Thursday, August 8, 2024

LOVE STORY complete




newa update
haƙiƙa tun da nake a rayuwata ban taɓa tunanin haka soyayyar social network take da matuƙar daɗi ba.

Na haɗu da haneefa tun kimanin watanni 5 dasu wuce a facebook.

Bari dai na fara baku labarin tun daga farko.

___Ni dai haifaffen jahar kano ne kuma Allah ya jarabceni da yawan hawa social network amma nafi jin daɗin facebook.

Haƙiƙa yawanci mutane suna hawa network ne domin suyi charting ko kuma su karanta labarai domin nishaɗi haɗe da ilimantuwa domin nima kaina ina matuƙar ƙaruwa da wasu muhimman abubuwa a social network.

Kwatsam wata ranar asabar da musalin ƙarfe 1:00 na rana, ina hawa online sai nayi ido biyu da posting ɗin wata mai suna haneefa, maganar gaskiya a wannan lokacin ban hau facebook domin karanta wani posting ba amma dolece tasa na tsaya domin karanta abunda haneefa ta rubuta saboda tun daga farkon posting ɗin ta ba komai ne a ciki ba illa cin mutunci da wulaƙanci akan mu maza.

Koda na karanta duk abun da ta rubuta kai tsaye nayi mata yar nasiha a game da posting ɗin da tayi ta Private wato massage kenan.

A wannan lokacin ko cikakkun mintina 4 ba ai ba sai replay ɗin haneefa ya shigo wayata koda na karanta sakon da haneefa ta turomin sai nayi shiru na rasa abun da yake min daɗi a rayuwata jim kaɗan bayan na karanta saƙon da ta turomin sai kuma na sake ganin wani message ɗin ya shigo.
Cewa tayi "dan Allah idan har uwarka ta haifeka da jini kuma ba'a kwararo a haifeka ba to kazo inda nake domin kamaimaita maganar da kayimin wallahi na tabbata da sai ka gwammaci mutuwa a game da abun da zan aikatama nan take ta turomin da full address ɗinta, koda na kalli agogon dake saman wayata sai naga ƙarfe
1:20am nan take na rufe datar dake wayata na fita free.

Bayan nayi alwalla sai na tafi masallaci domin yin sallar azahar.
Koda na dawo daga masallaci sai na shiga wanka sannan na dawo falo na zauna, jim kaɗan bayan naci abinci sai na fita wajan aikina.

Washe gari da safe bayan nayi breakfast sai na tari mota zuwa garin jos wato garin da haneefa take da zama kenan.

Tabbas babu ƙarya a game da address ɗin da haneefa ta bani.
Da isata dai-dai gidan su haneefa sai naga wasu yara suna wasa da wata ƙaramar kwallo a kofar gidan

Ganin haka ne yasa na tsaya domin tunanin hanyar da zanbi wajan ganin na shiga rayuwar waɗan nan yaran wanda hakan zai kaini ga cimma nasarar haɗuwa da haneefa.

Koda babban cikinsu yaga na tsaya ina kallonsu sai yace "ko kaima zakayi wasan ne?

Jin haka ne yasa na ɗanyi dariya haɗe da cewa "to ku bugomin domin nima ina son wasan motsa jiki.

Bayan mun ɗan taɓa wasa tare sai na shiga wani shagon dake kusa da gidan.

Haka na sai musu sweets haɗe da biscuits sannan na tambayi sunayensu ɗaya bayan ɗaya.
Bayan na koma ƙofar gidan su haneefa tare da yaran sai na kallesu cikin yanayin sakin fuska haɗe da cewa "to nifa ƙishin ruwa nakeji dan haka yaran da yake nan gidan ya shiga domin ya kawomin ruwan da zansha, sai usman ya shiga da sauri haɗe da cewa bari naje na kawoma, ta wannan hanyar ne na gane cewar Usman ƙanin haneefa ne.

Bayan Usman ya kawomin ruwa nasha sai na kalleshi haɗe da cewa "usman ina yayarka take?

Buɗar bakinshi sai yace "wace yayar tawa?

Koda naji yamin wannan tambayar sai naji ƙirjina ya buga wanda hakan yasa nayi shiru a zuciyata nace "Allah yasa dai haneefa ba matar aure bace.

Koda na kalleshi sai nace "au yayyun naka har guda nawa ne?

Sai ɗaya daga cikinsu yace akwai ummey da kuma haneefa.
koda naji ya ambaci haneefa sai nace yauwa ɗan gari ai haneefa nake nufi.

Sai usman yai dariya haɗe da cewa ai bata gida yau tayi tafiya zuwa bauchi kuma ba yau zata dawo ba.

Koda naga yamma tana neman yimin a garin jos sai na samu biro da takarda a shagon da na sai masu Sweet na rubuta wasiƙa a.

Bayan na rubuta wasiƙar sai na kalli usman haɗe da cewa "usman idan na baka wanna wasiƙar domin kaba yayarka haneefa zaka bata?

Sai yayi dariya haɗe da cewa "wallahi zan bata nan take na damƙa wasiƙar a hannunshi sannan na ɗauki hanyar komawa gida kano.

