nuhu ya sanar dani shifa kanshi ciwo yakemai wanda hakan yasa yayi gaggawar tun karar gida.
Ko cikakken 30 minutes da rabuwarmu ba aiba sai batun rasuwar nuhu ya karaɗe gari.
Ba kuma kowane yasan abun da ya faru kafin rasuwar Nuhu ba sai ni da abun ya faru a gaban idona.
Bayan kwana ukku da rasuwar nuhu wato abokina kenan sai babban kalubale ya fara bibiyata.
Cikin dare muslin ƙarfe 2 naji matsin wani abu a ƙirjina wanda ban gane ko menene ba.
Tsoran da naji ne yasa na kwalla ƙara ban kuma san lokacin dana faɗo daga kan gado ba.
Cikin yanayin furgici na haska tocila.
Ganin ƙadangaran da NUHU yayi ƙoƙarin kashewa a ɗakina ne yasa nayi matuƙar tsorata wanda hakan yasa nayi ƙaura daga ɗakina zuwa ɗakin anti zainab.
Da shigata sai na tashi anti zainan daga bacci haɗe da cewa anti wallahi tsoro nakeji.
Haka ta tilastamin akan saina sanar da ita tsoran da nakeji amma naƙi domin nasan muddun nayi gaggawar sanar da ahalina wannan batun to ba makawa sai an samu wanda zaiyi ƙoƙarin hallaka ƙadangaran.
Kuma na tabbata hakan zai iya haifar da sular hallaka rayuwar wasu daga cikin ahalina haɗe dani kai na.
Ni kuma faruwar haka ne banaso.
Ganin yadda naƙi sanar da ita ne yasa ta kyaleni mu kwanta tare a gado daya.
Ban saniba ashe akwai sauran rikici a gaba.
=> 12
Sannan na kalli Aisha haɗe da cewa "ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba a dalilin kasancewar wannan ƙadangaren a tattare dani, domin hanani sakeya yayi saboda duk inda zani dolene shima ƙadadaren ya kasance a wajan.
Idan ina cikin abokaina ko wasu mutanan da ban baya kusanto inda nake sai dai ya koma can gefe ɗaya ya tsaya.
Sai ya zamto har fargabar zama ni kaɗai nakeyi domin idan yaga ni kaɗai ne har hawa jikina yakeyi.
Aduk lokacin da naji yahau jikina zabura nake a guje.
Har faduwa nashayi wajan gudu wanda hakan yake sawa naji ciwuka a hannayena haɗe da kafafuwana.
Bana taɓa yadda na kwana ni kaɗai domin a ɗakin anti zainab nariƙa kwana.
Lokaci ɗaya yayata ta bayyana ɓacin ranta a game da kwanan da nakeyi tare da ita wanda hakan yasa tamin mugun duka alhalin kuma ba laifina bane domin duk laifin wannan addababban ƙadangaren ne.
Duk dukan da anti zainab zatamin baya taɓa damuna domin ko zubar da hawaye banayi ni dai kawai na gwammaci ta ganamin duk wata azabar da taga dama a maimakon na kwana tare da ƙadangarare a ɗakina.
Koda ta gaji da ganina a ɗakin nata sai ta gargaɗeni dana dai na shigar mata ɗaki kokuma ta sanar da mahaifinmu.
Tun daga wannan ranar sai na koma kwana a ɗakin abokina ANAS.
Sati na ɗaya da komawa ɗakin anas sai mahaifina ya gane cewar bana kwana a gida.
Duk da irin faɗan da mahaifina yakemin hakan baisa na daina kwana a ɗakin anas ba.
Ganin hakane yasa mahaifina yamin dukan da bantaɓa tunanin fuskantar irinshi a faɗin duniyar nan ba.
Gudun karna sake fuskantar irin wannan dukan ne yasa na buƙaci abokina ANAS da ya riƙa zuwa ɗakina muna kwana tare, amma sai yaƙi amince saboda shima mahaifinshi bazai laminci kwananshi a wani wajan da ba gidansu ba.