=>2
Bayan kwana biyu da dawowata daga garin jos, kwatsam ina zaune a ɗaki da yamma sai na hau online jim kaɗan da hawana sai naga haneefa itama a online amma sai na fuske mata ba tare da nayi mata magana ba.

Bayan na ɗan taɓa chat da abokaina har nayi minimize na koma whatsapp sai naji ƙarar shigowar message daga facebook.

Dubawar da zanyi sai naga ai haneefa ce tamin magana na ɗauka zanga sallama a farkon kalaminta to ashe abun ba haka yakeba saboda tunaninta yasha banban da na sauran mutane, cewa tayi "naga saƙonka ya iso gareni kuma wallahi nayi danasanin rashin haɗuwa da kai domin da ace Allah ya haɗani da kai to na tabbata da sai kayi matuƙar mamakin ganin abun da aikata a gareka wawa kawai.

Koda na fuskanci haneefa tana da muguwar zuciya haɗe da rashin tunani a ƙwaƙwalwarta sai na aje wayar tawa a gefe na ɗauki ruwa a kofi na sha sannan na kwanta a gefen gadona ina nazarin hanyar da zan bulloma haneefa.

Zuwacan sai na tashi zaune fuskata cike da murmushi saboda nasan abun da na tsara a zuciyata zai yi matuƙar bani nasara a game da haneefa.

Koda na dauki wayata sai nayi mata replay cewa nayi " amma gaskiya haneefa kin bani mamaki yanzu ashe bazaki iya gane ɗan uwanki ba, to idan baki saniba ni ɗan uwanki ne wanda bazai taɓa bari a cutar dake a gaban idansa ba, amma bazan bayyana miki koni waye ba har sai nazo gareki dan haka ina mai baki shawara akan ki daina irin wannan posting ɗin da kikeyi na cin mutuncin murane a facebook saboda aikata hakan ba abu ne mai kyau ba.

Ina tura mata da saƙon cikin gaggawa tamin reply.

Tabbas tambayar da haneefa tamin ce ta bani tabbacin haƙona zai cimma ruwa.
Domin cewa tayi "dan Allah ka taimaka ka sanar dani ko kai waye?

Jin haka ne yasa nayi murmushi sannan na aika mata da reply kamar haka "a'a ki kwantar da hankalinki domin zan kawo miki kaina har gida, kuma na tabbata sai kinyi mamaki sosai sannan na sauka daga online.

Bani na sake hawa online ba sai bayan kwana biyu.

Ranar talata da sassafe ko karyawa banyi ba sai na hau online.

Haka nai ta zuba ido ko zanga haneefa amma ina bansamu damar haɗuwa da ita ba zuwa can da misalin ƙarfe 7:30pm ina hawa sai nayi arba da ita a online.

Zanyi mata magana kenan sai message ɗinta ya riga nawa isowa.

Sallama ce a farkon kalaminta sannan tace "dan uwana kwana biyu na rabuda ganinka a online?

Sai nayi murmushi haɗe da cewa "lafiya ƙalau wallahi kinsan harkokin ne sai a hankali, a wannan ranar dai sai da mu ɗauki dogon lokaci muna chating a ƙarshe da zata sauka sai ta buƙaci na bata numbata.

Koda na tura mata da numbar tawa sai tace "to ɗan uwana na gode daga yau bazaka sake ganina a online ba sai dai muriƙa gaisawa idan munyi waya.

Cikin yanayin mamaki nace "amma haneefa dan Allah ko zan iya sanin dalilin da yasa zaki dai na hawa online?

Sai tace "wallahi mahaifiyata ce tace muddun banason ganin ɓacin ranta to karna sake hawa facebook, kuma hakan ya faru ne a dalilin labarin da na bata a game da abun da ya faru a tsakanina da kai.

Cikin yanayin mamaki nace haba haneefa me yasa kiyi gaggawar sanar da ita?

Sai tace "wallahi nima banyi tunanin faruwar haka ba.

Sai nace "to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkairi.

Sai ta amsa da ameen, sannan tace "dan Allah yaushe zakazo wallahi na matsu na ganka a zahiri domin na nemi yafiyarka a game da irin wulaƙancin da nayima?

Koda na fahimci cewar tana neman ƙureni sai nayi shiru ina nazarin amsar da zan bata zuwa can sai nace da ita " haba haneefa ki kwantar da hankalinki domin na riga na ɗaukar miki alƙawarin zanzo, kuma wallahi babu batun wasa a tsakaninsa da ke.

Sai tayi murmushi haɗe da cewa "to shike nan Allah ya kawoka sai nace ameen yar uwata sannan ta sauka daga online.

Da saukar haneefa ko cikakken munti 1 ba ai ba sai naji kira ya shigo wayata.
Koda na amsa kiran a yayin da na kara wayar a kunnena sai naji sautin wata daddaɗar murya ta sauka a kunnena.

Cikin yanayin sakin fuska na amsa sallame da tamin haɗe da cewa "haneefa wannan itace numbar taki.

Cikin yanayin mamaki tace "taya ai har ka gane nice na kiraka?

Buɗar bakina sai nace "ai hakan ba wani abun mamaki bane saboda ba yadda za'ai na iya mantawa da muryarki.

Bayan mun gaisa sai tace "dama na kiraka ne domin ku gaisa da umma.

Koda naji tayi batun mahaifiyarta nan take naji duk ilahirin hikima ya ɗauke wuta domin na tabbata a wannan lokacin dai ƙaryata ta ƙare.

Cikin yanayin mamaki nace " umma kuma?

=>3

Koda haneefa taji kamar na tsorata sai tace "me kuma ya faru ko dai bakason gaisawa da mahaifiyar tawa ne?

Cikin yanayin sanyin murya nace "dan Allah haneefa idan bazaki damuba inason nayi wata magana dake kafin ki haɗani da ita.

Sai tace "to shikenan inajinka.

Buɗar bakina sai nace "amma haneefa me yasa kikeson nayi magana da mahaifiyarki a dai-dai wannan lokacin?

Sai naji tayi murmushi sannan tace "zanbata kuyi magana ne a matsayinka na ɗan uwana tunda har yanzu kaƙi sanar dani ko kai waye.

Koda naji haka sai nace "dan Allah haneefa kiyi haƙuri a game da ƙaryar da nayi a gareki domin bansanki ba ban kuma taɓa ganin mahaifiyarki ba, kawai ni dai na ɗaukeki ne a matsayin ƴar uwata musulma wadda idan naga wani abun da zai cutar da ita to sai inda ƙarfina ya ƙare amma dan Allah kiyi haƙuri.

Na ɗauka haneefa zata hassala kamar yadda ta bayyana ɓacin ranta a baya amma sai naji tayi murmushi haɗe da cewa "khai ɗan uwa na, amma gaskiya ka iya tsari wallahi ban taɓa tunanin cewar zaka iya shiryamin wannan gadar zaran ba amma ba komai nagode kafin ta yanke wayar sai nace "to ai saiki haɗari da umman tamu domin mu gaisa ko?

Buɗar bakinta sai tace "nima da wasa nake domin a yanzu hakama ina gidan wata ƙawata.

Amma zuwa anjima zan sake kiranka.

Abu kamar wasa duk da cewar bamu taɓa ganin juna ba amma cikin ƙanƙanin lokaci sai muyi matuƙar shaƙuwa da juna.

Kwatsan rannan cikin dare da misalin ƙarfe 11:30pm ina a yayin da nake cikin bacci sai haneefa tayi calling.. ɗina a waya.

Haka na tashi cikin yanayin magagi bacci kafin na amsa kiran tuni kiran ya yanke.

Koda na duba naga haneefa ce a zuciyata sai nace "anya lafiya kuwa haneefa take kirani cikin dare saboda a iya tunanina bamu taɓa waya da junanku da daddare ba.

Ina cikin wannan tunanin sai naga kiranta ya sake shigowa a karo na biyu kenan.

Cikin gaggawa na amsa kiran, koda na kara wayar a kunnena sai naji tayi ajiyar zuciya cikin yanayin farinciki tace "ɗan uwana wallahi nakasa yin bacci saboda tunaninka.

Fuskata cike da mamaki nace "amma haneefa taya zaki kasa yin bacci a dalilina alhalin ko ganin juna bamu taɓa yi ba?

Cikin yanayin damuwa tace "amma karka manta ita zuciya basai taga abu ido da ido sannan take nuna damuwarta akan duk wani abun da yai mata ba, zuciya tana iya amincewa da abu musamman idan ta gamsu da labarinshi, haka zalika zuciya tana iya kamuwa da son abu musamman idan taji ƙamshinsa, sanan kuma zuciya tana iya kamuwa da ƙaunar abun da bata taɓa gani ba har taji tamkar ba wanda yafishi a faɗin duniya musamman idan taji daɗaɗan kalamanshi kamar yadda nima zuciyata ta aminta da soyayyarka ta hanyar jin daɗaɗan kalamanka.
Dan Allah ka karɓi soyayyata wallahi duk da cewar ban taɓa ganinka a zahiri ba amma wasu lokutan idan ina zaune ko ina tafiya ni kaɗai sai kariƙa yimin gizo, wannan itace rana ta farko dana taɓa bayyana soyayyata ga wani ɗa namiji.
Dan Allah karka ɓoyemin idan kaima kanasona tsakani da Allah to kasanar dani idan kuma babu tsarin soyayyata a shafin rayuwarka to kasanar dani domin nabi hanyar da ta dace wajan yage wannan soyayyar taka daga zuciyata domin karta zamemin ciwo.

Na buɗa baki zanyi magana kenan sai wayata tayi shutdown gashi an ɗauke wuta balle na ɗora chaji ba yadda na iya haka na aje wayar rai na a ɓace sannan na koma bacci, Allah sarki rashin sani yafi dare duhu domin ita a tunaninta yanke wayar nayi.

Haka dai a wannan daran tayi ta trying ɗin numbata yafi a ƙirga amma ina kota kira sai dai taji wayar a "switch up"  

Bayan gari ya waye ba ta haka ta sake kirana koda ta sake jin wayar a kashe nanfa ranta yai matuƙar ɓaci nan take ta cire layin daga wayar.