Haka dai wannan ƙadangaran ya hanani sakewa.
Lokaci ɗaya sai ƙadangaran ya bijiromin da wani sabon iskanci.
Dazaran na sayi wani abun da niyarci sai ƙadangaran ya rugo a guje zuwa gareni tsoran da nake tattare dashi ne yake sawa na saki abun ya faɗi ƙasa nan take shi kuma ƙadangaran zai hau abun da ci.
Misalin karfe 12 na rana na tunkari gida da ƙudirin cin abinci.
Da shigata ɗakina sai nayi ido biyu da ƙadangaran a saman marfin abincin da'a ajemin.
Maganar gaskiya nayi mamakin ganin yanda ƙadangare ya addabi rayuwata, kuma gashi idan na nemi takurama rayuwarshi to ba makawa sai na rasa tawa rayuwar kamar yadda abokina NUHU shima ya rasa tashi rayuwar.
Ganin hakane yasa na durƙusa har ƙasa ina zubar da hawaye domin neman sulhu a tsakanina da ƙadangaran.
Cikin yanayin kuka nace "haba bawan Allah meyasa kake neman takurama rayuwata ta hanyar bibiyata, alhalin ban aikata laifin komai a gareka ba?
Abokinanefa ya nemi kasheka ganin haka ne yasa na nemi ceton rayuwarka, kuma ai ka ɗauki fansar abun da ya aikatama meye zaisa kaci gaba da bina.
Dan Allah idan har bazaka daina binaba to kadaina hawa jikina kuma ka daina ƙoƙarin tunkarar inda abincina yake.
Kuma nayima alƙawarin duk abun da zanci zan rabashi biyu ɗaya naka ɗaya nawa.
Haka tunanin wannan ƙadangaran ya addabi zuciyata lokaci duk nabi na rame ganin haka ne yasa iyayena suyi yunƙurin tilastamin wajan ganin na sanar dasu lalurar da take damuna.
Ganin yadda naƙi yimasu cikakken bayani ne yasa su dangantani da asibiti domin duba lafiyata.
Likitan da ya duba lafiyar tawa sai yace "ba wani abu ne yake damun danku ba illah yawaitama zuciyarshi tunani.
Dan haka rage tunanin dake zuciyarshine kadai zai kawo mai sassauci a game da halin da yake ciki.
Anti zainabce ta tilastamin har sai da nayi mata cikakken bayanin abun da yake damuna.
Haka aita nemamin magani domin rabani da wannan ƙadangaran amma hakan yaci tura.
Haka wannan ƙadangaran yaci gaba da bibiyata na tsawon shekara 14 amma da taimakon Allah a dalilin maganin da iyayena su dage da nemamin sai Allah yasa wannan ƙadangaran ya rage bibiyata.
Yana zuwa gareni ne lokaci-lokaci kuma idan ya tashi zuwa gareni tofa a duk inda nake Kwatsam zan ganshi amma baya hawa jikina.
Yau kimanin shekara biyu kenan rabona da sake ganin ƙadangaran.
A yayin da na gama ba aisha wannan labarin sai ta matso kusa dani fuskarta cike da murmushi.
Buɗar bakinta sai tace "ba kaine ya kamata ka bani wannan labarin ba, domin nice wannan ƙadangaran kuma nice sular afkawarka a duk wani ruɗanin daka tsunci kanka a ciki.
Cikin yanayin tsoro haɗe da tashin hankali na miƙe tsaye a yayin da naji fitar wannan furucin daga bakin Aisha.
Tsoran da Aisha ta gani a tattare dani ne yasa tayi gaggawar rike hannuna.
Fuskarta ba alamar wasa tace ko kaɗan ban nemi shiga rayuwarka domin na cutar dakai ba.
Kawai buƙatar rayuwata da taka su zama ɗayane yasa nayita bibiyarka.