Ida nuwanta suna zubar da hawaye haka ta raba sim card ɗin gida biyu sannan ta watsashi a kwandon shara.
=>4
bayan gari ya ƙarasa wayewa da misalin ƙarfe 6:30 na safiya sai na ɗora cajin wayar tawa a motar mahaifina kafin ya fita wajan aiki.

Koda naga 7:00am tayi sai na kunna wayar kunna wayar kenan sai na shiga ɓangaran kira wato "call history" kenan cikin gaggawa na tura calling.. domin a numbar haneefa.

Koda na kara wayar a kunne sai naji wani turanci kamar haka "the number you trying to call is switch off.

Tabbas nima sai da rai na yai matuƙar ɓaci a dalilin rashin samun haneefa a waya.

Duk da cewar ban wani damu da ita a rai na ba amma a wannan ranar sai da na kirata yafi sau 10 amma shiru kakeji babu labari.

Abu kamar wasa har ayi kwana ukku duk lokacin da zan kira numbar haneefa sai dai naji "switch off.

Tun ina ƙoƙarin trying ɗin numbar har na gaji na daina a ƙalla an samu kimanin 5 months ba tare da na sake jin muryar haneefa ba, kuma ban sake ganinta a online ba wato facebook ko whatsapp kenan domin tun a baya ta sanar dani cewar mahaifiyarta ta hanata hawa social network.

Kwatsam wata rana sai invitation ɗin auran wani abokina mai suna ibrahim ya iso gareni wanda za'ayi a garin jos.

Koda naga sunan jos a jikin wannan invitation ɗin sai nayi matuƙar farin ciki domin na tabbata duk yadda za 'ayi sai na kaima haneefa ziyara.

Ranar litinin da misalin ƙarfe 8:00am nayi wanka haka na gama shirina tsaf sannan na tasarma wajan haɗuwa domin tafiya ɗaurin auren.

Da zuwana sai na samu yan uwa da abokan arzuƙi duk an haɗu ni kawai ake jira.

Bayan mun gama haɗuwa sai mu ɗauki hanyar jos tun a hanya nake zumuɗin haɗuwa da haneefa.

Haka nayi shiru a zuciyata ba abun da nake tunani illah tunanin yadda haɗuwata da haneefa zata kasance.

Koda Abdul ya kalleni yaga nayi shiru alamun na afka kogin tunani kenan.

Buɗar bakin Abdul sai yace "haba abokina tunanin me kake haka? To idanma tunanin aure kakeyi tun wuri gwara ka dai na domin kaima kwanan nan zamu sha naka bikin.

Koda na ɗago kai na kalleshi sai nayi dariya haɗe da cewa "to Allah yasa haka abokina.

A haka dai muna tafiya muna labari har Allah ya kaimu garin jos lafiya cikin kwanciyar hankali.

Bayan an ɗaura auren Ibrasim da Humaira sai na samu abokan tafiyar tawa nace dasu "to nifa sai dai ince Allah ya saukeku lafiya domin ni ba yanzu zan koma gida ba.

Koda isma'il ya fuskanci eh lallai da gaske nake cikin sauri ya fito daga motar haɗe da cewa "haba abokina ai bazai yiwu a matsayinka na abokinmu muzo garin jos tun daga kano kuma mu tafi mu barka ba, dan haka idan har uzurin da kake dashi mai muhimmanci ne to zamu iya jiranka koda kuwa zaka ɗauki tsawon awa biyu ne.

Jin haka ne yasa nayi dariya haɗe da cewa "haba abokina ai bazan ma ɗauki wani dogon lokaci ba zan dawo domin mu tafi.

Nan take na tsaida wani dan acaɓa, tun a hanya zuciyata take cewa "to waikai in banda abunka idan kuma kaje kaga haneefa batayima ba to yazakayi kenan?

Sai a zuciyar tawa na roƙi mahaliccinmu nace "Allah kasa dai haneefa kyakkya ce.

A haka dai muna tafiya ina nazari, har na ƙuduri niyar dakatar da wannan dan acaɓan domin ya juya dani amma sai na fasa da isarmu ƙofar gidan bayan na sallami ɗan acaɓan sai na tsaya a bakin gate ɗin gidan ina tunanin yadda zanyi domin na samu haɗuwa da haneefa ina cikin wannan nazarin sai naji ƙarar horn ɗin mota.

Koda naji sautin wannan horn ɗin sai na koma gefe na zuba ido kamar wani ɗan maula.

Zuwa can sai naga wata tsaleliyar baƙar mota ta fito daga gidan.

Nan take naji ƙirjina ya buga domin nasan duk yadda ayi mahifin haneefa ba ƙaramin mai kuɗi bane.

Ganin haka ne yasa gaba ɗaya naji zuciyata ta sare domin nasan soyayya a tsakani na da haneefa a matsayinta na ƴar manya bazata taɓa yiwuwa ba.

A yayin da motar tazo daf dani sai naga an zuge glass tabbas al'amarin yayi matuƙar bani mamaki sakamakon ganin wadda take tuƙa motar da nayi domin mace na gani a motar.