Ganin yadda ka tausayamin a yayin da abokinka yayi yunƙurin cutar dani ne yasa ruhina ya aminta da kai wanda hakan yasa naita bibiyarka a suffar ƙadangare alhalin kuma ni aljanace.
A duk lokacin daka kwanta bacci kai kaɗai ni kuma sai nazo na kwanta a saman ƙirjinka domin ba ƙaramin daɗi nakeji ba a yayin da sautin bugun zuciyarka yake ratsa kunnuwana.
Kwatsam sai naga take-taken soyayya tana neman shiga tsakaninka da UMMY alhalin kuma baka da masaniyar ita kanwarka ta jini ce.
Gudun karka takurama kanka wajan bibiyar ummey da sunan soyayya ne yasa nayi ƙoƙarin dakatar dakai ta hanyar yima hannunka mai sanda ba tare dana fito fili nayima cikakken bayanin cewar ummey ƙanwarka ta jini ba ce.
Bayanin da nayima a lokacin dana kiraka a waya ne ya tunzuraka wanda hakan yasa kayima ummey bayanin abun dana sanar da kai na cewar ba aure a tsakaninka da ummey.
Soyayyar da take zukatanku ce tasa baku ɗauki maganar tawa da mahimmanci ba.
Mahaifiyarka itace wadda ta fara gane alaƙar da take tsakaninka da ummey.
Buƙatar ganin farin cikin mahaifiyarka ne yasa ka shirya tafiyar da zaka dauki dogon lokaci kafin ka dawo ga ahalinka badan komai ba sai dan ka rusa soyayyar da ummey take nunawa a gareka.
A hanyarka ta dawowa gida ne nayi amfani da wannan damar domin kusanta kaina dakai wanda hakan yasa ka bani masauki a gidanku.
Tabbas banyima bayanin komai dangane da rayuwata ba mahaifiyarkace kaɗai taji labarina.
Amma ita a tunaninta kaima kana wajan a lokacin da nake bata labarin wanda hakan yasa ka ɗaukarmin alƙawarin kasancewa dani na tsawon har abada a sakamakon tausayamin ɗin da kayi alhalin kuma mahaifiyar taka batasan cewar duk shirina bane domin ba kai ɗin bane.
Batun mutuwatama ba gaskiya bane domin kai kaɗai ne kaga faruwar hakan saboda na jihar da hankalinka ne kuma na bayyana batun mutuwar tawa a mafarkinka.
Dan haka daga yau zan nisanta dakai na tsawon har a bada bazan sake bibiyarka ba saboda babu wata alaƙa a tsakanimu da yan adam.
Sai dai kuma akwai sauran kalu bale a gabanka domin tun daga lokacin daka dawo gida iyayenka haɗe da kanwarka ummey ba wanda yaji furucin komai daga bakinka.
Nan take naji kaina ya ɗaure wanda hakan yasa na kalleta haɗe da cewa "ban fahimci abun da kike nufi ba?
Cikin yanayin tausayawa tace "Dan Allah kayi haƙuri nasan nayi matuƙar rikitar da kai.
Ba kuma komai ne yasa na aikata hakanba sai dan buƙatar mallakarka a matsayin abokin rayuwata.
To amma idan na aikata haka banyima adalci ba wanda hakan yasa na yanke shawarar faɗama gaskiya a yanzu.
Durƙusawa naga tayi har ƙasa sannan ta ɗago kai ta kalleni tace "dan Allah kayafemin a game da ƙaryar da nayima akan cewar UMMEY ƙanwarkace domin ba wata dangantakar da zata hana yiwuwar aure a tsakaninka da ummey domin gaba ɗaya abun da ya faru a wannan al'amarin duk shirina ne domin har kawo yanzu ummey ba ta yi aure ba.
Kawai na aikata haka ne domin buƙatar na maye gurbin ummey.
Tabbas ummey tana matsanancin sonka domin bata da wani muhimmin tunanin da ya wuce tunaninka.
Na buɗe baki zanyi magana kenan sai ta ɓace.