Cikin yanayin yanga mai tattare da ƙasaita naga ta cire gilar ɗin dake fuskarta sannan tamin wani kallan rainin wayo wato irin wanda akema laƙabi da kallan hadarin kaji. 

Buɗar bakinta sai tace malan lafiya kuwa naganka tsaye anan ƙofar gidan? 

Cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba nace lafiya ƙalau nazo wajan haneefa ne.

=>5

Koda haneefa taji na ambaci sunanta cikin hanzari ta ɗago kai ta kalleni fuskarta cike da mamaki haɗe da cewa "what! meye kuma haɗina da kai?

Koda na fahimci cewar itace haneefa na buɗa baki zanyi magana kenan sai ta dakatar dani haɗe da cewa "kaga malan bana buƙatar jin komai daga bakinka idan maula kazo to kashiga ciki abba yana nan saika faɗa mai duk abun da kake da buƙata domin ya taimakama sannan ta zuge glass taja motarta tayi gaba.

A zahirin gaskiya tun da nake a rayuwata ban taɓa haɗuwa da cin mutuncin da ya ƙonamin rai kamar wanda haneefa tayi a gareni ba, to amma duk da irin wulaƙancin da haneefa tayi a garemi baisa nayi ƙasa a guiwa ba sai na samu takadda da biro a wannan shagon da ke kusa da gidan nasu na rubuta mata wasiƙa kamar haka
====>"Assalamu Alaiki.
haneefa nasan zakiyi mamakin ganin wannan saƙon nawa a gareki.
Azahirin gaskiya kinyi min wulaƙancin da har ƙarshen rayuwata bazan taɓa mantawa dashi ba, ko da yake wannan ba abun mamaki ba ne saboda tun a baya kinsha alwashin sai kin aikata min abun da zanyi mamaki sai gashi cikin ƙankanin lokaci kin cika burinki kuma na godema Allah da yasa zuciyata batayi gaggawar kamuwa da matsanancin sonki ba.
Dan haka na godema Allah da wayata ta ɗauke alokacin daki kira wayata cikin dare domin bayyana soyayyarki a gareni wallahi da ace bakina yayi gaggawar amincewa da soyayyar ki da sai nayi babban da na sani a rayuwata kuma ina mai shawartarki da kiyi gaggawar canza wannan mummunar halayyar taki ta wulaƙanta mutane domin wannan kyawun fuskar taki da kike taƙama da ita ba kowa ne ya baki ita ba face mahaliccinmu domin na tabbata idan mutuwa batazo cikin gaggawa ba to tsufa zai zo gareki idan kuma tarin dukiya kike taƙama da ita to Allah zai iya janye kayarshi saboda bada ita kizo duniya ba.
kuma inamai tabbatar miki cewar daga yau nanisanta zuciyata dake na tsawon har abada.
Bayan na kammala rubutawa wasiƙar ɗago kan da zanyi sai nayi ido biyu da ɗaya daga cikin yaran da na taɓa haɗuwa dasu tun a wancan zuwan da nayi.
duk da cewa rai na a ɓace yake cikin yanayin sakin fuska na kalleshi haɗe da cewa "ina usman? wato ƙanin haneefa kenan.
Buɗar bakin yaron sai yace bansan inda yayi ba amma bari na shiga gidan nasu idan yana nan sai na kiramashi.
Sai nace "a'a basaika kirashi ba nan take na damƙa wasiƙar a hannunshi haɗe da cewa "dan Allah idan kun haɗu ka bashi wannan wasiƙar kace yaba haneefa sannan na bashi naira 100 nace ya ɗauki #50 yaba usman #50. 

Bayan na koma wajan abokan tafiyata sai nayi musu godiya a sakamakon jirana da suyi amma ban bari sun gane ɓacin ran da yake zuciyata ba.

Bayan haneefa ta dawo gida sai saƙona ya isa gareta koda ta karanta duk abun da na rubuta a takaddar.
Saboda da ɓacin ran abun da ta aikata a gareni nan take hawayen baƙin ciki ya zuba daga idanunta.

A dalilin haka ne haneefa ta karya umarnin da mahaifiyarta ta bata a game da daina hawa social network.

Cikin gaggawa haneefa ta ɗakko wayarta ta hau online wato facebook kenan domin shine silar haɗuwarmu.

Koda haneefa tayi iya dubanta bata sameni a jerin friends ɗin taba sai tayi ƙoƙarin searching ɗina amma Allah bai bata ikon ganina ba domin tuni nayi deactivated ɗin account ɗin nawa.
Haka dai ta ƙaraci nemanta batare da ta samu ganina ba sai ta kwanta a gado tana kuka haɗe da cewa "dan Allah karka gujeni wallahi bansan kai bane akanka na daina kula duk wasu samari saboda ako da yaushe inasaran zaka dawo gareni tabbas yanzu nasan na aikata kuskure dana karya layina gashi na rasa numbarka kuma kazo gareni na wulaƙanta ka yanzu shikenan na rasaka rasawa ta har abada wallahi da nasan inda kake da sai nazo gareka koda kuwa hakan zai jawo sanadin rasa rayuwata na.