Ko cikakken munti ɗaya da bacewarta ba ai ba sai naji ƙarar buɗe kofa ummey na gani hannunta riƙe da abinci a plate.
Da zuwanta sai ta aje abincin a gabana sannan ta zauna a kusa dani.
Yanayin kallan da naga tamin ne yasa nayi murmushi!
Buɗar bakina sai nace "ummey wace alaƙace a tsakanina dake?
Cikin gaggawa naga ta miƙe tsaye cikin yanayin farin ciki ta fara kiran mahaifiyata "umma! umma!. Kizo yayi magana.
Cikin ba'a wani ɓata lokaci ba sai mahaifiyata ta shigo haɗe da anti zainab wato yayata kenan.
Cikin yanayin mamaki nace "umma wai me yake faruwane?
Cikin yanayin alhini zainab ta rungumeni tana kukan farin ciki.
Bayanin da ummey tayimin ne ya tabbatarmin da cewa maganar aljana Aisha gaskiyace domin ummey cewa tayi tun daga lokacin dana dawo gida bana iya furta kalmar komai.
Shiru nayi na ɗan wani lokaci sannan na jinjina kai haɗe da cewa "ashe dai Aisha da gaske take.
Buɗar bakin anyi zainab sai tace "wacece kuma Aisha?
Fuskata cike da mamaki nace "wai yanzu kuna nufin har kuna manta da aishar da nazo tare da ita gidan nan kenan?
Girgiza kai naga mahaifiyata tayi haɗe da cewa "haskiya ba wata macan da kazo da ita gidannan, amma tabbas bakai ka dawo da kanka ba domin wata baiwar Allah ce ta kawo mana kai a sakamakon ID CARD ɗin da ta gani a tattare da kai kuma sunanta ya banbanta da wanda ka faɗa a yanzu domin cewa tayi Amina ne sunanta kuma ko kwana batayi ba ta koma.
Fuskata cike da mamaki nace to amma umma wace alaƙace a tsakaninsu da ummey?
Cikin yanayin mamaki ummey tace "kardai kace har ka manta da soyayyar da take a tsakanina da kai?
Girgiza kai nayi haɗe da cewa a'a ban mantaba amma akwai sarƙaƙiiyar dana tsunci kaina a cikinta.
Banyi ƙasa a guiwa ba har sai da nayi masu cikakken bayanin abun da ya haɗani da Aisha wanda hakan yai matuƙar kiɗimasu domin basu da masaniyar komai dangane da bayanin da suji daga bakina.
Bayan na gane cewar akwai aure a tsakanina da ummey sai na nuna matsantawa ta wajan ganin anyi aurena da ummey domin gudun kar wata matsalar ta sake biyo baya.
Wani kallo naga anti zainab tamin haɗe da cewa "kai kaji yaro da rashin kunya ai komai gaggawarka dolene kajira sai nayi aure sannan ayi naku bikin.
Cikin yanayin dariya ummey taja hannuna muyi waje.
Da fitowarmu sai na kalli ummey haɗe da cewa "wai dama har kawo yanzu anti Zainab batayi aure ba?
Murmushi naga ummey tayi haɗe da cewa "gaskiya ya kamata ka mance da duk wata baƙuwar rayuwar da kayi a baya saboda wannan itace asalin rayuwarka domin ba wani auran da anti zainab tayi.
Haka naci gaba da kasancewa a tare da wanda hakan yasa Ummey batason na nisanta da ita.
Makarantace da kuma bacci suke rabamu da zaran an tasosu daga school ba inda take fara yada zango sai a gidanmu kuma ba zata fito ba sai tare dani duk da cewar tsakanin gidanmu da nasu ba wata tazara bace mai nisa haka zan rakata har cikin gidan nasu.
A haka dai har Allah ya bamu ikon cimma burinmu na kasancewa a matsayin ma 'aurata.
Alhamdulillah.
The End
0 comments:
Post a Comment