Koda mahaifiyar haneefa taji sautin kukanta kai tsaye ta shiga ɗakin hankalinta a tashe buɗar bakint mahaifiyar haneefa sai tace "haneefa lafiya kuwa, menene yake damunki?

Cikin sauri haneefa ta tashi zaune tana share hawayen dake fuskartar.
koda ta hada ido da mahaifiyarta sai ta sunkuyar da kanta ƙasa ba tare da tace komai ba.

Ganin haka ne yasa mahaifiyar tata ta matso kusa da ita haɗe da cewa "maganafa nake miki amma kinyi shiru banji kin bani amsaba.

Buɗar bakin haneefa sai tace "ba abun da yake damuna.

Nan take mahaifiyar tata tace to miƙomin wayar dake hannunki.

Jin haka ne yasa haneefa ta kalli mahaifiyarta a tsorace, ba yadda ta iya haka ta miƙawa mahaifiyarta wayar.

Dubawar da mahaifiyar tata zatayi sai taga ai akan facebook take.

Ganin haka ne yasa ta kalleta haɗe da cewa "wato facebook ne yasaki kuka ko ta bari abban naki ya dawo.

A taƙaice dai tun daga wannan ranar gaba ɗaya sai mahaifin haneefa ya hanata riƙe waya.
Kimanin wata ukku kenan rabona da garin jos.

Mahaifina yasha aikena wurare da dama a game da harkokin kasuwancinshi amma bai taɓa aikena garin jos ba.

Kwatsam wata rana da misalin ƙarfe 3:00pm lokacin bana gida ina tare da abokai na sai mahaifina ya kirani a waya.

Koda naje gareshi sai ya sanar dani cewar garin jos zai aikeni.

Koda naji ya ambaci Jos sai naji ƙirjina ya buga saboda ko kaɗan banason na sake taka ƙafata a garin jos amma ba yadda na iya.
Haka mahaifin nawa ya ɗakko wasu takaddu ya bani sannan ya bani key ɗin motarshi haɗe da wasu yan kuɗaɗan da zansa a aljihuna domin guzuri sannan yayimin bayanin wanda zankaima waɗan nan takaddun.

Haka dai na tafi jos kuma sai Allah ya taimakeni na isa jos da wuri.
Da zuwa na bayan na isar da saƙon da mahaifin nawa ya bani, sai wanda na kaima sauƙin ya kalleni yai murmushi haɗe da cewa abban naka yana lafiya dai ko?
Buɗar bakina sai nace yana nan lafiya ƙalau kuma yana gaisheka.

Bayan mungaisa sai yace to ai sai muwuce gida domin kaci abinci ka huta domin yau kwanan jos zakayi.

Sai na ɗan yi dariya haɗe da cewa "aini yau nakeson komawa gida.

Koda ya kalleni sai yace "ai wannan maganar ba mai yiwuwa ba ce domin kai tamkar ɗa kake a gareni dan haka ba yadda za'ai nabari ka koma gida tunda yamma tayi ba yadda na iya haka ya jani zuwa gidanshi.

Tabbas nayi matuƙar mamaki sakamakon ganin hanyar da yabi wanda hakan yasa a rai na naji cewar ba makawa sai na sake haɗawa da haneefa, domin hanyar gidan su haneefa naga mun tunkara.

Da isarmu ƙofar gidan su haneefa sai naga ya danna horn ganin haka ne yasa na zuba ido domin kallan ikon Allah.

Koda naga an buɗe Gate sai na saki baki fuskata cike da mamaki yana shiga sai nima nabi bayanshi.

Fitowata daga mota kenan sai na kalli alhajin fuskata cike da mamaki.
Buɗar bakina sai nace alhaji dama nan ne gidanka? 

Bai kaiga bani amsaba sai haneefa ta fito daga falo da sauri fuskarta cike da fara'a domin tarbar mahaifinta.

Koda haneefa tayi arba dani a Compound ɗin gidansu sai taci burki ta tsaya.
A wannan lokacin ne mu fara yima junanmu kallan kallo fuskokinsu cike da mamaki.

Nan take ta nunani da yatsanta haɗe da cewa "ashe dama akwai ranar da zaka sake dawo gareni?

Koda naji wannan furucin daga bakinta sai kai na ya ɗaure domin ko kaɗan banason mahaifinta yasan halin da muke ciki.

Ganin haka ne yasa mahaifin haneefa ya kalleni sannan ya kalli haneefa haɗe da cewa kinsanshi ne?

=>6

Koda haneefa ta kalleni sai ta kalli mahaifinata haɗe da cewa "abba nasanshi mana amma a facebook mu haɗu.

Buɗar bakin mahaifinta sai yace ikon Allah kenan gashi kin haɗu da yayanki a facebook domin shi tamkar yaya ne a gareki.

Cikin yanayin mamaki haneefa tace "abba ban gane me kake nufi ba?

Sai mahaifinta ya kalleni haɗe da cewa "shigo ciki nayi muku bayanin komai domin na tabbata mahaifinka bai sanar da kai abun da yake a tsakanina dashi ba.

Da shigarmu falon gidan sai haneefa ta kawomin abinci haɗe da rinks mai sanyi ta aje a gabana.

Bayan naci abinci nasha ruwa muna zaune a falo sai mahaifin haneefa ya kalleni sannan ya kalli haneefa haɗe da cewa "a zahirin gaskiya mahaifin wannan bawan Allan yayi matuƙar taimakamin domin yamin abun da har ƙarshen rayuwata bazan iya sakamai da kwatan-kwacinsa ba, dan haka bani da abun da zan iya furtawa mahaifin wannan bawan Allan face godiya domin duk wannan dukiyar da kike gani a gareni to ba tawa bace ta mahaifin wannan da kike gani ce.
Saboda ya ɗaukeni tamkar ɗan uwansa na jini tun muna yan ƙanana muke tare har Allah ya bashi dukiya mai ɗinbin yawa wadda shi kanshi ba zai iya cewa ga iyakarta ba.
To amma duk da irin wannan kuɗin da yake dasu baisa ya gujeni ba.

Haka ya damƙa ragamar dukiyarshi gaba ɗayanta a hannuna domin kaso 80 cikin 100 yana hannuna, saboda sauran danginshi basa raye sai wani guda ɗaya mai suna malan Abubakar wanda yake zaune a jahar taraba shi kuma ko kaɗan baya ƙaunar mahaifinka a raye badan komai ba sai dan buƙatar ya mallaki dukiyar da mahaifinka ya tara.

Haka ne yasa mahaifinka bashi da wani mai bashi shawara a game da harkokin rayuwarshi fiye da ni.

Wanna ne dalilin da yasa ya rikeni da muhimmanci kuma ya damƙa dukiyar da ya mallaka a hannuna badan komai ba sai dan yaddar da yayi dani a matsayinshi na abokina.

Kuma wani babban abun da yake bani mamaki a tsakanina da mahaifinka shine ko kaɗan bai damu da wannan dukiyar tashi ba.
Kuma yace karna kuskura na bari kowa yasan wannan sirrin da yake a tsakani na dashi domin hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kaga ko gidanku ban cika zuwa ba.
Dan haka na sanar da kai wannan maganar ne saboda nasan duk juyi kai ne magajin wannan dukiyar.
Kuma dan Allah karku bari wani yasan da wannan maganar. 

Tabbas ni kaina nayi matuƙar mamakin jin wannan labarin daga bakin mahaifin haneefa, koda na hada ido da haneefa sai tayi ƙas da kanta ba tare da tace komai a gareni ba.

Bayan gari ya waye a yayin da na kammala shirina na komawa gida sai haneefa tazo har gabana.
Haka ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa "dan Allah yayana kayi haƙuri a bisa kuskuren dana aikata a gareka domin nasan nayi kuskure.

Sai na ɗan yi murmushi haɗe da cewa "haba haneefa ai komai ya wuce, kuma dama kinsan ɗan adam ajizi ne ba wanda ya wuce aikata kuskure.

Har na juya zan fita sai ta dakatar ta hanyar cewa "yanzu shikenan tafiya zakayi?
Koda na juyo fuskata zuwa gareta cikin yanayin damuwa tace "dan Allah yayana zaka aureni?

Tabbas a wannan lokacin ba kaɗan naji daɗin wannan furucin da haneefa tayi a gareni ba, amma da yake ɗan adam ba'a rasashi da jan aji nan take na kalleta haɗe da cewa "gaskiya haneefa kiyi haƙuri domin wata ta rigaki mallakar zuciyata sannan nayi waje.

Bansani ba ashe wannan furucin nawa ya ƙara jefa rayuwar haneefa ne a cikin wani mummunan yanayi domin a wannan ranar har na dawo gida kano haneefa bata samu damar cin komai ba badan komai ba sai dan bacin ran maganar da na sanar da ita alhalin ni kuma da wasa nake mata.

Sannu a hankali har hanifa ta kamu da ciwon zuciya mai tsanani kuma gashi taƙi sanar da kowa dalilin da ya haifar mata da wannan rashin lafiyar.

Kwatsam wata ranar asabar da safe lokacin bana gida sai labarin rahin lafiyar haneefa ya isa kunnan mahaifina wanda hakan yasa a ranar da labarin ya isa kunnan mahaifin nawa ya tafi garin Jos domin ganin halin da haneefa take ciki.

Bayan mahaifina ya isa asibitin da a kwantar da haneefa koda haneefa tayi ido biyu da mahaifina sai ta riƙe hannunshi tana kuka haɗe da cewa "abba wallahi idan ban aureshi ba mutuwa zanyi.

Nanfa haneefa ta jefa mahaifina haɗe da iyayenta a ruɗani.

Jin haka ne yasa nan take hawaye ya zubo daga idanun mahaifina cikin yanayin tausayawa yace da haneefa "waye wanda yai sular jefaki a wannan yanayin, ki daure ki sanar damu domin musan hanyar da zamubi wajan ganin ya zama mallakinki.

Nan take ta fashe da kuka haɗe da cewa abba, yaya yaya Umar nakeso kuma yaƙi amincewa dani a matsayin wadda zai aura.

Koda mahaifina yaji abun da haneefa ta faɗa nan take ranshi yai atuƙar ɓaci.

Haka mahaifina ya kalli haneefa haɗe da cewa haba haneefa meyasa kiƙi gaggawar sanar damu? ai da tuni ankawo ƙarshen wannan matsalar.

Nan take mahaifina ya ɗakko waya domin kirana.

A wannan lokacin dai ba yadda za'ai kowa ya sameni a waya domin muna hannun da fitarmu sai yadda Allah yaso.
Nabar gida tun misalin ƙarfe 7:00 na safiya ni da wani abokina mai suna muktar domin zuwa garin kaduna.
Rashin Sani ne yasa mu tare motar ƴan mafiya wato yan yankan kai kenan.

Muktar ne ya ɗagawa motar hannu wanda hakan yasa kotar tayi burki a kusa damu.

Cikin yanayin ƙasaita haɗe da ɗagawa mushiga motar.

Ni dai nasan lokacin dana zauna amma bansan lokacin dana tsunci kaina kwance a wani ɗaki ba.

Koda na waiga bayana sai naga muktar kwance baimasan a halin da yake ciki ba.

Bayan wasu ƴan mintina sai Muktar ya tashi a gigice.

Koda shima ya tsunci kanshi a wannan ɗakin sai ya kalleni fuskarshi cike da mamaki haɗe da cewa "abokina me kuma ya kawomu nan gidan?

Yanayin tsoran da na gani a fuskar muktar ne ya bani dariya, buɗar bakina sai nace "abokina yaufa wayanmu da iliminmu bai amfanemu da komai ba domin a hannun miyagun mutane muke.

Ganin yadda muktar yai matuƙar tsorata ne yasa na dafa kafaɗarshi haɗe da cewa "kar ka damu duk tsanani yana tare da sauƙi musamman idan a miƙa komai ga ubangiji.

Haka a garƙamemu a wannan gidan har dare yayi ba wanda ya waiwayemu ga yunwa haɗe da ƙishin ruwa.

=>7

aƙalla munkai kimanin kwana huɗu a tsare gashi bama samun wadataccen abinci batun kwanciyar hankali kuma babu.

Koda muga abun yaci tura sai mu shirya hanyar da zamubi domin ceton rayuwarmu.

Haka Allah ya bamu sa'a cikin dare dai-dai lokacin da mai gadinmu ya kawo mana abinci sai muyi mai dukan kawo wuƙa sannan muyi waje gashi Allah ya taimakemu mun fito daga ɗakin da'a tsaremu amma sai katangar gidan ta gagaremu haurawa nanfa munufi bakin gate da gudu da isarmu sai mu taradda kofar gate a garƙame da kwaɗo.

Ganin haka ne yasa gaba ɗaya hankalinmu yai matuƙar tashi sai muktar ya kalleni yace abokina ba yadda zamuyi dole sai dai muyi ƙoƙarin haurawa ta katanga haka kuwa ayi da kyar mu iya haurawa koda naga mun isa garin kano sai muyi matuƙar jin daɗi.

Da isata gida ko falo ban shiga ba sai abbana ya dakatar dani cikin yanayin ɓacin rai ya kalleni haɗe da cewa "me kuma ya dawo da kai nan gidan, yanzu ashe har kanada ƴancin da zaka jefa yargidan aminina a mawuyacin hali sannan ka gudu ka bar gida ba tare daka sanar damu ba?
To bari kaji wallahi muddun ina raye to ba abun da zai hana ka aureta

Jin haka ne yasa naba mahaifina haƙuri sannan na sanar dashi cewar "nima inasonta kuma ban bar gida a dalilin soyayyar da take tsakanina da haneefa ba.

Bayan mun shiga falo sai nayimai bayanin duk abun da ya faru a tsakanina da haneefa tun daga lokacin dana haɗu da ita a facebook har izuwa tsaremu ɗin da yan mafiya suyi a garin kaduna.

Koda iyayena suji wannan bayanin daga bakina sai ɓacin ran da ke zuciyarsu ya ragu.

Tabbas alokacin da naje wajan haneefa nayi mamakin ganin yadda ta rame a wannan lokacin ne na tabbatar da soyayya ba ƙaramar makauniya bace.

Haka na sameta kwance a falo ga kuma mahaifiyarta zaune a kusa da ita, a dai-dai wannan lokacin sai naji kunya ta kamani.

Haka dai na gaishe da iyayan haneefa cikin yanayin kunya haɗe da basu haƙuri a game da abun da ya faru a tsakanina da haneefa.
Sannan na sanar dasu cewar ko kaɗan bani da niyar jefa rayuwar haneefa a mawuyacin hali domin nima ina sonta.

Koda haneefa taji wannan furucin daga bakina sai ta tashi zaune tamin wani kallo mai dauke da mamaki tace "haba dan Allah yanzu kanason nawa zaka bar gida na tsawan wasu kwanaki sannan kanasona zaka.... 

Nan take na dakatar da ita ta hanyar cewa "kinga dakata ai komai ya wuce dan haka nazo ne domin ki sanar dani yaushe ne bikin namu?
Sai tayi murmushi haɗe da rufe fuskartar da hannayenta.

Alhamdullah.
The End.

Rubutu Daya Gabata
Rubutu Na Gaba

Mawallafi:

0 comments: